Kurkukun Ƙaddara page 13 complete


Health College

Kurkukun Ƙaddara page 13 complete

 

Kurkukun Ƙaddara 13

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


daga alƙalamin Boss Bature✍️


   Dedicated to aunty Kubra❤


E13


"Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da ƙima a idona, dake da ƴar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin ɗa'a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,"?

  Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba,

  Sai da ta mula tasha iska tukunna tace"bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba,"

  Murmushin takaici yasaki kafin yace" Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saƙo a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waɗannan bayin Allahn, Rana ɗaya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata ɗaya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki"?

   Ta6e baki Laila tayi"Laifinsu ne ae, kasan ƴan jarida da kafiya, ga shegen naci da bin ƙwaƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi ƙarfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,"? Yadda tayi maganar ko ajikinta, 

  Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta"Hada jikarki fa a cikinsu,"

  "Jikarka dai, Ni ban haɗa komai da su ba, Auran benzir da yaron nan ƙaddara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi ƙarfin shi, Ni nayi tunanin ma ɗan Abdallan ne shima ashe ɗan wani faƙirin mutunne dake zaune a karkara....." rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita"Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya'yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi,"

  Murmushi tasaki tana kallon shi,"Nifa komai zaka faɗi akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee ɗinka nan Yana huce wa yakamata ka sha" tayi maganar tana nuna mashi Mug ɗin dake ajiye saman table,

  Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba, 

   Kashe murya tayi tare da cewa"Habibi fushi ka ke da Nooril ƙalbin taka"? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta ƙura mashi ido tana kallon shi,

  Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing,

    Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan,

      Girgiza kai lailah tayi"ɗan siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuƙa shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon ƙafar ta shi yayi sauƙi, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban ƙasa, Wannan shi ne burin da nake da shi,' takai ƙarshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a ƙalla takai shekara arba'en, jikinta na sanye da kayan aiki,

      Cikin harshen labaraci tace"ki sanar ma Sauran maids ɗin Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt"

     Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da"Toh, in sha Allah za'a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya," 

     Laila ta amsa mata "ameen"

      Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu,

      "Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya ƙafa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana," 

 On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana" Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi ɗaya ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci,"

 "zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba ɗaya yana a nigeria, nadamu da su," fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yakai ƙarshen maganar, abokin nashi da suke waya yace"Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne," muryarshi da alamun mamaki

   "kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce,"

   Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi, 

  Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buɗe mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faɗin"Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo ƙasar" Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani ƙamshi dake fita a jikinshi,

 Rungume juna su kayi kamar zasu haɗiye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden ɗin gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu Shimfiɗa Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su,


Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota?

 

   Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko'ina duhu, babu haske ko misƙala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an ɗaura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza ɗagawa, Wani baƙon yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko'ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu'a da tazo bakin ta,

  Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin"Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar,

   Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta  ya bushe ƙamas, 

  Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta,

  Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo,

tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je  da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar,  single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there's a table an ɗaura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar ɗakin akwai shimfiɗaɗɗen red carpet,

   Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu,

  Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su akan ƙopar dake a rufe, saman ƙopar taga an rubuta "Toilet" nan take ta gane makewayi ne, ɗakin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garƙame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi,

  A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1,

   Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta,

  Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce, 

  Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziƙi ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko'ina a kan fuskarta,

   Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail ɗin benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye ƴan hanjin cikinta,

   Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buɗe ƙopar ɗakin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls ɗin ta kan ƙopar tana jira taga wata ja'irar ce ko wani ja'irin ne xai shigo, domin kuwa ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wanda ya yi silar ɗauko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison.

