Kurkukun Ƙaddara page 14 complete

Kurkukun Ƙaddara page 14 complete

 

Kurkukun Ƙaddara 14

💋Kurkukun ƙaddara💋


By Boss Bature 


14


Tuntsirewa su hanna su kayi da dariya jin yadda ta gwasale Batool,

   "Bai kamata ki yi mun haka ba, kowa yaƙi kula ki a lokacin da ki ka suma ni ce kaɗai na damu da ke amma shi ne kika watsa mun ƙasa a ido"?

  Cigaba da kuka angel ta yi ba tare da tace mata uffan ba, ita kaɗai tasan raɗaɗin da take ji,

   Zuba mata ido Batool ta yi batare da ƙyaftawa ba,

    Adai dai wannan lokacin suka soma jiyo motsin buɗe ƙopa, gaba ɗaya suka kai idanuwansu bakin benan

      Turo ƙopar a kayi waɗannan Giants ɗin ne su uku masu sanye da baƙaken kaya su ka shigo hannayen su ɗauke da Faffaɗan wooden trays masu ɗauke da kayan abincin su, kowanne na a ruƙe da faranti ɗaya, 

      Bayan sun ƙarasa sauko wa kai tsaye su ka nufi jan carpet din nan, a saman shi su ka sauke farantan, kafin suka ja gefe ɗaya suka goya hannayen su asaman ƙirjinsu, dama ƙa'idar aikin su ce idan suka kawo masu abinci ba su tafiya tsayawa suke yi har sai sun kammala tukunna su kwashe kayan abincin su tafi, kuma basa magana sai in ta kama dole,

      one by one su ka soma saukowa daga saman gadajen su, izuwa gaban kayan abincin kowa ya samu wuri ya zauna, ruƙo hannun angel batool ta yi tare da cewa"ki taso muje mu ci abinci," fusge hannu angel ta yi" bazan ci ba, ni kawai a mayar dani inda aka ɗauko ni,"

      "This is the only chance u ave to eat, we get food once a day, if u don't eat it now, u will lose ur food," cikin sigar lallashi batool ke yi mata magana, ita kuwa ta kangare akan baza taje taci abincin ba.

      Miƙewa batool ta yi duk bata ji daɗi ba, taso ace yarinyar ta saki jiki da ita amma ta nuna kafiya, wuri ta samu saman carpet ɗin ta zauna,

    faranti na farko Grilled Chicken wraps ne guda goma sha biyar a jere, iya adadin su, faranti na biyu kayan marmari ne nunannu an yayyanka su, a faranti na uku wooden cups ne guda goma sha ɗaya, sai jugs guda biyu ɗaya na ruwa me sanye ɗaya kuma na Lemu ne da aka hada da nau'ikan kayan marmari,

      A tsanake kowa yakai hannu ya ɗauki chicken wraps ɗinsa, suna Ci suna satar kallon angel, batool dai bata ji daɗi ba, ganin taƙi tasowa taci, ga nata nan ajiye shi kaɗai, idan wani ya cinye tayi asara, in kuma ba'a samu wanda yaci ba, zasu tafi da shi ne.

     baiwar Allah ta galabaita sosai, ga jaraba nacin ta ga yunwa ga kuma abinci amma taƙi ta shi taje ta xauna cikin su ta ci, wani irin ƙululun baƙin ciki ne acan ƙasan zuciyarta, eyes ɗinta a rufe hawaye ke gangarowa saman kuncinta,

      Ƙasa ƙasa da murya batool ke yi mata magana"ki taso ko ci," maƙe kafaɗa angel ta yi, alamar baza ta zo ba,

      A ƙarshe ma sai ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta jure a haka ta taka izuwa gaban waɗannan Giants ɗin ta ci burki ta tsaya,

      "Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, bansan zunubin dana aikata ba, da har za'a sato ni izuwa cikin wannan kurkukun," magana take yi masu amma ko uffan basu ce mata ba, domin kuwa a tsarin aikinsu basa magana da prisoners, 

      "Dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa waɗannan da kike gani basa ji basa gani, idan kuma kika ce xaki matsa masu jikin ki ne zai gaya maki"

