Nihaad page 46 by Khaleesat Haiydar complete
Health College

Nihaad page 46 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 46 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖 Nihaad 💖💖

Page 46

Mikewa Khalil yayi ya tafi har bakin kofa ya tsaya ya rungume hannu yana kallon yanda take kuka, calmly yace "In da gaske kina son bin sa me yasa tun zuwansa baki ce masa xaki bi sa ba kika zo nan kina min kukan munafurci, tunda kinsan tafiya zai yi ba nan zai kwana ba" Nihad ta hadiye kukan da take ta daga kai tana kallonsa fuska daure, can ta mike tsaye tace "Ina ruwanka da ni? Kaga dai ba ruwana da kai a gidan nan, don yayana yace in daina kulaka duk abinda xaka min, kuma ni dai naji maganarsa, don haka kai ma ka fita harkata because bana son inyi disobeying yayana, idan baxa ka iya cewa inyi hakuri ba dole sai ka min maganan" ta karasa maganar kamar xata fashe da sabon kuka, kallon bakinta kawai yake, can yace "Ohk yace ki daina kulani kenan?" Tace "Ehh, kuma ko kana daga min shoulder dinka baxan san kana yi ba tunda ba ruwana da kai, I will pretend I don't know" Tana kai wa nan ta nufosa fuska daure tace "Ka matsa min ni in fita" ita haushinta maimakon yace tayi hakuri shine yake neman tsokanarta kuma, Yace "Aa bari dai a baki kudin mota ki bi sa kawai, ai yana nan Abuja bai yi nisa ba" Wani kallo ta dinga masa, ya sa hannu cikin aljihun 3 quarter din jikinsa ya ciro 100 dollar ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon kudin sai kuma ta kwace ta cukuikuye ta jefar kasa, tana kallonsa da kyau tace "Kudin da ba naka ba" Kallonta ya tsaya yi baki bude, can yace "Kinsan hukunci warce ke ma namiji rashin kunya, namijin ma wanda aka aura mata daga gidansu?" Ta wani kallesa tace "Ohh dama kai mijina ne? Ai ban san ina da miji ba, kuma ai shi namiji baya neman tsokanar mace" Jin yayi shiru bai ce mata komai ba ta dauke kai ta turo baki, a hankali ya kai hannu ya kashe switch din dakin ta juya da sauri ganin duhu ya gauraye ko ina sai ɗan hasken screen din Iphone dinsa da ya ajiye saman gado, taji kuma yana sa makulli a kofa, komawa baya tayi a tsorace tana zaro ido tace "Meye haka kake yi?" Ba abinda ta ji yace mata, Ganin he is advancing toward her ta fara komawa baya da sauri cikin rikicewa tana cewa "Wayyo don girman Allah kayi hakuri, duk abinda na fada ba da kai nake ba don Allah kayi hakuri, dama yayana yace in daina maka rashin kunya kuma na daina tun...." Wani kara tayi a tsorace jin saura kadan ta fada saman gado don bata san har ta iso wajen gadon ba, zata tashi da sauri ya mayar da ita ta fada kan gadon, zaro ido tayi a mugun tsorace ganin he just lied directly on her, cikin rawan murya ko ina na jikinta na ɓari tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi baxan sake maka rashin kunya ba har abada, kaji na rantse..." Gaba daya ta gigice tana kokarin turasa amma ta kasa, cause his weight is out of the world, nan kuma ba duk weight din nasa ya sakar mata ba, ta fashe masa da kuka tana sauke numfashi da kyar ga kamshinsa da ya cika ko wani breathing dinta, yayi kasa da murya still adjusting on her yace "Baki san kina da miji ba ko?" Cikin kuka tace "Wallahi