Kurkukun Ƙaddara page 24 complete

Kurkukun Ƙaddara page 24 complete

 

Kurkukun Ƙaddara page 24 complete

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


The prisoners🥺


DEDICATES TO AUNTY KUBRA


daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji✍️

  

E24


  Sai faman nishi yake yi, idanuwanshi suna arufe, long eye lashes ɗin shi duk sun jiƙe,

  calmly ta furta sunanshi"Danish are u ok"

  Jin muryar angel acikin kewayan yasa suka gane cewa tana a ciki, sunyi mamaki  yadda akai ta buɗe kopar, nan fa suka shiga kwala mata kira suna fadin ta bude masu ƙopa


  Ɗaga murya ta yi tare da ce Masu Bazata buɗe ƙofar ba, saboda sun ƙala mata sharrin cewa itace silar jefa shi cikin halin da yake Ciki, don haka idan har sunga ta buɗe masu ƙopa, danish ya samu sauƙi ne"


 Bugun ƙopar haris yake yi tamkar zai 6alleta" Bazaki zo ki buɗe mana ƙopar ba? a harzuƙe tace"Bazan buɗe ba,"

   Sassauta murya haris ya yi"pls angel  ki buɗe mana ƙopa, nasan bakya son danish kada kice zaki ƙarasa shi,"


  Girgiza kai ta ɗanyi cike da jin takaicin   maganar haris, 


   Tafin hannunta takai saman fuskar Danish ta shafa a hankali tare da ambaton sunanshi"Danish"


   Dogon numfashi taga yaja gami dasauke ajiyar zuciya, yana so ya buɗe idanuwanshi amma ya kasa, sai lumshewa eyes ɗin nashi suke, 


    "Danish pls try to open ur eyes,"


      Sama sama numfashinsa ke fita da hucin zafi, hannayenta ta sanya tare da tallabo kanshi ta ɗaura saman laps ɗinta,

   Shafa gefen fuskarshi taci gaba dayi, yayin da ta soma karanto addu'o'i acikin zuciyarta, tana ɗan tottofa mashi saman fuskarshi,


   Ba'a ɗauki tsawon lokaci ba, ya fara dawowa cikin hayyacin shi,


   Lokacin dare ya fara yi, su biyu acikin toilet, ya yin da su batool ke zazzaune bakin ƙopar shiga toilet ɗin, sun galabaita har sun gaji da bugun ƙopar suna yi mata magiya akan ta bude masu, suga a wani hali ɗan uwansu yake ciki, wasu har sun fara gyangyaɗin bacci,

    Itama angel ɗin baccin ta soma ji a cikin idanuwanta, 

  A lokacin da bata yi tsammani ba, taji ya ruƙo hannunta a cikin nashi sosai ya damƙe mata hannu, firgigit tayi tana kallon shi, 

   Lumshe idanuwanshi suke bai kaiga ƙarasa rufe su ba, He was calmly looking at her face without blinking his eyes,


   Furta sunanshi tayi"danish" muryar shi so cool ya ambaci sunanta "angel" for the first time da danish ya ta6a ambaton sunanta, 


  "Are u ok,"? Ta kuma tambayarshi, bai amsa mata ba, ƙoƙarin miƙewa zaune yayi amma jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai, da sauri ta taimaka mashi wurin tallabo shi ya miƙe zaune, tare da kwantar da kanshi saman kafadarta, still numfashin shi da huci yake fita, tana jin shi saman fatar wuyanta, saitin inda dogon hancin ya shafa,


 Sam bata ji komai ba, daya kwantar da kanshi saman kafadarta, sai taji tamkar ɗan uwanta ne na jini, ƙurawa sumar kanshi ido tayi, doguwa har saman bayan shi, kamar ta sanya hannu ta shafa sumar haka zuciyarta ke raya mata,


  'Pls angel open the door for us, mun ƙagara mu ga ɗan uwanmu," muryar hannah ce take yi mata magiya,