      Juyawa angel ta yi da sauri don taga wani ja'irin ne ya tsoma mata baki, ɗaya daga cikin matasan ne me suna naufal,

      Nuna shi ta yi da yatsan hannunta"karka kuskura ka ƙara shiga hurumina, ba ruwan kowa da rayuwata," juyawa ta kuma yi kansu  cikin xafin rai tace"magana nake yi maku, ku faɗamun wanene ya bada umarnin a kawo ni wurin nan? Shiru basu tanka mata ba ga shi bata iya ganin koda ƙwayar idonsu ce balle tasan ko suna kallon ta,

      Zubewa tayi saman guiwowinta tana raira masu kuka tamkar ranta zai fita,

      tana ji tana gani suka kammala cin abincin, Giants ɗin nan suka tattara kayan abincin suka kama hanyar fita daga ɗakin, ranta ya 6aci ta dunga ɗura masu ashar kamar ɗiyar maguzawa,

     Da gudu tabi bayansu tana kuka tana zagin su, ƙopa suka buɗe suka fuce, ƙopar ta datse, ta dinga bugun ƙopar tana kuka, silalewa tayi bakin kopar ta kwantar da kanta, tako ina babu sauƙi, 

     "Idan kina jin bacci, gadon ki shi ne no 1 zaki iya zuwa kije ki kwanta" batool ce ta yi mata maganar, tana a tsaye saman matattakalar benan, buɗe idanuwanta tayi waɗanda suka kaɗa su kayi jawur, ta watsa mata harara muryarta a disashe tace"wai ke mayyace? Ki rabu dani mana kamar yadda sauran ƴan uwanki suka yi," jinjina kai batool ta yi," I worry about you but you don't worry about yourself, i won't disturb u again tun da kin buƙaci hakan, just whenever u change ur mind, za ki iya yi mun magana,' jiki a sanyaye batool ta juya ta koma cikin ɗakin, 

     Tuni  kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, wasu suka kama bacci wasu kuma suna zaune suna fira,


      Yinin ranar angel a galabaice ta yi shi, sai da takai ga bata gane komai idanuwanta sun rufe saboda tsabar jin yunwa, ga raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far mata, a nan saman benan ta zube rai hannun Allah,

 lokacin da dare ya yi, hasken ɗakin da kan shi ya ɗauke, dama ƙa'ida ne idan dare ya yi gaba ɗaya hasken wurin yake kashe kan shi, sai dai mutun in yana buƙatar haske ya yi amfani da fitilun da ke ajiye saman table,

   Duhu ya mamaye idanuwanta, ta ƙuntata sosai ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wannan wata irin rayuwa ce me cike da ruɗa ni? taya zata ci gaba da rayuwa acikin kurkukun nan? ta gaza gane sarƙaƙiyar da ke acikin rayuwarta, shin wanene a cikin danginta ya kawo ta cikin gidan kurkuku da sunan araine ta? Anya kuwa wannan ba ƙanzon kurege bane? tabbas akwai mata maƙarƙashi a cikin gidan kurkukun nan,

  A cikin zuciyarta take wannan tunane tunanen, 

  Saboda tsabar yunwa ko yatsanta, bata iya ɗagawa,

  Batool sam ta kasa runtsawa saboda halin da yarinyar take ciki, ta damu da ita sosai ga shi ita kuma bata so ta kusanto ta, kowa ya yi bacci ban da ita,

 Saukowa ta yi daga saman gadonta cikin duhu ta shiga laluban inda fitilun suke, har Allah yasa ta gano table ɗin takai hannu ta ruƙe handle ɗin fitilar bayan ta kunnata, tafiya ta soma yi Cikin ɗakin har zuwa saman benan anan ta samu angel cikin mawuyacin hali, zuƙunnawa ta yi agabanta, muryarta ƙasa ƙasa tace"Yar uwa" angel bata iya amsa mata ba, domin kuwa takai mataki na ƙarshe wanda ko la66anta bata iya motsawa, a lokacin jikinta ya yi mugun yin sanyi ta fidda rai da rayuwa, cikin zuciya ta dinga yi furta kalmar"ruwa! ƙishi nake ji! A taimaka mun," batool batasan me take cewa ba, saboda a cikin zuciya ta yi maganar, Allah dai ne kawai ya taimake ta, batool ta yi tunanin ko tana buƙatar ruwa, dama ɗazu ta 6oye mata chicken wraps ɗinta, tun ɗazu taso ta bata taci sai dai taƙi bata fuska, shiyasa ta ajiye mata zuwa lokacin da zata neme ta,

 Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta inda take ajiyar ruwa acikin bottle water, ta zuƙunna tana haskawa da fitilar hannunta, kwando ne ajiye a karkashin gadon, a cikin shi take 6oye abinci idan ta rage saboda gudun yunwa, zura hannu tayi ciki ta ɗauko Chicken wrap ɗin, Ta tura cikin aljihunta, sannan ta ɗauki robar ruwan ta ruƙo a hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana a ruƙe da fitila, da sauri ta koma saman benan saitin inda angel take ta zuƙunna, ta sauke fitilar ƙasa, tare da bottle ɗin, hannu tasa ta tallabo kan angel ta jingina shi gefen shoulder ɗinta,

  Sannan ta ɗauki bottle din ta buɗe murfin ta kafa mata bakin robar,

  yadda kasan mafaraucin da yayi rashin ruwan sha na tsawon sati ɗaya  haka angel ta shiga ɗaɗɗakar ruwan, maƙoshinta har wani sauti yake badawa, kwat kwat!

  Murmushi batool ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba ganin yadda take shan ruwan,, Yarinya taji ƙamshin mutuwa,

  Sai da ta shanye ruwan nan tass tamkar xata haɗa da robar ruwan duka ta shanye,

  Janye bottle ɗin ruwan ta yi daga bakinta, ta ajiye ta saman matakalar, ta mayar da murfin a mazauninsa,

  Hannu ta zura cikin aljihun ta, ta ciro chicken wrap ɗin duk ta rugurguje, a haka ta dinga tura mata abaki, la66anta har kerma suke yi wurin ci, kuma har lokacin kanta yana asaman ƙirjin batool, sai da ta cinye tass ta soma jin wani irin tashin zuciya, yunƙurin amai ta soma yi, a ruɗe batool ta shiga bubbuga bayanta tana faɗin"Sorry sis, bari na raka ki toilet" kafin batool ta miƙe ta yi yunkurin tallabota, tuni Ta saki aman anan saman benan, ta dinga kwararo shi gaba ɗaya ya 6ata hada jikin rigarta, baiwar Allah taji jiki, saboda tsabar tausayinta da batool take ji, batasan lokacin da ta fashe da kuka ba, duka chicken wrap ɗin da taci sai da ta amayar da ita, tun ruwa na fita abakin ta, har yakai ga babu komai sai dai kawai kakarin aman da take yi,

  Ganin mawuyacin halin da ta shiga ne yasa batool ta miƙe tare da ɗaukar fitilar, ta ruga da gudu zuwa ƙopar ɗakin tsohuwa, knocking ƙopar ta soma yi tamkar zata 6alleta, 

  Mutun uku dake bacci saida su ka farka, Danish da ya kasance baisan hayaniya ko misƙala zarratin, Sai hanna da kuma Haris, Har suna haɗa baki wurin tambayar Batool lafiya take neman tsohuwa, ko ta kansu bata bi ba, har saida tsohuwa ta buɗe ƙopar, Hannunta ruƙe da sanda ta fito, batool na kokarin buɗe baki ta yi mata jawabi, tariga ta cewa"Kada ki damu, ki koma wurinta zata dawo dai dai, nayi mata addu'a daga cikin ɗaki," tana faɗin hakan ta juya ta koma cikin ɗakinta, tare da jan ƙopa ta rufe,

  Jikinta asanyaye ta juya sam ba haka taso ba, taso ace tsohuwa tazo ta duba jikinta, saboda halin da yarinyar take ciki, muryar Haris ce ta ratsa kunnanta"Just because her duk kin damu kanki, kin hana idonki bacci, meye alaƙarki da ita"?

