LARURAR SANYIN GABA WATO GENITAL INFECTION

LARURAR SANYIN GABA WATO GENITAL INFECTION

LARURAR SANYIN GABA WATO GENITAL INFECTION

Ma'aurata kunsan Ciwon SANYI, da RASHIN TSAFTA suna matukar sa rashin sha'awan jima'i kuwa? Sukan hana jituwa tsakanin mata da miji. Kuma komi iya kwanciyarki da cushecushen kayan mata inbaki magance infection ba akwai matsala.

Irin wannan infection din yana hana jin dadin jima'i, yana hana daukar ciki, yana kuma cutar da maigida ya cutar da abokiyar zama ma inba ke kadai bace.

Domin akan sami amarya me tsafta, yayin da uwargida kuma kazama, ko kuma uwargida me tsafta yayin da amarya kuma me karancin tsafta... wanda illar infection shine inde mijin zai jewa waccan me karancin tsaftar kuma kema yazo miki toh duk kokarinki tsaftarki bazaki tsira ba saide abun yai miki da sauki.

Haka zalik in Mace mai biye-biye ce tana iya debowa ta sawa miji ko Miji in me neman Mata ne yana iya debowa ya sanyawa Mace, shiyasa dole likita yai tambaya ya tantance pattern of sexual activity, boye gaskiya ka iya sa kuita magani abanza ba canji domin kun ɓoye likita bazai taba tunanin baku wani magani daban ba. Shyasa a tsaida gaskiya, likita ba a masa karya, hakan cutar da kai ne.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

ALAMOMIN SUN HADA DA

■ Daurewar mara akai akai ba lokacin period ba

■ Jin motsi kamar wani abu na tafiya acikin farji

■ Jin zafi yayin fitsari

■ Jin zafi yayin saduwa

■ Ganin fitar farin ruwa me kauri

■ Ganin fitar abu kamar dusadusa daga farji

■ Jin discharge na fita da karni kamar karnin kifi ko doyi

■ Kai kayin gaba

■ Gani kurji ko kumburi agaba

Da de sauransu

Al'amarine me nauyi amma kar ai kunyar zuwa ga likita neman lfy, wasu nadashi amma sam basusan menene ba sai daga baya in abun yayi yawa. Wasu kuma basa ganin discharge din komi saide ciwon mara.... shima managing dinsa daban. shyasa ko yayshe nake cewa aje ga kwararrun jami'an lfy.

🌷

Ga jami'an lafiya musamman kananu kusani vaginal infection ya kasu iri da yawa akwai viral, bacterial, fungus da parasitic don haka wajibi ne ka fahimci meke jawosa kafin dora mutum a magani. Ba duk infection ne ake bada antibiotics ba, akwai infections din da inka ba mace antibiotics ka kara haukatashi ne.

Sannan kuskure ne dora mutum akan babban antibiotics wato broad spectrum antibiotics akan karamin abunda bai kai ya kawo ba, hakan kuna jawowa jikinsu yai developing antibiotics resistant ta yadda zaima ki aiki nan gaba in wata cutar ta samesu, a kiyaye pls! Narrow spectrum sune first line ko yaushe na antibiotics. 

Don haka wajibinku ne ku fahimci abunda ya jawo infection din da kyau kafin bada magani. Shyasa manyan asibitoci wasu sai mun dau sample na discharge din mun turama masanan kimiyya wato Medical lab's scientists sun tantance mana domin dora mutum kan maganin da ya dace dashi.

Sannan yana da kyau jami'in lfy yasan wadanne irin tambayoyi ya dace yai da kuma sanin dalilin yinsun, karkurum mace tazo da complain kai kuma ka saki layi ka tafi wata tambayar can mara mahimmanci tare da alaqa da matsalarta... daga lokacin bazata kuma dawowa gurinka ba domin zata fahimci kaima din duk bigece bakasan komi ba. 

Sannan ku dena jin haushi don an muku tambaya kusani ayanzu yancin mara lafiyar da yazo gabanka ne.. ya tambayeka daya bayan daya game da maganin daka rubutamasa, kai masa bayani kuma harsai ya gamsu, sannan yana da hakkin ka sanar dashi damuwarsa matukar akwai bukatar hakan domin yasan abunda zai kiyaye.... Don haka batun wani harden rubutu a likitanci yanzu bashi. Kai rubutun magani straight and clear shine sanin aiki.