    Hannu tasa ta dafa kafaɗar shi"danish suna son ganin ka, mu koma ɗaki," kusan minti biyar da yin maganar, ya ɗan dago da kan shi, still jikin shi ba kwari kerma yake yi,


Rarrafawa tayi ta ruƙo rigarshi ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a  ya zurata ajikin shi, Sai da ta taimaka ma shi wurin ruƙo shi tukunna ya samu ya miƙe, a haka suka soma tafiya har suka ƙaraso bakin ƙofar ta buɗe ta fito da shi, gaba ɗaya suka miƙe tsaye zasu rungumo shi,


  Da sauri batool ta ware hannayenta wurin kare shi"Jikin shi ba ƙwari, danish yana buƙatar hutu," A jiyar zuciya kowa ya sauke, wuce wa angel ta yi Cikin ɗakin, Su Batool suka Bi bayan su,  ya rurruƙeta ji yake kamar zai faɗi ƙasa, wani irin jiri jiri yake gani a Cikin idanuwanshi, a saman gadonshi ta tsaya tare da taimaka mashi ya kwanta sama,


   "Sannu danish, Allah ya baka lafiya," batool ce ta yi maganar, su haris ma duk su kayi mashi ya jiki, sam ya kasa amsa masu amma duk yana jinsu,

   

  Sunyi tsaitsaye cirko ciko a gefen da gefen gadonshi, hasken ɗakin ya yi duhu, alamar dare yayi lokacin bacci ne, da sauri Javed yaje gaban table ya kunna masu sauran fitilun, ɗakin yayi haske ya ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ya ajiye ta daga gefen gadon Danish,


   Motsin buɗe ƙofa suka jiyo, da sauri kowannan su Ya juyo yana jiran ganin wanene zai 6ullo daga saman benan


  Biyu ne daga Cikin Giants dake kawo masu abinci, Abun mamaki ɗaya daga Cikin su hannun shi na ɗauke da wooden tray, samanshi an rufe da jan ƙyalle, da alama kayan abinci ne, ɗayan Giant ɗin kuma Syringe ne a hannun shi, already an zuba ruwan allurar a ciki,


  Me ruƙe da syringe ɗin ne ya yi masu nuni da hannunshi su matsa su basu wuri, da sauri suka ja baya, me ruƙe da tray ɗin ya sauke shi ƙasa gefen gadon danish, Kafin ya matsa zuwa saman gadon, wata irin zabura danish ya yi, ya daddafe kanshi yana faɗin baya so kada su matso kusa da shi, ya dinga ambaton sunayen su haris yana faɗin ba zasu taimake shi ba? Suna ganin za'a cutar da shi,


  Tsananin tsauyin shi ne ya kama su batool, idanuwan kowannan su ya ciko tab da kwalla, 


  Ruƙe shi sosai Giant ɗin ya yi, shi kuma ɗayan Ya daddage ya caka mashi allurar a wuyanshi, nan take jikin shi ya saki, ya sulale saman katifar idanuwanshi a rufe,


  Sakin shi su ka yi, a tare suka juya cikin takun nan nasu, suka fuce daga cikin ɗakin,

 

  Fitar su keda wuya Su hannah suka yi mashi rumfa suna ambaton Sunanshi, danish danish


  Haris yace subar shi ya huta zai ji sauƙi tunda anyi mashi allura,


  Angel tace"Wai kun yadda allurar magani ce su kayi ma shi? Meyasa danish yake kuka yana faɗin bayaso sai kace ƙaramin yaro? Kuma har yana faɗin mu taimake shi, u ave to think about it, ni sam ban yarda da waɗannam mutanan ba, Allah kaɗai yasan me su kayi ma shi"


  Yatsina fuska deeja tayi cike da jin haushin angel ta soma magana"babu abunda su ka yi ma shi, tun da muke dasu basu ta6a cutar da wani daga cikin mu, koma meye kece kike da alhakin ciwon da.......' Bata kai ƙarshen maganarta ba, sakamakon naushin da angel ta sakar mata a saman fuskarta, tsabar raɗadi yasa Deeja ta dafe kuncinta,


