Kurkukun Ƙaddara chapter 19 complete

Kurkukun Ƙaddara chapter 19 complete

 

Kurkukun Ƙaddara

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


daga alƙalamin Boss Bature


E19


Kamar afarmaki take ganin lamarin, Tsabar ruɗi tarasa me zatayi, Tsananin tsoro ne bayyane akan fuskarta, Ƙarasawa tayi gaban sofa ɗin ta sanya hannu tana shafa Saman kujerarar, ta tabbatar cewa an ɗauke Mata Yaronta, tunani tayi kodai Musa ya shigo ya ɗauke shi ne? da gudu ta zabura Ta fito daga cikin falon, Har ta kusa kaiwa Bakin gate ta juyo kukan baby junaid ɗinta, a matuƙar gigice ta juya ta koma Cikin gidan, duk inda ta nufa sai taga babu shi, Rushewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin"Innallalahi wa'innna ilaihirraji'un! Wayyo Allah na! dan Allah wanene ya shigo? kada ku cutar mun da yarona na roƙe ku, ku ƙyale mun shi, ' tana Cikin maganar nan tajiyo takun tafiyar mutun a firgice ta juya bayanta, gifcin shi ta gani koma wanene yana a sanye Cikin bakaken Kaya, Fuskar shi tana sanye da face mask, Hannunshi na ruƙe da Baby Junaid, Da gudun gaske Aneeelerh tabi bayanshi, sai dai kafin ta ƙarasa tuni ya 6ace ma ganinta,

  Gaba ɗaya ta haukace Jikinta sai tsuma yake yi ga wata uwar zufa data tsastsafo mata, ita ba kanta take ji mawa ba, Ɗanta take jimawa ba, shida bai mallaki hankalin shi ba,

  "Dan Allah na roƙe ka ka dawo mun da ɗana, Kome kakeso zan baka, Amma kada ka cutar mun shi, idan ma ni kakeso ka dauke ni ka ƙyale mun shi pls," cikin shessheƙar kuka tayi maganar, 


Motsi ta kuma Ji daga can saman stairs ɗin gidan, A hautsine ta ɗaga ido tana kallon mutun dake atsaye, Hannun shi ruƙe da baby junaid, ƙarfin hali hada ɗaura shi saman kafadarshi, yana shafa bayanshi, kuma yaron yayi shiru,


Zuba ma shi ido tayi tana kallon shi batare da ƙyaftawar ido ba, Koma wanene wannan mutumin ba ƙaramin karkarfa bane, Yana da tsayi da kuma faffaɗan Ƙirji, ta ko'ina ya rufe jikin shi, ta yadda mutun bazai iya shaida shi ba,

  Muryarta na kerma tace"Dan Allah kada ka cutar mun da shi, kome kakeso zan baka," ta yi maganar tana kallon shi, zufa ta ko'ina saman fuskarta,

   Gani take kamar zai jefo shi ta saman bene ne ya faɗo kasa kanshi ya fashe, 

  Fashewa ta kuma yi da wani sabon Kukan, Tunawa tayi da musa driver da gudu ta juya ta nufi hanyar fita don taje ta sanar da shi abunda ke faru, 

  Harta ruƙe handle ɗin ƙopar, Muryar mutumin ta ratsa kunnnuwanta,

 Cikin harshen Turanci yace"idan kika kuskura kika fita, zan wurgo da shi ƙasa," Ras Taji gabanta ya faɗi, Kamar gunƙi haka ta ƙame, zuciyarta a cunkushe Ta juyo tana kallon shi, Har lokacin Yana a can sama, 

   Muryarta na kerma tace"Na fasa bazanje ba, wlh bazanje ba, dan Allah ka bani ɗana, wlh nayi maka alƙawari bazan ƙara zuwa gidan ba,"

   Dawowa cikin Falon Ta yi, A bakin stairs ɗin ta tsaya, fuskarta jaga jaga da hawaye, Bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na yau, Ko wanene wannan mutumin? Taya akai ya shigo Cikin gidan? Bayan makullan gidan Suna a hannun jami'an ƴan sanda? Anya kuwa mutunne kodai ta bango ya ratsa Ya shigo?

