Nihaad page 69

Nihaad page 69

 

Nihaad page 69

💖💖 NIHAAD 💖💖

69

Tun daga nesa Khalil ke kallonta har ta karaso ta ajiye masa tray din hannunta me dauke da drink da glass cup sannan ta zauna tana danna wayarta, bayan few seconds yace "Nadeeyah" Ta daga ido ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Do u have anything in mind that u are hiding away from me?" Tace "Iike?" Yace "You act strange this days, i don't understand u anymore" Tace "Really?" Yayi shiru yana kallonta, ta karyar da kai tace "I am not acting strange, kawai dai ina baku enough space da ku ke bukata ne da kai da matarka" a hankali yace "But ai kema matata ce to be...." dariya kawai tayi bata ce masa komai ba, sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, yace "Nadeeyah" Ta daga kai ta kallesa, yace "Seriously bana jin dadin abinda kike min, you are making me feel kamar i am wronging u without me knowing" Ita dai kallonsa kawai take, can tayi murmushi tace "Ohk sai yanzu ka gane hakan?" Yayi kasa da murya yace "But how? Ta yaya nake wronging din ki?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta bata dai ce masa komai ba, yace "Don Allah kiyi min magana" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "You should have told me to move on Kjay, da baka ci gaba da ɓata min lokaci ba kana ce min in jira ka, you wasted my time for 4 years, i neva double dated because of u, da kayi aurenka da tun sannan ka gaya min in ci gaba da rayuwata...." Ya dakatar da ita yace "Haba Nadeeyah, why are u saying all this pls, how many times do i have to explain things to you, wallahi wallahi ban je gidansu da niyyar aurenta ba, hasalima ni bn santa in person ba naje gidansu, hadin mahaifinta ne aurenmu and i can't say no to him, kawai Allah ya kaddara aurena da ita ne, i neva bargained for it" Cikin kuka tace "Yanzu ai da son ranka kake zaune da ita, kuma kana sonta fiye da yanda kai kanka kake tunani yanzu, saboda son nata da gudun bacin ranta yasa kayi kamar baka gan ni ba a airport ai" Ya buda baki yana kallonta da mamaki, can ya kwantar da murya yace "Amma fa kinsan ke na fara so Nadeeyah, kuma har a yanzu ina sonki fiye da tunanin ki, babu abinda ya ragu a son da nake maki, don Allah ki cire Nihad a ranki Nadeeyah, you are my first love and u will remain my first love, and kowa yana da matsayinsa a zuciya ta" Ita dai kuka kawai take, ya dafe kansa don shi baya son wannan kukan nata, can ya dago yana kallonta yace "If Nihad is just ur problem now shikenan ke zaki zauna a nan Abuja ita kuma ta zauna either in kaduna or Kano, kinga babu ta inda za ku fara ganin juna, is that okay by u?" Ta goge idonta tana kallonsa, yace "No say something, idan da yanda kike son ayi sai ki gaya min" A hankali tace "I am not to tell u what to do Kjay, and i will neva do that, kawai dai ni nasan i have no bad intention against her, and i am trying my best to be friends with her amma she is taking me for a foe, tun asali dama bata so na, even before i know she is ur wife" Ya girgiza kai da sauri yace "Aa it's not that bata sonki Nadeeyah, kawai dai she is a kind of person da bata sakin jiki lokaci daya da mutum, tana dadewa bata saba da mutum ba, that is just it" Ɗan murmushi Nadeeyah tayi tace "No, ba haka bane, tana min kallon kishiyarta, ni kuma bana mata wannan kallon har cikin raina, duk da we were together before u met her, amma ni ban ji haushinta don ta aureka ba, i have nothing against her" Yace "I will talk to her about that i promise, gradually nasan zata saki jiki da ke in sha Allah" Murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba, yace "Ni nasan baki da matsala Nadeeyah, u are a good girl kamar yanda na san ki a ko da yaushe...." Wayarsa dake ajiye ne ya fara ring, ya dauka yana duba me kiran nasa, ganin Nihal ce ya daga ya kai kunne, ya amsa sallaman da tayi masa jin yanayinta yace "Are you okay?" Daga daya bangaren tace "Alhamdulillah, ya Nihad?" Ya ɗan yi shiru jin kamar her voice is shaking yace "Hope everything is fine Nihal?" Tace "Lafiya lau, ina son zan maka magana ne...." Yace "Oh ok, zan kira ki zuwa dare don bana gida yanzu" jin tayi shiru yace "Hello" Sai kuma tace "Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka ta katse wayar, Nadeeyah dai sai kallonsa take, Yace "Hope everything is settled now dear?" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "Can we go out for shopping?"

