Tabarmar Ƙashi page 12 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 12 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 12 by H U G U M A

*H U G U M A*

_*TABARMAR ƘASHI*_💔

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma

Page 12

          Tunda yaa zaid ya sauketa a jiyan abun yaqi barin ranta,kusan zata iya cewa dashi ta kwana,wanda ya haifar mata da wani irin bacci mara dadi,da mafarkai barkatai wadanda suka shafi wasu al'amura dake da alaqa da rayuwarta. Cikin dare ciwon kai ya saukar mata,wannan ya sabbaba mata makara a sallar asuba,kuma ko bayan tayi sallar wani baccin ya sake daukarta,sam ta mance da batun fara zuwa aikinta a yau,wanda dama zataje ne kawai don ta fara karantar yanayin yadda abubuwan suke.


          Kwata kwata bata tashi farkawa ba sai qarfe goma na safe,ta tashi da sauqin ciwon kan,ta miqe daga gadon tana shirin shiga toilet akayi knocking qofarta.


            Maama ce ta shigo,cikin kamalar nan tata wadda kusan a nan da wajen abba sãahar din ta gadota


"Kina lafiya kuwa?" Tayi mata tambayar tana kallon qwayar idanunta tare da fatan ba damuwarta ce ta sake motsawa ba


"Ina kwana maama" ta maida mata da gaisuwa


"Lafiya qalau,kin tashi lafiya?"


"Alhamdulillah,na dan tashi da ciwon kaine,bayan asuba kuma saina samu bacci"


"Subhanallah,Allah ya sawwaqe,ko zaki asibiti?,banason zama da ciwo" ta fada cikin damuwa,saboda tasan yanayin ciwon kan sãahar din,baya yi mata da sauqi idan ya tashi,saboda ciwo ne da ya samo asali ta Wani dalili,ba hakanan ta sameshi ba


"Alhamdulillah naji sauqi yanzu,wanka kawai zanyi na sauko"


"To alhmdlh,yayanki ne ya dameni da waya tun dazu,yace yana kiran wayarki bata shiga ba"


"Ya muhyi" ta fada kai tsaye,tasan yanason jin ta fita aikinne ko kuwa


"Zan kirashi idan na fito a wanka"


"To madalla,yayi" saita juya tana shirin fita


"Abbanku ya fita,amma shima ya tambaya kafin ya fita din"


"Zan kirashi shima" ta sake fada tana yunqurin zare rigar baccin jikinta


"Don Allah maama,baba rabi ta kawomin ruwan dumi a cup"


"Shikenan" ta amsa tana qarasa fita a dakin.


              Da ruwa me dumi sosai tayi wankan nata,ta fito fatarta na wani irin sulbi da qamshi daya hade da tururin ruwan dumin da tayi wankan,ta fito ta tsaya gaban mudubi tana kallon fuskarta dake subul kamar ta jariri,babu tabo babu komai,sai tsananin taushi da sulbi da take sakeyi,alamun product din da take amfani dashi ya karbeta. Tasa hannu ta dauki mug din ruwan dumin da baaba rabi ta kawo mata ta aje ta soma kurba a hankali,saboda muhimmancinsa a jiki bata skipping shansa kowacce safiya kafin taci komai,koda kuwa ta makara bata tashi da wuri ba.


             Da wani irin sauri sautin marin jiya ya gilma a kunnenta,ta runtse idanu kamar a sannan abun ya faru,ta cire cup din da takai bakinta a hankali ta ajjiye saman madubin sannan ta bude idanunta tarwai tana kallon fuskarta. Tsantsar rashin sanin darajar dan adam ta tabbata ga duk mutumin da zai iya shimfida yatsunsa akan muhallin da yafi ko ina daraja a jikin dan adam,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,ta saka hannuwanta biyu saman kuncinta,tana tuna wani lokaci can baya daya wuce,tana tuna marukan da tasha saman fuskarta,wanda batasan iya adadinsu ba.


           Sauke hannuwanta tayi taja da baya tana barin gaban madubin ganin bacin ran da bataso tana yawan ji yana qoqarin taso mata,sai ta koma gefan gadonta ta zauna tana hadiyeshi,idanunta suka sauka kan ledar siyayyarta data shigo da ita jiya,ta miqa hannu ta janyota,ta fara buda kayan ciki tana sake dubawa,bawai don batasan me ta siya din ba,a'ah tanason kore bacin ran dake taso mata ne. 


          Sai data shirya kayan cikin walking closet dinta sannan ta fara gyara jikinta,ta shirya kanta cikin wata sassauqar gown fara,alamu suna nuna ita din ma'abociyar son fararen abubuwa ne,musamman kayan zaman gida da qananun abubuwan amfani irin haka. Cikin qasa da awa daya ta sauko qasan riqe da system dinta tana amsa wayar afifa,ta saka system din a chargy,ta leqa ta gayawa maama ta fito wadda ke saman abun sallah zata tayar da salatud duha(sallar walaha),sannan ta nufa kitchen ta samo abinda zata iya ci.