  "Ka faɗamun ko nawa kakeso zan baka ina da kuɗi, Ni dai kawai burina ka bani Yarona,"

   Tana magana tana taka staircases ɗin, a kokarin ta nata haura inda yake,

  "Hajiya" Muryar Musa driver ce, A firgice aneelerh ta juya tana kallon musa, Ai koda musa yayi arba da mutumin dake A can saman stairs sanye da bakaken kaya, Nan take jikin shi ya hau yin kerma, Ya shiga ambaton"Ƙalu Innallahi wa'inna ilaihirraji'un hajiya wannan kuma daga ina"?

  Cikin muryar kuka aneelerh tace"Nima bansani ba, Daga shiga Cikin ɗaki na dawo na taras ya dauke mun baby junaid ɗina, dan Allah kataimaka ka sanya baki mu bashi haƙuri ya bamu junaid mu tafi mubar masa gidan,"

  Kallon shi musa Ya kuma yi"Bawan Allah, Don son da kake ma iyayenka Ka taimaka ka bamu yaron nan, Wlh tsautsayi da ƙaddara ne ya kawo mu Cikin gidan nan, dama saida na gargaɗi hajiya nace mata kada mu zo, Amma ta sanya naci akan sai mun zo yanzu ga irinta nan"

  Roƙonshi suka dinga yi ko tanka masu baiyi ba, tamkar baijin me suke cewa, Ya ƙanƙame Yaro a hannunshi sai shafa sumar kanshi yake yi,


    "Hajiya wannan mutumin fa, ba bamu yaron nan zaiyi ba, Kizo muyi ta kanmu kawai, Allah zai baki wani ɗan, idan ba haka ba mu duka zamu rasa ranmu," 

      "Wlh ba inda Zanje sai ya bani yarona, saboda bakasan ciwon haihuwa ba shiyasa zaka ce mu tafi mubar ma shi yaro a hannu, " rai a6ace takai ƙarshen maganar, Duk yana atsaye yana sauraron su,

    Suna Cikin yin maganar nan, gaba ɗaya hasken gidan ya ɗauke, duhu ya mamaye ko'ina, 

      Aneelerh ta shiga matsanancin tashin hankali, Cikin duhu taci gaba da tattaka matattakalar benan, Tana jiyo muryar musa yana kwala mata kira, amma ina kota kanshi bata bi ba, lokacin da ta ƙarasa hawa benan, Muryarta na rawa take faɗin"Bawan Allah, ka bani yaro na in tafi, nasan kana jina, dan Allah kada ka cutar mun shi," tana magana tana lalube Cikin duhu,

      Motsin shi ta dinga Ji acikin kunnuwanta, alamun yana a kusa da ita, Kamar ma zagayeta yake yi, Jikinta sai kerma yake yi, ga wata uwar zufa dake tsastsafo mata, mugun tsoro take ji, amma saboda soyayyar dake a tsakanin uwa da ɗa, ta kasa guduwa ta kwammace komai zai faru ya faru, koda zata rasa ɗanta ne,

      Wani irin daddaɗan ƙamshin turare ta soma shaƙa Cikin hancinta, koma wanene wannan Ba 6arawo bane, Kuma ba da niyar mugunta yazo ba, Lamarin ya rikitar da ita,

      Cikin sanyin murya tace"Dan Allah ka bani shi in tafi, wlh bazan faɗi ma kowa naga mutun acikin gidan ba,"

      Hannunta taji ya ruƙo, ras taji gabanta ya faɗi, ɗaura mata baby junaid yayi asaman ƙirjinta, da sauri ta tallebe shi, ta rungume abunta ajikinta, Natsuwa tayi tana jiran jin ya furta wata magana sai dai baice komai ba, 

     Lokacin da ta daina jin motsinshi a kusa da ita, a dai dai wannan lokacin hasken Gidan Ya dawo gaba ɗaya ya gauraye ko'ina,

      Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura idanuwanta kan baby junaid dake ta sharar bacci, saman ƙirjinta,

      Ƙara ƙanƙame shi tayi ajikinta, kamar zata mayar dashi Cikin cikinta, Yau da ace ɗan tahalinkin nan ya kashe mata shi, da kuwa har ranta zata iya rasawa,

      "Hajiya zamu iya tafiya yanzu"? Musa ne yayi maganar jikinshi sai kerma yake yi, yana daga can down stairs, Harara ta wurga mashi,

