Tabarmar Ƙashi page 26 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 26 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 26 by H U G U M A

*H U G U M A*


*_TABARMAR ƘASHI_*💔

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 27



         Shuru motar ta dauka,sai sanyin ac da qamshin turarensa daya cika motar,ko sau daya bai motsa ba,sai aikin danna wayarsa da yakeyi,har zuwa sanda motar ta motsa tana fita daga cikin company din,cikin wani irin yanayi da ba lallai ka fahimci ma tafiya motar takeyi ba,iya wannan kadai ya isa shaida maka zunzurutun kudin da aka narka kafin a siya motar.


          Wani qaramin sassanyan ringin wayarsa tayi,ya dauke manyan idanunsa daga wayar hannun nasa ya maida ga qaramar wayar dake gefansa,sai ya ajiiye dayar ya daga wancan kiran bayan ya sanya earpiece a kunnensa.


             Tuni ta lumshe idanunta ta hade jikinta tsam a waje daya,duk da tazarar dake tsakaninsu,amma sai takejin kamar idan tayi qwaqwaqwaran motsi jikinta zai taba nasa,kamammiyar muryarsa me wani iri amo dake da taushi da dadin sauraro ce ke fita cikin nutsuwa,har kamar baka tantance abinda yake fada cikin wayar. 


          Bai jima sosai ba ya ajiiye kiran,ba dadewa wani kiran ya sake shigowa,tadan gyara zamanta tana sake jin yadda ta takura a zamanta tare dashi cikin motar,tana son taja tsaki amma karon farko zuciyarta ta tuna mata abinda ya faru da ita dazun sanadin hakan,duk da haka bata haqura ba,cikin zuciyarta tayita mita gami da tura baki gaba,kamar ta bude idonta ta ganta a gida.


             Ringing wayarta ta fara yi,sai a sannan ta bude idanunta,ta zaro wayar daga jaka,afifa ce ke kiranta,wani haushin afifan ya kamata,kamar itace tayi mata laifin,sai tayi rejecting ta dora wayar saman cinyarta.


          Sake kira tayi,amma harta katse bata daga ba,a karo na uku yayi magana cikin izza


"whether you answer your phone call or turn it off, I don't want noise" yayi maganar kamar ba da ita yake ba,don bai kalli inda take zaune ba. Tanason ce masa ya sauketa kawai,amma tana tuna idan ta aikata hakan kamar bata girmama tsohon daya tako da qafafunsa don kawai a bata kulawa ba,sai ta zabi kawai ta shareshi,tayi kamar bata jishi ba.


          Ci gaba da kira afifan tayi,mahmud yana tayata,a qalla sai da suka kira sau bibbiyu,ba zato ba tsammani taji ya saka hannu ya suri wayar dake ajjiye saman jakarta data dora kan cinyoyinta,yayi switching nata off,ya jefota saman wani dan abu me kama da akwati dake a tsakaninsu.


"Wannan shine karo na qarshe da zan gaya miki dole ki dinga yimin biyayya,you must remember that i am your boss"


"And then what?!,zamowana ma'aikaciyarku bawai yana nufin zamana baiwarku bane!"


"What's the difference?,kina aiki ne domin kudi,kina kuma aiki domin a biyaki" murmushin takaici ne ya qwace mata


"You are too proud mr jarma,sannan fahimtarka bata baka dai dai ba,am not one of the women who can lose their dignity saboda kudi ko qyale qyalen duniya,drop me please" ta fadi wani abu na zabalbala daga cikin zuciyarta,tsanarsa na ninkuwa a ranta,tana jin a duniya bayan adam,shine namijin da tafi tsana a rayuwarta"


"you can say whatever you want,but.....babu abinda zai canzaku daga yadda kuke.....and bazan saukeki ba,don baki isa bani umarni ba,amma doing it for the sake of  Dr jarma,umarninsa ne" tamkar ya watsa mata wuta a fuskarta haka taji, hawaye suka cika idanunta fal,to amma batason ya gansu har ya fuskanci rauninta,don ta rantse ta daina gwadawa kowanne d'a namiji rauninta,bare ya samu hanyar takata tare da illata rayuwarta.


          Titi ta zubawa ido tana jin kamar ta balle murfin motar ta fice abinta,to amma kwata kwata komai na motar ba irin wanda ta saba gani bane,tilas taci gaba da rintse idanunta,don bata qaunar ganin koda shatin inuwarsa,idan kuma tace zata ci gaba da bashi amsa,may be ta amsa masa da maganar da zata zunda kimar yaa muhyi a idanunsu,dama familyn Dr mamman girema gaba daya.


            Tana daga cikin motar amma tana iya hangen tsaruwar asibitin da suka shiga,umarni yayi a duba masa likitan da yake on duty,cikin gaggawa da son cika umarni suka fita,yadda baice mata ci kanki ba,haka bata motsa ba,har zuwa sanda suka dawo suka shaida masa


"Dr raheema ce" kai kawai ya gyada musu,ya musu wani sign da batasan na meye ba,sai taga daha driver har security din nasa sun fita daga motar.


