Hukumar NSCDC sun kama mutum 76 da ake zargin ‘yan luwadi ne a Gombe

Hukumar NSCDC sun kama mutum 76 da ake zargin ‘yan luwadi ne a Gombe

Gombe

Ƴan sanda sun kama maza 67 da ake zargi Ƴan luwadi ne a Delta

Hukumar Sibul Difens ta NSCDC a jihar Gombe ta bayyana cewa dakarunta sun kama mutum 76 da ake zargi ‘yan luwadi ne a jihar.

Shugaban hukumar Mohammed Mu’azu ya sanar da haka ranar Lahadi.

Mu’azu ya ce daga cikin mutum 76 din da aka kama akwai maza 59 da a cikinsu akwai 21 da suka tabbatar wa jami’an tsaron cewa su ‘yan luwad1 ne sannan da mata masu madigo 17.

Ya ce sun kama wadannan mutane a Duwa plaza dake hanyar Bauchi zuwa Gombe yayin da suke taron tunawa zagayowar ranar haihuwa da daurin auren mambobin su.

Mu’azu ya ce zai mai da wadannan mutane da suka kama makaranta yadda ba za su samu lokacin aikata muggan aiyukka irin haka ba.

Daga nan kuma ya ce da zaran sun kammala bincike za a kai su kotu domin yanke musu hukunci.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa dakarun ‘yan sandan jihar Delta sun kama mutum 67 da ake zargin ‘yan luwadi ne a kauyen Ekpan dake karamar hukumar Uvwie.

Dakarun sun kama wadannan mutane a taron daurin aure da suke yi wa wani otel dake hanyar Refinery a Uvwie.

Rigunan mata da mazan ke amfani da su domin taron daurin auren, kwalban kodin guda daya, kofuna uku da kwayar Canadian Loud a ciki, fakitin ganyen SK, fakitin kwayar Tramadol daya da kwayar Molly guda hudu na daga cikin kayan da ‘yan sandan suka kama a wurin taron.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post