Kurkukun Ƙaddara page 22 complete

Kurkukun Ƙaddara page 22 complete

 


💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E22


Daga alkalamin Boss Bature writer of Abban Sojoji🌹


Zuba ido tayi tana jira taga me zasu Yi mata, wani irin zazzafan taku giant ɗin yayi yadda kasan Zaki Ya nufi abun harinsa, tuni jikin angel ya soma kerma, ta ƙanƙame jikinta tana girgiza mashi kai, muryarta na kerme ta shiga faɗin"wlh kada ka kuskura ka ta6a....."bata kai ƙarshen maganar ba, Taji ya damƙi qugunta ya ɗaga ta sama, yadda kasan ƴar tsana, ta dinga ihu tana kuka tamkar ranta zai fita, saukowa da iya yayi daga saman benan, Su batool duk sunyi tsuru tsuru suna kallon shi, 


  Daga inda yake yayi wurgi da angel Wani iko na Allah, Saboda tsabar iya saitinsu, bata faɗa ko'ina ba sai saman gadonta, gaba ɗaya ta kife sumar kanta duk ta tarwatse saman mattress ɗin, Juyawa Giant ɗin Yayi ya koma inda sauran ƴan uwan nashi suke, buɗe ƙopar su kayi suka fuce tare da datseta,


Kusan atare su Azeeza suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa suka nufi angel, wadda tunda giant ya wurgar da ita saman gado bata ƙara motsi ba,


Jikinta gaba ɗaya ya mutu, tamkar wadda aka zarewa laka, Ta furgita sosai lokacin Daya jefar da ita, har wasu baƙaƙem turari  masu wutsiya ta dinga gani acikin idanuwanta,


  Hayewa saman gadonta, Batool hanna da azeeza sukayi, Sai kokari suke yi wurin ɗago da ita,


  Su javed mubeen da Su Deeja duk suna a kewaye da gadon, 

 "Angel,angel.pls wake up! dan Allah ki tashi angel, Muna atare dake Kinji? 

  Suna magana suna jijiga jikinta, Haris yace"laifinta ne, tun farko saida muka gargaɗeta amma saboda taurin kai irin nata taƙijin maganarmu, yanzu wa gari ya waya " yayi maganar Cikin halin ko'in kula,

  Eve tace"bari naje na fada ma tsohuwa, azo a duba lafiyar jikinta" da hanzari ta juya ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Kafin ta kwankwasa ƙopar ɗakin sai ga tsohuwa ta buɗe ta fito hannunta ruƙe da sanda,


  "Meke faru wa ne yara"? Her voice was shaking tace"an...gel...ce 

.....bata motsi...' 

  "Keep calm and tell me what's wrong, with her? is she not feeling well?


 Jinjina kai Eve tayi"Giant ne ya wurgar da ita, Tun ɗazu muke akanta, bata farka ba, ko motsi ba ta yi"


Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan tsohuwa suna jira suji amsar da zata basu,


Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tare da cewa"Yarinyar ce taci ka kafiya, sam bata jin magana, shiyasa bana so kuna yin koyi da ita, domin kuwa zata 6ata maku tarbiya ne, tun tana yarinya  ba ƙaramar hatsabibiya bace......." gaba ɗaya tsohuwa ta takwashe tarihin rayuwar angel ta sanar dasu, hatta bugun da tasa ƴan ƙato da gora su kayi ma Mahaifinta, kuma a ƙarshe tace masu itace silar da mahaifinta ya rasa ranshi,'  da alama tsohuwa tana ƙoƙarin dasa masu kiyayyar angel acikin zuciyoyinsu ne, gaba ɗaya sun saki baki galala suna kallonta,


  Batool ce tayi kokarin cewa"Amma angel ta faɗa mun cewa daddynta wasu ne suka kashe shi, kuma shine ya jefa ta Cikin ruwa, " bazawarin murmushi tsohuwa tasaki tare da girgiza kai tace"Ƙarya take yi maku, muguwar makirace, Ta faɗa maku hakanne don ku tausaya mata ba"


 Aruɗe azeeza tace"amma angel bazata ta6a yi mana ƙarya ba, saboda tana son mu dagaske, Kuma idan bazan manta ba, lokacin da aka kawo ta kurkukun nan, kefa da kanki kika ce zaki faɗa mata waɗanda suka kashe mahaifinta, meyasa yanzu kuma zaki ce mana  itace tayi silar mutuwar shi!"? Cike da tuhuma azeeza ta jefa mata tambayar, sam tsohuwa batayi tsammani wani daga Cikinsu zai iya yi mata gaddama ba, tabbas an fara samun matsala,


  "Kinyi shiru baki bamu amsa ba tsohuwa? Kodai azeeza tayi gaskiya ne? 

 Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa tsohuwa kai,

 Javed yace"Nima idan zan Iya tunawa keda kanki tsohuwa kika ce Iyayenta sun rasu, hakan na nufin ita kanta angel ɗin batasan cewa iyayen nata sun rasu ba, sai a bakin ki taji hakan, But why kike kokarin ɗaura mata laifin kashe Daddynta? anya kuwa tsohuwa?ya kai ƙarshen maganar da alamun kokwanto,

   Haris dai ya rasa bakin magana ba, hatta sauran duk sun natsu suna jiran amsar da tsohuwa zata basu,

  

Rai amatuƙar 6ace, tsohuwa ta buga sandar hannunta kasa, Nan take kowannan su ya toshe kunnuwanshi, sakamakon sautin buga sandar daya doki dodon kunnuwansu,


Da kakkausar murya tace"Zan sake maimaita maku, Kudaina yarda da maganarta, Ni kaɗai ce na isa da ku, Babu wani mahaluƙin daya isa ya sarrafa tunaninku, Ina fata an fahimce ni" Da sauri suka amsa mata da toh, 

Cigaba da magana tayi"Angel ba sonku take yi ba, sam bata ƙaunarku, tana so ta shiga tsakanina daku ne, Ni kuma bazan bari hakan ta faru ba, saboda bana so ta gur6ata ku kamar yadda take gur6atacciya" A ladabce suke amsa mata da toh, deeja tace"Amma idan muka ce zamu ƙi bin Umarninta, Zata karanta mana charman dudu ne Cikinmu ya kumbura, shiyasa muke jin shakkarta", 

  

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta saki aranta tace"Yarinya sai ɗan banzan wayau uwa dila agari" a fili kuma tace masu"Charman dudu ba wani mummunan abu ne, Angel tayi maku wayau  ne don ta tsoratar daku, Saboda ta lura bakusan ainihin ma'anar kalmar ba" cike da mamaki suke kallon Juna, Jin abunda  tace, Batool tace"zamu iya sanin ma'anar Kalmar"?

Jinjina kai tsohuwa tayi, Cikun hikma ta fayyace masu komai game da asalin kalmar charman dudu, har waƙar ta raira masu, ' ransu ya 6aci sosai, irin yadda angel ta azabtar dasu da kalmar ashe ma waƙa ce ba abun cutarwa ba, sunji haushi sunji takaici, musaman haris da Deeja,


"Daga yanzu, Ku daina yarda da duk wani abu da zata faɗa maku, saboda wayau ne da ita, so take ta burkita maku lissafi" acewar tsohuwa,


Parveen tace"Amma tsohuwa menene ma'anar Sunan Allah dakuma Bil'adama? Angel tace mana Allah shine Ya halicce mu dagaske ne"? 


Har saida tsohuwa ta zabura jin tambayar da parveen tayi mata, Lokaci ɗaya kuma ta murtuƙa fuskarta tare da cewa"Shima duk ƙarya take Yi maku, babu wani Allah, idan harta ƙara matsa maku akan Ku yarda cewa akwai Allah, Ku sanar da ita cewa Ta kira maku shi ku ganshi da idonku, Kafin Ku yarda dashi anan zaku tabbatar da cewa ita ɗin babbar maƙaryaciya ce," takai ƙarshen maganar fuskarta ɗauke da wani irin munafukin shu'umin murmushi, irin na tantiran ƴan duniyar nan waɗanda suka ga jiya suka ga yau,


Aka ce rashin sani yafi dare duhu, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar tsohuwa, 


