Kurkukun Ƙaddara episode 15 complete

Kurkukun Ƙaddara episode 15 complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dada alƙalamin Boss Bature


E15


Cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, hawaye ta ko'ina akan fuskarta, tabbas jikin kowannan su ya yi sanyi, banda mutun biyu, danish dake kwance saman gadon shi sai Haris dake zaune ƙasa ya dafe cikin shi,

   Saukowa batool ta yi tare nufar inda angel take tsaye agaban tsohuwa, ta dafa shoulder ɗinta"I feel ur pain angel, abun da ciwo labarin ki akwai ta6a zuciya, dole kiji ɗaci aran ki, kuma dole ki ƙuntata acikin kurkukun nan, abunda yasa kika ga mu ba mu damu ba saboda bamu da wanda zai yi kukan rashin mu! Mu matattu ne a idon jama'a kamar yadda tsohuwa ta faɗa mana, a gidan nan aka raine mu agidan nan muka taso, tunda mu ke bamu ta6a yin tozali da hasken daya fito daga wajen kurkukun nan ba, ina yawan tambayar kaina koya wajen kurkukun nan zai kasance? Ya mutanan dake rayuwa a wajen sa su ke? Bani da amsar tambayata amma ina fata wata rana nima wata rana in fita daga cikin sa, sai dai nasan abune mai wuya......" cikin sanyin murya takai ƙarshen maganarta,

  "Zan iya zuƙunnawa saman gwiwowina in roƙe ki akan ku fitar dani daga cikin kurkukun nan, inaso na rayu cikin ƴan uwana" angel ce ta yi maganar  muryarta a rauna ce,


   Jinjina kai tsohuwa ta yi a yayin da take binsu da kallo da waɗannan kwarkwararrun idanuwan nata, tsawon mintuna kafin tace"koda ace kin zuƙunna saman gwiwowin ki don ki roƙe ni akan in fitar dake daga cikin prison ɗin nan, hakan bazaiyi aiki ba idan ku ka yi haƙuri a sannu zaku fahimci manufar wannan kurkukun na tara ku acikinsa, Amma a yanzu shawarar da zan baku shi ne, ku so junan ku tun da baku da kowa ku xama naku ku kaɗai, ku kasance masu faranta ma juna" daga haka bata ƙare cewa komai ba, ta dogara sandarta tare da juyawa tana ɗangyala ƙafa ta nufi cikin ɗakinta, tana shiga taja ƙopa ta datse,


  Zubewa angel ta yi saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsancin kuka mai cin rai tamkar ranta zai fita,


   Rankwafawa batool ta yi tare da ruƙo hannayen angel cikin nata, ta miƙar da ita tsaye, ta rungumeta ajikinta tana lallashin ta, sun ɗauki tsawon mintuna, kafin ta raba jikinsu, 


  Kallon sauran ƴan uwan nasu ta yi, kowa yana a tsaye banda Danish dake kwance


   Ɗaya bayan ɗaya ta shiga kiran sunayen su"Hannah, Hibba, deeja parveen, Eve, yasmin, rubina, Aziza" kowa ya kasa kunne yana sauraron abunda zata ce masu, juyawa tayi kan mazan dake acikinsu ta ambaci sunayen su one by one"Danish, javed Haris, mubeen, naufal" sai faman huci haris yake yi saboda haushin bugun da angel ta yi masu,

   Calmly ta soma magana cikin sanyin murya"kamar yadda tsohuwa tace mu so junan mu, Let's consider ourselves as blood relatives, inaso mu yi ma juna alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, Sa'annan bana jin daɗin yadda ku ke ware angel acikin mu, i thought we are all the same, bamu da banbanci jinsi ɗaya ne mu da ita duk abu ɗaya ne, idan ba mu so juna ba, wa zamu so? Nasan kuna jin haushin angel ne saboda abubuwan da take yi wanda bakomai ya jawo hakan ba face ƙuntata rayuwarta da a ka yi, taya mutumin da ya saba rayuwar shi a sake rana ɗaya a tsamo shi daga cikin danginshi a kawo cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA! taya bazai ƙuntata ba"? dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana bin fuskokin su da kallo, 