      "Ka bani key ɗin motar, ka kama gabanka, Sakaran Namiji kawai, hada cewa in bar mashi yarona in Zo mu tafi, ban ta6a ganin ragwon namiji irin ka ba, duk macan da ta aure ka tayi asara, " zuru musa yayi mata da ido,"

     Saukowa down stairs tayi tare da miƙa mashi hannu"bani key ɗin motar"

      Cikin sanyin murya yace"ayi haƙuri hajiya ruɗu ne ya jawo hakan"

      A fadace tace"dalla ni bani key," 

      Zaro key ɗin motar yayi daga Cikin aljihun shi ya miƙa mata, tasa hannu ta fusge shi, Cikin fushi ta fuce daga cikin falon, 

     Da gudu musa yabi bayanta yana lallashinta. 

      Bayan ta rufe gidan da key ta buɗe mota zata shiga driver seat, da sauri musa Yayi hanzarin cewa"Dan Allah aunty aneelerh kiyi hakuri wlh bana Cikin hayyacina ne, su6ul da baka nayi wurin furta maganar, ban kaiga tace ta ba,"

      Daƙyar musa ya samu aneelerh ta haƙura ta miƙa mashi key din motar, ta shiga passenger front seat ta zauna shi kuma ya zauna a driver seat,"

      Da gudun gaske ya fusgi motar, kafin su ƙarasa gida saida ta gargaɗe shi akan karya kuskura ya faɗa ma su abie dangane da mutumin da suka gani Cikin gidan, yaja bakin shi yayi shiru tun da bai cutar dasu ba, su ɗauka tamkar mafarki su kayi, Yace mata toh, 


Lokacin da suka ƙaraso Cikin gidan, A parking space Musa ya yi parking ɗin motar, ya fito ya zagaya ta other side ɗin ya buɗe ma Aneelerh mota,

  Fitowa tayi hannunta rungume da baby junaid, Har lokacin Jikinta kerma yake yi, ta tsorata sosai da wannan tahalikin da ya kai masu farmaki,

  Kallon musa tayi shima kallon nata yake yi, harara ta jefa mashi ya sunnar da kan shi ƙasa, Ni zan wuce ciki, "

  "To hajiya sai Allah yakaimu, Allah ya kyauta gaba," bata amsa ma shi ba ta nufi Cikin gidan,

  Da alama duk sunyi bacci, bata nufi ko'ina ba, Sai Cikin Bedroom ɗinta, a saman gado ta kwantar da junaid, sai baccin shi yake yi hankali kwance,


  Rage kayan jikinta ta yi, ta shiga toilet domin yin wanka, after 15 mins ta fito waist ɗinta ɗaure da towel fari,

    Walking slowly ta nufi Saman mirror chair ta zauna, tare da ɗaura gwiwar hannunta gaban madubin, ta zabga uban ta gumi,

  Zuciyarta a cike take da tunanin mutumin nan, ko wanene shi? Taya akai ya samu damar shiga Cikin gidan dake a garƙame? Kodai bayan shigarsu ciki shima Ya samu damar shiga Cikin gidan?  Shin me yaje yi acikin gidan, gaba ɗaya ta burkita ma kanta lissafi, kusan raba dare ta yi azaune tana tunani akan shi, bata iya gano komai ba, a ƙarshe ta miƙe taje gaban closet, ta buɗe ta curo kayan baccinta, Ta sanya su ajikinta,


 Komawa saman gadon tayi, ta kwanta tare da janyo junaid ta rungume shi ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci yae awon gaba da ita, Ko da gari ya waye Aneelerh bata sanar da kowa game da mutumin da suka gani acikin gidan Uzair ba, ita kanta tarasa gane dalilin dayasa ta kasa buɗe baki ta faɗa masu cewa wani ya shiga gidan, wata'ƙil ta hanyar hakan asamu wata evidence da zata bayyana ainihin meya faru da su tajo, kuma tun daga ranar bata ƙara gigin zuwa gidan ba, gani take kamar mutumin yana bibiyar rayuwarta, kodan kada ta tona ma shi asiri dole ya bibiyeta, shiyasa take tsoran fallasawa,