Don haka jami'in lfy a duk sanda mace ta zoma da korafi na alamun infection ne ke damunta baya ga magani karku mance da bata wadannan shawarwarin da zan lissafo; sune ginshikin cin nasara wajen magancesa. Ku sanar da ita cewa;


1. Zaifi kyau ki rika sanya pant na cotton bana roba ba. Sannan a rika canza pant din sau 2, 3 zuwa 4 arana a irin wannan yanayin. Dalilin shine farji ba gurine da iska ke ratsawa ba ko yaushe sanya panta na roba karawa gurin damshi zaiyi... damshi ko yanayi ne da irin wadannan kwayoyin cutar keso. 

2. Duk sanda zaki wanke unders dinki kike amfani da ruwan dumi kina wankewa dashi, inkuma ruwan na sanyine to a zuba gishiri aruwan wankin kadan domin kashe wasu kwayoyin cutar koda akwaisu ajiki. Sannan inda hali ake shanyasu acikin daki ko inda akasan Qurar kasa bazatake tasowa tana budesu ba kafin su bushe.

3. Sannan akiyaye kai hannu wajan farji, Musamman yana dakyau hannu ya zamto anwankeshi kafin ashiga bayan gida koda babu datti da kuma bayan anfito.

4. Kar kike tura sabulu yayin wanke farji zuwa ciki, inda hali ma sam babu bukatar sabulu wajen wankesa domin gurine dake wanke kansa da kansa, shyasa wani lokacin kina zaune kurum saikiga abu me yauki na fita... ba duk abunda ke fita batare da sha'awa banr infection... 

Sannan ake aske gaban fes duk bayan sati 4 ko 6. Amma akeyi sama sama, sannan ba direct ba, ko yaushe kafin ki askin ki sami ruwan duminki ki zuba a bowl kikai bandaki inkinje ki zauna aciki na minti 5 zuw 10 tukun kafin fara shaving din saboda yin hakan zai hana kuraje da kaikayi.... bama sai me infection ba ga dukkan maza da mata ya dace kui hakan. Inda hali adansa gishiri cikin ruwan dumin kafin azauna ciki.

5. Ake tabbatar da tsafta bandakuna pls, Ake kad'a ruwa da gishiri ko da Omo Ana watsawa acikin bandakin ana wankesa, ko ta hanyar amfani da sauran maganin kashe kwayoyin cuta na ruwa.

6. Ake tsarki da ruwan dumi zaki iya dumamawa ki zuba a cikin flask duk sanda zaki kama ruwa sai ki tsiyaya in kina gida. sannan anaso ake sa gishiri daidai misali a ruwan dumin da za'ake tsarkin. A dena tsarki da ruwan sanyi sam inda Hali amma inba yadda Za'ai to shima asa gishiri kadan ciki. Ko namiji inda hali inkana gida ka jimanci tsarki da ruwan dumi

7. kike canza pads yayin period akalla Sau 3, xuwa 4 arana, insun Jima koda basu 6aci da jini ba. Saboda jini culture media ne me kyau dake ba kwayoyin cuta damar rayuwa...

8. Matsayinki name fama da infection Inda hali inke kadai ke kwanciya adakinki ki rika cire pant dinki inzaki kwanta ki bar iya siket yadda iska zatake ratsa zuwa wayewar gari ki rika haka kullum har matsalar ta tafi... 

9. Karka mance duk matar auren da tazo da Infection wajibi ne mijinta ma adorasa a magani daidai da irin nata, hakama insu 2 ko 4 ne wajen mijin kaf dinsu sai sunsha maganin daidai da nata.

Inde an kiyaye wannan Insha Allah za'a samu sassauci akan kari, magani kadai babu counseling a infection baya aiki... abun dadin ma yawancin magungunan infection ma wani sha sau 1 ne shikenan wani kuma sau 2 anjima anayi kwana 5 saide in ansami treatment failure. Fatan harma wadanda basu dashi sun ilmantu.

✍🏼

[Ibrahim Y. Yusuf]

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post