 Ganin taci galaba akansu yasa  ta Juya tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, Tare da jan ƙopa ta datse,


Abunda ya faru tun lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, gaba ɗaya Tunaninsu ya canza, daga gardamar da suke yi mata zuwa bin umarninta, yanzu gaba ɗaya sun ɗauki maganarta, aransu duk sunji sun tsani angel saboda ta kashe mahaifinta, tsoronta ma suke Ji yanzu kada suma ta kashe su, ga haushin ƙaryar da tayi masu na Kalmar Charman dudu da take yi masu barazana da ita, jira suke tafarka suci ubanta, Bayan wannan kuma tayi masu ƙaryar cewa akwai wanda ya halicce su, lallai angel tana a tsaka mai wuya  fidda ta sai ALLAH,


 Ta yi matuƙar karya masu zuciya, Jikin su duk yayi lakwas tamkar an zare masu laka, tafiya suke yi kamar mashayan giya, Idon kowa na akan gadon angel dake kwance magashiyan rai hannun Allah, Ji suke kamar su rufe ta da bugu har saita gaza tashi, 


Komawa su kayi saman gadajensu Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar 6acin rai, Kowa ya shiga faɗin Laifin da angel ta aikata mashi da kuma irin fansar da zasu ɗauka akanta idan ta farfaɗo, don sunci alwashin sai sun  raunata Sassan Jikinta, 


Tsawon awanni angel ta ɗauka, Ba ita ta ta shi farkawa ba, Sai Wuraren marece, Da wani irin yunƙurin amai ta farka, da gudun gaske ta duro daga saman gadonta, idanuwansu akanta babu wanda yayi yunkurin zuwa ya taimaka mata,


  Toilet ta shige a galabaice Ta zuƙunna gaban  tap tana kwarara amai, bakomai ke fitowa daga Cikin bakinta ba, face xallar ruwa, Cikinta sai tuƙuƙun azaba yake yi mata, har wani jiri take Gani, Cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan Batool don tazo ta taimaka mata, 


Batool tana jin muryar angel cikin mawuyacin hali amma zuciyarta ta hanata zuwa inda take, Kowa haushinta yake ji, An canza masu tunaninsu, hatta azeeza da tafin kowa jin tausayi ayau itama ta juya ma angel baya,


Koda taji batool bata amsa mata ba, sai ta shiga kiran sunayensu ɗaya bayan ɗaya, suna jinta amma su kayi kunnan uwar shegu da ita,


Numfashinta sama sama yake fita da hucin zafi, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai, hakanan ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, dakyar ta samu aman ya dakata da zubowa, ta kunna tap ruwa ya shiga kwararowa, Ta tarba tafin hannayenta, ruwa ya taru acikinsu, ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta, 


Sam takasa ta6uka komai, saboda tashin zuciyar da take ji, Ga jiri da take gani acikin idanuwanta, temperature ɗin Jikinta yayi zafi sosai da alama zazza6i ne ke shirin yi mata mugun kamu, tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa cos she's feeling dizzy idan ta yi attempting miƙewa tsaye, 


  Bata fasa neman ɗauki daga wurinsu ba, Taci gaba da ambaton sunayensu"Batool! Azeeza! hibba" muryarta a disashe take maganar daƙyar ma take ƙoƙarin ɗaga muryarta, Jin basu amsa mata ba, yasa ta soma kiran sunayen mazan dake acikinsu


  "Javed! Mubeen! Naufal!' nan ma taji shiru basu amsa mata ba, lumshe runannun idanuwanta tayi tare da cizon lower lip ɗinta,


Daga Can Cikin ɗakin kuwa, Hankalin batool yaƙi kwanciyar, tana so taje ta taimaka mata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai, Idan ma tayi motsi kamar zata sauko daga saman gadonta, sai haris ya dakatar da ita tare da cewa"duk wanda ya kuskura yaje da niyar taimakata, babu ruwan mu da shi,"  tunzurasu yake yi duk don saboda kada suje su taimaki angel 


