Kurkukun Ƙaddara Page 16

Kurkukun Ƙaddara Page 16

 


💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E16


Daga alƙalamin Boss Bature


*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*


Hararar shi batool ta yi, tare da kawar dakanta, Cigaba da magana Haris ya yi"Saboda ita duk kun ta shi hankalin ku, yarinyar nan fa ba son mu take yi ba, saboda bata son tsohuwa....." kafin yakai ƙarshen maganar shi, Danish yace"haris, pls stop talking about her,' shiru haris ya yi saboda Danish ya nuna baya son yana maganarta,

   A gefen gadon angel su batool suka zazzauna suna jiran ta farka, hankalansu sam bai kwanta da irin baccin da angel ta yi ba, shiyasa suka gaza komawa saman beds ɗinsu,

    Lamarin ya ɗaure masu kai, tsawon awanni tana bacci, Tun suna sanya ran zata farka har suka fara fidda rai, 

 "Kodai inje in faɗa ma Tsohuwa ne? Acewar Hibba, Batool tace"Mu ɗan ƙara jira mu gani, wata'ƙil kafin dare ta farka,' Azeeza duk tafi shiga yanayi saboda ita tausayi gareta ga tsoro, muryata a sanyaye tace"Ni bana so wani abu ya samu angel, saboda ina sonta,'


  Haris dake sauraron su, kamar ya miƙe yaje ya rufe su da bugu haka yake ji, don shi ya tsani ya ji suna damuwa da ita, 


  Saukowa javed yai daga saman gadon shi, hannyen shi Cikin Aljihun wandonshi ya nufi gadon angel, inda suke a zazzaune, a tsaye ya tsaya yana kallon su"ku kwantar da hankalin ku, zata farka ne, zaman ku anan yana ƙara takura mata"

  "To kai meye ruwanka da ita'? Haris ne yai maganar, Kallon shi javed yai tare da cewa"Cos she's my sis, i must worry about her, " yakai ƙarshen maganar shi, tare da janye idon shi daga kan haris Ya mayar da shi kan su batool da har yanzu basu matsa daga saman gadonta ba,

  Dogon tsoki Haris Yaja rai aɗan 6ace yace"daga zuwanta har ta fara canza maku tunanin ku," Mubeen yace"Ka fa iya bakin ka, halan ka manta bugun da muka sha a hannunta ɗazu da safe, kodan kaga tana bacci ne"? Cike da zolaya yakai ƙarshen maganar yana dariya, Janyo pillow haris Yayi tare wurga ma mubeen saman fuskar shi, Cafke pillown mubeen ya yi a hannun shi still da dariya akan fuskar shi yace"Yarinyar fa akwai ƙarfi, Na lura gaba ɗaya tsoranta ku ke ji, duk masu nuna basu sonta sunfi kowa jin shakkarta,' wannan maganar da mubeen ya yi ce tasa Danish satar kallon shi ta wutsiyar idonshi, yadda mubeen ya yi maganar kamar ya karanci abunda ke a cikin zuciyoyonsu, shifa a halin yanzu bai ƙi angel taƙi farkawa ba, saboda ko motsi ta yi sai yaji gaban shi ya faɗi, Ya tsani mutun mai tsiwa ita kuma taci ka kwakwazo, ɗazu a cikin toilet ɗinnan da ta rufe shi da faɗa har zazza6i ya ji a jikin shi, dauriya kawai ya yi wurin mayar mata da martani, don baiso ta gane yana jin shakkarta,

  "Zan koya mata hankali ne, ai ba ƙyale ta nayi ba," haris ne yayi maganar fuska a ɗaure,

  Javed yace"Zaka koya mata hankali ko zata koya maka hankali? Nakasa fahimta,' shiru haris yae bai tanka ma shi ba, 

   "Yarinyar nan fa duk cikin mu babu tsaranta, saboda ƙarama ce, amma sai shegen wayau ga ƙarfi, Ni  har tsoro take bani in tana magana, ƙwayar idonta ma tsoro take bani, Ita sam bata jin shakkar kowa" Deeja ce ta yi maganar,


   Naufal yace"Ni kuma ba ƙaramin burgeni take yi ba, yanayin rayuwarta ya banbanta da namu, tana da ƙwarin gwiwa sosai, babu tsoro acikin lamuranta,"


   Naufal nakai ƙarshen maganar shi, Batool tace"Ni ina ji araina zuwanta cikin rayuwar mu, tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, idan har zamu zauna da ita cikin lalama zata koya mana abubuwa da dama waɗanda bamu sani ba, saboda ita ta yi rayuwa A wajen kurkukun nan, muna buƙatar neman ƙarin haske dangane da rayuwar mutanan dake a wajensa"

