Gaskiyar batun juyin mulki a Congo Brazzaville

Gaskiyar batun juyin mulki a Congo Brazzaville

gaskiyar batun juyin mulki a Congo Brazzaville

Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta musanta labaran da ta kira na "Ƙanzon kurege" a kafafen sada zumunta wanda suke cewa an yi Juyin mulki a ƙasar. Wasu labarai marasa tushen sun ce ana shirin gudanar da wani abu a Brazzaville.

Gwamnati ta musanta waɗannan labarai. "Muna tabbatarwa da mutane babu wani abun tashin hankali kuma muna ba su shawarar kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa na yau da gobe," kamar yadda kakakin gwamnati Thierry Moungala ya wallafa a shafin X wanda a baya ake kira da Twitter.

Juyin mulki a yankin Yammacin Afrika na neman zama ruwan dare a 'yan shekarun nan.

Sojoji ne ke shugabantar ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar da kuma Gabon, suna kafa hujja da cewa shugabannin da suka hamɓarar sun gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro musamman a ƙasashen yankin Sahel.

Congo Brazzaville ba ta cikin yankin Sahel, inda barazanar masu jihadi iƙirarin jihadi ta zama jiki, kuma wataƙila wannan raɗe-raɗin ya samo asali ne saboda daɗewar shugaban ƙasar na yanzu a kan mulki, ina ya jagoranci ƙasar a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1992 sai kuma ya ci gaba daga 1997 har ya zuwa yanzu.

Ana sa ran Shugaba Denis Sassou-Nguesso zai halarci taron MDD na 78 wanda zai gudana a ƙasar Amurka daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Satumba.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post