In taƙaice maku zance, A gajarcanshi Har dare yayi babu wanda ya motsa daga Cikin su, Sun bar angel acikin toilet ita kaɗai, tun tana kiran sunayensu har tagaji tadaina,  baiwar Allah ta shiga mawuyacin hali, anan cikin cikin toilet ɗin ta kwanta saman floor ɗin, abu uku suka haɗe mata a lokaci ɗaya, Ciwon kai, raɗaɗi da  Cikinta ke yi mata da kuma matsiyaciyar yunwar data addabe ta, yinin ranar ko ruwa bata kora ma maƙoshinta ba, ya bushe ƙamas har wani ƙaiƙayin azaba yake yi mata,


Kafin su kwanta bacci, sai da suka cinye abincin angel da batool ta ajiye masu ita da haris, Koda  su ka kammala cin abincin, Zaman jiran dawowar Danish Suka tsaya yi, har saida tsohuwa ta fito daga Cikin ɗakinta ta same su a zazzaune saman gadajensu, ganin damuwa akan fuskokinsu yasa tace"Akan danish ne"? Har suna haɗa baki wurin amsa mata da eh, Shiru ta ɗanyi tana kallonsu kafin tace"ku ƙara haƙuri, danish bazai samu damar dawowa yau ba, jikin nashi yayi tsauri sakamon Illar da ƴar uwarku angel tayi mashi, akwai wani dafi a hannunta wanda ku baku sani ba, idan har ta yakushi mutun kota gartsa mashi cizo, ya ɗauki tsawon lokaci ba'a bashi emmergency treatment ba, Dafin yana Illata sassan jikin shi ne, kuskuren da mu kayi shi ne, da bamu yi gaggawar miƙa dashi zuwa treatment room ba, lokacim da Angel tayi mashi wannan jahilin bugun, Shiyasa har Dafin yayi mashi illa ajikinshi........." dakatawa ta yi da yin maganar fuskarta duk a harmutse duk don su yarda da abunda take faɗa masu, Cikin jin ƙunar rai haris yace " idan har ɗan uwanmu ya rasa ranshi saboda ita, bazamu ƙyale ta ba, ita ma sai mun kashe ta" yana rufe baki deeja tace"Ae dama ba son shi take yi ba, muguwa kawai, tun da tazo gidan kurkukun nan, ta ɗaura mashi karan tsana ni bansan me danish ya tsare mata ba, " takai kai karshen maganar tana huci,


 Haris Yace" Yadda tayi ma danish Jahilin bugu, muma sai mun rama mashi, In yaso suyi jinyar atare" 


 Yasmin tace"ƙwarai kuwa, Muje mu same ta har inda take, mu nakaɗa mata bugu har sai ta kasa tashi,"

  

Tsohuwa ta fakaici idonsu ta saki wani irin kafin murmushi, hanya mafi sauƙi da zata koya ma angel hankali, saboda rashin kunyar da take yi mata,


Cikin sanyin murya batool tace"Bai kamata mu ce zamu bugeta ba, wannan ba dai dai bane, saboda ita ɗin yarinya ce duk mun girmeta, bugu bashi zaisa ta gane kuskurenta ba, idan muka daina shiga sabgarta ma ya wadatar, daga yanzu babu ruwanmu da ita, har sai danish yaji sauƙi ya dawo cikinmu tukunna zamu waiwayeta," 


Azeeza tace"na goyi bayan shawarar da batool ta bada," suma sauran su ka ce duk sun goyi bayanta, banda haris da deeja,


"Tsohuwa yanzu Sai yaushe kenan zamu sake ganin ɗan uwanmi? Idanuwanmu sun yi maraicin rashin ganin shi"  javed ne yayi maganar muryarshi a sanyaye,

 

  Tsohuwa tace" A yadda mu ka tattauna da giant, Ya sanar dani cewa"Danish zai ɗauki Tsawon kwana Biyar Kafin ya dawo cikin ku," 


Ransu ya ƙara 6aci jin cewa sai ya ɗauki tsawon kwana biyar kafin ya samu sauƙi, Kamar su ɗaura hannayensu saman kawunansu su fasa ihu, haka suke ji saboda tsabar takaici, tsanar da su kayi ma angel ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarsu,


