*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 14
"Daddy" ta fada da siririyar muryarta da zazzabi ya jigata ta qara laushi ainun,Hannuwansa yaji ta kama ta riqe tsam,sai ya waiwayo ya kama hannuwan nata ya sanya cikin nashi,idanunsa suna canza launi saboda bacin rai da damuwa,ya miqa hannunsa zuwa gefen wuyanta don sake jin adadin zazzabin,har yanzu dai kamar dazun
"Am sorry angel,yanzu likita zaizo ya dubaki,zaki samu sauqi in sha Allah" da ido kawai take binsa,ya durqusa a tausashe yayi kissing bayan hannunta yana sake riqe hannun nata da kyau,yanajin kamar ya maidata cikinsa. Qararrawar falo ce tayi qara dai dai sanda wayarsa tayi qara itama,ya fara duba kiran
"Ku shiga dashi waiting room" ya fada a taqaice,sannan ya zare bluetooth din kunnen nasa ya ajjiye,ya sunkuya ya sake daukan fadeelan suka fita.
Qaramin clinic ne da ya kasance mallakin gidan,wanda ke dauke da dakin magunguna,dakin jinya guda biyu da gadajensu,da daki guda na gwaje gwaje da sauran ayyuka wato mini laboratory,kusan duk wani qaramin ciwo da zai samu iyalin gidan a nan ake dubasu bisa jagorancin likitan gidan wato Dr anwar ko kuma Dr raheema. Dukkan wasu kayan amfani da suka shafi magunguna na clinic din ana yawan dubasu da sabuntasu qarqashin jagorancin likitan amana Dr anwar bisa kulawa da kuma qwarewa,zallar karamcin MT jarma ya shafe idanunsa,ya kuma bashi dukkan wani matsayi da martabawar da baya iya tsallake kiransa shi da dr raheema kowanne irin aiki sukeyi,matuqar bai wuce gaban tasu buqatar ba.
Cikin lokaci qanqani ya gama checking dinta,ya soma hada allurai zaiyi mata
"Yanzu yanzu zazzabin zai sauka in sha Allah,ba wani ciwo bane me zafi,don't bother sir" a nutse ya gyada kansa,dukka idanunsa da damuwarsa suna kanta.
Mutsu mutsu ta fara yi,qaramin murmushin da bai shirya zuwansa ba ya kufce masa,yasan anzo gurin dama,muddin idanunta suka qyalla akan allura to yanzu zata daga hankalin kowa,a tausashe ya matsa kusa da ita,ya dagata cak ya sanyata a jikinsa,ya dora hannunsa saman lallausan gashinta yana shafawa a hankali
"Relax angel..... relax,bazaiyi miki da zafi ba" ya fada yana tausasa muryarsa sosai,saita tsaya cak din,ta runtse idanu tana jin shigar allurar a jikinta,ta kuwa matseshi gam har aka gama.
Da kansa ya isa dining room bayan zazzabin ya saukar mata,ya dudduba abinda cook dinsa ya dafa,ya zari plate ya debo dai dai iyakar abinda yasan tanaci.
Cikin tsantsar kulawa ya zauna ya dinga diban abincin da spoon yana bata,yana yi yana janye tab din hannunta,don daga saukar zazzabin har ta yiwa game dirar mikiya,tana masifar qaunar game,babu abinda yake bata nishadi kamar ita,idan ta kalleshi ta tabe baki zata sa masa kuka saiya kada mata yatsansa alamun a'ah. Yafi fahimtarta fiye da mahaifiyar data haifeta,ya gama haddace duk wani abu data fiso da wanda bai dameta ba,harma da wanda bataso,sai daya tabbatar ta qoshi sannan ya barta,ya miqa mata tab din yace mata zaije yayi wanka,ta gyada kai ta kuma waving masa hannayenta alamun bye
"See you soon dad" qaramin murmushi ya fita a fuskarsa,ya kada mata nasa hannayen,sannan ya juya a hankali ya wuce bedroom dinsa,hankalinsa da tunaninsa yana kanta.
Kayan jikinsa ya fara ragewa,yanayi yana kokawa da tunaninsa,hutu yake da buqata a yanzu,bawai tuna wasu tarkacen abubuwa marasa muhimmanci ba,tunasun da bazai haifar masa da komai ba sai zallar bacin da kwana cikin damuwa,damuwar da a wannan yanayin da al'amura suka cushe masa abubuwa sukayi masa yawa bashi da buqatarta,gobe ranar hutunsa ce,yana da buqatar ya wuni tare da ita,ya debe mata kewar data jima tanayi tasa. Babban towel fari qal ya daura iya qugunsa,faffadan qirjinsa dake cike da gargasa da murdaddun damtsensa ya bayyana sosai.