  "Batool ni dai inason Angel, kuma bazan ta6a faɗa da ita ba, zan ɗauke ta tamkar yadda na ɗauki kowannan ku," bakowa bace ta yi maganar fa ce AZIZA, yarinya ce me ƙarami jiki fara ce sosai duk cikin su babu me gajartar ta, 

   ɗaƙyar angel ta iya buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗaura su akan fuskar aziza da ta yi maganar, ba ƙaramin son yarinyar ta ji ba, saboda ita kullum a cikin fara take baka ta6a ganin fuskarta a ɗaure,

   "batool, nima xan ɗauke ta tamkar yar uwata," kallon wadda ta kuma yi magana angel ta yi, hibba ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

  Lumshe ido angel ta ɗanyi tare da buɗe su tana ci gaba da kallon su, 

  "Nima na goyi bayan Batool, angel tamkar ƴar uwa take acikin mu" acewar Parveen 

  Murmushi batool ta ɗan saki, har cikin zuciyarta ba ƙaramin daɗi taji ba,

  Miƙa hannunta na dama tayi saman iska tare da kallonsu tace"ina so muyi wa juna alƙwarin kasancewa atare, zamu so juna kuma zamu taimaki juna, sannan babu faɗa atsakaninmu kuma babu nuna wariya, duk wanda ya amince ya ɗaure tafin hannun shi a saman nawa,"

  Angel ce ta fara ɗaura tafin hannunta saman na batool, matsawa aziza ta yi itama ta ɗaura nata hannun, Hibba ta ɗaura nata parveen ma ta ɗaura nata, kallon sauran Batool ta yi ganin sun ƙi matsowa su ɗaura nasu hannuwan,

  "Duk wanda bazai so zaman lafiya a cikin mu ba, babu ruwan mu da shi domin kuwa baya atare da mu"

  Jin wannan maganar da batool ta yi yasa Eve ta matsa ta ɗaura nata hannun, rubina ma ta sanya nata, mutun biyu suka rage Cikin mata basu sanya hannayensu ba, deeja da yasmin Sai kuma mazan su, don shi danish har yanzu bai motsa daga saman gadon shi ba, 


   Zuba masu ido batool ta yi tana bin sauran da su ka rage da kallo, Masu girman kan Cikin su,


   "Idan har baku ɗaura hannayen ku ba, kada ku yi tsammanin idan wani abu ya faru da ɗaya daga cikin ku, xamu share mashi hawayen shi,"


   Gyaɗa kai Javed ya yi tare da kallon su haris, kafin ya wuce su zuwa inda su batool su ke A tsaye shima ya ɗaura hannun shi fuskar shi ɗauke da murmushi ya ce"Nima ina goyon bayan ki batool, kuma ina ba angel haƙuri akan irin wariyar da muka nuna mata" yakai ƙarshen maganar idanuwan shi akan fuskar angel, itama kallon nashi ta ke yi, har cikin ranta taji daɗin waɗanda suka nuna suna sonta,

    Matsowa kusa Yasmin ta yi, "idan muka yarda da junanmu, muka so junanmu  tabbas xamu cimma nasara, nima ina goyon bayan batool," takai ƙarshen maganarta tare da ɗaura hannunta saman nasu,

      Kallon deeja su ka yi  dake a tsaye ta toge saboda haushin angel take ji,

      Matsawa mubeen ya yi da sauri haris ya ruƙo hannun shi"badai zuwa zaka yi ba"? Jinjina mashi kai ya yi"zuwa zanyi, saboda inason mu samu maslaha a tsakaninmu," ya janye hannun shi daga ruƙo da ya yi mashi, ya wuce wurin su shima ya ɗaura hannun shi, murmushi batool ta saki tana kallon shi, 