"Kowa ya je ya kwanta, Mu kwana lafiya Yara na" takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana dogara sanda Ta nufi ɗakinta, ta shige tare da jan ƙopa ta datse,


Kallonsu batool tayi"Mu yi haƙuri muje mu kwanta," gyaɗa kai su kayi kowa Ya wuce zuwa saman gadon shi Ya kwanta,


Gaba ɗaya duk tattaunawar da su batool su kayi tare da tsohuwa akan kunnan angel, baiwar Allah da rarrafe ta fito daga Cikin toilet, ɗin abakin ƙopar shiga ɗakinsu, Ta zauna tare da jingina bayanta, saboda takasa ƙarasa tafiya cikin ɗakin, Kaf taji irin ƙalin sharrin da tsohuwa tayi mata, sai yanzu ta gane dalilin dayasa suka juya mata ba, Lokacin ta take ta kiransu acikin toilet don su kawo mata agaji, ashe sun jita suka ƙi zuwa, saboda tuggun da tsohuwa ta ƙulla mata,


Jikinta duk yayi sanyi, zuciyarta ta karaya, Don sun ɗauki gaba da ita wannan ba damuwarta bace, ta yi masu uziri saboda jahilcin dake ɗawainiya dasu, ita tausayinsu ma take ji, yadda ake ta juya masu tunaninsu, wanda da ace suna da wayau babu wanda ya isa yayi masu haka,


Abu uku ne yafi tsaya mata arai, na farko shine Batool, bata ta6a tsammanin batool zata Juya mata baya ba, Tunanowa tayi da maganarsu ta jiya da kanta take faɗa mata cewa"Koda ace kowa zai juya mata, Ita tana atare da ita, kuma a koda yaushe zata kasance a hannun damanta, amma sai gashi yau ba irin kiran sunan batool da batayi ba aka tazo ta taimake ta amma taƙi zuwa, Abu na Biyu kuwa meyasa tsohuwa take Yi masu ƘARYA? da girmanta tsofe tsofe da ita? ƙaryafa alamace dake nuna cewa mutun baida gaskiya, lallai wannan matar ba ƙaramar makira bace, abu na ƙarshe daya tsaya mata aranta shi ne DANISH! A wani hali yake ciki? Meke faruwa da shi? meyasa baza'a dawo da shi cikinsu ba? Jiyafa tsohuwa da kanta tace masu yau zai dawo, amma kuma yau sai gashi ta canza magana, meyasa❓❓❓


Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, 


A hankali ta kifa kanta saman gwiwowinta, yalwatacciyar sumar kanta ta yi mata rumfa tamkar hijabi, shessheƙar kuka taci gaba da yi ita kanɗai a cikin toilet area, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, gaba ɗaya ta tsani Gidan Kurkukun ƙaddara, A yanzu bata ƙi ta samu hanyar da zata gudu daga Cikin shi ba koda kuwa ita kaɗai ce, tunda ta lura Yaran da take son taimaka ma rayuwarsu, Zaiyi wuya taci galaba akansu, saboda already an juye masu tunaninsu, 


Dare yayi sosai, duhu ya mamaye Cikin idanuwanta, ƙasa ƙasa da murya take ambaton sunan daddynta, wata magana ce ta faɗo mata acikin ranta wanda daddynta ne ya ta6a faɗa mata ita

    

_Ki sama ranki cewa ko babu ni zaki iya rayuwa, nasan cewa ƴata jaruma ce, mutane suna yabonki saboda ƙwarin gwiwar dake gare ki, Angel bana so rashina yayi silar canzawarki_ a lokacin da taj yayi mata wannan maganar saita fashe da kuka tana faɗin"Nidai daddy kada kayi mun maganar mutuwa bana so," murmushi taj yayi idanuwanshi cike tab da kwalla yace"daughter mutuwa dole ce, ni dai kawai alƙawarin da nake so kiyi mini, shi ne, ki kasance a yadda kike ko bayan raina, kada ki bari wani abu ya canzaki, kada kiyi tunanin idan kika rasa ni xaki rasa gatanki, Domin kuwa Allah yana atare dake, kuma shine gatan kowani bawa, idan kika shiga hali na ƙunci Allah zaki kaima kukanki, In sha Allah zaki samu mafita_