na sani, kawai wasa nake maka, don Allah ka yafe min kayi hakuri baxan kara ba.... Wallahi numfashina zai iya daukewa" a hankali yace "Ya dauke mana" Bata san sanda tayi wrapping hannunta a bayansa tana kuka sosai tace "My chest is paining me plss" ai ko ya lumshe ido ya kara sakar mata weight hakan da tayi masa, as if he is going to sleep, sae kuma yayi placing forehead dinsa kan nata, joining his nose directly with hers, cike da karfin hali tace "I am sorry plsss" murda kofar dakin aka yi, yayi brushing lips dinsu ya mike da sauri ya sauka saman gadon, Nihad ta ja wani numfashin wahala ta mike da sauri, jikinta na rawa ta silalo kasa hawaye na sauka idonta, ya tafi gun switch din dakin ya kunna, ya fara dube duben Jallabiyarsa a dakin ya dauka ya daura kan kayan jikinsa sannan ya tafi ya bude kofar dakin, Mimi dai sai bin su take da ido ya amshi cup din hannunta da sauri yace "Thank you dear... Zata bi yayanta inda ya tafi shine na kulle kofar har ki zo, may be u can tell her not to" Nihad dai ta kasa dago kanta daga inda take durkushe a kasa har sannan bata ji kirjinta ya dawo dai dai ba, ga wani bugawa da zuciyarta yake alamar ba karamin tsorata tayi ba, Mimi ta karasa ciki ta durkusa gabanta soothingly tace "Kiyi hakuri, tunda yasan gidan definitely zai dinga zuwa wajenki ai, so ba sai kince zaki bi sa ba" Nihad taki yarda ta kalleta kamar munafuka, Khalil dake tsaye bakin kofa yace "Kawai ki tafi ki kyaleta idan ta gama kukan sai ta fita...." Zumbur Nihad ta mike har sai da ta ba Mimi tsoro, Mimi ta mike tana kallonta ganin she looks so afraid tace "Are you alright Neehad?" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Mimi tace "Toh mu tafi" Tana makale bayan Mimi suka nufi kofa, taki yarda ta kalli inda yake tsaye, ya bi ta da ido har suka fita sannan yayi wani murmushi ya kulle kofarsa... Duk zaman da Nihad tayi part din Mami bayan sun koma da Mimi she is so silent duk da dama can ba wai tana magana bane amma na yanxu yayi worst, gaba daya ta kasa cire abinda yayi mata a zuciyarta, abincin ma kasa ci tayi wai ta koshi, Mimi duk tunaninta ai tafiyar farooq ne ya sa ta zama haka, shi yasa ma bata yi bothering dinta ba. Wajen karfe tara Khalil ya shigo parlon wearing on his pajamas, sai da gaban Nihad ya fadi ganinsa da tayi taki yarda kuma su hada ido, yana kallon Mimi yace "Mami na ciki?" Mimi tace "Aa tana downstairs tun dazu" Yace "Ohk, ni bani da abinci yau a gidan kenan?" Mimi ta ɗan zaro ido tace "Yayanmu wanda muka kai maka daki fa?" Yace "I called Noor ta fita da shi ban ci ba, ai wannan yayi yawa sosai" Mimi tace "Ohk sorry pls, should i get you another one now?" Yace "Yeahh, but ba nan zaki kawo min ba, and ki ɗan kara hada min irin wannan coffeen da kika yi min" Sosai gaban Nihad ya fadi da ta lura Mimi fita zata yi daga parlon, sai zazzare ido take uwa warce tayi ma sarki karya, Mimi ta dau after dress dinta ta daura kan sleeping dress din jikinta tace "I am coming Nihad" Nihad was shocked and confused on what to do, haba ai bata san sanda ta mike da sauri xata ce mata tana son bin ta amma tuni Mimi har ya fita, kamar munafuka ta fara tafiya zuwa kofa, Khalil dake