      Kallon haris naufal ya yi tare da cewa" am sorry bro but am not supporting, also am advising u, ka aje makaman yaƙin ka kazo mu rungumi junanmu," yana kai ƙarshen maganar shi yaje wurin su, sai da ya fara kallon angel ya sakar mata murmushi kafin ya sanya nashi hannun, kallon kallon aka koma yi a tsakanin Deeja da haris da kuma mr arrogant dake kwance saman gadon shi, ganin suna kallon shi yasa shi rufe eyes ɗinshi tamkar mai yin bacci, tasan indai ba sanya hannun shi yayi ba, haris bazai ta6a supporting ɗinsu ba, gyaɗa kai ta yi tare da kallon deeja tace"ke baza ki goyi bayan mu ba? Bana so ki yi abunda zaki yi danasani, duk wanda bai sanya hannun shi ba, to baya a tare mu" 

      Kallon harris tayi ganin yana maƙe mata wuya alamar karta shiga cikin ku, ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kan fuskar batool, ganin ba ta da mafita yasa ta shiga cikin su, itama ta sanya nata hannun 

      Murmushi batool ta saki, kafin ta ce su maimaita duk abunda tace, suka amsa mata da toh, alƙawari ne suka ɗaukarwa juna,

      Banda mutun biyu Haris da Danish, bayan sun kammala yi ma juna alƙawari gaba ɗaga suka shiga rungume junansu, a yau suna jin kansu tamkar ciki ɗaya suka fito, 

   Bayan kowannan su ya samu natsuwa, Batool da angel su ka kalli juna, lokaci ɗaya suka sakar ma juna murmushi,

   "Idan zaki shiga toilet, muje tare nima ina so zanyi wanka,"


  Gaba ta yi angel tabi bayan ta, har zuwa ƙopar shiga toilet ɗinsu hannu batool ta sanya tare da tura ƙopar suka shiga daga ciki, ƙofofi ne kusan guda uku kowanne a rufe ya ke, ɗaya daga ciki angel ta shiga, itama batool ta buɗe ɗayan toilet ɗin ta shige ciki,


 Sai yau ta samu damar ƙarewa toilet ɗin kallo na ƙurulla, ko'ina a tsaftace ya ke, sai dai babu wadatattu kayan amfani, akwai dai toilet seat, sai shower ta tsaye wani ajiyayye bucket, kwandon wanka me ɗauke da soap and  sponge, a kwai cabinet dake ɗauke da sabulai da hada ledar detergent da kuma Shampoo ɗaya, saman ceilling ta wurga idonta, wasu munafukan tagogi ne kusan uku, masu murfin ƙarfe an garƙame su da kwaɗo jikin su har ya yi tsatsa, mayar da idanuwanta ta yi akan tagar  jigin bango guda ɗaya jikinta wani tsohon glass ne duk yayi ƙura, tunani ta shiga yi idan har zata iya samun makamin da zata iya fasa glass ɗin jikin glass ɗin da shi tabbas zata iya kutsawa ta cikin tagar ta dira ta baya, daga nan zata samu damar shiga cikin kurkukun taga me ke wakana, jinjina kai ta yi tare da cewa"I will try", sauke idanuwanta ta yi akan tukunyar fular dake ajiye daga ƙasa jikin bango tana da girma, fulawar  cikinta duk ta yagalgale saboda rashin kulawa, ta6e bakinta ta yi kafin ta mayar da idonta kan igiyar da ke a ciki da a lama ta sagala kaya ce, 

  tafiya ta soma yi tana bin kowace kusurwa ta makewayin da kallo, bakin magudajin da ruwa ke bi ta tsaya wasu ƙananun hudoji ne da basu fi shida ba, tanan ruwa yake bi ya wuce, akwai wasu fanfuna guda biyu da su ke a kashe,


     Sai da ta kammala bin ko'ina da kallo tukunna ta sanya hannayenta ta kamo ƙasan rigarta, ta cireta tare da rataya ta saman igiyar, 


  "Ko madubi babu da mutun zai kalli fuskarsa, ta ya zan gane ina ƙara kyau ko muni nake yi"? tayi maganar acikin zuciyarta,


   Bokitin nan ta janyo tare da tara shi gaban fanfon ta kunna, ruwa ya soma bulbulowa daga cikinsa, tafi sha'awar ta yi da bokin akan ta kunna shower,


   Zuƙunnawa ta yi tana jiran ruwan ya cika, kamar daga sama taji an banko ƙopar toilet ɗin da ta ke ciki, A gigice ta ɗago tare da wurga idonta kan door ɗin don taga wanene ya shigo,


   *DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe da rigar shi, tun daga ƙasa har sama take kallon shi, kamar wani bugagge sai faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, shafaffan cikin shi tamkar wanda bai ta6a cin abinci ba, ranta a matuƙar 6ace ta miƙe saboda tsabar fusata bata ɗauki rigarta ta sanya ba, ta rufe shi da faɗa" kai wani irin jaki ne ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko?