Sosai angel ta fashe da kuka tunawa da wannan maganar ta mahaifinta, wani irin yanayi ta shiga mara misaltuwa, kusan raba dare Tayi acikin toilet area ɗinsu, batare da ta motsa ba  Jikinta duk yayi tsami babu daɗi, ga kaɗaici dake damunta, ga yunwa da ciwon da take fama dashi duk ita kaɗai,


Ɗagowa ta yi  da fuskarta wadda ta kumbura suntum tayi jawur, Tsinin hancinta yayi Ja, saboda matsar daya sha, Idanuwanta sun kumbura sun ƙanƙance, daƙyar take iya buɗe su, dogayen yatsun Hannayenta sai kerma suke Yi, wani irin matsanancin sanyi ne ya mamaye Jikinta, ta ko'ina babu sauƙi,


Daƙyar ta samu ta lalla6a Jikinta, Ta buɗe kofar da rarrafe Ta shiga Cikin ɗakin, tana tafiya tana kallon gadajensu duk sun kwanta sun lullu6e da bargo, hankalinsu kwance sai sharar bacci suke yi, adai dai bakin gadonta, Ta yunƙura ta miƙe ta haye sama ta kwanta, ta janyo bargo ta ƙudundune jikinta,


Acikin Ƴan kwanakin Nan angel ta fuskanci Mawuyacin Hali, saboda juya mata bayan da su kayi, Haris Ya samu damar fanshe haushin shi akanta saboda sunga bata da ƙoshin lafiya, wani sabon wulaƙancin, Sai haris yaga tana bacci, Ya je toilet ya Ciko bokiti da ruwa ya sheƙa mata ajikinta, Idan aka kawo masu abinci tana bacci, babu me tashinta daga Bacci, Haɗuwa suke su cinye mata abincinta, Sai da ta jera kwana Uku bata Ci abinci ba, Ta rame ta ƙanjame, Ta zama abun tausayi, ko magana daƙyar take iya furtata, yanzu takai ga ita ke ji shakkarsu, saboda Rashin lafiyar da take ɗawainiya da ita, bata son abunda suke Yi mata, duk Cikinsu mutun uku ne basu ta6a yi mata wulakanci ba, Batool Azeeza da Javed, basu atare da ita amma kuma ko kallon banza bai ta6a haɗa su da ita ba, kawai dai sun janye jikinsu daga nata ne, ita kanta angel ta lura da wani abu agame dasu, Sam wani abun bada son ransu suke yi ba, kamar ana tunzurasu ne, Shiyasa take Yi masu uziri, Duk wani plan ɗinta a yanzu ya tarwatse, Saboda juya mata bayan da su ka yi, Yanzu takaiga Ko sunan Allah da suke fadi sun daina, taya zata fahimtar dasu Cewa Akwai wanda ya halicce su, Bayan Sun ƙureta akan sai ta Kira masu Allah yazo sun ganshi tukunna zasuyi Imani dashi? Wa'iyazubillahi, Tsohuwa ta gama da rayuwar bayin Allahn nan, suna A cikin duhun jahilci, zaiyi wuya ta shawo kansu Cikin sauƙi, Saboda tsanarta da su kayi ayanzu tafi sha'awar zama Cikin toilet, akan ta zauna Cikin ɗakinsu suna yi mata gal6anci da rashin wayau ba, Sun kasa banbance tsakanin gaskiya da ƙarya, Duk da ba laifin su bane,  


*Boss Bature🌷✍️*


Runtse idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su, ita kaɗai zaune Cikin duhu, Ta gaza runtsawa, 


Shessheƙar Kukan Azeeza Taji, Tasan bai wuci fitsari take Ji ba, ganin ita kaɗaice idonta biyu Yasa ta sauko daga saman gadon, Ta je inda fitilun ɗakinsu suke tabi kowacce ta kunna ta, kafin ta ɗauko ɗaya tana haska Cikin ɗakin, A tsaye ta hango azeeza ta matse idanuwanta, hawaye sharkaf, ƙarasawa tayi da sauri ta ruƙo hannunta, 