kallonta yace "Kee" Ta tsaya a tsorace ta kallesa kamar zata yi kuka tace "Ni rakata zan yi" Bata jira me xai ce ba ta karasa kofar da gudu ta bude ta shige next parlor amma taga Mimi har ta fice daga nan ma ta kulle kofar, bin bayanta Khalil yayi tana ganin haka ta kwasa a guje ko kusa da kofar bata kai ba ta take dogon hijab din dake jikinta na Mimi, sai ga tim a kasa ta zaro ido tana yarfe hannu, dai dai nan aka bude kofar parlon, Mami ta koma baya tana kallonta tace "Subhanallah, garin yaya?" Nihad ta mike tsaye da sauri xuciyarta na bugawa tace "Zan tafi in kwanta ne, shine na fadu" tuni khalil ya koma daya parlon, Mami na kallonta tace "Toh ki dinga yi a hankali, Hope you are not injured?" Ta gyada mata kai da sauri, Mami tace "Toh sai da safe" Nihad tayi saurin fita daga parlon, Mami ta bi ta da kallo, sai kuma ta karasa next parlor din, zaune ta tadda khalil yana waya, the way he is talking on the phone xaka yi zata ya kai minti talatin yana wayar, Mami tayi wucewarta cikin bedroom dinta. Sai da Nihad ta shiga dakin da take taji knees dinta na mata zafi, ta zauna gefen gado tana dubawa taga ba ciwo amma zafi yake mata, da kyar ta samu ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, ta saka kayan barci bayan ta shafa turare ta kwanta saman gado tayi lamo, incident din daxu ne ya dinga dawo mata, but what's the meaning of that?? Lokaci daya ta kawar da tunanin ta jawo wayarta a hankali tana dubawa, taga miss calls din Ayman har biyu, zata ajiye wayar sai ga wani kiran nasa, dagawa tayi ta rufe har kanta da duvet, ko minti goma basu yi da fara wayan ba taji an kwankwasa kofar dakin, da sauri ta mike zaune ta katse wayar tana kallon kofar, aka sake Knocking sauka tayi a hankali ta tafi gun kofar tace "Waye?" Mimi tace "It's me" Daga haka Mimi ta bude tana kallonta tace "Mami said i should ask if u are okay?" Nihad tace "Sure, thank you" Mimi tace "Ohk good night" Nihad ta dan mata murmushi ta gyada kai kawai, daga haka Mimi ta juya ta bar wajen Nihad ta kulle kofarta ta koma ta kwanta. Washegari Khalil na tare da Mami a parlonta Aunty Hassana ta shigo da sallama, Khalil na jin muryarta yayi saurin kara waya a kunne yana maganan da babu shi, Mami dai bata ce komai ba, har Aunty Hassana ta karaso, shi kuma ya mike ya fice daga parlon still making fake call, Mami tace "Mun tashi lafiya Hajiya Hassana" Aunty Hassana da ta bi sa da kallon gefen ido tayi saurin cewa "Lafiya lau, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, ya su Sajidah" Aunty Hassana tace "Toh ni naji kin min shiru, baki ce ga abinda ake ciki ba, don last week naji Abbansu yace xa a kai kudin auren yaron nan, to mu ba wani shirye shiryen da xa muyi a nan ne?" Mami tace "Ai gobe ne idan Allah ya kai mu" Aunty Hassana tayi shiru tana kallonta da mamaki, can tace "Gobe goben nan amma ba labari?" Mami tace "Ni ai na zata Amina ta gaya maki don muna tare da ita a parlon Yallabai ya saka lokacin, and that was last week" Aunty Hassana ta hade rai tace "Saboda Amina ce tafi kusanci da ni ko me?" Mami tace "Ba dai ta yanda xa ayi kice baki ji daga bakinta ba Hassana, ko ita bata gaya maki ba ai yaci yayan naki ya gaya