Kukan Zuci page 2 - Novels Elite

Kukan Zuci page 2 - Novels Elite

 

Kukan Zuci  page 2 - Novels Elite

💔💔 Kukan Zuci 💔💔

Written by Novels Elite.


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da wata manufa ba sai don nishaɗi. Wannan Labarin kuma kajere ne ba mai tsawo ba saboda wannan shine littafina na farko.


Page 2.

Kiran waya ne ya shigo wayar Alh. Kabir, ya ɗauka da Assalamu alaikum, ba sallama na kira naji ba, na kira ne naji kana Raye ne ko ka mutu, Rawa jikin Alh. Kabir ya fara sakamakon jin abin da baiyi tsammanin jinsa ba a wannan lokacin, ya amsa da ina raye ban mutu ba sai lokacin da Allah ya so.

Kamal ya kara da cewa in sha Allah nine nan ajalinka domin kuwa ina bakin ciki da duk wani cigaba da kake samu.


*******Wanene Alhaji Mahi?

Alhaji Mahi dai Attajirin Dan Kasuwa ne wanda ya shahara wajen gudanar da kasuwanci, Alh. Mahi yana da mata biyu wanda Uwargidan sa sunanta Rabi, Dayan matar kuma sunanta Hajara, Rabi na da yara hudu (4) Kamal, Sani Jafar da kuma Safiya a inda Hajara ke da ‘d kuda daya mai suna Kabir. Matar Alh. Mahi sun Kasance basa jituwa ko kadan sakamakon son da Alhaji Mahi ke ma dan Hajara (Kabir) hakan ya samo asaline ta hanyar Kokarinsa da son duk abinda mahaifin nasu yakeyi domin kuwa yana da hankali da tarbiya wanda ya samu wajen mahaifiyar sa, duk da irin tsantsar tsanar da suke nuna masa hakan baisa shi jin haushin su ba, Safiya ce kawai take son Kabir saboda bata son irin abinda akeyi masa tare da mahaifiyar sa.


Hajiya Rabi da yaran ta suna ta kulle-Kullen yadda zasu ga bayan Hajara da dan ta Kabir so da yawa suna yunkurin kasha su amma Allah Baya Basu sa’ar yin hakan. A haka dai Kasuwancin Alh. Mahi sai kara Habaka yakeyi da taimakon Allah da na kabir wanda dama Kasuwanci ya karanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke  Zaria a inda ya gama da kyakkyawar sakamako sabanin yan uwansa da basuyi karatu ba a sakandire kawai suka tsaya basu cigaba ba sakamakon gatar da suka samu wajen mahaifiyar ta su da hakan ya sa ko Alh Mahi baya iya kwabar su.


Hajiya Rabi ta kware wajen shiga bokaye da malaman tsibbu ta hakan ne yasa mafi yawan lokaci take juya Gidan yadda take so amma wasu lokutan asirin baya tasiri akan Hajara da Dan ta Kabir Sakamakon yawan Azkhar da sukeyi na safe da maraice hakan yasa ko da anyi baya aiki.

Tun suna yara Kabir ya fita daban wajen tarbiya da kula da ibada da mahaifiyarsa ke koya mishi domin bata wasa wajen koya masa yadda zai gudanar da ibada, sabanin yaran dakin Hajiya Rabi wanda basu san komai ba saboda basa ko zuwa Makarantar boko bare makarantar Islamiya saboda duk abinda suke so Hajiya Rabi zata musu. 


Wata ranar juma’a da yamma yaran Hajiya Rabi suka hadu a falo tare da ita hajiyar har da Karamar yarinyar ta wand aba son ran ta bane ake ma Hajara duk abubuwan da akeyi mata tare da Kabir, suna kulla yadda zasu kore ta a Gidan ta ko wani hanya, Kamal Shine baban yaron Hajiya Rabi kuma ko a Gidan ma shine babba ya fi kowa jin haushin irin son da Alhaji Mahi ke ma Kabir ta yadda ya dora shi akan duk wasu harkokin sa. Kamal y ace “Ni a Gani na a kasha su kawai kowa ya huta” Safiya dai kallon su kawai takeyi domin ko Magana ma ba’a barin ta tayi domin bata kaunar abin da za a musu, Sani kuwa cewa yayi kawai a sa boka ya haukata su, Safiya ne tace kai yaya……… rufa ma muta ne baki sakarya wacce bata san ciwon kanta ta, in ace duk wannan abin saboda ku nakeyi, Hajiya ce ta katse Safiya. Baki ganin yadda yanzu komai na kasuwanci Alhaji da Kabiru  ne akeyin komai yayinki kuwa an zubar dasu duk da sune manya, bana son wannan shahshancin naki, in kina so ne ki koma can wajen su. Da alamu duk aikin da nayi a kansu ya lalace dabbas sai na koma wajen boka domin ya sake farraka min su, zan je Gidan kawata mu tafi tare.