*M O N D A Y*
Tun qarfe biyar na asuba data kammala salla tana saman abun sallarta,koda ta gama azkar dinma saita samu kanta da sanyin jiki da kuma sanyin gwiwar kasa tashi tabar wajen,don haka ta buda qur'ani tayi tilawar wasu shafuka daga ciki sannan ta maida ta rufe. Agogo ta kalla,har yanzu akwai sauran lokaci kafin fitarta,sai ta jawo wayarta ta kunnata daga kashetan da tayi. Har yanzu cikin jikinta tana jin wani yanayi mara dadi,wanda duka baya rasa nasaba da fara fitarta aiki.
Saqon barka da asuba daga wajen mahmud gana ta fara cin karo,ko da wasa bata taba gwada saving number dinsa cikin wayarta ba,to amma yadda yaketa binbininta,da yawan cikata da yakeyi da saqonni safe rana dare yasa ta fara shaida number din tasa a idanu. Qaramin tsaki taja,bata koda bari ta buda saqon taga cikakken abinda ya qunsa ba ta shareshi daga wayar tata gaba daya,kusan hakance take faruwa dama,duk sanda saqonsa ya shigo wayarta bata tsaiwa dubawa bare ta karanta,ta riga ta quna daga lamarin maza,batajin akwai wani abu nasu guda daya da zai burgeta,dukkansu a wajenta tamkar hankaka suke,gabansu fari bayansu baqi,kamar hawainiya dake iya canza ainihin launinta zuwa dukka launin da takeso,babu wani abu daga garesu da yayi saura wanda zai dauki hankalinta ko yaja ra'ayinta,tafi ganewa ita dasu din ya zamana kowa yana daga nesa yana sabgarshi.
K'arfe takwas saura ta fito a wanka,tadan makara kadan saboda wani littafi data soma dubawa wanda ya dauki hankalinta har taso gota lokaci,babban towel ne daure ajikinta daya bayyana fararen fatar dake qirjinta zuwa bayanta da kuma sambala sambalan hannayenta. Gaban madubi ta tsaya tana tsane jikinta da towel,sannan ta saka hannu ta zare shower cap din dake kanta,take gashin kanta ya warwatsu a kafada da kuma gadon bayanta,ta ajjiye towel din,ta jawo wata qawatacciyat stool ta zauna a kai,sannan ta jawo cream dinta ta fara shafawa. Batayi nisa da shafan man ba kiran afifa ya shigo,wanda shi ya qara mata nauyin shiryawar,sai data cinye kusan awa guda sannan ta kammala komai.
Ta fito d'as cikin wani atamfa me asalin tsada da taushi,wadda ta yane atamfar da wata tsadajjiyar laffaya ruwan golden yellow da brown,kalolin da suka hadu sukayi masifar fidda kyanta.
Kanta irin daurin nan da ake kira zahra buhari ne,wanda ya baiwa gashinta data nannade damar fitowa ta qasa,tsadadden agogon rolex ne a hannunta da wani sisirin zobe me qananun fararen duwatsu masu walwali,ta zura fararen qafafunta cikin wani lafiyayyen takalmi me matsakaicin tudu qirar kamfanin gucci mahadin qaramar handbag dinta. Bata wani tsaya batawa kanta lokaci wai ta duba komai yayi perfectly fine ba ta fesa lallausan turarenta ta dauki wayarta ta fito.
Kamar ko yaushe muddin bawai baqi ne dasu ba falon gidan nasu shuru yake,ta duba agogon hannunta taga dai dai yake aiki da na falon,saita maida dubanta ga dining dinsu. Dan qaramin murmushi ta saki,baaba rabi kenan,komai ta shiryashi cif,saboda tasan yau zata fara fita aiki,duk da cewa tasan ita ba ma'abociyar cin abinci bace koda rana tayi ma sosai bare yanzu da sassafiyar nan,don ko tara na safe batayi ba.
Tana shirin bullawa sassan maama,idan bata sameta ba ta qarasawa wajen abba don tasan bata wuce can saiga baaba rabi
"Allahu akhbar kabiran,dawisu gwanar ado,ummin abba uwar masu gidan,wannan kyau wannan kyau,hohoho" ba kasafai takeson wannan kodatan da baaba rabi takeyi ba,to amma ya zamewa baba rabin sara da dabi'a yabi jikinta,uwa uba kuma suna martabata saboda dadewarta dasu,suna bata wani girma na musamman
"Barka da warhaka baaba"
"Barka kadai uwarmu,an fito kenan,to ubangiji yasa a fara a sa'a,ya kauda dukkan abunqi,ya kuma kade fitina"
"Ameeen ya hayyu ya qayyumu,maama fa?" Ta tambayeta har cikin zuciyarta tana jin dadin addu'ar da tayi mata
"Ta shiga wajen alhaji" saita juya a nutse tana nufar can.
