💖💖 NIHAAD 💖💖
65
Mami ta koma ɓangarenta tana hada sauran ankon da zata tura Drivernta ya kai ma kawayenta da bata tura ma ba Noor ta shigo parlon, hankali tashe tace "Mami Aunty Hassana da Mumy suna ta fada fa tun daxu" Mami ta mike tsaye tana kallonta da mamaki tace "Fada kuma?" Noor tace "Wallahi har da dambe" Mami ta zaro ido tace "Damben lafiya" Noor tace "They are fighting seriously fa a part din Mumy" Mami ta nufi kofa ta fita da sauri, Noor ta bi bayanta, tun daga Babban parlon gidan take jin muryoyinsu suna kunduma ma juna zagi kafin ma ta karasa bangaren Hajiya Amina, tsaye ta ga Janar bakin kofa yana kallonsu, bai kuma yi attempting dakatar da su ba, Suhaila da mai aiki na ta rirrike Aunty Hassana warce ke kokarin kara finciko Hajiya Amina su fara wani sabon damben ga Attachment dinta yashe a kasa Hajiya Amina ta tuge, Hajiya Amina na huci tace "Ku saketa don Allah ta zo, Banza kawai er wahala, kafura...." Aunty Hassana na tura su Suhaila da karfi take cewa "Ku bar ni in illata yar iskar, ni kike kira da er wahala? Ni? Toh wallahi zaki san ni kika ce ma er wahala" Hajiya Amina na tafe hannu tace "An fada, er wahala, dama ba wahalalliyar bace?" Cikin daga murya Aunty Hassana tace "Yanda nayi sanadin aka aureki haka duk abinda zan yi sai nayi an sakeki Amina, wallahi karshenki ya zo a gidan nan, ke banda na shiga na fita ko a er aikin gidan nan kin isa ki shigo balle matar gidan? Waye bai san karuwancin da kika yi ba a baya ba?? Waye bai san har madigo kin yi ba, ke da har London ana booking dinki ki ayi iskanci dake? Banda ni din ina za ki san Janar ki auresa???" Hajiya Amina tayi wani shewa tace "Riiii, ai abokin barawo barawo ne, madigo kuma tare muka fara da ke, kuma karuwancin ma duk tare mu ke yi, gwara ni ba baƙin cikin karuwancin da nake bane ya kashe uwata har lahira, lafiya lau muka rabu da ita, ke kuwa waye bai san har da bakin cikin karuwancinki da kike yi tun da aurenki ne ya kashe taki uwar ba? Sannan uwa uba alhakin mijinki Iliya da kika raba da 'ya yansa yau shekara ashirin kenan, kika gudo daga kauyen da dangin ubanki suka maki aure da shi sbda shashancin da kike na karuwanci, kika dawo garin Adamawa garin uwarki kika ci gaba da karuwancinki babu kama hannun yaro, waye bai san Sajida a titi kika yi cikinta kika haifeta ba??" Aunty Hassana tayi wani kukan kura tayi watsi da mai aikinta da Suhaila dake rirriketa, tayi kam Hajiya Amina ta cakumota iya karfinta, nan suka fara sabon dambe ba ji ba gani, Janar ya nuna ma Suhaila da Mai aikin kofa alamar su fita, sum sum suka nufi kofar suka fice daga parlon, Mami da hankalinta yyi mugun tashi zata karasa ciki da nufin rabasu, Janar ya dakatar da ita fuskarsa a murtuke, dambe iya dambe suka sha har sai da suka kusa yi ma junansu zigidir a parlon, ga jini a bakin ko waccensu, zuwa yanzu babu Attachment ko daya a kan Aunty Hassana duk Hajiya Amina ta tugesu, Sai da suka gaji lilis sannan aka ci gaba da zage zage ta uwa ta uba ana tsine ma juna, Aunty Hassana ta juya tana kallon Janar jini na zuba ta hancinta tana huci tace "Ita ce ta dauke maka miliyan 800, ka tuhumeta, ba wani ya dau kudin nan ba ita ce wllh, wallahi ita ce, sannan sai da tabi ta kashe duk cctvn gidan kafin ta aikata mugun nufinta" Hajiya Amina tayi wani shewa tana tafe hannu tace "Muka dauke dai tare Hassanaaa, banda kin masu labe shi da ɗan nasa a ina zan san an shigo da kudi gidan?? Ai kece babban barauniya Hassana, kudi kuma suna kugunki...." Hajiya Amina na kallon Janar tana huci tana nuna masa Aunty Hassana tace "Ita ta saka na dauko mata kudin na bata wallahi, idan karya nake Allah ya dau raina nan take, kuma ko miliyan 5 bata bani ba cikin kudin nan wallahi tallahi, zuwa yanzu da zaka ji gidaje nawa Hassana ta siya da motoci daga ita har ɗan ta