 Hanna tace"tambayar da nake so na yi mata kenan, shi dai danish baice komai ba, bacci ne dai an hana shi yi, ya takure saman gadon shi, sai faman lumshe ido yake yi,

 Batool ku wa Ko kallo basu ishe ta ba, lokacin da ta koma wurin angel, wani abun mamaki a zaune ta same ta, ta jingina kanta jikin bango, shanyayyun idanuwanta a buɗe sun kaɗa sunyi jawur, Sumar kanta duk ta barbazo mata har saman fuskarta, la66anta na kerma take ambaton"rabbi yassir wala tu'asir watammim bil khairi" wani irin farin ciki ne ya lullu6e batool, har batasan lokacin da ta saki murmushi ba, maganar tsohuwa ta tabbata ga shi ta farka har tana magana, duk da batasan me take cewa ba,

   "Yar uwa" ta ambaci sunanta, idanuwanta Jiƙe sharkaf da hawaye ta ɗago ta kalle ta, wato duk irin korar da take yi mata hakan baisa ta guje taba, lallai ba ƙaramin so take yi mata ba, batool ba tayi tsammanin zatayi mata magana ba, sai ji tayi tace"Ina so in wanke jiki na, bana jin daɗi,"

  Miƙa mata hannu batool tayi"ki taso na raka ki toilet" miƙa mata hannu angel tayi, ta ruƙo nata daƙyar ta samu ta miƙe, ita kanta ta yi mamakin yadda ta rayu don ba ƙaramar azaba tasha ba, taji jiki sosai, amma yanzu ko yunwa bata ji, jikinta ba wani ciwo, sai dai ciwon dake a cikin zuciyarta dake tafarfasa,

  Har toilet batool ta rakata, da yake babu wadataccen haske bata iya kallace shi da kyau, A bakin fanfo suka tsaya ta wanke mata gaban rigarta daya 6aci da kuma wandonta, wani irin sanyi jikinta, tuni ta soma kerma,

    Fitowa su ka yi daga Cikin toilet ɗin hannunsu cikin na juna, batool ta kai ta har saman gadonta mai ɗauke da no 1 kusa dana danish na shi no 2 ne, sai na batool no 3, hawa saman gadon ta yi batool ta lullu6a mata bargo asaman jikinta, sosai ta ƙudundune, 

 Komawa batool tayi ta gyara inda angel ta 6ata da aman, ta goge ko'ina duk ita kadai baiwar Allah, bayan ta kammala ta dawo Cikin ɗakin ta ajiye fitilar saman table ɗin, ta kukkuna sauran fitilun ɗakin ya yi haske,  danish da bai koma bacci ba ya lafe saman mattress ɗinshi, yana fuskantar angel dake ƙudundune cikin bargo, babu tazara tsakanin gadajensu gab su ke da juna, idan har mutun zai iya miƙa hannu to xai iya ta6o gadon dake a kusa da nashi, shi dai hakanan sam yarinyar bata kwanta ma shi ba, ji yake kamar an kawo masu monster acikin ɗakin su, bargo yasa ya lullu6e fuskarshi,


   Dawowa batool ta yi wurin angel don taji idan ta yi bacci, a gefen gadonta ta zauna, Cikin sanyin murya tace"sister kinyi bacci"

   Hannu angel tasa ta yaye bargon da ta lullu6e kanta da shi, fuskar nan tayi jawur ta kumbura, daƙyar take iya kallon fuskar batool,

  Hannu batool takai tare da shafa fuskarta, Cikin sanyin murya ta soma magana" i know we don't know each other that well, but i'm still worried about you, nasan irin raɗaɗin da kike ji acikin zuciyar ki, bazan iya yaye maki shi ba, amma abu ɗaya nake so in tunasar da ke, duk abunda haƙuri bai baka ba, to rashin haƙuri bazai ta6a baka shi ba, tsohuwa ce ta ta6a faɗa mana haka," shiru ta ɗanyi na wani lokaci, angel na sauraronta kafin taci gaba da cewa" yau kika tsinci kanki acikin kurkukun nan ni kuwa tun ban mallaki hankali na ba nake acikinsa, bansan kowa nawa ba abun da nasani kawai tsohuwa ce ta raine mu........" bata kai ƙarshen maganar ba, cikin shessheƙar kuka angel tace"bazan iya jure zama acikinsa ba, cewa fa ta yi daddy na ya mutu, yanzu ni marainiya ce amma ae ina da dangi masu ƙaunata aunty aneelerh tana so, mommyna adama tana so na, don me za'a kawo ni gidan marayu"? daƙyar take magana saboda yanayin da take ciki,