    "Ni kika buga"? Harara angel ta jefa mata"kaɗan kika gani, in har kika ci gaba da faɗin cewa ni ce silar da danish yake a wannan halin saina zubar maki da haƙoran gaba, wawuya kawai, don kinga kwanakin nan nayi sanyi shiyasa har kika samu damar gaya mun magana" 


    Ganin sun harzuƙa yasa javed yin saurin shiga tsakaninsu, cikin sanyin mirya yace" kodan saboda danish, kuyi haƙuri kuyi shiru," jinjina kai deeja ta yi"na ƙyale ki a yanzu, amma wlh saina rama naushin da ki kayi mun" Tsoki angel taja"duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake, mai rabon shan duka,"


     Daga haka su ka yi shiru, Can Haris ya hango parveen zuƙunne gaban Kayan abincin da aka kawo, sai faman shinshina su take yi, hannu yakai tare da ruƙo wuyan rigarta, ya ɗago da ita tsaye ta maƙe wuya 


  "Abincin Mara lafiya ne, Kada ma mutun ya sanya rai," harara parveen ta ɗan jafe mashi"Amma ae muna jin yunwa sosai, wannan dama ce a gare mu, kuzo kawai mu zauna muci mu ƙoshi, in yaso sai mu rage mashi kaɗan, bama lallai ya iya cin abincin ba"


  Wani kallo Hannah tayi mata" ke fa dama indai kan abinci ne, Ba imani kika cika ba, Kinsan dai sau ɗaya ake kawo mana abinci, wannan kuma da kika ga an kawo na danish ne, ina ma laifin kice idan yaci ya ƙoshi ya rage sai muci kingin"?


  Murmushin yaƙe parveen ta saki"Ae naga bacci yake yi, zamuyi ta jiran shi ne har saiya farka yaci ya rage tukunna muci"? ta yi tambayar tana ƙyafƙyafta ido, yadda tayi ba ƙaramin dariya ya  basu ba,


  Mubeen yace"Ni kaina yunwa nake ji, Don ba yadda zanyi ne Allah," yana rufe baki naufal yace"ae ba kai kaɗai ba, ina ɗazu ɗinnan da muka dinga bugun ƙopa, to anan duka abincin da muka ci ya zube,"


  Murmushi haris ya ɗan saki tare da cewa"duk bala'in ku dai bazaku ta6a abincin ɗan uwana ba, har saiya ci ya rage" dariya su kayi gaba ɗayansu, da alama suna farin cikin dawowar ɗan uwansu,


  Dare fa ya yi sosai, yakamata kowa yaje ya kwanta, acewar yasmin, juyawa su kayi kowa ya nufi gadonshi, Banda mutun ɗaya Parveen ta yi tsaye agaban gadon danish 


  Dawowa Haris ya yi tare da kai hannu ya ruƙo wuyan rigarta" muje ki kwanta" bubbuga ƙafa ta yi tare da cewa"Mara lafiya ne fa shi, taya zamu barshi shi kaɗai, Ni inaso Inyi jinyarshi ne",


  "Saboda shi kaɗai ne a ɗakin ko"? Ya yi tambayar yana kallonta, shiru tayi tana faman tur6une fuska,


  "Oya muje ki kwanta, sarkin wayau" ya ambaci hakan tare da janta, sai da yakai ta har saman gadonta, tukunna shima ya wuce nashi gadon ya kwanta, 


  Gaba ɗaya sun kasa runtsawa, bakomai suke jira ba, face farfaɗowar Danish, 


  "Kinyi bacci"? Muryar haris ce, yana daga kwance yayi maganar yana kallon Parveen dake a kwance saman gadon ta dake a kusa da nashi 

  "Taya zan iya bacci da ƙamshin abinci a hanci na," dariya haris yayi,


 "Amma Haris baka ganin abincin zai iya lalace wa, tunda shi danish ba'asan lokacin da zai farka ba,"


  "Calm down ur mind, tun da ki ka ga sun ajiye abincin nan, sunsan zai farka ne, Giants ne fa Sunsan me suke yi," sun jima suna tattaunawa, da haris before bacci yayi awon gaba da parveen,