            "Barka da fitowa" baba rabi ta fada cikin girmamawa,tadan murmusa kadan,baba rabin ba zata taba daina gaisheta ba


"Ina kwana?"


"Kin tashi lafiya farar d'iya" suna ne da takan kirata dashi lokaci lokaci


"Lafiya qalau,me zan samu?" Fara bude mata abubuwan da suke dashi da safen a kitchen tayi,kusan duka ba cimarta bane,amma batason bawa kowa aiki da safen nan,ita kuma qyuyar aikin yau takeji,don haka sai ta jawo plate ta tsakuri iya abinda take ganin zata iya a plate daya,ta fice zuwa Parlor din.


           Tana cin abincin kamar wasan yara ta kunna laptop din nata,gidan gaba daya ya mata shuru ba dadi,afifa bata dawo ba kwata kwata wannan satin,shi yasa takeson yara,bata rabo da dauko 'ya'yan yayyen nata,to wannan karon su fadil suna umra duka gidan,khalifa na exam,aleena tayi qanqanta don ko yayeta ba'ayi ba,ya zaid kuma ya maidasu na'eem canada,cikin satin nan shima zai bisu,dole ta zauna zaman kadaici,idan taji ta matsu da yawa kuma tabi afifa.


              Sai data gama duk uzurinta sannan ta shiga ma'ajiyar saqonnin email dinta da nufin share saqonnin da suke kai ko zata ragewa computer din nauyi,har ta fara marking idanunta suka kai kan sabon saqon daya shigo mata daga MT GLOBAL COMPANY,ta dan tsaya tana tunanin inda tasan sunan,kafin daga baya hankalinta yakai kai,takai arrow din kai tayi clicking ta shiga.


          Dogon tsaki taja bayan ta gama karanta abinda saqon ya qunsa,and so what don zasu canzata da wata muddin bata shiga aiki ba on Monday,ko an gaya musu aiki da su damuwarta ne?,ko basusan alfarma zatayi musu ba saboda darajar masu daraja?,cikin jin haushi ta soma rubuta musu reply na basu damar sanya watan,cikin ranta tana jin ta samu hanya mafi sauqi ma da zata sabule wannan alaqaqai din aikin,saidai tana kammala rubutawa kafin ta tura taji muryar yaa muhyi yana magana da masu aikin gidan dake harabar gidan,saita dora hannuwanta saman fuskarta tana jin ba dadi,a sanyaye tayi highlight na duka rubutu tayi cutting dinsa,ta goge email din ta sauka daga ciki,tayi shutting down na system din,dai dai lokacin ya sanyo kansa cikin parlor din.


           A nutse ta amsa sallamarsa,tayi masa barka da safiya sannan ta miqe ta yiwa maama magana,ta kuma wuce kitchen ta hado masa dan abin motsa baki,ta kawo ta ajjiye masa


"Ya na ganki gida,nayita kiran wayarki kuma bakiyi picking ba,kada dai ace tun ranarki ta farko kin fada wasa da aikinki?" Yaa muhyi ya fada yana kallonta hadi da dan kada key din hannunsa.


          Fuskarta ta tattare tayi alamun tausayi ta zauna daga kujerar dake gefansa


"Da ciwon kai na tashi yaa,kuma ma Allah......" Kasa qarasa masa tayi,tadan lanqwasa yatsun hannunsa


"Eheenn,Allah me?" Ya tambayeta kai tsaye yana dubanta bayan yadan tsuke fuskarsa kadan,don bayason jin wani zance sabanin wanda sukayi da ita


"Yaa ko zaka taimakamin su sauyamin position din da suka bani,bana son president din nan wallahi" ta qarashe fada tana narke murya. Ajiyar zuciya yadan sauke yana furzar da iska daga bakinsa sannan ya sake maida dubansa kanta


"Dr yana da matuqar kirki da sanin ya kamata,haka d'an nasa,yana da kamewa da sanin ya kamata,na tabbatar ba zaki taba fuskantar wata matsala wajen yin aiki dasu ba,inda nasan akwai matsalar kema kin sani,bazan karba miki ba,so please accept it,kiyi aiki tuquru,ko don saboda ni" qas tayi da kanta,tanason tilastawa zuciyarta da har yanzu taqi jin nutsuwa aminci wa aikin kan ta karba buqatar dan uwanta,sake gyara zamansa yayi sannan yace


"Shi da kansa Dr yin ya zaba miki position din,ya fimu shekaru da hangen nesa,yana ganin kin cancanta ne,ko abba dana gaya masa baice wani abu ba,kuma koni din nasan you can do it,so please kada kiyi discouraging kanki,you will made it in sha Allah" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya qasan ranta,bai fahimceta bane,bawai ba zata iya bane,ita sam harkar da duk zai hadata mu'alama da jama'a ne bataso. Ganin ta shiga tunani sau ya katse tunanin nata ta hanyar miqa mata key din mota


"Gashi,gift na fara zuwa aiki,daga ni da kuma Saifullahi" hannu biyu tasa ta karba tana masa godiya,saidai sanda ta duba sunan motar sai da zuciyarta ta tsinke,motace sabuwar qira me kyau ta mata,tana kuma da dan tsada,lallai da gaske sukeso sai tayi aikin nan,zatayi addu'a ta kuma roqi Allah ya dafa mata,kada ya bata ikon watsa musu qasa a ido.