Karfe shidda na ranan Nihal na kwance dakin Nihad don Umma ta hanata zuwa dakinta yanzu, zazzaɓi ne me karfi ya rufeta, tun dawowarta daga waje Raliya bayan la'asar take kwance dakin nata, da Umma ta shigo ta tambayeta result din makaranta sai ce mata tayi ai ba a saki nasu ba, duk da tana jin zazzabin tun a lokacin amma bata nuna ma Umma ba, kawai ce mata tayi bacci zata yi, Umma ta fita ta bar mata dakin shine take ta kwance, Mumy ce ta shigo dakin ganin tun dazu bata ga ta fito parlor ba, ta cire duvet din da ta kulle jikinta tace "Nihal jikin ne..." Shiru Mumy tayi jin yanda jikinta yayi zafi qau, gashi sae rawan sanyi take, Mumy tace "Ke dae baki jin magana Nihal, tun yaushe ake bin ki aje asibiti kin ki?" Nihal dae bata ce komai ba, Mumy ta dauko mata Hijab dinta tace "Sa mu tafi asibitin yanzu" Lokaci daya hawaye ya kawo Idonta tace "Ban son zuwa asibitin Mumy" Umma ce ta shigo dakin ita ma jin shiru shiru Nihal bata fito ba, Ganin Mumy tsaye kanta ta karasa da sauri tace "Menene, zazzabin ne ya dawo?" Mumy tace "Ehh shi ne nace ta tashi mu je asibiti" Umma ta kwace hijab din Nihal a hannunta ta saka mata ta kamo hannunta tace "Sauko in kai ki asibiti" Mumy dae ta koma gefe tana kallonsu, hawaye kawai Nihal take Umma ta dagata daga kan gadon, da kyar tace "Umma amai nake ji" Umma tace "Kin san yanda Malaria ke maki kika bar sauro suka cije ki a makaranta Nihal" Nihal ta nufi banɗaki da sauri tana ganin jiri, nan ta dinga yunkurin aman amma yaki tahowa don babu abinda ta ci, juyawa Mumy tayi ta fita ta koma bangarenta. Umma ta saka ta gaba suka fita compound, ta kwalo ma Iliya dreba kira ya taho ya bude masu motar bayan sun shiga, yayi hanyar asibiti da su, a hanya Umma ta ciro wayarta a jaka tayi dialing number Abba, yana fara ring taji gabanta ya fadi don tun bayan da ya saketa sai yau tayi dialing number sa, Ba a dau lokaci ba ya daga yace "Ina jin ki" Zuciyarta na bugawa, murya can kasa tace "Dama Nihal ce bata da lafiya mun tafi asibiti yanzu, saboda yanayin jikin nata ban san ko za su ce za a kwantar da ita ba shiyasa nace in kira in gaya maka" Yace "Tun yaushe take rashin lafiyar?" Umma ta gyara zama cikin sanyin murya tace "Tana tayi a tsattsaye wllh, sai yau ne yayi tsanani, tun dai da ta dawo makaranta bata jin dadi gaskiya" Abba yace "Allah ya sauwake, idan kun je asibitin duk abinda ake ciki a gaya min" Umma tace "Toh in sha Allah, nagode" Katse wayar yayi, taji hankalinta ya ɗan kwanta tun bayan da ya saketa, idan ko haka ne ai zata dinga son irin cases din nan su dinga faruwa yanda za su dinga ko da magana ce ta waya da shi, kilan ta hakan sai Allah ya daidaita su ya hakura har ya maida ta.... Har suka isa asibitin Nihal kuka take, tun Umma na tunanin zafin ciwo ne har dai da taga irin kukan da take tace "Ke kukan lafiya kike yi haka kuwa? Meye haka??" Nihal dai bata iya tace komai ba bata kuma fasa kukan da take ba, she wish kafin su shiga asibitin Allah zai dauki ranta kawai, a haka har Umma ta sa ta sauko daga motar tana rike da hannunta suka shiga cikin asibitin, da yake asibitin da suka saba zuwa ne kati kawai Umma ta bada suka biya kudin ganin likita, suna zaune reception wata nurse ta sanar masu turn dinsu ne na ganin Dr, Umma ta mike tana rike da hannun Nihal tace "Kiyi ta yin abu kamar ba mace ba Nihal, ni dai ki kama jiki mu shiga office din" ko rufe baki bata yi ba taga yarinya ta sulale kafin ta kai kasa tayi saurin kamota tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nurses din suka taso da sauri, nan aka yi emergency ward da ita aka tafi kiran likita, Hankalin Umma yayi mugun tashi ta dinga salati tana zaga reception din, Patient din wajen sai cewa suke ta kwantar da hankalinta Allah zai bata lafiya, jakarta da ta bari kan kujera wata mata ta dauka ta kai mata tace "Ana ta kiranki a waya Hajiya" Umma ta amsa da sauri, ta bude jakar ta ciro wayar taga Abba ne ke kiranta, daga kiran tayi ta fashe da kuka tace "Yallabai muna shigowa reception din asibitin ta suma yanzu haka an shiga da ita emergency ward" Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, bari