Kukan Zuci page 1 - Novels Elite

Kukan Zuci page 1 - Novels Elite

 

Kukan Zuci page 1 - Novels Elite

💔💔 Kukan Zuci 💔💔

Written by Novels Elite.


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da wata manufa ba sai don nishaɗi. Wannan Labarin kuma kajere ne ba mai tsawo ba saboda wannan shine littafina na farko.


Page 1.


Misalin ƙarfe 7:20am (na safe) Zaune suke a falo suna karin safe (breakfast) domin su tafi makaranta Nabil ya Kalli Annan su yace, "Abba idan na girma na gama karatu zan zama likita idan baka da lafiya Ni zan dinga kula da kai," kallon sa kawai Abban nasu yayi tare da sakin Murmushi na jin daɗin abinda yaron nashi ya fadi, domin kuwa yaji dadi sosai. Nabil yaro ne wanda bai wuce shekaru biyar da haihuwa ba, kyakkyawa ne kuma shi kaɗai ne Alhaji Kabir Mahi ya haifa Bayan shekaru goma (10) da Auren su tare da Hajiya kubrah. Ƙarfe 7:40 Alh. Kabir Mahi ya kammala cin abincin sa domin shima zai tafi ofis ya ɗauki Nabil da jakar makarantar sa da abincinsa, Hajiya Kubrah ta taki su har wajen da motarsasa ke ajiye suka shiga Hajiya na ɗaga musu hannu alamun sai sun dawo.


Suna tafe a hanya suna fira da ɗan nasa wanda ya zama tamkar abokinsa domin kuwa yana jansa a jiki domin nuna kulawa ta yadda idan yana da wata matsala zai iya samun sa ya faɗa masa abinda yake damu da, wanda kuma hakan yana da kyau ka ka ɗan ka ko ƴar ka a jiki ta haka ne zai sa ba zasu dinga fita sosai ba har su haɗu da abokai ko ƙawayen da zasu lalata musu tarbiya.


Ba daɗewa suka isa ƙofar makarantar su Nabil sai da Alhaji Kabir ya tabbatar ya shiga makarantar sannan ya ta fi wajen aikin sa.


Nabil yana matakin aji uku na primary kuma ɗalibi ne mai ƙoƙari sosai a cikin abin su domin daga anyi tambaya shine ke saurin bada amsar abinda aka tambaya, kuma shima ya kanyi tambaya akan abinda ya ga bai gane ba ko idan ya Lura sauran abokanshi basu gane ba.


Hajiya Kubrah ta dawo daga rakon da tayi ɗakin ta kawai ta wuce domin ta kammala duk wani abu da yakamata ta yi saura gyaran gida ne kawai kuma dama suna da me aiki, Lauren. Lauren dattijuwa ce wacce aƙalla ta kai shekaru hamsin da ɗaya, tana da kirki da haƙuri, ta kai kimanin shekaru huɗu tana yi ma Hajiya Kubrah aiki, suma suna kyautata mata sosai domin kuwa suna cikin halin babu wanda dole suna buƙatar tallafi. Ƴaƴan Baba Laure biyar (5) wanda mijin ta ya rasu ya bari.


Alh. Kabir kuwa ya isa kamfanin sa ke nan na Mahi Motors, Mahi Motors Mallakin Alhaji Kabir Mahi ne inda ake sayar da motoci kala daban-daban dake cikin Garin Kaduna, wanda ake shigo dasu daga ƙasar waje duk kalar motar da kake nema zaka samu, Alhaji Kabir ya iya kasuwanci da hazaƙa domin hakan yasa mahaifin su Alhaji Mahi ya fi don sa akan dukkan sauran ƴaƴan sa.


Alh. Kabir Mahi yana da ƴan uwa guda huɗu inda shi kaɗai ne a wajen mahaifiyarsa sauran suma mahaifiyarsa daban wanda mahaifiyar Alhaji Kabir Mahi itace Karama.

Misalin ƙarfe Uku na rana (3:00pm) Hajiya Kubrah tayi ma Laure Sallama domin ta fita domin ɗauko Nabil daga makaranta, Laure kuma tana ƙarasa sauran aikin da ba ta gama ba.

Kiran waya ne ya shigo wayar Alh. Kabir, ya ɗauka da Assalamu alaikum, ba sallama na kira naji ba, na kira ne naji kana Raye ne ko ka mutu?


Shin wanene ya kira Alhaji Kabir kuma me ke tsakanin su.

Kuyi comment, like da share domin cigaba da samun wannan littafin.

Novels Elite.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post