  Jinjina kai eve ta yi tare da cewa"Kalamanta na ɗazu sun tsaya mun araina, har na fara tunanin Ina iyayen mu su ke waɗanda suka haife mu? Ina dangin mu? Nafara doubting akan wani abu, Amma kafin nan, inaso angel ta farka ta bamu labarin rayuwarta, Inaso inji, kuma inaso ta faɗa mana wanene Ya halicci kowa, kuma wanene ɗan adam da ta take magana akai,"


   Maganganun da su ke yi ba ƙaramin ƙona ma haris rai su ke yi ba, ganin Yarinyar ta fara cin galaba akansu, taya wata can baƙuwa zata shigo cikinsu, ta soma kokarin canza masu tunanin su'

  A harzuƙe ya daka masu tsawa, har saida Danish ya firgita, don baisan Tsawa ko kaɗan, Jikin shi har kerma yake yi, idon shi akan Haris dake ta faman huci,

  Nuna su ya yi da yatsan hannun shi "kada wanda ya kuskura ya ƙara magana makamanciyar wannan acikin ku, ban ta6a sanin baku da hankali ba, sai yau, taya zaku fara ɗaukar maganganun ƙaryar da take faɗa maku? Yarinyar na fa bata da cikakken hankali, batasan me take yi ba......" muryar shi a disashe yakai ƙarshen maganar idon shi akan danish daya daddafe kanshi da hannayenshi biyu, jikinshi nata kerma


  Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan Danish, Sun san lalurar shi ta rashin son hayaniya, idan abun ya motsa kusan burkice masu yake yi, 


  Sassauta murya haris Yayi"danish am really sorry, raina ne ya 6aci sam na shafa'a," ya yi maganar yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, ya nufi gadon danish ya zauna daga gefe yana lallashin shi, 

   "Pls kada wanda ya ƙara magana a cikin ku, kowa ya koma gadon shi ya kwanta" acewar javed, Miƙewa su batool su kayi kowa ya nufi gadonshi, Ya zauna,

  Shima javed ɗin Ya koma nashi gadon Ya zauna, ya rage saura haris dake aikin lallashin Danish, daƙyar ya samu ya shawo kanshi, ya saki kanshi daya tallabe da hannayen shi, bai ta shi daga wurin shi ba har saida  yaga ya kwanta tukunna ya miƙe ya koma nashi gadon,

Lokacin da dare Ya tsala, hasken ɗakinsu ya ɗauke gaba ɗaya, kowannansu Ya nutsa Cikin bacci, a wannan lokacin ne ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta da su ka yi mata nauyi, jikinta duk ba da daɗi ga zufa,

  Ambaton sunan Allah ta cigaba da yi har ta samu ta buɗe idanuwanta, duhu ko'ina saboda basu kunna fitilun ɗakin ba kafin su kwanta,


  Lalla6awa ta yi ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin bango, Sam ta manta abunda ya faru da ita, hatta maganganun da su ka yi kafin ta kwanta baccin duk ta manta su,


   Wata irin matsiyacin yunwa ta soma ji, ga ƙishin ruwa, tunawa da ragowar naman kazarta da ta jiye yasa ta saurin saukowa daga saman gadon, cikin duhu ta dinga laluban hanya, har Allah ya kawo ta saitin inda table ɗinsu yake, hannu takai ta ruƙo handle ɗin fitila, ta kunnata tare da ɗago da ita, da sauri ta tunkari wurin gadajen su, ɗaya bayan ɗaya ta shiga haska fuskokinsu, wasu sun ƙudundune cikin bargo wasu kuma basu lullu6e jikin su ba, adai dai bakin gadon Batool ta tsaya tare da zuƙunnawa daga gefen gadon, ta zura hannu ta janyo kwandon, tana hamma ta buɗe shi, shiru ta ɗanyi tana kallon Ikon Allah, An samu wani ya gwaigwaye tsokar jikin naman sai ya bar mata ƙashin kaɗai, Apples ɗinta guda uku anciye biyu, sai ɗaya aka bar mata shima ɗayan saida aka Cinye kusan rabin shi, sam bata yarda da abunda idanuwanta suka nuna mata ba, hannu ɗaya ta sanya tana murza idanuwanta, don ta ƙara tabbatar da abunda suke gane mata,


 Dagaske dai an cinye mata Abincin da ta ajiye, a ruɗe ta ruƙo hannun kwandon, tare da jijjiga shi taga dai ba komai sai wannan guntun apple ɗin da aka rage mata,


Ranta yayi bugun 6aci har wani jiri take gani acikin idanuwanta, tsabar takaici tuni idanuwanta sun cicciko da kwalla,

 