  Tunda ta soma balbale shi da masifa bai yi yunƙirin tanka mata ba, kuma bai motsa ba ya dai yi kasaƙe yana kallonta, sai da takai ƙarshen maganar tana haƙi cikin sanyin murya yace"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."kafin ya kai ƙarshen maganar, ta sunkucin bokitin ruwan da ta tarba, gaba ɗaya ta sheƙa mashi ruwan a jikin shi, sharkaf ta jiƙa shi,

  Runtse idanuwan shi ya ɗanyi saboda ruwan daya shiga ciki, long eye lashes ɗinshi sun jiƙe sharkaf, hannu ya sanya tare da share ruwan dake akan fuskarshi, kafin ya buɗe idanuwan shi, ta yi saurin ɗaukar rigarta da ke a saman igiyar ta zurata a jikinta,

  Tana huci ta ci gaba da kallon shi tana fadin"Zaka fita ko saina ƙara watsa maka wani ruwan? Ƙaton banza kawai matsalar ace mutun baida addini kenan, ko dabba tafi shi kan gado,"

    A lokacin ya ƙarasa buɗe idanuwan shi, jinjina kan shi ya yi still bai tanka mata ba, ya juya ya fita daga cikin toilet ɗin,

  Lamarin ya ɗaure mata kai, har ta soma tunanin kodai yana da ta6in hankali ne? In ba haka ba taya zai faɗo mata bagatatan Cikin toilet batare da ya tambayi ko akwai mutun aciki ba, idan ma ya yi tunanin babu kowa ne why bazai yi knocking ba? Guntun tsoki taja, aranta tace"Amma dai wannan anyi sullu6iyo, Shashasha sauna, next time idan ya kuskura ya ƙara faɗo mun irin haka, saina koya ma shi hankali," takai ƙarshen maganar tare da nufar ƙopar toilet ɗin da nufin ta rufe, hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙopar, shiru ta ɗanyi jin alamun bai tafi ba, zurfi tunani ta shiga lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin ta manta bata yi locking ɗinta ba, kodai ya yi tunanin babu mutun ne shiyasa ya faɗo ciki? Don ta lura Haka suke yi idan suka ga ƙopa ba a datse ba, shi ne babu mutun a ciki, idan kuma suka ganta a datse to shi ne ke da akwai mutun, kenan itace ta yi ba dai dai ba? Da ace ta rufe ƙopar danish bazai iya shigowa ciki ba, 


   Ta6e baki ta yi, ta tura ƙopar ta rufe, ta koma ciki domin yin wanka,

 Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin wankan, ta mayar da kayan jikinta, ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, tana buɗe ƙopar ta same shi a tsaye ya jingina bayan shi jikin bangon toilet ɗin, da alama  jira yake ta fito ya shiga,


   Wuce shi tayi zuwa cikin ɗakin,

  A tsaitsaye ta same su, banda mutun biyu Batool da Aziza, 

  "angel" hannah ce ta kira sunanta, ƙarasawa ta yi kusa da ita ta tsaya,

   Fuskarta ɗauke da murmushi tace"kin fito kenan,  nima wankan nake so inyi ina jira su batool su fito sai in shiga,"

   "Idan ku kayi wanka babu wani abu da ku ke shafa ma jikin ku"? Angel ce ta yi mata tambayar,

   girgiza mata kai ta yi tare da cewa babu, mu ma haka muke zama duk in mu ka yi wanka,

   "Comb fa? Ina so in taje gashin kaina",

 "Guda ɗaya ne muke da shi, kuma yana a wurin danish, da shi muke amfani in kina so sai in aro maki," da sauri tace"a'a na fasa" aranta kuma tace komai danish danish sai na koya mashi hankali, sullu6uyo kawai,