  Tsakiyar dare lokacin rabi da kwatarsu sunyi bacci, banda mutun ukun, Angel data ɗaurawa kanta alhakin ciwon danish, sai kuma Haris da yake na hannun damarshi, bayan su sai Batool, kowannansu yana kwance sunyi likimo tamkar masu yin bacci, 


Ashe zuƙunne bata ƙare ba Kamar daga sama su ka ji danish ya fasa gigitacciyar ƙara mai matuƙar firgitarwa, farfaɗowarshi kenan, ya ta shi da wani sabon Ciwon, a matuƙar gigice angel ta yaye bargonta haris da batool duk suka cire bargunansu, hatta masu bacci sai da suka farka sakamakon Ƙarar danish data karaɗe Cikin ɗakin,


 Gaba ɗaya hankalin su yae matuƙar tashi, ganin Danish Zaune saman gadonshi sai ƙara yake saki, ya daddafe kanshi da dukkan hannayenshi, tamkar wanda ake cikin zare ranshi saboda tsabar yarda yake fitar da sautin ƙarar har wani jijjiga muscles ɗin Jikin shi ke yi,


  Durowa su ka yi daga saman gadajensu, jikinsu har kerma yake yi wurin tunkarar shi, Haris ne ya hau saman gadon, Javed da Mubeen hada naufal da sauran Ƴan matan duk Suna a tsaitsaye fuskokinsu da alamun ruɗu,


  "Danish meya faru? meke damunka? dan Allah kayi mana bayani, " magana suke yi mashi amma sam baya sauraronsu ihu kawai yake yi, shi kaɗai yasan Raɗaɗin da yake ji bawan Allah,


  "Bari naje na kira tsohuwa" Acewar Batool, juyawa ta yi da niyar taje ƙopar ɗakin tsohuwa, Angel tayi wuff ta ruƙo hannunta, tsayawa tayi tare da waigo wa ta kalli hannun angel da ta ruƙe ta, suka haɗa ido da juna"Ki jira akwai abunda nake so, in jaraba yi mashi idan bai ji sauƙi ba sai kije ki faɗa mata,". Rai a6ace haris yace"don me zaki hana ta zuwa ta kira ta? So kike mu rasa ɗan uwanmu? Baki ga halin da yake Ciki bane? Yana rufe baki Deeja tace"Da alama so take ta ƙarasa kashe shi, dama ni ban yarda da ita ba, ko me take da shi da zata iya taimakon shi? 


 angel bata tsaya sauraronsu ba. Kota kansu bata bi ba, batool ta kuma kallo tare da cewa"Ku bani dama," jinjina kai batool ta yi tare da kallon su haris tace"Tun da ta nemi alfarma, mu barta ta jaraba, amma kuma komai ya biyo baya, ke kija tun da kin hana a kira tsohuwa" gyaɗa kai angel ta yi, tare da matsawa ta haye saman gadon danish, ya kakkame Jikinshi sai kerma yake yi, yana sakin ihu ga zufa duk ta wanke jikin shi, duk da weather ɗin prison mai sanyi ce,


  Miƙa hannu ta yi da niyar ta ruƙo shi, Ya buge hannun nata alamar baiso, duk yabi ya birkice masu,


  Ganin yaƙi bata damar ruƙe shi yasa haris jan dogon tsoki tare da cewa"U just wanna waste our time, pls batool go and call her" tafiya batool ta soma yi ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,


  Rufe ido angel tayi, Cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa da cikar kamala, ta soma raira qira'ar karatun alqur'ani mai girma, 


 Gaba ɗaya suka bita da kallo, sam basu san me take karantawa ba, amma tunda suke basu ta6a jin sautin abu mai daɗi ba, irin wanda angel take Rairawa ba, hatta batool dake ƙokarin kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa, tana fara jiyo sautin karatun da angel keyi nan take ta dakata, tamkar an dasa mata aya, da matuƙar mamaki ta juyo tana kallon inda suke.