in taho yanzu dama ina hanya" Daga haka ya katse wayar, Umma ta mayar cikin jakan ta zauna tana share hawayen idonta.... Bayan kusan minti arba'in wani likita ya fito yana kallon Umma yace "Hajiya mu je office" Umma ta mike da sauri ta bi bayansa zuwa office dinsa, Zaunawa tayi kujeran dake gaban table dinsa tana kallonsa, ya gama kauda files din table din sannan ya kalleta, hankali tashi tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Alhamdulillah, ina mijinta?" Umma tayi kasake tana kallonsa sai kuma tace "Miji kuma?? Budurwa ce fa Dr, bata yi aure ba, Ni mahaifiyarta ce kuma ni na kawota" Likitan ya dinga kallon Umma, can yace "Kuma er cikinki?" Umma tace "Kwarai kuwa, second to the last born dita ce, ta gama final exams dinta a Ahmadu Bello University ta dawo gida shine take ta zazzabi sama sama, to dama idan sauro ya cije ta gaskiya tana wahala haka, nafi tunanin fita karatun daren da take ne yasa ta kwaso malarian" Likitan ya girgiza kai yace "I am sorry to say Madam, mun gano tana dauke da ciki wata biyu da sati biyu" Still Umma tayi tana kallon bakin likitan kamar yare yake mata ba Hausa ba, Likitan ya girgiza kai ya ajiye mata takardan test din yace "She is 2months 2 weeks pregnant" zumbur Umma ta mike jin pregnant, tana kallonsa bakinta na rawa tana zaro ido kamar zasu tuttulo waje tace "Meye kuma pregnant likita nace maka budurwa ce, ko dai result din wata ka kawo min, meye haka kake gaya min don Allah, bata taba aure ba fa, ta yaya zaka gaya min haka kamar kana shaye shaye?" Ya dau takardan da ya ajiye mata ya mika mata yana kallonta yace "Ga test result din Hajiya" lokaci daya Umma taji wani azababben jiri ya ziyarceta, kan kace me taga office din ya fara juya mata, sai taga ko ina ya koma bakikirin, kafin likitan ya taso ya yo kanta ji kake timmm a kasa ta kara buga goshi dai dai inda bai gama warkewa ba a tiles din office din sai ga jini kamar an buda pampo, Likitan ya fita ya kira nurse biyu... Wani dakin daban aka kwantar da Umma da har bayan minti ashirin bata farfado ba, sai tsarkewa numfashinta yake kamar zai dauke har sai da aka saka mata oxygen, ga wani bandage da aka tula mata a goshi inda ya kara fashewa, likitocin suka ji tausayinta sosai bayan likitan da ya sanar mata Nihal na dauke da ciki ya gaya masu duk yanda aka yi a office dinsa, duk suka dinga Allah wadaran Nihal. Tun shigowar Abba asibitin yake kiran wayar Umma bata dagawa, hakan yasa ya kashe motarsa kawai ya shiga cikin asibitin, bayan sun gaisa da nurses din yace "An kawo wata mara lafiya yanzu, tare da Baabarta suka zo...." Wata nurse da ta ganesa don in dai Nihad bata da lafiya shekarun baya yawanci shi ke kai ta asibiti, kuma duk tunaninta ma Nihad ce aka kawo yanzu, Nurse din sai duk jikinta yayi sanyi tace "Ina zuwa sir" Wajen likitan da yayi attending ma Umma ta tafi ta sanar masa ga mai gidan Umma ya zo, yace tayi masa iso zuwa office dinsa, Nurse din ta kai Abba har office din likitan, Abba ya zauna yana kallon likitan bayan sun gaisa yace "Jikin nata yayi critical ne haka? I need to see her first pls" Likitan yace "It's okay sir, daughter dinka ce ko?" Abba yace "Sure, she is my daughter" Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "I am sorry to say sir, mun gano er ka na dauke da cikin wata biyu da sati biyu" Abba ya dinga kallonsa babu ko kiftawa as if trying to apprehend what he just said, Likitan ya ajiye masa result din yana kallonsa, Abba ya sauke idonsa kasa, the Dr can see tension and shock written all over him, Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "Kar ka daga hankalinka Alhaji, it shall be well in sha Allah, daga hankali da mahaifiyarta tayi ya janyo tayi pass out dazu, yanzu haka ita ma tana kwance ba a kuma jima da cire mata oxygen ba, kuma jininta ya hau, don haka kayi hakuri ka dauki dangana, ka kuma kula da matarka har Allah ya bata lafiyarta, yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba, sae dae a bi su da addu'ar shiriya kawai" Duk wannan abinda yake fada Abba bai ma san me yake cewa ba, Likitan ya mika masa bill din