   Tafiya ta yi zuwa gefen gadonta, ta zauna tana bin kowannan su da kallo,


  Motsi buɗe ƙopa su ka jiyo daga can kusurwar da benan ya ke,


  Nan fa su Hannah suka fara murna sunsan abinci ne za'a kawo masu,

 

  Takun tafiyarsu tamkar na dawakai, saukowa su kayi daga saman matattakalar benan, Giants ne

  Hannayen su ɗauke da farantai, shiga ciki su ka yi a dai dai saitin carpet ɗin nan suka ɗaura sauke tray ɗin,


  Kafin su ka ja baya tare da goya hannayen su saman ƙirjin su, 


   Fuska a ɗaure angel ke kallonsu, ko gunki bazai nuna masu iya tsayuwa ba, abun na ci mata tuwo a kwarya, wai su waɗannan mutanan su wanene? Basa ji basa magana, kullum kuma cikin shiga iri ɗaya kuma sun 6oye ainihin suffar su, 

  Jin jina kai ta ɗan yi aranta tace"A sannu zan gano ko su wanene ku,"


   "Angel ki taso mu ci" Hibba ce ta kirata ganin ta yi zugudum saman gadon,


  Saukowa ta yi tare da tunkarar inda suke zaune itama ta zauna gaban farantan, ta lanƙwashe ƙafafunta, mutun uku suka rage basu ƙaraso ba,

 

  Javed yace"wai ina danish ya ke ne? da su batool, wani yaje ya yi masu magana su zo mu ci," yunƙurawa haris ya yi da niyar yaje ya kirasu sai gasu sun fito daga cikin ƙopar shiga toilet ɗin a tare, komawa ya yi ya zauna, gefen angel batool da aziza su ka zauna, danish kuma ya zauna gefen javed, yana fuskantar angel tun da suka haɗa ido, ta wurga mashi harara tare da murguɗa ma shi  small mouth ɗinta,


  Bin ta ido kawai ya yi, don baima san menene ta ke yi ba, haushin shi take ji ta ƙara jin tsanar shi saboda sharrin da yayi mata, da ya ce ƙirjinta kamar bangon ɗakin su, tsohuwa ma tafi ta abun kirki, kalaman nan sun baƙanta mata rai, kuma taci alwashin sai ya ɗanɗani kuɗar shi,


  Batool ce ta ya ye jan ƙyallen da aka rufe saman trays ɗin, Hamburger suka samu tare da chicken legs na ƙosassun kaji anyi masu jar suya har wani maiƙo suke yi, kowa zai samu burger ɗaya da kuma Chicken leg ɗaya, a tray na biyu Tea pot ne sai jerin wooden Cups, faranti na ƙarshe basket ne mai ɗauke da kayan marmari, a gefe ɗaya kuma bottle waters ne' fuskar kowannan su awashe, baƙaramin daɗi suka ji ba, duk da sau ɗaya ake a basu abinci arana, Amma suna Ci su ƙoshi wani lokacin ne ba'a basu abun da zai ƙosar dasu, amma yau kam ba laifi, kowannan su Tunanin wanda zai rage yaci da anjima yake yi,

   Batool ce ta zuzzuba masu kakkauran tea a kowani Cup, ta miƙa masu ɗaya bayan ɗaya, kusan atare suka kai  baki suna sha, Idonta idon danish Sun hana juna sakat, gani take kamar wani abun yake ayyanawa aranshi tun da ya ganta babu riga a jikinta, nan take ta murtuƙe fuska, a ƙule tace"Stop looking at me" 

 "Ae bani ke kallon ki ba, ke kike kallona," amsar daya bata kenan, daga haka ya ɗauke idonshi daga kanta, ya kai hannu ya ɗauki burger ɗinshi yana ci, 