ai sai Allah, sannan duk rashin ci gaban da kake gani a kasuwanci da kake daura Khalil ita ke bin boka da Malamai kudin su tarwatse kar yayi nasara duk don a daura nata ɗ'an, kuma hakan ne ya faru kusan shekara biyu a gidan nan in ba Aliyu ba baka daura kowa kan harkokinka ɗan naka ma taje tayi asiri ta sa ka koresa gaba daya, tunda ai sanda aka nemi kudin aka rasa baka koresa ba, ganin haka yasa ta banka uban asiri har sai da ka koresa, Hassana bata sonka bata son ɗan ka tana tare da kai ne kawai saboda abun duniya kuma kam ta tara don a yanzu Hassana ta mallaki gidajen kanta ya fi takwas duk a kudin da ta saka na dauko mata, Kullum sunanka a wajen Malamai yake don ta mulkeka son ranta duk abinda zata yi ka kasa yi mata magana, ai ba a banza ta kori sojojin dake gadin bangarenka da kofar babban parlor nan ba, a lokacin ta laka masu sharri wai suna kalle yan matan gidan idan sun zo wucewa duk don ta samu ta ci ma mugun kudurinta, sannan babu me turning off din Cctv din gidan nan sai ita, duk sanda take shirin yin mugun nufinta abinda take yi kenan, da kasan da irin zuciyar da Hassana ke tare da kai ko, to ba uwa daya ba, ko uwa daya uba daya ne wallahi sai ka nisanta kanka da zuri'arka daga Hassana, Matar da ta hada maka tuggu gun mahaifiyarku an kamata dumu dumu tana zina sai tace ai kai ka hadata da mutumin wai abokinka ne, alhalin shi abokin naka da ka hadata da shi ko ta samu ya aureta tunda zawarcin ya ki ci yaki cinyewa sun rabu tun tuni, amma tayi maka wannan sharrin, ko ka manta ne Janar????" Aunty Hassana ta shige dakinta da gudu tana dube duben abinda zata dauko ta rotsa ma Hajiya Amina a kai, Karasawa cikin parlon Janar yayi ya saka ma kofar dakin key ta waje, Hajiya Amina dai sai huci take, yana kallon Mami da duk jikinta yayi sanyi qlau ta kasa kwakkwaran motsi a inda take yace "Fita mu je" Mami ta juya ta fita daga parlon, shi ma ya fito ya saka ma kofar parlon makulli ta waje. Bangarensa ya tafi ya kira barracks a turo masa sojoji a mota, sannan a hada da mata ciki. Babu bata lokaci sai ga sojoji sun iso gidan, Janar ya sa sojoji matan suka shiga suka fito da Aunty Hassana da Hajiya Amina, duk aka kwama masu handcuff, Aunty Hassana na kallon Janar tace "Yanzu yaya ni zaka sa a saka ma handcuff? Ni? Duk inda mahaifiyarmu take zata yi alfahari da abun nan da ka min Yaya?" Ko rufe baki bata yi ba ya sauke mata tagwayen mari wanda sai da taga stars, ya kuma umarci Sojojin da su zane su idan za su kawo masu taurin kai, Ita dai Hajiya Amina ba abinda tace amma ranta fari kal ta tona ma Hassana asiri, don shekara kusan 17 kenan Hassana ke amfani da ita a gidan, don dai ita ma tana da wayo da sai dai ta tashi a tutar babu, Aunty Hassana ta juya da sauri tana kallon Janar kafin a fita da ita daga parlon tace "Kuma wallahi wallahi Hanan ba er ka bace, bata da gadonka, boka ne yayi mata cikinta don juya ce ita bata haihuwaa...." Sojan ta kwada mata mari ta turata suka fita daga parlon..... Kamar yanda Janar bai yi bacci ba daren ranan nan haka Mami warce ta ma fi sa girgiza da wannan abu da ya faru, da ya tuna abinda Hassana ta fada na karshe sai hankalinsa ya tashi, wai Hanan ba er sa bace, then there is need for a DNA test.... Mami na idar da sallah da asuba Aunty Maryam ta fara kira don bata mance furucinta a jiya da yamma kafin ta tafi airport ba, sai gashi hakan har ya faru, amma bata sameta a waya ba, can ta mike a hankali ta fita daga bangarenta, dakin Aliyu ta fara zuwa don duba kafarsa, amma taga dakin wayam kuma bata ma ga alamar ya kwana a dakin ba, juyawa tayi ta fita ta karasa bangaren Janar, ta samesa zaune saman kujera still pondering, bata taba ganinsa a yanayin nan da yake ciki ba sai many years ago, kana ganinsa kasan abun ya tsaya masa a rai, ta gaishesa cikin