Washe gari bayan Sallar Asuba tayi bayan ta idar da sallah tana azkhar na safe kamar kullum tare da yin addu’o’in tsari daga ko wani irin sharri na mutum da aljani, gari yayi haske sosai Kabir ya Shiga sasan Hajara domin gaishe ta, a inda tayi sallah ya same ta kan Sallaya ya gaida ta har ya kai kofa zai fita, Kabiru, ya amsa da na’am umma, da wo ina son Magana da kai. Kabir ya zauna cikin ladabi da kulawa. Hajara tayi masa nasiha mai ratsa jiki tare da ce masa a ko wani lokaci ya rike kowa tsakaninsa da Allah, kayi gaskiya a dukkanin al’amuran ka, ka so yan uwanka tare da girmama duk n agama da kai, yace, nagode Umma, kuma in sha Allah bazan baki kunya ba.


Kabir ya fito daga sashin mahaifiyara ne ya hadu da Hajiya Rabi a kofar shiga nata sashin, ya gaida ta amma a tsatstsaye ta masa kamar wacce aka ce mata dole sai ta amsa.


Hajiya Rabi ta koma sashinta ta sami Jafar da Safiya a falo suna zaune suna hira domin tana son dukkanin yayyin nata, Hajiya kin tashi lafiya, in ji Jafar da Safiya, ta amsa da lafiya lau, Hajiya ta zauna tare da tambayar ina sauran suke, Jafar ne ya amsa da cewa basu tashi ba, Hajiya ta Kara da cewa ni zan je Gidan Hajiya Saratu zamu tafi unguwa da ita, bari ma na kira naji ko tana gida, Hajiya Rabi ta daga waya ta kira kawarta Saratu, ba tare da bata lokaci ba kuwa ta dauka, da gaisuwa suka fara sannan Hajiya Rabi ta ce mata dan Allah gani nan zuwa zamu koma wajen malamin nan domin kuwa duk aikin da mukayi ya lalace harda na Alhaji, “To ba damuwa sai kin zo”, Hajiya Rabi ta Ajiye wayar da nagode nan ba da daewa ba zaki ganni.

Hajiya Rabi bata kaunar Hajara ko kadan domin a cewar ta tun da ta haifi Kabir Alhaji ya daina son nata yaran, wanda azahirin gaskiya bah aka bane halinsu ne da irin hanyar da ta dora ’ya’yan nata wanda duk mai hankali ba zai so zama tare da wanda ke da irin wannan halin ba.

Babu jimawa da yin wayarsu, Hajiya Rabi ta tafi Gidan Hajiya Saratu inda ta mata bayanin yadda duk suka shirya yi da irin abubuwan da suke son yi ma Hajara da dan ta Kabiru. Ba tare da sun dade a zaune ba wanda dama tun da suka yi waya, Hajiya Saratu ta shirya, nan da nan suka fita zuwa Gidan bokan da suka saba zuwa.


Boka mun dawo aikin…….. kai kai, ba sai kin fada min ba domin kuwa an fada min komai duk aikin da mukayi miki ya karye sakamakon kuwa tana yawan addu’a kuma tana sallah akan lokaci ta yadda aikin mu bazaiyi tasiri akan ta ba, Amma yanzu zamu canza yanayin aikin a wannan karon baza ta tsalla ke ba, boka yay a shafi bakin wata kwarya dake gaban shi, yace leka nan me kika gani, Hajiya Rabi kuwa tayi kamar yadda Boka ya umarce ta, Hajara ce kwance tana bacci a dakin ta, Boka yace me kikeso ayi mata? Ina so a haukata ta ta bi duniya tayi nisa da inda mu ke kada a sake jin labarin ta, boka ya bata wani bulala yace daki wannan bakin kwaryar inda kika ga abokiyar zaman ki, kina dukan ta zata firgita, daga nan shike nan zata haukace, tayi kamar yadda boka yace tayi.

Laifin dadi karewa domin cigaba mu hadu a page 3 don jin Hajara zata haukace ko a wannan karon ma asirin bazaiyi tasiri ba?


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post