Back To prison🌷


A kwana a tashi ba wuya wurin Allah A yau angel ta cika shekara 1 da rabi A gidan KURKUKUN ƘADDARA, tun daga ranar da tayi ma batool tambayoyin nan bata ƙara tambayarta wani abu dangane da gidan kurkukun ba, dalili kuwa shine a duk lokacin da zata tambayi batool game da prison ɗin, Sai wani abu ya faru, wanda zai ɗauke masu hankali, Haka xalika a duk lokacin da ta yi yunƙurin sanar dasu wani abu game da addinin musulunci sai wani abu ya faru wanda zai dakatar da ita, ta ko'ina an toshe mata hanya, 


Abu ɗaya ne take kokarin Koyar da su shine yawan ambaton sunan Allah acikin maganarsu, saboda kwata kwata basa furta sunan Allah, zuwan angel cikin rayuwarsu sun fara koyan wasu abubuwan wanda basu iya ba, salon maganarsu ya fara komawa irin na angel, ta zama tamkar malama acikinsu, Idan suka kammala Cin abinci, bata bari su koma bacci, motsa jiki take sanya su suna yi, Ko kuma suyi wasa a tsakaninsu, bakomai yasa suke jin shakkarta ba, face rashin tsoranta, da kuma wannan kalmar ta charman dudu da take yi masu barazana da ita, shiyasa a kullum take Cin galaba a kansu, duk wannan tsawon lokacin da angel ta ɗauka acikin gidan kurkukun ƙaddara, har yau babu jituwa tsakaninta da Haris da kuma mr sound hater wato DANISH, su biyun nan sunƙi yarda da ita, duk da sunfi kowa jin shakkarta, kuma in ta bada umarni dole kowa yabi hada su ɗin,


Zaune suke gaba ɗayansu sun kewaye Kayan abincin da aka kawo masu, giants suna a tsaye sun kasa sun tsare suna jiran su kammala Ci su kwashe Kayan su tafi,

  Hanna ce ta ya ye jan kyallen da aka rufe saman trays ɗin, tray na farko fried meat ne,  sai faffadan plate me ɗauke da Snacks a tray na ƙarshe kuma jug ɗin ruwa ne, sai kofuna Bayan su kuma sai kwandon dake ɗauke da kayan marmari da ƴar ƙaramar wuƙa, wadda zasu yi amfani da ita su yanka fruits ɗin,

 Kowa yakai hannu ya dauki fried meat yana Ci, 

 Gaba ɗaya hankalin angel na akan wuƙar da aka sako Cikin kwandon kayan marmarinsu Cin naman take yi kamar zata shaƙe, so take ta sace wuƙar batare da sun gani ba, ɗagowa ta ɗanyi tana kallon Su Giants dake a tsaye, abinci ma baza a bar mutun yaci a tsanake ba sai an tsare mutun da ido, a cikin zuciyarta ta yi maganar don tasan suna kallon su,

  Cikin ƙankanin lokaci ta cinye nata abincin, miƙa hannu ta yi tana nuna jerin Cups ɗin dake a jiye Javed yace"ruwa zaki sha"? Ta ɗaga mashi kai alamar eh,

 Da kanshi ya zuba mata ruwan ya miƙa mata, ta kar6a tana yi mashi godiya, bayan ta shanye ruwan ta ajiye kofin, xama ta yi tana jira sauran su kammala cinye nasu, ko ta samu a zo kan fruit ɗin yadda zata ji daɗin sace wuƙar,

  Sun ɗauki tsawon mintuna kafin suka kammala, kowa ya sha ruwa Kafin suka kai hannu suna ɗaukar kayan marmarin, ganin basu yi amfani da wuƙar ba, yasa tace ma batool" ba zasu yanka ba" batool tace mata"A jiyewa zamuyi sai anjima mu sha," yatsina fuska angel ta yi ganin zata rasa damar da take da ita, ta ɗaukar wukar,

  Dabara ce ta faɗo mata aranta, miƙewa ta yi tsaye tamkar zata bar wuri, ta ɗan ɗaga kafarta alamar za ta yi tafiya, gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗa saman kayan abincin, aruɗe su hannah suka kewaye ta suna jijjiga jikinta, hankalinsu a tashe suke ambaton sunanta,

  Ganin sunyi mata rumfa ta yadda waɗannan Giants ɗin bazasu iya ganin meke wakana ba, a hanzarce ta yi wuf ta zura hannu ta ɗauke wuƙar tare da saƙe ta gefen qugunta, mutun ɗaya ne ya ga lokacin da ta ɗauki wuqar don ta fakaici idon su ne,