sanyin murya, ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ta kwantar da murya tace "Plss kar ka sama kanka damuwa Yallabai, this isn't proper for ur health, sannan ina rokon ka ka dubi albarkacin zumunci ka kyale Hassana, sai kaga Allah ya maka sakayya ta inda baka zato...." Janar ya kalleta da sauri kuma a fusace yace "Amma ina ga baki da hankali ko Fatima??" Mami dai tayi shiru, yace "Then if u have nothing good to say ki bar min parlona kada ki kara bata min rai don Allah" Mami ta sauke ajiyar zuciya bata dai sake cewa komai ba, Khalil ne ya shigo parlon da sallama, shi fa duk abinda ya faru jiya a gidan bai sani ba don yana barin bangaren Aunty Hassana dama gidansu Nadeeyah ya tafi kuma bai dawo ba sai kusan karfe goma saura, Ya zauna saman kujera ya gaida Janar, Janar ya amsa without looking at him, he felt guilty duk abubuwan da ya ma ɗan nasa a baya, Khalil ya gaida Mami ita ma ta amsa, bayan few seconds Janar yace "When are you leaving?" khalil ya daga kai ya kallesa yace "Later in the day in sha Allah" Janar yace "Da matar taka zaka tafi can din?" Khalil ya ɗan yi shiru, he felt unhappy da bazai iya tafiya da ita ba, ya so ace da ita zai yi tafiyar but it's not going to be possible in ba dai daga tafiyar zai yi ba, a hankali yace "Ai bata da passport" Janar yace "Ohk, sai ayi kokari tayi, it's important...." Khalil yace "Is the trip urgent sir?" Janar yace "It is, tun 5 days ago ya kamata" Khalil yace "Ohk" Daga haka ya mike ya basu waje ya fita daga parlon. Karfe takwas Janar ya shirya da escort dinsa suka tafi barikin da aka kai Aunty Hassana da Hajiya Amina, ai ko ya tarar sojojin sun ci ubansu dai dai gwargwado, tun karfe hudun asuba suke tsaye har zuwa yanzu da Janar ya zo, ga tsallen kwadon da suka yi daren jiya na kusan awa biyu, banda azaba babu abinda cinyoyinsu ke masu, ga sauro da zafi a inda aka ajiyesu, duk sun yi duhu kamar basu taɓa shan Ac ba, Janar na kallon Hajiya Amina bayan ya shiga har inda suke ya ajiye mata farin takarda a gabanta, Hajiya Amina taki daukan takardan, yace "Na sake ki, saki daya, biyu, har uku, Hanan kuma zan kai ta ayi DNA test, if i should find out that she isn't my daughter, you are to go with her" Yana gama fadin haka ya juya ya fita ya shigo tare da sojoji murdaddu har biyar yana kallonsu ya nuna masu Aunty Hassana yace "Ku bi duk hanyar da za ku bi sai ta furta maku inda takardun gidajen da take siya da motoci suke" Suka ce "Yes Sir...." Juyawa yayi ya fice daga babban guardroom din.
Inna ce tsaye tsakar parlon tayi mitsi mitsi da ido tana bin duk masu kallon akwatunan kayan Nihad da kallo kada ko tag a nema a rasa cikin kayan, akwatuna 12 ne tsadaddu, 6 iri daya sauran shiddan ma irinsu daya, kayan ciki kuwa sai son barka, Aunty Jamila da kawarta da wata kawar Mumy basu siya mata kayan banza ba, kaya ne na gani na fada masu tsada, matan yayan Abba ne da yan uwa da abokan arziki cike a parlon ana ganin kaya kowa sai sa albarka yake, Umma dai na zaune one sitter sai bin kowa da ido take bata cewa komai, gaba daya tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita fa har yanzu gani take zata farka taga duk wannan abun mafarki take, da ko anyi mummunan mafarki in haka ne, amma dae shiru shiru bata ga ta farka ba, gashi duk dare da kyar take rintsawa saboda sai taji kamar an soka mata mashi a zuciyarta, ta dingi juye juye kenan tana numfashi da kyar, Kamila ma na tsaye bayan kujera duk ta rame saboda damuwa, sai bin akwatunan take da kallo, wanda ko rabin kayan ciki ita bata samu ba, Inna na daga hannu tace "Toh a gaskiya idan ba ganin haramun ku ke son yi ma kayan nan ba kuma ae ya isa haka, ganin kaya kusan minti ashirin yanzu kamar wa enda aka ajiye ma kwari, ai yawansu bazae sa ma a gama ganinsu ba don ma ku ji, kai wllh