CIWON KIRJI IRIN WANDA BAI KAMATA AYI WATSI DASHI BA

CIWON KIRJI IRIN WANDA BAI KAMATA AYI WATSI DASHI BA

CIWON KIRJI IRIN WANDA BAI KAMATA AYI WATSI DASHI BA

Ciwon kirji alamane na cututtuka na zuciya da huhu.Anan zamuyi tsokaci akan irin ciwon kirjin dabaikamata kayi wasa ko watsi dashi ba,sau dayawa mutane na dauka olsa kadai ke kawo ciwon kirji,nasha ganin marasa lafiya Wanda sukazo asibiti da ciwon kirji Kuma bayan gwaje gwaje aka gano wani Abu daban Kuma!Dan haka ka zauna ka natsu kakaranta dakyau!


1.Ciwon kirji na angina

Angina ciwone na zuciya,Yana faruwa ne alokacin da isasshen jini baya zuwa zuciya.

Angina na da ga cikin abunda yafi kawo Yawan ciwon ƙirji.

Idan mutun na da angina yakan fuskanci matsanancin ciwo wanda zai runka jinshi a tsakiyar kirjinsa,sannan ciwon yakan yi yawo daga kirjinsa har zuwa hannayensa,makogaro, kashin hakori(wani sa'in mutun na iya kasa banbanceshi da ciwon hakori),baya da Saman cibiya.


har ila yau,ciwon baya wuce minti 10.

Ciwon yafi tashi alokacin da mutun ke cikin nishadi,aiki,motsaka jiki bayan cin abinci,ko lokacin hunturun sanyi.

Ciwon yakanyi sauki ko ma yabace lokaci daya alokacin da mutun yasamu guri ya huta ko bayan yasha magani(sublingual glyceryl trinitrate).

Amafi lokuta marasa lafiya su kan kwatantashi da kamar ana matse musu ƙirji ko kamar an Dora musu wani Abu mai nauyi a kirjinsu.ciwon kirjin kanzo ne tare da wahalar numfashi ko haki,yawan gumi,tashin zuciya da amai. 


2.Ciwon kirji na mi

wannan ciwon kirjin Shima kusan iri dayane da na angina,Amma saidai shi yafi na angina tsanani,azaba da radadi Kuma baya sauki ko tafiya idan yafara Koda kuwa ansha magani(sublingual glyceryl trinitrate).Haka zalika zakana iyajinshi da haki,sannan kakasa sukuni da nutsuwa,karunka ji kamar mutuwa zakayi.


Meyakamata kayi

Duka wadannan ciwoka na janyo ciwon zuciya ko mutun lokaci daya yafadi ya mutu batare da ansan dalilin ba.

Yanada kyau idan kana samun irin wannan ciwon kirjin dakaje asibiti kaga likita a Dora ka akan magunguna.


Lafiya uwar jiki

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post