  Yunƙurawa tayi tare da miƙewa, kowa yabi ta ido, batool tace"Har kin ƙoshi"? Fuskarta a  hautsine tace"Zan ajiye ne da anjima inci" takai ƙarshen maganar tare da kai hannu ta ɗauki Chiken leg ɗinta, ta ɗibi fruits, ta kuma ɗaukar bottle water ɗaya,' duk fa don saboda danish tabar wurin, Saman gadonta ta koma ta zauna, kuma still bata daina kallon shi ba, lamarin ya ɗaure ma shi kai, shi dai baisan zunubin daya aikata mata ba, sam ta tsani ganin shi, abunda bata sani ba danish mugun shakkarta yake ji, shifa har yanzu kallon monster yake yi mata, bai yarda cewa itama mutun ce kamar su, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi gadon batool, ta zuƙunna bakin gadon ta zura hannu a ƙarƙashi ta janyo kwandon da batool ke ajiye ragowar abincin ta, a ciki itama ta ajiye Fruits ɗinta, apple uku sai ayaba guda biyu, ta raba cinyar kazar biyu ta tura rabi aciki, rabin kuma anan zuƙunne ta cinye ta, tana kammala ci ta buɗe murfin robar ruwan tasha rabi, bayan ta gama ta rufe kwandon, ta tura shi Ciki, kafin ta miƙe hannunta ruƙe da bottle water ɗinta, ta koma saman gadonta, daga ƙasa ta ajiye bottle ɗin, 


 a lokacin suma sun kammala cin nasu abincin, wasu sun rage cinyar kazarsu, wasu kayan marmari suka rage, kowa dai ya ɗauki robar ruwanshi don ya ajiye zuwa anjima,


  Tattara kayan abincin giants su kayi, A jere suka fuce daga cikin ɗakin, prisoners kowa Ya koma saman gadon shi, Anci an ƙoshi saura bacci, aikin su kenan Abun ba ƙaramin ɗaure wa angel kai yake yi ba, wai su kwata-kwata basa gajiya da rayuwar kulle? Daga ɗaki sai toilet, daga anci abinci kuma sai hawa gado ayi bacci, anya kuwa suna da lafiyar kwakwalwa?

 

 Ganin da gaske bacci za suyi yasa tayi saurin cewa""Wai ku baku tunanin fita daga cikin kurkukun nan? Ko baku da ra'ayin yin rayuwar ƴan ci ne, Cikin mutane? 


   "Ta ya zamu sanyawa ranmu fita daga cikinsa, bayan tsohuwa ta faɗa mana cewa mutanan dake awajen kurkukun nan baza su ta6a ƙaunar mu ba, wahala zamu sha tunda bamu da kowa a ƙarshe ma akashe mu da ranmu," yasmin ce ta bata amsa,


  Rubina tace" bamu da kowa tsohuwa itace gatan mu, taya zamu yi tunanin barin kurkuku bayan babu ƙofar fita daga cikin shi? idan mun fita wurin wa zamu je"?


  Guntun tsoki angel taja"daga anyi magana sai kuce tsohuwa, bansan me ta jiƙa ta baku kuka sha ba, wanda har ya gusar maku da tunanin ku, Amma ni inada tabbacin ba hakanan aka ƙyale ku ba, saboda babu mutumin da zai juri a kulle shi, tamkar yadda ake kulle dabba,"


  Harara danish ya jefa mata, dama haushin ta yake ji, bai dai ce komai ba haris ne yace"yanzu kina so mu yadda dake mubar 6angaren tsohuwa? Wai ke da me kike taƙama ne?  idan bakisan wacece tsohuwa ba, bari in ƙara tunasar dake, itace ta raine mu ta kuma gatanta mu, bamu da tamkarta a duniyar nan,'


  Cike da takaici angel tace"dukkan ku baku da tunani, bakusan ciwon kan ku ba, Ni bansan taya zan fahimtar daku ba, gidan kurkukun nan ba alkhairi bane, gatan da kuke faɗin tsohuwa ta baku, ba gata bane gata shine abar mutun ya yi rayuwar ƴanci, amma ku an killace ku, an hana ku ganin hasken rana, acikin kurkukun ma an yi maku iyaka da shiga ko'ina, a rana sau ɗaya kuke samun abinci, an haɗa maza da mata ɗaki ɗaya suna kwana shin wannan gata ne? Kullin mu ne yawo cikin uniform kala ɗaya, wai ku baku gajiya da rayuwa a kulle ne? Kuyi tunani mana babu alkhairi atattare da kurkukun nan"