           Hannu ya sanya ya dauki suit jacket dinsa ya zura,ya daidaita zamanta a jikinsa,ya danna Lock password na qofofin,suka bada 'yar qara alamun sun bude,ya tura ya zura qafarsa sanann yayi magana a qasaice


"Follow me"


"Allah ya kiyaye na jera da kai" maganar dake qasan zuciyarta kenan,tsananin yadda ya bata mata rai ya kuma cikata maganar ta fito ba tare data shirya ba.


         Cak ya dakata daga nufin fitar da yakeyi,ya maido qafafunsa ciki,ya kuma sake maida lock din ya rufe,maida jikinsa yayi makarin kujerar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,for the first time da wata mace tayi disgracing dinsa,why?,me yasa yarinyar taketa karya masa record?,who is she?,ya qare da tambayar da bashi da amsarta. Banda darajar Dr jarma,banda shi din ubane a gareshi da bai taba saba umarninsa ba,yarinyar sam bata isa ya hada koda hanyar wucewa da ita ba,bare ta samu daman maida masa magana.


         Bluetooth din kunnensa yadan taba da dan yatsansa manuni,sannan yace


"Tell dr raheema to meet me in the car,ina tare da patient" abinda ya fada kenan a taqaice,ya bude tafukan hannayensa yana kalla hadi da murzasu guri daya. Me zaiyi mata wanda zaiyi matuqar bata mata rai?,ya kuma kashe wannan bakin me kama da gidan tsutsa na rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da ita?.


          Knocking glass din akayi,hakan ya tabbatar masa da isowar dr raheema din,qasa yadan sauke glass din,muryarta me cike da fara'a da matuqar kirki tace


"You are welcome sir,kaine yau da kanka?" Ta qarasa maganar tana sauke dubanta akan kyakkyawar balarabiyar fuskar sãahar dake cike da fushi. 


"Yes,please come in" ya fada yana dage glass din window sama ya rufesu ruf kaman dazun.


         Daya daga cikin guard dinne ya shigo,ya juyo ma dr raheema da kujerar gaban sãahar,ta zamana tana facing dinta,ya qara mata fadi da zurfi yadda dr zataji dadin zama.


"Gud evening madam" dr raheema ta fada da fuskarta da bata rabo da murmushi. Idanu sãahar ta daga ta kalleta,saita gaza tankwabar da gaisuwar tata,ta maida mata a taqaice


"good evening dr" abinka da likita,nan da nan ta fahimci ba meson dogon magana bane,don haka ta maida dubanta ga jarma


"Sir,i hope ba wani babban abu bane ya faru ba,naji kace na taho da kayan aikina" gyara zamansa yayi bayan ya cire suit jacket din nasa


"Yes,yau car service zakiyi,ga patient din nan,ta gaya miki damuwarta" daga haka ya maida hankalinsa ga dan qaramin computer din dake maqale da seat din yana ci gaba da duba aikinsa na dazu daya katse.


"Sannu madam,meye damuwar?" Ta sake tambayarta da dakakkiyar fuska. Qafarta ta daga mata,dr raheema ta kalli qafan,sai ta kalleta cikin sauri,abinka da farar fata,fatar wajen tayi jajur


"Sir,me ya samu qafarta hakanan"


"Ask her" ya amsa mata carelessness. Wannan karon batasan sanda ta jefa masa wata muguwar harara ba,tana jin tabbas inda tana da dama sai tayi masa mugun duka. Dr raheema data gani sai murmushi ya qwace mata,abun ya burgeta sosai,har ta kasa yin shuru


"Baka kyauta ba sir......you must show your care and concern,kasan mu mata bamason rashin nuna kulawa"


"Do your job dr.....am in hurry please,banason jira"


"Okay sir"ta fada cikin girmamawa tana ajjiye maganar a gefe.


         Saida tayi mata allurar anti tetanus saboda batasan dame taji ciwon ba,sannan ta bata pain killers,tace kuma zata iya gasa gurin da lukewarm water,sannan ta hada kayan aikin nata ta fito. Tana fita suka dawo,dukka motocin suka dauki saiti suka sake fita a asibitin.


        Ko sau daya bai tambayeta address dinsu ba,tadaiji yana magana a waya,amma zugin da qafarta keyi bai barta taji abinda yake fada bama,daga bisani taji yana basu umarnin yin amfani da map dake jikin motar. Sanda motar ta tsaya data bude idonta sai gata qofar gidansu,ta boye mamakinta ta dauki jakarta cikin kamewa da takatsantsan da qafafunta ta fice daga motar,tana jin kamar an zareta daga cikin tarin qayoyi.