maki, yaushe rabon mu hadu dake cikin gidan nan balle maganar ya hadu mu? Ai mun kwana biyu bamu hadu ba" Aunty Hassana tace "Gaskiya ne, kya yaɓa min magana son ranki ai, ba laifin ki bane" Bude baki Mami tayi tana kallonta tace "Meye abun ɓacin rai a zancena Hassana?" Tuni Daga Hassana ta mike fuuu ta fice, tana komawa bangarenta ta dau waya ta hau kiran kawarta Chamo, ta yaya za ace gobe xa akai kudi ita da ta zata Mami zata ce mata an daga lokacin kai kudin, Chamo na dagawa Aunty Hassana tace "Ke gobe fa naji ana cewa xa a kai kudin auren, yaya haka?" Chamo tace "Toh in kai kudin aure sai aka yi yaya? Baki ta6a ganin inda aka fasa aure ranan daurin auren bayan an tara jama'a ba?" Aunty Hassana tace "Haka ne, to amma idan kuma hakan bata kasance ba fa? Ai risk ne wannan Chamo, kamata yayi ko kudin ma kar a kai balle a saida rana" Chamo tace "Ke dadina dake gajen hakuri wallahi, sai kace yau aka saba maki aiki kiga aikin ya ci Hassana?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciya tace "Aa ba haka bane Chamo, ni dai kawai ina ga ba sai an wani je ga ranan daurin aure a fasa ba, kawai tun ba aje ko ina ba a fasa gaskiya hankali na zai fi kwanciya" Chamo tace "Toh ai abinda baki sani Malam yace min dole ne xa a kai kudin amma a banza tunda ba auren za ayi ba, daga sanda aka kai kudin matsaloli xa su dinga billowa daga both part har aure ya ruguje daga karshe" Aunty Hassana dai tayi shiru don ita fa bata gamsu ba, tasan karkari aka kai kudin nan a sa wata daya in dai yayanta ne, can tace "Toh daga ina ne xa su bukaci a fasa auren Chamo?" Chamo tace "Shi da kansa Khalil din xai ce ya fasa, ke ni bari kiji wllh malamin ma ce min yayi bai ga auren ba kwata kwata, xa dai ayi ta kashe kashen kudi, a siya wancan a siya wannan na biki amma fa ba auren" Aunty Hassana tace "Toh yanzu Sajidar ce ko farhana?" Aunty Hassana tace "Toh ai kya bari maganar auren ya ruguje tukunna ki kawo wannan ko?" Aunty Hassana tace "Toh shikenan, sannan abu na karshe kinsan ɗan iskan yaron nan ko gaisheni ya daina yi a gidan nan?? Wallahi tun da ya dawo ga maciji bai hadani da shi balle yarana, iyaka yayi da kanninsa ko Hanan" Chamo tace "Shi khalil din??" Aunty Hassana tace "Wallahi nake gaya maki" Chamo tace "Wannan ai abu ne me sauki, xan kira malamin in gaya masa xa a san yanda xa ayi...." Aunty Hassana tace "Toh Nagode, za mu yi magana zuwa anjima" Daga haka ta katse wayar tana ta tunane tunane, ita wallahi ko kudin auren ma bata son ya shiga hannunsu, don tasan ba amsa xa ayi ba idan aka fasa auren ai, ga kudi ba na wasa ba xa a kai ta sani. Throughout ranan Nihad taki fito dakinta don ko by mistake bata son haduwa da Khalil, wani sabon tsoronsa take ji har cikin zuciyarta, saboda yanda ta sa abinda yayi mata jiya da daddare a ranta sai da tayi mafarkinsa cikin dare, wajen karfe shidda na yamma Mami ta shigo dakin nata tana tsaye bakin kofa tace "Why are you inside throughout?" Nihad ta ɗan yi yake tace "Aa ina kallo a waya ne" Mami tace "Ohk, ga can takalmi Noor ta siya har da ke" Nihad ta dinga kallon Mami jin wai Noor, ko dai Mimi take son cewa, da sauri tace "Toh Mami, xan fito yanzu" Mami ta juya ta fita, a