  Miƙewa ta yi tana faman haki tace su bata ruwa tasha, jiri ne ya kwashe ta,

 Da sauri Hibba ta cika mata kofi da ruwa ta miƙa mata, kaɗan tasha ruwan don bata jin ƙishir ruwa duk cikin plan ne,

  Ganin sun kammala cin abincin yasa Giants matsowa suka tattara komai da suka yi amfani da shi, har fa sun Kama hanyar fita, danish ya ɗaga murya tare da cewa"She took a knife" tashin sense a razane angel ke kallon shi, kafin ta ɗaura idonta akan giants gani ta yi sunja burki sun tsaya cak, ɗaya daga cikin ne ya jiyo tare da nufar inda suke, tamkar zaki

  Saboda tsabar ruɗi tunkafin ya ƙaraso angel ta curo wuƙar ta miƙa mashi yasa hannu ya kar6a, ƙiris ya rage ta fashe da kuka kamar jira take su fita, ta yi wani irin kukan kura ta daka tsalle ta faɗama danish, kokawa ta 6arke a tsakaninsu bugu ta shiga kai mashi, ta yakushe shi da akaifun hannunta, hada cizo ta gartsa mashi gefen wuyan shi, 

  Su batool suna ta ƙoƙarin rabata da jikin shi, amma ina duk wanda ya yi gigin ta6a ta wurgi take yi da shi, daƙyar haris ya cakumota, rai a 6ace ya yi wurgi da ita gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya bugu sosai, 

  Zuƙunnawa su kayi agaban danish dake yashe ƙasa yana fitar da numfashi sama sama, farar fatar wuyan shi tayi jawur ga sahun haƙoran angen nan tamkar an zana su, duk ta 6ata ma shi wuya da yakushi red marks ta ko'ina,

  Ran kowannan su sai da ya 6aci, musamman haris, rai a 6ace ya ke faɗin 

  "Dama ae ba sonshi ki ke yi ba, shiyasa ki ke son kashe mana shi, na rasa me danish ya yi maki, bafa shi bane ya yi silar zuwanki prison ɗin nan ba, ballanta na kice xaki ɗauki fansa a kanshi, ki bar ganin ana jin tsoronki, Allah daga yau idan kika kuskura kika ƙara ta6a fatar jikinshi saina karairayaki,


  ɗagowa angel tayi idanuwanta sunyi jawur, batool da aziza suna a 6angarenta,


   Cikin shessheƙar kuka tace"Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da rai na, meyasa zai ce na ɗauki wuƙa? Ina ruwan shi? Idan har bai shiga hurumina ba ni zan shiga nashi ne"? Ta yi tambayar a ƙule,

  Batool tace"ban goyi bayan wani a cikin ku ba, Amma laifin danish nafi gani, meyasa za ka tona mata asiri don ta ɗauki wuƙa? Menene naka aciki? Juyawa ta yi kan angel'ke kuma angel baki kyauta ba, kalli yadda kika raunta shi, sai kace ba ɗan uwanki ba...."tunkafin takai ƙarshen maganar angel tace"danish bazai ta6a zama ɗan uwana ba, bana son shi bana ƙaunar ganin shi," 

  Jinjina kai batool ta yi"its okey, daga yanzu zan shiga tsakanin ku, kada wanda ya ƙara shiga hurumin wani ina fata hakan ya yi,"

  Javed yace"idan ma suka ƙara ni da kaina zan sanar ma tsohuwa a ɗauki mataki akansu,"

  daga haka Haris da su mubeen suka kama hannun danish su kayi mashi jagora zuwa saman gadonshi, kwanciya saman gadon ya yi bawan Allah har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi, shifa bakomai yasa ya tona ma angel a sirin ta ɗauki wuƙa ba, face sanin irin tsanar da tayi mashi, tsoron shi kada ace shi zata yanka da wuƙar wannan dalilin ne yasa shi tona mata asiri, ashe da rabon yaci na jaki a hannunta, 

  Miƙa mata hannu azeeza ta yi"ki tashi muke ki kwanta, ki huta" sai da ta ɗanyi jim kafin ta ruƙo hannun azeeza ta miƙe, saman gado ta koma ta zauna, hawaye sha6a sha6a akan fuskarta, danish ya tarwatsa mata plan ɗinta, taji takaici kamar ta sanya pillow ta taushe ma shi fuska haka take ji,

