Kukan Zuci page 3 - Novels Elite

Kukan Zuci page 3 - Novels Elite

 

Kukan Zuci page 3 - Novels Elite

💔💔 Kukan Zuci 💔💔

Written by Novels Elite.


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da wata manufa ba sai don nishaɗi. Wannan Labarin kuma kajere ne ba mai tsawo ba saboda wannan shine littafina na farko.Page 3.


Tun daga lokacin da Hajiya Rabi ta daki wannan kwaryar Hajara ta tashi a firgice tun daga nan ta haukace ta fita kan ta ba komai.

Hajiya rabi da ƙawar ta suka yi wa boka sallama suka fita, tun daga wannan lokacin Kabiru ya shiga cikin rayuwar ƙunci da baƙar wahala da yake sha a wajen Hajiya Rabi da 'ya'yanta. Bacci ya ƙauracewa idon Kabiru ko da yaushe tunanin sa inda za'a ga mahaifiyarsa.


Hajara dai babu ko labarinta duk inda aka san za a same ta anje ba'a ganta ba. Kabiru da Alhaji Mahi sunyi nema har sun gaji. Bayan wata biyu da ɓatar ta Hajiya rabi ta sake komawa wajen boka domin malleke Alhaji Mahi, a wannan karon kuwa tayi nasara domin kuwa sai yadda tayi da Alhaji Mahi,don ko soyayyar da yake nuna ma Kabiru ta fara baya sakamakon biye-biyen gidan bokaye da Hajiya Rabi take yi.

Kabiru ya ga canji sosai wajen mahaifin nashi domin ya fara cire shi a dukkanin wasu harkoki na kasuwancin sa, yana ɗora 'yan uwansa duk da Basu san komai ba.


            ************


Hajara kuwa tun lokacin da ta tashi a firgice ta fita bata san inda take tafiya ba, saboda bata cikin hankalinta, tana ta tafiya ba dare ba rana domin abinci kuwa sai dai duk abinda ta samu taci. Tana cikin wannan hali ne zata tsallaka titin abinka da wanda bashi da hankali ba tare da dubawa ba ta shiga titin, shigar ta ke da wuya wata mota ƙirar Mecedez Benz ta ɗauke ta. A ruɗe durbar Motar ya fito tare da abokin sa, nan da nan ya ɗaga waya ya kira ofishin 'yan Sanda sakamakon haɗarin da ya faru, cikin ƙanƙanin lokaci wani ɗan sanda ya yazo, aka ɗauke ta zuwa asibiti.


Accident and emergency aka wuce da ita, abinka da masu hali, nan da nan likitoci suka zo domin bata agajin gaggawa kafin a ɗauki hoton kan ta a ga menene matsalar. Cikin abinda bai wuce mintuna talatin ba aka shirya shiga da ita ɗakin tiyata domin ta samun buguwa a kanta. Professor Umar,  Mutum ne wanda bai wuce shekaru 56 da haihuwa ya saka hannu a takardar aikin da za ayi wa Hajara.

Karanta litafin Kukan Zuci page 2 

Aikin Tiyatar ya ɗaukesu aƙalla awa ɗaya da mintuna arba'in kafin su gama, likitan yana fitowa yace ma professor Umar zo office ɗina ina so muyi magana, Dr. ya wuce Prof. Umar ya bi bayansa tare da abokin sa, suna shiga Dr. Habib ya nuna musu waje su zauna. Dr. yayi musu bayanin anyi aiki lafiya lau sai dai da yiwuwar zata iya mantawa da duk wani rayuwar ta na baya. Yanzu dai muna jira ne ta farka mu gani. Prof. Umar ya taɓe baki yace ikon Allah, to Allah ya bata lafiya.


Cikin ƙanƙanin lokaci bayan kammala aiki sai dai abinda ake gudu shine ya faru, domin kuwa Hajara ta buɗe ido, buɗe idon ta ke da wuya ta fara tambayar maikaciyar jinya wato Nurse a turance, dan Allah ina ne nan kuma kuma me nake yi anan? Nurse ta kalleta cikin kulawa tace, nan kina asibiti ne kin sami wani haɗari ne wani ya bugeki da mota, bari na kira likita.


Nurse ta yi nocking ƙofar ofis ɗin likita wanda dama su Professor Umar suna tare, Yes shigo, "Dr. yayi mata umarnin ta shigo" ta shigo tayi ma likita bayani patient ɗin da akayi mata aiki akai ta tashi. Dukkansu suka fita domin zuwa ɗakin da aka kwantar da Hajara, Dr. Habib ya sake duba ta sosai yayi mata yan tambayoyi dai Hajara dai ido ta zura musu domin bata iya gane komai sai wani ciwon kai mai tsanani ke samun ta sakamakon buguwar da tayi a kai, wanda hakan shine yayi sanadiyyar manta komai da ya faru da ita a baya.


Hajiya Rabi kuwa ranta yayi fari tas domin kuwa ta sami duk abinda take so abu ɗaya ne kawai ya rage mata babba, wato Kabiru shine babbar matsalar ta da ya rage domin kuwa Alhaji Mahi sai yadda akayi dashi hakan yasa Kabiru ke shan tsangwama wajen ta da yaranta, domin sun cire shi a duk wani harkokin Alh. Mahi, hakan yasa Kabir ke zaune a gida duk wani aiki na gidan shine yake yi, ba yadda zai yi duk wannan abinda akeyi ma Kabir Safiya bata jin daɗin hakan.


Novels Elite

08062334828

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post