Ta rasa wa zata zarga acikinsu, tasan dai batool bazata iya cinye mata abinci ba, sai dai Cikin sauran ƴan uwan nasu,


Cikin shessheƙar kuka tace"Wlh tun da aka cinye mun Cinyar kaza ta saina hana kowa bacci a adaren yau," 


  Runtse ido tayi tare da kwatsa wata irin gigitacciyar ƙara mai matuƙar tsiwar gaske, Har Cikin kokwan kansu, kusan atare Suka farka Sai faman zare ido suke yi, kowa yana tambayar lafiya wanene? Duk sun bi sun ruɗe, batool ce ta lura da angel dake atsaye, yaye bargon jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadonta, ta nufi angel tana faɗin"Sister kin farka, Meya faru? Lafiyarki kuwa? a jere ta jefa mata tambayoyin, Su hanna ma duk suka shiga tambayarta lafiya meya faru,


  Zuciyarta na tafarfasa tace"Uban wanene ya cinye mun tsokar namana yabar mun ƙashi? Wlh kodai ku faɗa mun ko kuma in hana kowa runtsawa acikin daren nan,' 


  A ruɗe Batool tace"A ina kika a jiye ne"? 

  "Cikin kwandon da kike ajiye ragowar abinci, anan ciki nasaka, an samu wani mara imanin ya cinye mun kaya na"

  Parveen tace"Zai iyayiyuwa 6era ne ya cinye shi," 

  "Dama kuna da 6eraye"? Jinjina kai parveen tayi alamar eh,"Muna dasu kuma duk in muka ajiye abinci, suna bi su cinye"


  Wata irin dariya angel tasaki"wannan dai ba 6era bane ya ci shi ba, Sai dai 6eranya, ku faɗa mun wanene ya cinye mun abuna idan har kuna saman lafiya" 


   Guntun tsoki Haris Yaja"Wannan wani irin rainin wayau ne? Munyi maki kama da 6arayi ne? Saboda kin raina ma mutane wayau, " yana rufe baki deeja tace"wama ya sani, ko ke ce kika cinye abunki cikin magagin bacci shi ne xaki zo ki ishi mutane da tsiwa, muna yin baccin mu mai daɗi kin katse mana shi,"


  Jinjina kai angel tayi"Shikenan tun da bazaku faɗi mini wanene ya cinye mun tsokar kaza ta ba, da apple ɗina guda biyu, Zaku ga abunda zai biyo baya, Bakusan wacece ni ba, Kafin zuwana kurkukun nan, Duk wanda ya 6ata mun rai, idan har na karanta mashi Carman dudu, Bai ƙara kwana ɗaya yake mutuwa, Cikin shi zai kumbura, ya fashe daga nan shikenan tashi ta ƙare" In a serious matter ta yi maganar, da yake ta raina musu wayau, Ta riga ta gane cewa basu san komai ba, Shiyasa tace musu haka,


  Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi, ruƙo hannunta batool tayi"Pls Angel kada ki karanta mana wannan abun, daga ji wani mugun abunne, nidai nasan bani naci ba, amma ina tsoro ace wani ne yaci acikin ƴan uwanmu kinga zai cutu," Ta6e baki angel ta yi"nidai nace a faɗamun wanene yaci mun abuna, in ba haka ba zan karanta ne"


  Fashewa da kuka azeeza tayi tana faɗin" Wai bazaku faɗa mata wanene ya cinye mata abinci ba," 


  Shidai haris yayi zuru da ido yana jira yaga me zata yi musu,


  "Angel, kiyi haƙuri kada ki karanta mana, kinga mu nan duk ƴan uwanki ne. Ke kanki ba zaki so wani ya cutu ba" acewar javed,


  Girgiza kai angel ta yi"Ba kunce akwai 6eraye ba? To ai su zan karantamawa, tun da su suka cinye mun Abuna, meye naku na damuwa ne"? Shiru su kayi suna kallonta kowa yasha jinin jikin shi,


  Zuƙunnawa tayi a ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, kafin ta runtse idanuwanta, motsa lips ɗinta ta soma yi tana karanta Carman dudu, batare da sautin yana fita ba,


  Cikin shessheƙar kuka Parveen tace"ba ni kaɗai na ci ba," angel bata buɗe idanuwanta ba, taci gaba da karantawa, a gigice parveen ta duro daga saman gadonta, Ta zube agaban angel tana kuka, ta ruƙe kafafunta, gaba ɗaya ido ya dawo kan parveen, Dariya ƙunshe abakin angel ta buɗe idonta,

  "An samu 6eran kenan"? Murya na kerma parveen tace"Eh ni ce," ɗagowa ta yi da idanuwanta waɗanda suka kaɗa su kayi jawur tace