baza ma a sake bude kayan ba koma wa zai zo, iyaka ya ga akwati mu ce masa kayan miliyan goma da dubu goma ne a ciki ya juya yayi tafiyarsa, idan ana yawan bude akwatin ma ai sai su samu matsala mu shiga uku su ce sakwan muka siyo...." Aunty jamila dake kan kujera tace "Gaskiya kam Inna" Inna tace "Toh kun gani, ae ba ayi ma lefe kallon haramun haka, idan anyi saisa saisa sae a tashi kuma" Wata er uwar Mumy dake zaune parlon tace "Toh yanzu yaushe za a kai kayan Hajiya?" Inna tace "Aa wannan sai sanda Ibrahim ya sa mana lokaci, muna isa Habujan dama sai ayi waya da Halilun ya sanar a gida ga fa mu nan zuwa da kaya niki niki, kun ga ai kafin mu karasa sun mana girki irin tasu ko? tunda ance Abujan ma tana da girma" Matar tace "Toh mutane nawa ne za su je kai kayan idan lokacin yayi?" Inna ta kalleta daga sama har kasa, ta sake kallonta da kyau, can dai tace "Sirara ma za a tafi da saboda matsi a cikin mota, dama daga ni sai Jamila da wannan da aurenta ya mutu wato Kamila za mu je, kinga ai duk bamu da jiki, Ita Sumayya an barta ta ji da jinyar goshinta da hannu kar a fama mata a hanya, amma dama ai ba gayya za ayi ba" Matar bata sake cewa komai ba, bude kofar parlon aka yi Nihal ta shigo da trolley dinta, Inna tace "Oyoyo yan makaranta"
Khalil bai ji dadin rashin ganin Nihad ba sanda zai tafi wajen karfe sha daya da rabi na safe, wai Mami tace su tafi su yi gyaran gashi da Mimi, he don't know how to ask Mami wani saloon din suka tafi, don yayi ta kiran layin Nihad din a kashe, Mimi kuma bata picking, sai yayi tunanin ko Mimi bata tafi da wayarta ba, Har ya isa airport mood dinsa was so dull.... Da yammacin ranan sojoji suka shigo da Hassana gidan tana dingishi da kyar, kana ganinta kasan ta ci baƙar azaba hannunsu, dama basu shigo gidan ba sai da suka Sanar ma Janar zuwansu, yana tsaye babban parlor kuma suka shigo, har bangarenta ta kai su suna biye da ita babu rahama a fuskarsu, Janar ya bi bayansu, tsabar yanda hannunta ke ciwo ta kasa daga wani babban akwatinta dake dakin, wani soja ya sauke mata akwatin ta bude lock din ta hau ciro atamfofi kusan kala talatin wanda bata dinka ba, yawancinsu super ne da holland, can kasan akwatin ta ciro wani envelope, sojan ya dauki makeken sarka da dankunnen gwal da zobe sun kusa biyar dake kasan akwatin, Tana zare ido tace "Takardu fa ku ka ce, kuma ga su" Sojan ya fizge envelope din hannunta ya mika ma Janar ya amsa ya bude ya ga takardun gida ne har hudu, Ya mayar cikin envelope din yace "Akwai saura..." Hassana ta fashe da kuka tace "Ni su kenan wllh wllh, ba wani takardan gida..." Wani naushi sojan kusa da ita ya kai mata a baki, Janar ya mika masu envelope din yace "Ku mayar ku kulle akwatin ku fitar min da shi" Suka yi yanda yace, Janar na kallon Hassana yace "Na baki awa daya ki tattara komai naki ku bar min gidana dake da yaranki gaba daya" Ta fashe da matsanancin kuka ta durkusa kasa tace "Yaya ka mance tsakanina da kai ne? Kanwarka ce fa ni, Yanzu duk inda mahaifiyarmu take zata ji dadin wannan walakanci da tijaran da ka min Yaha" Yana kallon sojojin strictly yace "Awa daya za ku jira ta hada komai nata ta bar min gidana ita da yaranta, sannan ku yi alerting sojojin anguwan she is no longer welcome in my house.... Yana gama fadin haka ya juya ya fita, babu bata lokaci Aunty Hassana ta hau hada kaya tana kuka sosai kamar ranta zai fita, ga gwala-gwalan nata ma duk suna akwatin, sai ma sun bude wani zip din za su gansu kaca kaca sun yi na miliyan 40, duka duka account din nata ko dubu dari bakwai bai kai ba, ta ina zata fara???? cikin minti arba'in ta dau iya abinda zata iya dauka a dakinta, ta sa su Sajida ma duk suka hada kayansu suna kuka, sojojin suka tasa keyarsu aka fitar da su daga anguwan gaba daya suka yasar da su bakin titi....