yace "This is the bill sir, in kuma tare kake da dreba yayi kokari ya maida ka gida Alhaji, you need to relax and accept this with good faith" Abba ya mike yace "It's okay, it's okay" Kudi masu yawa ya ciro aljihunsa ya ajiye kan table din likitan ya juya, Maimakon yayi hanyar kofar fita, sai yayi hanyar bandakin likitan, Likitan yace "Ga kofar can Alhaji, don Allah ka kwantar da hankalinka saboda shekarun ka" Da sauri Abba ya nufi kofar fita bai dai ce ma likitan komai ba har ya fita ko rufe office din bai yi ba, likitan ya ga ya bi right maimakon left, Likitan ya girgiza kai with pity, suna samun ire iren cases din nan sosai, but ya za ayi? Sai dai kawai Allah ya kyauta ya shirya yan baya. Wata nurse ce tsaye kan Umma tana duba ko jininta ya dawo dai dai amma taga har yanzu 180 ne, Umma ta bude Idonta da yayi mata nauyi da kyar tana kallon nurse din ta cafko hannunta tana harhade magana tace "Nurse a ina ake cire ciki a garin nan? Ko kuna cirewa a nan??" Nurse din ta girgiza kai tace "Ba a cire ciki a asibitin nan Hajiya" Umma tayi karfin halin mikewa zaune cikin rawan murya tace "Don Allah gaya min inda kika san ana cire ciki, don Allah ba don ni ba, ki rufa min asiri ki gaya min er nan" Nurse din tace "Hajiya ban san asibitin da ake cire ciki ba gaskiya, nima sabuwa ce a nan" Umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace, komai ya tabarbare min ni Sumayya, wayyo Allah na" Nurse din dai sai kallonta take, Umma ta fizge ruwan hannunta ta sauka daga kan gadon tana share hawayenta da sauri tace "Ina jakata, ina aka kai jakata" Nurse din ta nuna mata, Umma ta dauka da sauri da nufin ciro waya ta kira Abba tace masa an sallamesu ba sai ya karaso ba, ko ina na jikinta rawa yake ga wani ciwo da zuciyarta yake, sai hada zufa take ta ciro wayarta taga miss calls din Abba har biyu, da sauri tayi dialing kiran, yayi ring har ya katse bai dauka ba, ta kara kira nan ma har ya katse no response, Nurse din dai ta juya ta fita tana girgiza kai, Umma ta sauka daga kan gadon tayi zaman dirshan a kasa tana kuka kamar ranta zai fita tace "Allah na tuba ka yafe ni, Allah na tuba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace duniya tayi min zafi, na shiga uku ni Sumayya" Sai kuma ta mike kamar mahaukaciya ta figi jakarta ta fice daga ward din, Nurses din ta sama a reception jikinta na rawa tace "Tana ina?" Duk suka tsaya kallonta, wata nurse ce ta kai ta ward din da Nihal take, zaune take ta hada kanta da gwiwanta tana kuka kamar ranta zai fita, tun dazu take kukan amma daga nurses har Doctors din babu wanda yace tayi shiru ko tayi hakuri, gaba dayansu ma haushinta suke ji, Umma ta fashe da matsanancin kuka ta jingina da bango tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Nihal dai ta kasa dago kanta, har shidewa take saboda kuka, Umma tayi kukan har sai da taji ba dadi sannan ta nufeta tace "Allah ya isa tsakanina dake Nihal, sakayyar da zaki min kenan duk so da kaunar da na nuna maki cikin 'ya yana? Da cikin shege zaki biyani? Me na maki zaki min haka Nihal?" Nihal dai bata dago kanta ba sai kuka kawai, Umma ta goge idonta da sauri tunawa da tayi Abba zai iya karasowa yanzu, Da kyar tace "Sauka mu tafi, munafuka matsiyaciya, Allah ya isa tsakanina dake wllh, sauko daga kan gadon nan" Nihal ta sauko daga saman gadon tana kuka sosai, Haka Umma ta tasa ta a gaba suka fice daga asibitin ita gaba daya tama manta ana biyan wani abu wai kudin asibiti, bata ga iliya a haraban asibitin ba duk da tace ya jira su, bata damu da hakan ba don hankalinta baya jikinta, a haka har suka isa titi Umma na can gaba tana rusa kuka, Nihal na biye da ita a baya, suka samu adaidaita a haka har suka isa gida, Kafin su karasa gate din gidan Umma ta goge hawayenta ta sa adaidaitan ya saukesu ta basa kudinsa, Nihal dai na tsaye tana jin dama kawai a dau ranta a wajen, Umma na kallonta da kyau tace "Don kaza kazanki ko wani tambaya aka maki kice Malaria ne an maki allura gobe kuma za mu koma asibitin da safe" Ita dai Nihal bata ce komai ba hawaye ne me zafi ke sauka idonta, a haka suka shiga gidan.... 