  "bazan iya amsa tambayarki ba, amma shawarar da zan ba ki shi ne ki bi komai a sannu, idan kika ce zaki bi ta ƙarfi da yaji don ki bar cikinsa to kuwa kece a wuya domin kuwa ni tun da na taso a cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA yau tsawon shekara da shekaru banta6a ganin hanyar fita daga cikinsa ba, babu wanda yasan ta hanyar da aka shigo da shi, balle kuma yasan hanyar da zai fita daga cikin sa, sa'annan duk wani motsin mu a tafin hannunsu yake suna kallon mu, kewaye ne kaɗai idan kika shiga basa iya ganin ki........"

  Cikin rashin fahimta angel tace"Idan har dagaske orphanage home ne meyasa xasu ƙuntata rayuwar mutun babu shige babu fuce kenan ko makaranta mutun baida ikon zuwa? Gaskiya bazan ta6a yarda da gidan nan ba......."

  Batool tace"bana son muja zancan nan da tsayi, kamar yadda ba zaki fahimce ni ba, nima bazan iya fahimtar ki ba, saboda dukkan mu cikin ruɗani mu ke, abu ɗaya zan sanar dake GIDAN KURKUKUN ƘADDARA ba gidan cutarwa bane, saboda ni tunda na taso a cikinsa ba'a ta6a cutar dani ba kuma banga an cutar da wani ba, sai dai abu ɗaya ne da ya ke ci mun tuwo a kwarya shi ne kullan da a ke yi mana, ba ko'ina bane muke da ikon taka ƙafarmu ba acikinsa, najima ina tunanin ya wajen sa yake? Saboda ni ban ta6a fita daga cikinsa ba," 

  Shiru angel ta yi batare da ta kuma cewa wani abu ba, saboda har yanzu tana ɗan jin jikinta ba daɗi, amma tabbas tana da tambayoyi dayawa da suka cunkushe zuciyarta, Dama gidan marayu bibiyar rayuwar mutun suke yi idan suka ga iyayen shi sun mutu sai su sato shi zuwa cikinsu? Meyasa batool tace sau ɗaya ake basu abinci a rana kamar yadda ta faɗa mata ɗazu!  Meyasa za'a haɗa maza da mata a ɗaki ɗaya? Meyasa mutanan dake kawo masu abinci su ka yi 6adda kama!? Meyasa ba'a shige da fuce acikinsa? saboda me a ka yi masu iyaka da komai na cikinsa? Tabbas kuwa akwai wata maƙarƙashiya da ake shiryawa acikinsa, kodan saboda wannan tambayoyin da suka toshe kwakwalwarta, dole ta sanya nutsuwa don ta gano komai dake wakana,

  "Zanje na kwanta, Amma kafin nan i naso ki faɗa mun sunan ki, duk da naji ɗazu kamar tsohuwa ta ambace shi, sai dai ban ruƙe ba," muryar batool ce ta katse mata zancen zucin nata,

   Ajiyar zuciya angel ta sauke kafin tace"Sunana ANGEL ke fa?" batool ta bata amsa da cewa"Ni sunana BATOOL inaso ki ɗauke ni tamkar ƴar uwarki, kuma ina so ki saki jikin ki acikin mu, ta hakanne zaki samu duk abunda ki ke so,"

      "Kin wahaltu sosai yau, ki samu ki yi bacci, takai ƙarshen maganar tare da jan bargo ta lullu6e fuskar angel da shi,

   "Sleep well my lovely sister" ƙasa ƙasa da murya angel ta furta mata"thank u, Sister" murmu shi batool tasaki ba ƙaramin daɗi taji ba, da angel ta kira sunanta da sister, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta kwanta, kamar daga sama ta jiyo muryar hannah"kin gama kula da jinjirar ta ki? Tsoki batool taja" mind ur own business" tana faɗin hakan bata ƙara tanka mata ba,