  Murmushi Batool ta ɗan saki, kafin tace"angel, dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa indai akan tsohuwa za ki yi magana babu wanda zai ta6a fahimtar ki, its better ki yi shiru da bakin ki, yadda kika ganmu kibar mu kawai mu haka ƙaddarar tamu rayuwar take a cikin kurkuku"


  Shiru angel ta ɗanyi, sai lokacin ta ƙara tabbatarwa kanta cewa An gama dasu tabbas ba hakanan tsohuwa ta ƙyale su ba, batasan wata irin huɗu ba ta yi masu ba, da har suka gaza fahimtar dai dai, taso ace sun yarda da maganarta ta hakan ne zasu haɗa hannu wurin nema ma kansu mafita, sai dai kash sunƙi bata haɗin kai,


  "Ina son fita daga cikin kurkukun nan, amma bansan meyasa ba, bana jin zan iya rayuwa awajensa, a duk lokacin da nayi tunanin fita daga cikinsa sai inji ƙunci da raɗadi suna taso mun acikin zuciyata" javed ne ya yi maganar, 


   "Nikaina ina sha'awar wata rana in ganni awajen kurkukun nan, but i don't know why bana jin zan iya fita daga cikinsa koda na samu damar yin hakan"


  Kasa kunne angel ta yi tana sauraron su kowa yana tofa albarkacin bakinsa, banda Danish, da ya lumshe idanuwan shi tamkar mai yin bacci,  


  "Tsohuwa ba gaskiya take faɗa maku ba, nasan zaiyi wuya ku fahimce ni, amma kuyi tunani mana, Kowani ɗan adam Da Allah ya halitta A duniyar nan, ba daga sama ya faɗo ba, shin kun ta6a tunanin Ina iyayen ku su ke? Meyasa kuka kasance marayu? Idan iyayen ku sun rasu ina danginku su ke?  Idan na baku labarin rayuwata ina da tabbacin zaku fara kwaɗayin yin rayuwa a wajen kurkukun nan, kuma zakuyi tunanin Ina iyayen ku da dangin ku su ke......." muryar Deeja ce ta katse mata xancen nata da cewa,


  "Kince kowani ɗan adam da Allah ya halitta? Waye ɗan adam ɗin kuma wanene Allahn da kike magana akai" 


  Mamaki ƙarara akan fuskar angel ta ɗago tana kallon deeja dake zaune can saman gadonta, fuskarta babu alamun wasa ta yi tambayar,


  Speechless sam ta kashe mata baki, tsabar mamakin tambayar da Deeja ta yi mata, har wani shock taji, sai lokacin ma ta tuna dasu wa take magana, ta jima tana mamakin wannan ikon Allahn, Gaskiya yaran nan an cuci rayuwar su, basu san komai ba game da wanda ya halicce su, wato su kawai rayuwa suke yi kara zube,


   "Kinyi shiru baki ce komai ba"? Deeja ce ta yi maganar, jin tayi shiru bata ce komai ba, buɗe baki angel ta yi da niyar ta bata amsar tambayarta, ba zato ba tsammani taji an daki kokwan kanta, wani irin duhu cikin idanuwanta, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta dake yi mata raɗaɗi muryarta na kerma ta shiga ambaton"LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!" gaba ɗaya suka tsareta da ido ganin ta runtse idanuwanta, Jikinta na kerma, da sauri batool da su hanna suka sauko daga saman gadajensu suke nufi gadon angel, Suna tambayarta lafiya meya faru, bata basu amsa ba, jiki ba ƙwari ta sulale saman mattress ɗinta ta kwanta, 

  Kallon juna su ka yi cike da tsantsar mamaki, 

  Hanna tace"Anya kuwa lafiya? Kodai bata jin daɗin jikin ta ne" miƙa hannu batool ta yi saman wuyan angel ta shafa shi, Sanyi taji sosai " kallon su tayi"lafiyarta qalou, bacci ta ke yi,"

  Sautin dariyar Haris suka ji, a tare suka juya suna kallon shi, hannun shi rungume da pillow, 

  "Dama karta farka, kowa ya huta"

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post