hankali Nihad ta mike ta dau mayafinta sannan ta fito daga dakin. Tana shiga parlon Mami taga Mimi zaune tana operating laptop dinta, Mimi tace "Kinyi scarce yau fa, hope you know you are having lectures tomorrow" Nihad ta ɗan yi murmushi kawai ta zauna ta gyada mata kai, Mimi ta dau takalmi ta mika ma Nihad tace "Noor got this for us all, same color same design" Nihad ta amsa tana kallon takalmin tace "I appreciate it" bude kofar parlon aka yi Khalil ya shigo, Mimi tace "Awnn Yayanmu you look good daga wajen Sis Nadeeyah kake ko?" Yace "Yeah, ina Mami?" Tace "She went in not too long" Ya ɗan kalli Nihad suka hada ido, ta ɗan daburce tace "erm... Good evening"  Yace "Evening" Daga haka ya nufi dakin Mami yana murmushi, Mimi ta wara ido tace "That's sweet of u Nihad, kuma naji dadi da kika ji maganata" Nihad dai bata ce komai ba, can kuma dai ta dau takalminta tace "Zan je inyi sallah, it's almost magrib" Mimi tace "Ohk" Daga haka Nihad ta mike ta fice daga parlon don bata ma son ya fito ya sameta. Tare Khalil da Mami suka tafi bangaren Abba ta dalilin kiranta da Abban ya aika khalil yayi, Mami ta gaishesa bayan sun samesa a parlor tare da Aunty Hassana, Mami tace "How was the trip?" Yace "Alhamdulillah" Mami tace "I was thinking ba sai ka dawo ba, representative dinka kawai zaka aika goben" Abban ya ajiye takardun hannunsa yace "Ni ba saboda shi na dawo ba ai, kuma i think gobe xan yi tafiya portharcourt..." Mami tace "Allah ya kai mu" Shi dai khalil na zaune nesa da su yana danna wayarsa, Abba na kallon Mami yace "Dama i want to confirm if ke ce ke aikosa ya zo nan yayi min rashin da'a" Aunty Hassana ta sauke wani ajiyar xuciya, Mami ta kalli khalil da sauri, Khalil ya ajiye wayarsa yace "But i see nothing wrong don na tambayi hakkina Abba, i am asking you for my property, i seriously need them" Abba ya mike yace "Toh daga yau ka sake shigo min nan da wannan maganar i am promising u i won't take it likely with you..... Nace baxan bayar ba kuma i mean it" da mamaki Khalil yace "But why? I have all right to ask Abba" cike da damuwa Mami tace "Me yasa idan na maka magana baka ji Khalil? Me yasa kake daukan maganata for granted pls" Khalil ya mike yana jin ransa na ɓaci yace "Mami to saboda me za a rike min abubuwana akan laifin da ban aikata ba? Akan something i knew nothing about, why???" Aunty Hassana ta bude baki tace "Akan laifin da baka aikata ba? Ehh lallai ka cika mara kunya kuma fitsararre, Sannan da ka mike a zabure haka dukan uban naka za kayi ko yaya?" A fusace yace "Kee ni ban sa bakinki ba Hajiya, babu ruwanki da issue dina da mahaifina, stay in ur lane and stay out of family issues da bai shafe ki ba" Aunty Hassana ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da gefen gyalenta tana girgiza kai, sake baki Abba yayi yana kallon Khalil, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon fuuu, Mami dai ta ma rasa abun cewa, wato khalil baxai ta6a canzawa ba kenan, Abba ya hau kai komo a parlon fuskarsa a murtuke, cike da karfin hali Mami na kallon Aunty Hassana tace "Kiyi hakuri Hassana zan je in...." Wani tsawa ta daka ma Mami tace "Bana bukata, duk ba ke ke sa shi yake