      Kowa ya runtsa a daren ranar banda mutun ɗaya! Dama taya zata iya bacci? ya yin da zuciyarta ke a cunkushe a ƙuntace da rashin mahaifinta, duk da har yanzu bata gasgata kalaman dattijuwar nan ba, ita dai tana ji aranta daddyn ta he's still alive! kuma taci alwashin duk runtsi duk wuya sai ta nemi hanyar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, ni dai nace Allah ya ba mai rabo sa'a,

      Ataƙaice cikin ƴan kwanakin nan ba irin haukan da angel ba ta yi masu ba akan su fitar da ita daga cikin kurkukun amma duk a banza, babu mai saurarenta acikinsu batool ce kaɗai ke lallashinta, duk ta bushe ta rame dama ba ƙiba gare ta ba, yadda kasan ɗiyar roba haka ta koma cikin sati ɗaya kawai, duk ta fita hayyaci kuma taƙi sakin jiki da su, musamman mazan haushin su take ji, saboda wannan Danish ɗin da basa jituwa da shi, ta tsane shi kamar mutuwarta shima haka ya tsaneta ko kallon arziƙi bai haɗa ta da shi, ko fira suke yi ta sanya masu baki to ya gama magana, ita kallan ɗan iska ta ke yi ma shi saboda doguwar sumar dake akan shi ita a ganinta ta ya yana namiji xai tara suma? tsayin sumar shi har ya kusa taddo nata, gaba ɗaya dai haushin mazan take ji saboda an haɗa su rayuwa a wuri ɗaya sam bata so ko kallonta su na yi ae ita a wurinta iskanci ne hakan, abunda bata sani kwata kwata basu da feelings a tare da su, suna ɗaukar kansu tamkar jinsi ɗaya da matan, ita ce kawai ta sanyawa ranta hakan, bakomai ya ƙara ɗaure mata kai ba fa ce rashin barin su yin ibada, batool ta sanar da ita cewa basu da addini, duk wanda ke rayuwa acikin kurkukun ƙaddara baida addini, rayuwa kawai suke yi tamkar arnaku ko sunan Allah basu ambato acikin maganar su, ba sallah ba sallati, bama su san yadda akeyin ta ba, dokar prison ɗin ce ba'a ibada acikinsa, wani irin kurman kurkuku ne, baka sanin lokaci dare ne kaɗai  idan ya yi suke ankara saboda hasken ɗakinsu da ake ɗaukewa sai kuma idan safiya ta yi sun ta shi daga bacci, ita kanta angel ɗin ta ta6a gigin yin sallah, duk da basu da hijabi, ranar da tayi alwala ta  yafa bargon lullu6arta da sunan za ta yi sallah,  zagaye ta su ka yi suna kallonta da mamaki don basu san menene take yi ba, da zarar ta ɗaura niyya zata kabbara, sai ta dinga jin kukan mahaifinta, idanuwanta su dinga nuna mata fuskar tajuddeen wuta na ƙone jikin shi, gaba ɗaya take rikicewa ta gigice ta dinga kuka ire iren irin wannan gane gane da take yi yasa ta daina yunƙurin yin sallar, abun yana affecting ɗin ta


    Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma'anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta, 


*Boss Bature✍️💋* 


 *After some weeks*


Zaune take a tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, idanuwanta suna arufe fuskar nan ta yi jawur idanuwan sun kumbura, ga busassun hawaye duk akan fuskarta,

   Kasancewar safiya ce ba su jima da farkawa daga bacci ba, 

  Sautin dariya taji ƙasa ƙasa taji muryoyinsu suna yin gulmarta "Wari take yi, tun da tazo bata yi wanka ba daga gani dai ƙazama ce," can ta ji muryar wani ya kuma cewa"idan muka ƙyale ta mu zamu cutu, jiya fa daƙyar nayi bacci saboda warin jikinta gaba ɗaya ya cika ɗakin nan," tuntsure wa su ka yi da dariyar shaƙiyanci, 

  "Ku ta shi muje muyi mata magana, ta je ta yi wanka, in ba haka ba mu zamu yi mata da kan mu,"  haris ne ya bada wannan shawarar,