***********Duk daga inda ka daga kanka cikin layin,daga farko ne qarshe gaba ko baya na layin kana iya hangen katafaren ginin mansion house din daya amsa sunansa ta kowacce fuska a idanun me kallo,saidai daga ainihin cikin zuciyar gidan akwai naqasu me tarin yawa a ciki,birnannen tarihi da memories masu daci tsananin quna da soya zukata,memories da suka dakushe jin dadi da walwala mafi rinjaye ta dukka mutumin daya shafi gidan,gefe guda kuma akwai wani boyayyen muhimmin al'amari wanda yake sarrafa duk wani motsi da rayuwa ta al'ummar gidan.


          Idan nace al'ummar gidan kada ka dauka wasu jama'a ne masu yawa,a'ah......dai daikun mutane wanda rayuwa cikin gidan ga zame musu lazim.


            Kamar kowanne lokaci,qarfe takwas da wasu mintuna na dare,lafiyayyun hamshaqan motocin nasa suka tsaya babbar gate din gidan me kama da qofar masarauta ko shiga wata kasuwar duniya,cikin qasa da second biyar aka soma motsa qofar gate din bisa sahalewa da sarrafawar daya daga ckin security din gidan dake tsaron qofar,wanda ke tsaye daga gefe kusa da na'urar dake tura gate din cikin uniform din da dukka ma'aikatan gidan suke amfani dashi,wato baqin wando da farar riga,sai baqar hula me kama da hular 'yan sanda.


             A nutse suka kutsa kai lafiyayyar harabar gidan me matuqar girma da tsari,wadda aka qawatata qwarai da shuke shuke,fitilu masu tsananin kyau da haske,da kuma ainihin fuskar gidan dake manne da wasu gilasai tamkar dasu akayi bangon gidan. Tun daga harabar tsarin gidan zai fara tafiya da imaninka,tsaftatattun tsirrai masu bada wani irin iska qamshi da koke koken tsintsaye daban daban,wasu siyansu akayi aka ajesu don bawa gidan dukkan ni'imar data kamata,wasu kuma daga Allah ne,sukanzo su wuce,kosu samawa kanau gurin kwana cikin tsirran dake wajen wadanda suka dace da tsarinsu,hakan sai ya sake qawata wajen,ya wadatashi da wani irin yanayi me sanyaya zuciya.


            A nutse ya fito daga motar kamar kowanne lokaci cikin tsananin kamewa da izza,yauqi da aji irin na hadaddun mazan da suke ji da kansu suka san kuma waye su. Yana sanye da wani yadi da aka samar dashi daga merino wool dan asalin qasar spain me asalin kyau da tsada,wanda wani qwararren telan ya zauna ya shiryawa dinki na zamani daya sake qawata yadin fiye da kima,ya kuma qawata kwalliyar mamallakin suturar. Yana daya daga cikin jerin mutanen dake da tsari da kuma zabi a dukka sutturar da zasu sanya,hakan sai ya cakudu da baiwar dacewa da kowacce shiga keyi da jikinsa,koda kuwa pajamas ya sanya,duk da wasu matan dake da qarancin kunya a idanunsu......sun sha gaya masa yana da kyau ne,hakanan komai nasa me kyau ne,wannan ya sanya kome zai raba a jikinsa yake dacewa dashi,ya kuma sake qara masa kwarjini da cikar haiba da kamala.


           Daya daga cikin yaransa ne ya matso da sauri yana masa bayanin wasu tarin takardu dake hannunsa,sai ya masa nuni da matashin dake tsaye a gefansa,yayi handing over dashi sannan ya taka a hankali yana nufar ainihin main entrance na gidan,ya barsu a wajen kowa yana qoqarin hattama aikinsa na ranar.


              Duk taku daya yana jin yana qara masa kwadayin isa gareta,zuciyarsa ce ita,rayuwarsa ce,hakanan farincikinsa.


             A nutse ya buda qofar lafiyayyen falon farko da zaka soma tararwa,falon da dukka kalolin kayan ado da qawa da aka zuba masa warm beige color ne da ratsin rusty red,tun daga manya manyan curtains na alfarma,kujerun da aka zuba carfet da aka malaleshi dashi ac da paint na ainihin bangon,hatta da frames dake parlor din masu dauke da ayatul kursiyyu falaq da nas da sauran ayoyin tsari color din dake jikinsa kenan,sai ratsin gold kadan a jiki.


            Iya dubansa tsaf ya qarewa falon,ya sanya qafafunsa a hankali ya saka kai ciki hannayensa cikin aljihun wandonsa yana ratsa falon,wani yanayi yana saukarwa gangar jikinsa har zuwa zuciyarsa,wasu emotions da baisan yadda zai raba kanshi dasu ba,yayita kokawa da kansa yana danne fushin dakeson motsa masa yana ci gaba da saka kai ciki.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post