raina mu ba, kiri kiri yaron nan ya daina gaishe da ni da Amina a gidan nan, yaron da a haife na haifesa, yanzu kuma rashin kunyar tasa da fitsara har ya kai kan ubansa, kayi laifi amma kafi kowa bakin magana, miliyan dari takwas wasa ne yanzu? An daga maka kafa albarkacin tausasa yaya da muke tayi ka dawo gida amma kace mune makiyanka? Yanzu da nawa ɗan nan zai yarda da abinda khalil yayi min yanzu? Ba tashin hankali xa ayi ba kenan??" Abba yace "Ki bar zancen nan, i know how to handle it, ke Fatima yarinyar da kika kawo gidan nan without my knowledge wacece? Kuma daga ina take??" Mami ta kallesa da mamaki, sai kuma tace "Sauran yaran da ake kawowa gidan nan su karaci zamansu su wuce ka ta6a tambayar daga inda suke ko wa ya kawosu Yallabai? Yaran da har kudin makaranta kai ke biya masu sai wannan da ko biyar dinka babu a makarantar da aka biya mata?" Hassana ta mike a fusace tace "Kar ki kuskura kice zaki masa magana yanda kika ga dama a gabana Fatima, ke kiyi ɗan ki yayi, to baku isa ba, kuma wallahi baxan dauka ba don kiji in gaya maki" Mami ta daga kai tana kallonta, can ta kalli Abba tace "To er ɗan uwana ne, kuma karatu ya kawota gidan...." Mami na fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Aunty Hassana tace "Toh wa yaki zamanta a gidan nan dama? Abinda Allah kadai yasan ladan ciyar da ɗan mutum, ai mu bamu ki tayi ta zama har abada ba ma, kawai damuwar mu kamar yanda na gaya maka Yaya, kwanaki can wani videon yarinya tsirara na ta yawo a kafofin sada zumunta, to ita ce yarinyar" Abba na kallonta da kyau yace "Ke kin tabbata Hassana?" Aunty Hassana tace "Zan maka karya ne yaya? Wallahi ita ce yara duk sun shaida mu ma kuma mun shaida, babu amfanin nuna video din ne yanzu da sai in nuna maka, sannan tun da yarinyar ta zo gidan nan bata gaida mu, sai dai mu wuce ta wuce saboda ta isa" Abba ya dinga zaga parlon yana nazari bai dai ce komai ba, ran Aunty Hassana yayi fari tass don duk hanyar da zata kuntata ma Mami nemansa take ido rufe.....

Mumy ce ta shigo bangaren Umma ta sameta a parlor tare da Kamila, Mumy tace "Dama kina gidan nan Kamila?" Da sauri Umma ta amshe tace "Daxu ta zo, yanzu ma mijin take jira wai" Mumy tace "Ohk, dama tambayarki zanyi kinji daga Nihal kuwa? Tun jiya bana samunta a waya wallahi" Da damuwa Umma tace "Yanzu ma abinda muke jajantawa kenan, har na gaji da kiran wayartata wallahi, na kira farooq yace min yana Abuja amma gobe zai shiga kaduna sai ya karasa Zaria yaga ko lafiya" Mumy tace "Toh duk yanda aka yi sace mata wayar aka yi" Kamila tace "Nima abinda nace kenan, amma Umma duk ta daga hankalinta, babu tantama an dauke wayar ne" Umma tace "Sai ta rasa wayar da xata kira mu da shi a kawayenta tace an dauke mata waya?" Mumy tace "In sha Allahu lafiya lau take" Umma tace "Toh Allah ya sa" Juyawa Mumy tayi ta fita daga parlon, Kamila tace "Ke abu indai ya shafi Nihal duk ki daga hankalinki ki daga na wasu, ni gashi na kawo maki damuwata ko bin ta kaina baki yi ba sai korata kike in bar gidan nan tun jiya" ko kulata Umma bata yi ba ta mike ta fita daga parlon.

TWINS NEEE... BIYU TA FI DAYA

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post