   Angel dai ta natsu tana sauraronsu, dama mugun haushin su take ji, tana jiyo sautin tafiyar su a bakin gadonta suka tsaya kusan su shida,

  Gyaran murya ɗaya daga cikin su yai mata"ke tashi ki je ki yi wanka" a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗan kalle su, wanda ya yi magana shi ne Haris, a halitta baƙi ne yana da jiki, 

   "Ba zamu zuba maki ido kina cutar damu ba, jiya nan daƙyar mu ka yi bacci saboda warin jikin ki, don haka ki tashi kije ki yi wanka ko mu yi maki da kanmu" cike da ƙwarin gwiwa javed ya yi maganar, dogo ne launin fatarsa chocolate,

    Jin ta yi banxa ta ƙyale su yasa Mubeen jinjina kai ya kalli naufal dake a gefen shi yace "je ka cika mana bokiti da ruwa," ya yi maganar yana naɗe hannun rigar shi,

      Danish da ke a kishingiɗe saman gadon shi bai tanka masu ba, yasan suna yi duk don su ƙuntata mata ne saboda tsanarshi da ta yi, 

     ƴan matan dake a tare da su Deeja da yasmeen, sun ruqe qugu suna sakin murmushin mugunta,

      Da alama dai hada ƙuruciya ke damun su, don dukan su gaba ɗayan su baza su wuce shekara shabiyar ba, mazan cikinsu ne ke akwai ƴan shekara sha bakwai, kamar danish dasu haris,

     "Bakya ji ana maki magana"? muryarta na kerma tace" duk wanda ya yi gigin ta6a ni, zanyi mashi illah, babu ruwanku da rayuwata," tamkar xata fashe da kuka ta yi maganar,

      "Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, zamu gani mu dake wazai ma wani illah," haris ne ya yi maganar, tare da naɗe hannun rigarshi yace dasu Naufal su ɗauko mashi ita, akaita toilet su yi mata wankan tsarki,

      Jin haka yasa ta durowa daga saman gadon, Duk da jikinta ba ƙwari daure wa kawai take yi, hannu haris yakai zai ruƙo kwalar rigarta, aikuwa ta daddage ta ɗaga kafarta tare da kai mashi naushi tsakiyar cikin shi, azabar zafi yasa ya yi saurin dafe cikin shi, rai a6ace javed ya kai mata bugu aikuwa ta damƙi ƙafar shi ta hagu ta dinga janta har saida ta yarfar dashi ƙasa, faɗa ne ya kaure a tsakaninsu, bugu tadinga kai masu da naushi, dama ta ƙware wurin iya cixo da yaku shi, duk sai da ta raunata su, sai faman nishi suke yi, da taga ta gama da mazan ta koma kan matan,


Haɗe kawunan su tayi, ta ruƙo gashin kansu, tadinga ja tamkar xata tsunka su, kuka hada majina suka dinga yi, 


    koken koken da suke yi ne ya farkar da su Batool da sauran ƴan uwan nasu dake bacci, ganin yadda Angel take Mazgarsu yasa suka sauko daga saman gadon suka nufeta suna ƙoƙarin rabata da su, daƙyar suka samu nasarar janye Angel gefe ɗaya, sai huci take yi kamar kuranya, Su deeja da yasmin suna zuƙunne ƙasa, dafe da kawunansu sai kuka suke yi,  


     Duk wannan abun dake faruwa tsohuwa tana a tsaye baƙin ƙopar ɗakinta, hannunta ruƙe da sanda, ta yi tsaye tana kallon sabuwar ƴar wasan damben da suka samu,


      Danish kuwa dake kishingiɗe saman gadon shi, hankalin shi kwance dama yasan za'a rina, shiyasa bai shiga cikinsu ba, koda suke xancan zasu je suyi mata magana akan wanka, don ya lura ƙarfi ne da ita, gashi duk cikinsu itace ƙarama amma tafi su ƙarfi,


  Gyaran murya tsohuwa ta yi, da sauri angel ta ɗago tana haki, suka haɗa ido da ita, 


  "Aikin ki ya yi kyau, tsanar da ki ka yi masu har takai ga bugunsu so ki ke ki kashe su?"