Sai data tsaya ta ware igiyar takalminta a nutse tayi sallama ta shiga falon. Dattijon da fuskarsa me cike da kamala da kwarjini yana zaune cikin couch,hannunsa riqe da takardun qur'ani da yake zuwa pieces. A gefe ya ajiiye qur'anin cikin martabawa,ya daga kai yana dubanta tare da amsa sallamar tata,qaramin murmushi na fita saman fuskarsa,can qasan zuciyarsa kuma cike yake da fata,fata da buri me tarin yawa akan rayuwarta gaba daya.
Daf da qafafunsa tazo ta rusuna har qasa
"Barka da safiya abba" gyara zamansa yayi yana dubanta
"Barka kadai ummin abba,an tashi lpy?"
"Alhamdulillah abba ya qarfin jiki?"
"Muna godewa Allah"
"Allah ya qara lafiya da nisan kwana me amfani"
"Ameen don nabiyyur rahmati,an fito aikin kenan?" Kai ta gyada a sanyaye
"Eh abba"
"To Allah yasa a fara a sa'a,yasa ya zamewa dukiyarki da lahirarki alkhairi,ki kare mutuncin kanki da kyau,don ke din ba yarinya bace qanqanuwa,duk da bani da haufi akan tarbiyyarki,amma dan adam saida tunasarwa da nuni,ki tsare gaskiya da amana,ki riqe aikinki da muhimmanci sai Allah ya dafa miki"
"In sha Allah abba,na gode Allah ya qara girma" kafin wani a cikinsu yace wani abu an turo qofar falon an shigo,maama ce da afifa da alama wani saqon ta kawo mata suke magana akai. Tayi mamaki da taga afifa din,ta dauka da wasa take mata sanda tace ita zata zo da kanta ta kaita office a ranarta ta farko,ta duqa gaban maama suka gaisa,al'adarta ce ba kasafai take iya gaida babba a tsaye ba,musamman mahaifanta,saita juya ga afifa daketa kallonta,bakinta fal da magana,idanun su abba ne kawai ya hanata cewa komai,har zuwa sansa suka fito.
Bayan sunyi addu'a sun shiga sabuwar motar sãahar din saita waiwaya tana dubanta
"Bestie,kinga kyan da kikayi?,don Allah ki sassauta,karkije ki dinga hada ma'aikata fada a kanki" sosai sãahar ta tsuke fuska,saita sauke madubin gaban motar tana kallon kanta. Tabbas tayi kyau qwarai,komai data saka ajikinta ya haskata sosai,sai kawai ta sanya hannu zata balle murfin motar. Da sauri afifa ta tayar da motar tana dariya,saboda ta gama karantar abinda take da nufin yi
"Kome zakiyi,ke koda kashi zaki shafawa jikinki hakan bazai hanaki yin kyau ba sayyada" harara ta watsa mata
"Kinzo ne to spoiling my whole day afifa da maganganunki?" Ta fada manyan idanunta dake kan afifa kamar zasu fado. Kai ta girgiza tana dariya
"Ni na isa?,kefa yanzu amanar mahmud ce a wajena" fuska ta tsuke sosai tana kallonta
"Waye mahmud?,amanar me?"
"Ba zaki gane ba,amma dole na kula dake don amana ba wasa bace" ranta ya sosu sosai,saidai afifa tafi gaban haka
"Wai kasuwanci na kika fara afifa?" Dariya sosai afifa ta qyalqyale dashi har tana dan duqawa ga sitiyarin motar
"Idan ma shi na fara aiba laifi bane,tunda hankalinki yaqi dawowa gangar jikinki har yanzu" rasa me zatace da afifa tayi,sai kawai ta dauke kanta ta maida gefe tana kallon hanyoyin da suke wucewa,hanyoyin kano da safe wandada suke da qarancin kai kawo na jama'a,maganar duniya afifa tayi mata amma 'yan miskilancin sun motsa,taqi koda waiwayowa bare ta tanka mata.
*************
Kamar ko yaushe daya bayan daya motocin masu kama daya suke kutsawa kan titin da zai sadasu da katafaren kamfanin MT GLOBAL COMPANY,duk da cewa cikin combo suke,amma mota guda dayaa a ciki ta fita zakka,mercedes maybach s580 sand color dake masifar daukan hankulan jama'a duk inda ta gifta.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