           Afifa dake tsaye jikin motar mahmud ta nufota da hanzari,wanda sam bata lura dasu ba,saboda Allah Allah take ta isa gida ta sake rage kukan dake cin zuciyarta karo na biyu. Gwanar kuka ce sosai,duk wanda ya santa ya santa da wannan dabi'ar,kuka baya mata wuya


"Bestie,lafiya?" Afifa ta fada tana qoqarin riqeta,hannu ta daga mata


"Ki barni don Allah,koma meye ke kika jawomin"


"Da nayi me?, Ta tambayeta cikin mamakin bacin ran data gani a fuskarta


"Mahmud yaje har kamfanin akace boss yasa a kawoki,sai musa ya samu yana gyaran motarki,tare muke dashi tun dazun a nan muna jiran isowarki,ganin kinyi delay yasa muka fara kiranki,kuma daga qarshe wayar a kashe, hankalinmu ya tashi" dai dai sanda takai qarshen maganar mahmud shima ya iso,dukka jikinsa a sanyaye,bayan ya gama kallon motocin da suka sauke sãahar din yanzu,wadanda suke dauke da number MT JARMA tun daga 01 har zuwa 05


"I hope she's fine" ya tambayi afifa,don tuni ita ta soma shigewa gidan ma


"I don't think so,naga yanayinta kamar akwai damuwa" idanunsa ya sake mayarwa kan shacin tayoyin motocin,kamar a nan zaiga amsar tambaya da kokwanton da suka cika masa zuciya,tun daga dannowar motocin street din nasu,har zuwa fitarsu


"Don't bother,zan shiga naji me ya faru,koma meye i will let you know"


"Thank you afifa" ya fada yana zube hannayensa a aljihun rigarsa. Yana yabawa gudunmawar da take bashi wajen samun soyayyar sãahar din


"No worries" ta bashi amsa tana gaggawar cimma sãahar din,sauqin abunma daya,anty farheen na ciki,koma meye tasan zata tari matsalar,tunda tasan halin 'yan kayanta sosai.


            Da sallama ta shiga parlor din,ba kowa sai maama dake gyarawa aleena socks dinta,khalipha kuma ya gaggwafe a qasa yanata qoqarin hada wani maths puzzles,tun dazun ya fara,har yanzun kuma bai hadasu dai dai ba


"Maama,sãahar fa?" Dan tabe baki kadan tayi 


"Suna ciki ita da uwarta" juya akalarta tayi zuwa dakin,tana cewa khalipha dake kiran tazo ta duba masa ya kasa hadawa


"Drop it aside son,i will be back".

 

        A hankali ta tura qofar dakin nasu,daidai lokacin da sãahar din ke zaune gefan gadonsu,ta zuba hannayenta saman fuskarta tana sheshsheqar kuka,anty farheen na zaune saman stool tana fuskantarta,tana tallafe da bayan hannunta tana dubanta kawai ba tare data hanata kukanta ba. Tun daga sanda adam yayi breaking heart dinta,yayi breaking dukka wani trust nata akan kowa,saita zama me raunin zuciya,wanda a times kuka ne kawai yake sanyawa ta samu tayi controlling anger dinta. Ko yanzun ma ta fara gaya mata amma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka,farheen tasan crying is the one way to calm her self,wannan ya sanya batayi qoqarin hanata ba.


           Taji motsin shigowar afifa,saita bude fuskarta wadda harta hada jaaa


"Me kika shigo kiyimin?"


"Afifa fita please" anty farheen ta fada. Harara afifan ta watsawa sãahar


"Ba inda zani,inkinso ki hadiye zuciya,duk wanna fushin nasan kawai don kinganni da mahmud ne,to zama daram a dakin nan" tasan halin afifa da kafiya wani lokacin,batason suyi ja'inja da ita alhalin tana cikin irin wannan bacin ran,afifa means alort to her,ba zata taba iya bata mata rai ba,wata sashe ce ta rayuwarta,don haka ta wuce toilet,ta qarasa matse hawayenta ta dauro alwala. Tun kafin ma ta gama alwalar taji sanyi yana sauka a zuciyarta,ita kanta wannan tsananin fushin bata sonshi,to amma yata iya?,wata qaqqarfar qaddara ta keto tsakiyar rayuwarta ta sauya mata abubuwa da dama.


             Ta sake yarda afifa da anty farheen din wasu mutane ne na musamman Allah ya ajiye mata,duk cikinsu babu wadda ta tashi,idan ta lura kamar damuwa ce saman fuskar kowannensu,duk da afifa ta maze tanata danne danne a wayarta,kamar komai bai sha mata kai ba. Wannan caring din data gani tattare dasu yasa ta kasa sauya kayan jikinta da tayi niyya,ta koma inda ta tashi dazu ta zauna,anty farheen na ankare da qafarta da tayi jazur


"Daga yau na ajjiye aiki da companyn MT JARMA,don Allah anty ki tayani fahimtar da yaa muhyi" ta fada a raunane,tana jin dacin abubuwan da yayi mata a yau.


        Furucinta dukkansu yaja hankalinsu,har afifa tabar danna wayar da takeyi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon sãahar din.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post