  Ta rakata Cikin Toilet, Tayi fitsarin A bakin fita daga Cikin toilet area ɗinsu, Angel ta tsaya tana haska fuskar azeeza,

  "Angel" taji ta ambaci sunanta, ba ta yi tsammanin zata Shaida ta ba,


"Taya akai kika gane ni ce"? tayi tambayar tana kallonta,


"Naji ajikina cewa ke ce, " shiru angel tayi na ɗan wani lokaci suna fuskantar juna kafin tace"Azeeza kema kin tsane ni ko? Baki son ganina ? Shiyasa ko magana ba kuyi mun,' idanuwanta acike tab da kwalla tayi maganar,


Girgiza kai azeeza tayi fuskarta da alamun rauni attare da ita tace"ba haka bane angel, dai dai da rana ɗaya ban ta6a jin tsanarki acikin zuciyata ba, kawai ba yadda zamuyi ne, sai kina yi mana uziri,  mu kanmu bamu jin daɗin abunda ke faru atsakaninmu, " takai ƙarshen maganarta, tare da rungume angel a jikinta, kusan atare suka fashe da kuka, 

    Cikin shessheƙar kuka azeeza take faɗin"ni nasan cewa angel ba cutar mu kike yi ba, kamar yadda tsohuwa take faɗa mana, ke mai son mu ce, kina ƙaunar mu, kamar yadda kikayi niyar taimakon mu, kada ki fasa angel," 


Kalaman azeeza ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sosai ta ƙara huggin dinta tightly a jikinta,


Suna Cikin wannan yanayin su ka ji sautin shessheƙar kukan mutun, da sauri angel ta saki azeeza, ta wurga idonta kan mutumin dake tsaye abakin ƙopa, Da fitilar hannunta ta yi amfani wurin haska fuskarta, bakowa bace face batool,  fuskarta sharkaf da hawaye Allah kaɗai yasan tun lokacin da take atsaye tana sauraronsu,


Muryarta adisashe tace "Ki yafe mun angel, nayi kuskuran juya maki baya dana yi, bada son raina hakan ta faru ba, Na zauna nayi tunani duk irin ƙuntata maki da su haris su kayi dai dai da rana ɗaya baki fasa tashi tsakar dare Kinyi mana addu'a ba, saboda ƙaunar mu da kike Yi........" dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya, kafin taci gaba da cewa"Bana so kiyi kokwanto akaina angel, nasan abunda ya faru cikin ƴan kwanakin nan zaisa Kiji aranki kamar bana ƙaunarki ne, ko kusa angel, har yanzu kina nan yadda kike acikin zuciyata,'


Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, Matsawa batool tayi inda suke Ta janyo Angel ajikinta ta rungumeta sosai, Ta mika hannu ta ruƙo azeeza itama ta rungumota, atare suka cigaba da yin kukan,


Muryar Javed su ka ji yo daga bayansu


"Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki" raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba,


Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace"basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni' 


Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace"Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa,  sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan," yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta,


"Ku bani lokaci,  bi'iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA,"


Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana"Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake,"


Angel tace"Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,'


Atare suka haɗa baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu,


"Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa" ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba'a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba'a dawowa!!!!!


Ɗaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling, 


"Menene ma'anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ' lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai,


Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko'ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu,


"ƴar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane"? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta,


🥺🤣 Mu haɗu next page don jin yadda zata kaya, Idan Allah yakai mu da rai da lafiya, shin meyasa tsohuwa take Yi masu ƙarya ne? Meye manufarta akansu? Ya batun danish da har yanzu shiru ba'a dawo masu da shi ba, tsawon kwana biyar? Shin dagaske Gidan Kurkukun Ƙaddara Yana da Prisoners sama da mutun ɗari huɗu kamar yadda batool tace? Kuna tunanin Angel zata samu damar rotsa gilashin windon nan don taje yi masu lekan asiri? Tambayoyin suna da yawa sai dai mun nutsa Cikin labarin, har yanzu dai muna a takun farko, bamu je takun tsakiya ba balle kuma takun ƙarshe🤣*  


 Much luv My novel's fans, Allh yabar xumunci a tsakaninmu, Keep sharing my novel✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post