   "Angel me zaki yi da wuƙa"? batool ce ta yi mata tambayar, ɗagowa angel ta yi tare da kallonta, tana a tsaye gefen gadonta,

   Girgiza kai ta ɗanyi"babu komai, kawai inaso na mallake ta ne," ɗan zaro ido batool ta yi"karfa ace wani kike harin kashewa a cikin mu" cikin zolaya ta yi mata maganar,

  Cikin sanyin murya angel tace"a'a batool bazan iya kisan kai ba, ni kawai naso ace na mallaki wuƙar,"

   "Da ace kina shiri da danish, da ya aro maki wuƙar shi," da mamaki angel ta kalle ta tare da cewa"yana da wuƙa"? Jinjina mata kai ta yi eh, akwai wata ƙaramar wuƙa da yake amfani da ita wurin datse gashin kan shi, tsohuwa ce ta bashi wuƙar lokacin da ya ta6a tambayarta yana so ya rage tsayin sumar kanshi, shi ne ta ba shi wuƙar to bai mayar mata da ita ba, har yau tana nan a wurin shi,"

  Dafe kai angel ta yi tare da satar kallon danish dake a kwance saman gadonshi, da alama bacci ya yi awon gaba dashi, yadai sha wahala,

    "Ga samu ga rashi" ta ambaci hakan acikin azuciyarta, tasan koda me take yawo danish bazai ta6a ara mata wuƙar shi ba 

      Kallon batool ta yi"kinsan inda yake 6oye wuƙar" kallon sama batool ta ɗanyi da alama tunani take yi, can tace"a ƙarƙashin katifar gadonshi naga yana 6oye ta,

      Angel tace"ki taimaka kice ya ara maki ita a matsayin ke zakiyi amfani da ita,

      Ɗan zaro ido batool ta yi"ae bai yadda ya fiddo da wuƙar nan, kaifi ne da ita tana da haɗarin gaske, kona tambaye shi bazai bani ba, saboda yasan ba abun da zan yi da ita,"

      Jinjina kai angel ta yi"shikenan na haƙura" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma ta kwanta amma fa bawai ta haƙura bane, a can cikin zuciyarta tana shirya yadda zata sace wuƙar danish batare da sanin shi ba, da wannan tunanin ta yini da shi kuma ta kwana,

  

      A daren yau ta kammala shirya yadda zata ɗauke wuƙar, kowa ya yi bacci saman gadonshi, duk sun lullu6e da bargunansu, angel ce kaɗai idonta biyu tana kwance idonta na fuskantar ceilling duk da duhu babu wadataccen haske saina fitilun ɗakinsu da suka kunna,

    

   "Lokaci ya yi da zan tashi inje saman gadon danish in ɗauke wuƙar sa," acikin zuciyarta ta yi maganar, tana ƙoƙarin miƙewa tajiyo takun tafiyar mutun acikin ɗakin nasu, da sauri ta koma ta kwanta cike da fargabar wanene a dai dai wannan lokacin ya faɗo masu ɗaki,

    Ƙyalla ido ta yi daga kwancen da take tana satar kallon inda take jiyo sautin tafiyar, kaskon turaren wuta ta hango a hannun mutumin dake zarya cikin ɗakin nasu, wani irin baƙin hayaki ke tashi daga cikin kaskon, kamar ana turara turaren wuta,

  Mutumin dake ruƙe da kaskon turaren wutar, jikin shi na a sanye cikin doguwar riga me hula launin ja, rigar har ja take ƙasa,

  Kasa kunne angel tayi tana sauraron muryar mutumin dake magana, kamar muryar tsohuwa sai dai bata iya tantance da wani yare ake magana ba, wani irin gu6ataccem yare mara daɗin ji,

    Nan fa hankalin angel ya ɗan tashi, xufa ta wanke fuskarta, duk ta sha jinin jikinta, tsoro take ji kada ace wani mugun ne yazo cutar da su,

  Bata kai ƙarshen zancem zucin nata ba, ta hango mutun yana tafiya a bakin gadajen su Hannah, yana tafiya yana hura masu hayaƙin zuwa saman jikin su,