  Cikin ƙanƙanin lokaci aka buɗe ƙopar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon ƙafar mutanan da suke ƙoƙarin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaɗan ƙirji, Wata kalar ƙira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baƙaƙen kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, ƙafafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko'ina arufe ya ke, motsa lips ɗinta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunƙurin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan ƙafar matashin saurayin da ke ƙoƙarin shigowa, kalar uniform ɗinta ne ajikinshi baƙaƙe masu ɗauke da No 1  A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes ɗin shi farare ƙyal da su, Yana da dogon hanci, full lip ɗinsa red colour ne, yana da dimple ɗaya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips ɗinsa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back ɗinsa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba, 

   ta yi tunanin shi kaɗai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips ɗinta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta, 

  Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya, 

  A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar,

  Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace"wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaƙata da ku!"nuna matasan ƴan matan ta yi da yatsan hannunta "ku faɗamun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na" a harzuƙe ta yi maganar,

   ɗaya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci"kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu ɗaya na sani shi ne, kurkukun ƙaddara gida ne na marayu wanda basu da gata,'

   girgiza kai angel ta yi'ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave........" kafin takai ƙarshen xancen nata wata matashiya me ɗauke da uniform jajaye no 4 baƙa siririya tace"ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun ƙaddara shi ne gidanmu"

  Uwar harara angel ta wurga mata"prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za'a sato mutun akawo shi wani baƙon wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faɗo ba," yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta,

   Takun tafiya suka jiyo daga cikin ɗakin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faɗin"Ina Magana"da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin ɗakin hada angel,

    Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma, 

      Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo? 

      Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace"ko ɗaya! ta ƙopa na shigo ciki" ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata ƙopa dake a ɗaya daga cikin kusurwowin ɗakin,

      "Nan ɗaki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan  wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da BATOOL!" ta kai ƙarshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faɗi, masu kalar uniform ɗin angel,"

      Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saƙawa acikin zuciyarshi"?

      "Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace,  Ko da ace ni marainiya ce taya za'a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka ɗauko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh?

      "Gidan kurkukun ƙaddara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison ɗin nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa'annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi" tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin,

     Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin ɗaga murya tace"If it's an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won't believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka ɗauko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku" takai ƙarshen maganar tana haki ta harzuƙa sosai,

    Sauran prisoners ɗin duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baƙuwar yarinyar da su kayi tare  da tsohuwa, tun da suke a gidan prison ɗin ba'a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baƙuwar da suka tsinta yau acikin su, 

      "Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!"

     A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi,"

     "Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!"

     Tana huci takai ƙarshen maganar tare da ɗauke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar" ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, Kuma a faɗa mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naƙasa rayuwar shi"

    Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya, 

      Sassauta murya ta yi"idan kun saba rainawa mutane hankali kuna ɗaukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buƙatar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah,"

 Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace"buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke ɗiya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya"

  Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata,

  "Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu ɗaya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damƙa mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaƙin ɗaukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu....idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki,"

 Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheƙar kuka tace"kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma ƙarya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun,"

  Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa"ƴar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buɗe baki ki kace mun ƙarya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa ƴan uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa'annan ina mai ƙara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki"

  Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta,

   Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waɗannan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta,

  Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton"Innallahi wa'inna ilahirraji'un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka ɗauki raina nima in huta........."sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina,

  Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu,

  Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faɗi a sume.

  Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips ɗinsa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me ɗauke da no 2 haka kowani gado yake da number,

  Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun ɗaya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta,

  Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a ƙasa ta ɗaura shi saman cinyarta, juyawa ta ɗanyi tare da kallon kowannan su dake kishingiɗe saman gadonshi, tsayar da ƙwayar idonta ta yi akan Hannah ta ɗan ɗaga murya tare da cewa"abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta? 

   Ta6e baki hanna ta yi"rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaɗai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta," Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace"nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, "yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa"bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba'a gama rainon ta ba,"

  Gaba ɗaya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci,

  "Is enough, kunsan bana son hayani ya" wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow,

   Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai,

  Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana"SISTER" har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buɗe idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta ɗauke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa"bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa,"


Mu haɗu next page  

  


(bakuyin Liking Da comment maganar gaskiya, shiyasa sometimes ma baku samun update akai Akai, tun da alama ce dake nuna baso ku ke yi ba👌 idan kinsan kina son cigaba da karanta book dinnan kiyi comment da like, daga yau idan naga babu likes ba comment, bazan cigaba da wahalar daura shi ba)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post