Khalil na zaune bayan isha wayarsa na kare kunnensa yana magana da Mami, yana son tambayarta Nihad amma ya kasa, gashi ita ma bata ce masa ga ta ba duk da ko minti biyu basu yi suna wayar ba, Can dai yayi karfin halin cewa "Mami ya me jikin?" Mami tace "Da sauki, gobe za mu taho in sha Allah...." A hankali yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Ameen, sai anjima" Daga haka ta katse wayar, ya dinga kallon screen din, he is missing his wife badly amma ko ɗan gaisawa Mami taki bata wayar su yi tun da suka isa can, Number Nihal yayi dialing for the 3rd time yanzu, don tun bayan magrib yake kiranta bata dagawa, yanzun ma har ya katse bata daga ba, ya ajiye wayar ya fita zuwa parlon Abbansa don yana gidan, don yana son jin yaushe yayi fixing na tafiyarsu Yemen din.... Kallonsa kawai Janar yake yi har ya gama tambayar tasa, can Janar ya sauke glass din idonsa yace "Ka samu wani abokinka ku je, don bani da lokacin zuwa kasar..." Khalil yayi shiru yana kallonsa, Janar yace "Sun ma raina ma mutane hankali, kuma duk inda tsabga ta rainin hankali yake to babu ni a ciki, tun asali me yasa basu kawo wannan zancen ba sai yanzu? So i don't think da wani abu da zai kai ni kasar nan yanzu" Khalil ya sunkuyar da kansa kawai.

 Umma na shiga parlor taga Mumy ta fito daga bangaren Abba, Mumy na kallonsu tace "Ya jikin Nihal" ba tare da Umma ta kalleta ba balle taga idonta tace "Da sauki" Daga haka ta tura Nihal suka yi gaba zuwa ɓangarenta, Mumy dai ta tafi ta zauna parlor har family Dr din wan Abba wato Alhaji Abubakar da ta kira dazu ya iso gidan, ta kai sa har ɓangaren Abba, tana kai sa dakin ta fito ta zauna parlor, ita dai tasan lafiya ya fita yau babu ko alamar ciwon kai amma ya dawo a haka, a zuciyarta kuma tace ikon Allah kenan, bayan kusan minti talatin likitan ya fito, ta mike ta nufesa tana kallonsa tace "Dr ya jikin nasa?" Yace "Dole sai mun je asibiti, jininsa ya hau over" Hankali tashe Mumy tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mumy bata san sanda ta tafi ta dauko Hijab dinta ba a ɓangarenta da sauri.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post