  Rai amatuƙar 6ace tace" bugun su yanzu na fara idan har ba su daina shiga gona ta ba, kuma wlh idan har baku fitar dani daga cikin kurkukun nan ba, zan addabi rayuwar kowa ne, nace banaso ku ƙyale ni inyi rayuwata na tsani gidan nan, Natsani kowa dake acikinsa, kince nan gidan marayu ne kuma za'a gatanta mu but why kuka killace mu sai ka ce dabbobi? haka ne gatancin Abinci sau ɗaya a rana? Kun hana mun yin ibada, uwa uba kun haɗa mu rayuwa da maza a ɗaki ɗaya? Me hakan yake nufi iye"? Idanuwanta azazzare ta yi maganar, tamkar ta sanya hannu ta shaƙo wuyan tsohuwar hake take ji,


   Maimakon tsohuwar ta bata amsoshin tambayoyinta sai ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya, 

  Runtse ido angel ta yi cikin jin zafin dariyar tsohuwar, cije lips ɗinta ta ɗanyi kafin ta buɗe eyes ɗin nata, 


    "Wlh ban yadda dake ba, saboda gaba ɗaya babu gaskiya acikin kurkukun nan, idan kun 6oye mana manufarku ta killace mu anan baku isa ku 6oyewa Allah ba, yana ganinku kuma asannu Allah zai warware mana komai, ni nasani zuwana gidan kurkukun nan jarabawa ce ta ubangiji........."daƙyar takai ƙarshen maganar saboda hawayen da suka cika mata idanuwanta,


   "Dabbar dake yawo a daji, tafi mu gata tafi mu ƴan ci, idan su basu damu ba, zai iyayiyuwa don sun taso rayuwarsu acikin kurkukun ne, kuma sunsan basu da kowa, amma nifa ina da dangina masu sona, hakanan anje an sato ni an kawo ni cikin wannan munafukin ƙaddararran kurkukun mara kan gado,"

   "Angel" muryar batool ce ta ambaci sunanta, a harzuƙe angel ta juya baya tana kallon batool tace,

  "Nasan bai wuci ki ce xaki bani hakuri ba, akan inja bakina inyi shiru, Batool bazan Iya ba, narasa gane meyasa bakwa fahimtata ne, iya cutuwa an cutar da rayuwata, tun ina jinjirata mahaifiyata ta gudu tabarni a wulaƙance cikin kwamin wanka, nata so cikin so da ƙauna na mahaifina, An raba ni da shi, An kashe mun shi duk da har yanzu ban gasgata hakan ba, sannan na faɗa hannun fulanin daji, na rayu acikin daji tare dasu a matsayin tsintacciya, wai ni Angel ƴar gidan daddynta, na shiga mawuyacin hali  na rashin mahaifina atare dani, na saba dashi mun shaƙu sosai, komai shi yake yi mun wanka, ya gyara mun gashin kaina mu kwana rungume da juna, dama haka rayuwa take? Lokaci ɗaya narasa gatancin nan, na dawo ina kwana a saman tabar ma cikin bukka, bani da abinci daya wuce gasassar masara da fura, yanzu kuma gashi na tsinci kaina acikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, ya a ke so inyi da raina? Wlh da rayuwa acikin kurkukun nan kwara na ƙare rayuwata a hannun fulani daji, koba komai zan sha iskar duniya, in yawata inda nakeso, inyi rayuwar ƴan ci, Amma nan fa? Ta karfi ta tsiya aka kawo ni cikin shi banma san ta ina aka shigo dani cikin gidan kurkukun nan ba, don kuwa sai da aka fara gusar mini da hankalina tukunna, in banda munafurci taya xa'ace gidan marayu ne? Meyasa da za'a kawo ni cikinsa ba'a barni cikin hayyaci na ba? Meyasa za'a hana mu shige da fice, An tauye mana haƙkin mu na rayuwa an hana mu sakat wai da sunan za'a gatanta mu......................' 


    (SHIN ME KU KE TUNANI AGAME DA GIDAN KURKUKUN ƙaddara, WASAN FA YANZU AKA SOMA BUGA SHI, DOMIN KUWA BAMU NUTSA CIKIN LABARIN BA, YANZU AKA FARA)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post