  Da sauri angel taja bargo ta lullu6e fuskarta, acikin zuciyarta tana ambaton la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalamin," lokacin da mutumin yazo saitin gadonta, da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyun ta toshe bakinta da hancinta, duk don saboda kada hayaƙin ya samu damar shiga jikin ta,

    Tana jiyo takun tafiyar mutumin yadda kasan takun tafiyar jaki,

     Lokaci ɗaya tadaina jin takun tafiyar da kuma surutan da mutumin ya ke yi, da sauri ta ya ye bargonta, tabi ko'ina da kallo bata ga kowa ba, alamar mutumin ya tafi, sai dai hayaƙin daya turara masu har yanzu bai gushe ba,

      Saukowa angel tayi daga saman gadonta, Zuciyarta cike da ruɗani, ko wanene mutun nan daya zo masu a tsakiyar dare, sanye da jajayen kaya? Turaren menene yake hayaƙa masu a cikin ɗakinsu da kuma saman jikin su? sam bata yadda da hayaƙin nan ba, tafi tunanin wani mugun abunne aka turara masu,

      Tunawa ta yi da surori da kuma  addu'o'in da malaminsu na makatantar islamiyya ya ta6a koya masu yace su yawaita karansu domin neman kariya daga sharrin mutun sharrin aljan da duk wani abun cutarwa,

  "Zan tai taimaka masu, saboda basu da maiyi masu addu'a, a kullum in na kwanta ina bacci, daddyna yana yi mun addu'a, su kuwa basu da iyayen da zasu yi masu addu'a" acikin ranta tayi maganar  

      Kamar yadda mutumin nan yabi ko'ina na ɗakin yana turara Masu baƙin hayaƙin nan, itama haka ta soma bin kowace kusurwa ta ɗakin nasu tana karanta Ayatul kursiyyu, da amanar rasuli, Suratul mulk, Suratul kafiroon, Suratul ikhlas, falaqi da nasi, duk in ta karanta kowannan su Saita maimaita, daga bisani tabi kowani gado tana tottofa masu addu'oin saman bargunan da suka lullu6a da shi, daga kan gadon hanna ta faro xuwa gadon mubeen har zuwa gadajen su batool, tana zuwa kan gadon danish taja guntun tsoki zata wuce, sai kuma taji aranta kamar bata kyauta ba, don me zata yi ma kowannan su addu'a amma shi ta kasa yi ma shi saboda me? Lafin me ya yi mata? shiru ta yi tana tunani, menene ribar ta idan taƙi yi mashi addu'a, 


      Har ta kusa wuce gadon shi taja da baya ta koma tare da shiga daga gefen gadon, ranƙwafawa ta ɗanyi saitin fuskarshi ta soma karanto addu'o'in bayan ta kamalla ta tottofa mashi saman fuskarshi, kamar daga sama taji an damƙi hannunta, a razane ta kalle shi ashe ya farka, muryar shi a disashe yace"tsanar takai har ki zo kan gadona kina tofa mun miyau asaman fuskata"? Zuba ma shi ido angel ta yi batare da tace Furta komai ba, tama rasa bakin magana, yadda ya yi mata maganar ita kanta ta yi mamaki sai kace ba wannan mai jin shakkartata ba, bakomai yake jima tsoro ba, face wannan kalmar da take faɗi na cewa zata tofa ma mutun charman dudu Cikin shi ya kumbura, tuna wannan yasa shi ƙara tsorata, shi kanshi baisan yana da ƙwarin gwiwar yi mata magana irin haka ba,

      tsawa ya ɗanyi mata tare da cewa"Ba ki ji ina magana ba"? Still ta yi ma shi shiru saboda bata jin zata iya faɗa mashi cewa addu'a take yi mashi, don ma kada yaji kamar tana ƙaunarsa ne,

      Ganin ta yi mashi shiru ya ƙara har zuƙa, A tsananin tsorace Ya damƙo ƙasan rigarta da ƙarfi da niyar ya goge abunda ta tofa ma shi asaman fuskar shi, Cikin rashin sa'a ya janyota gaba ɗaya ta faɗa saman jikin shi..................🥱


  (Nasha wahala wurin haɗa page ɗin nan, Jiki duk ba lafiya, To jama'a Mu haɗu Next page  in Allah yakaimu da rai da lafiya) Game neman ƙarin bayani 08103884440) 

     Boss Bature ce✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post