  "Bani kaɗai bace, Hada yasmin da deeja, Su suka cinye maki apples, ni kuma naci naman, ki yafe mana bazamu ƙara ba"


 Jinjina angel tayi"tun da ke kin bani haƙuri, Na yafe maki, amma su kuwa zasu Gane kuren su," tana kai ƙarshen maganar, ta rufe idanuwanta kamar wata bokanya ta ɗaga hannanyenta sama, taci gaba da sambatu,


  Kallon Juna deeja da yasmin su kayi, idanuwan su cike tab da kwalla, Batool tace"ku bazaku je ku bata haƙuri ba? So ku ke Cikin ku ya kumbura,"


  Saukowa su kayi daga saman gadajensu, da rarrafe suka ƙarasa inda angel take zaune, Har suna haɗa baki wurin bata haƙuri, batare da ta buɗe ido ba, tace"Kun yi jinkirin tuba, Don haka zaku yi tsallan kwaɗi, duk idan ku kayi tsalle ɗaya zaku ce Aunty angel kiyi haƙuri bazamu ƙara ba, bayan haka kuma gobe idan aka kawo mana abinci, Zaku raba shi biyu kuban rabi, kun amince? Murya na kerma suka ce Eh,


  Fuska a ɗaure ta buɗe idanuwanta, tana kallon su"nan gaba idan kuka ƙara satar mun abinci na, kada kuyi tsammanin zan yafe maku, " atare suka ce bazamu ƙara ba,

  Gyaɗa kai tayi tare dakai hannu ta ɗauki filitar data ajiye a ƙasa, ta yunkura ta miƙe tsaye"Oya ku fara tsallan kwaɗi, " 


  "Ae bamu san yadda ake yi ba" deeja ce ta yi maganar, kallon su tayi ganin yadda jikinsu keta kerma, sai taji tausayinsu ya kamata,


  Ta6e baki ta ɗanyi"Kada ku ƙara na yafe maku, Abunda kuka aikata baida kyau, domin kuwa sata ce, kuma haramun ne mutun ya ɗauki abunda ba na shi ba, babu daɗi ni yanzu baku kyauta mun ba, yunwa nake ji sosai, banci haƙƙin wani ba, nawa ne na ajiye saboda gudun yunwa amma kunbi kun cinye mun kaya ne, wannan ba adalci bane, idan naku aka ɗauka zaku ji daɗi" girgiza mata kai su kayi alamar a'a,


  "Kada ku ƙara, ko ba nawa ba kada ku ƙara ɗaukar abunda ba naku ba," amsa mata su kayi da toh,


  "Ina danish ya ke"? Haris ne ya yi tambayar ganin gadon shi wayam babu kowa" sai lokacin su ka lura da babu danish A cikin shi, Nan fa hankulansu suka ta shi, 

 "Wai dama tun ɗazu Danish baya acikin mu? Amma kafin mu kwanta danish yana atare damu" Rubina ce ta yi maganar fuskarta da alamun ruɗu,


  Da sauri Javed Ya sauko daga saman gadon shi, yaje saman table ya ɗauki fitila ɗaya, batool ma ta ɗauki ɗayar fitilar duk suka kunna su don ɗakin ya yi haske,


 "Ku duba ko'ina, Allah yasa dai ba wani abunne ya faru da shi ba," haris ne yai maganar, gaba ɗaya sauran dake asaman gadajen su duk sun sauko, sai zagaye cikin ɗakin suke yi suna neman Danish, Saƙo da lungu ko'ina suka shiga dubawa amma babu shi, lamarin yayi matuƙar ɗaure masu kai, 


  "Yakamata mu sanar ma tsohuwa halin da ake ciku" Acewar Mubeen,

  Deeja tace"bari naje na kirata," tana kokarin zuwa taje ta sanar da ita, Batool tayi saurin cewa"ku dakata" gaba ɗaya suka Juyo suna kallonta,

 Haris yace"kin gano inda ya ke ne?


 Girgiza kai tayi"a'a, " kafin ta kalli angel da ke a tsaye tace"lokacin da kika saki ƙarar nan, baki ga gifcin mutun ba"? 


  Shiru angel tayi tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru, 


  "Gaskiya ni banga gifcin kowa ba, amma meyasa kika tambaye ni"?


  "Saboda danish baya son tsawa, zai iyayiyuwa lokacin da kika saki ƙarar nan. Har muka farka daga bacci, a wannan lokacin danish ya rikice ya sauko daga saman gadon shi ya faɗa wani wurin" 


 Sakin baki angel tayi galala tana kallon batool, da mamaki akan fuskarta tace"saboda kawai nayi ihu sai ya 6ace a neme shi arasa, ko dai yana da ta6in hankali ne"? Tayi tambayar tana kallon batool,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post