  Bakomai yafi ɗaure masu kai ba, Fa ce yadda danish ya yi shiru, yadaina ihun da yake yi, kuma jikin shi ya daina yin kerma, 


 A hankali angel ta buɗe idanuwanta, ta ɗaurasu akan fuskar Danish still bai buɗe idanuwanshi ba, matasawa ta ƙarayi kusa dashi sosai, ta sanya hannayenta biyu tare da ruƙo doguwar sumar kanshi, ta tattare ta zuwa bayanshi, moving lips ɗinta ta yi xuwa saitin kunnanshi na dama, sosai taci gaba da raira mashi karatun har cikin kanshi yake jin wani irin baƙon yanayi mara misaltuwa, zuciyarshi tayi sanyi, kasala ta baibaye shi,

,

 Haƙiƙa Angel tabar ƴan kallo, Su haris sun saki baki kamar lehen sakarai sai kallonta suke yi, ta kawo masu wani baƙon abu da basu ta6a ji ba,


 He slowly wrapped his arms around her waist and squeezed her tightly tamkar zai shige cikinta, sai faman nishi yake yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri, tana jin zafin jikin shi sosai ajikin nata, saboda matsewar da suka yi ajikin juna, tana jin yadda heart ɗinsa ke beating very fast, ƙasa ƙasa da murya yake furta mata, kada tadaina, taci gaba yi mashi yana samun sauƙi," kamar yadda ya buƙata haka taci gaba dayi mashi karatun, har sai da taji tempreture ɗin jikin shi ya dawo normal, numfashinsa da natsuwarshi sun daidaita tukunna ta dakata da yi mashi karatun acikin kunnuwanshi, zame jikinta ta yi daga nashi, tare da sanya hannayenta ta dafa shoulders ɗinshi, eyes ɗinta na kallon Fuskarshi, idanuwanshi tamkar na mashayin giya,


  "Danish can u see my face" tayi maganar tana nuna mashi fuskarta, jinjina mata kai yayi alamar eh, ɗagowa ta yi tare da kallon su Haris dake a tsaitaye, Yadda kasan ƙerarrun gumaka, tsabar mamaki yasa sun kasa rufe bakunansu, Kowa zuciyarshi acike take fal da tunanin menene angel ta karantawa ɗan uwansu danish harya dawo cikin hayyacin shi,


  "Angel kinyi matuƙar bamu mamaki" batool ce tayi maganar a lokacin ta dawo inda suke.


  "Duk da bamusan menene kika karanta ma danish a kunnanshi ba, amma nayi matuƙar jin wani irin sanyi da daɗi acikin zuciyata, sai naji dama baki daina ba, kin cigaba da yi," 


  Batool nakai ƙarshen maganarta, Javed yace"Nikaina naji wani irin daɗi mara misaltuwa, nayi mamaki kuma ganin yadda danish ya samu natsuwa yadaina haukan da yake yi," yakai ƙarshen maganar idonshi akan danish,


  Hanna tace"i  feel the same, zanso nasan menene angel kika karanta mashi me daɗi," tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,


  "Zanyi maku bayani, amma yanzu danish yana buƙatar kulawarmu," tayi maganar tana kallonsu, 


 Haris dai yayi shiru shi da deeja kowa na tofa albarkacin bakinsa kan irin dadin da suka ji amma banda su, saboda tsabar kunyar da suka ji, 


  "Ga abincinsa kar ya lalace, aba shi yaci" parveen ce tayi maganar,  tare da rankwafawa ta ɗauko tray din ta miƙa ma Angel, hannu biyu angel tasa ta ruƙe handle ɗin tray ɗin a tsakiyarsu ta sanya tray din, ta cire jan ƙyallen, waro ido parveen tayi ganin Roasted Chicken guda ɗaya sai maiƙo take yi ga wani irin ƙamshi, gefe kuma Milk ce a cikin bottle me sanyi, sai wooden bowl mai ɗauke da Fruits salad,' 


"Zaka iya ci"? Ta yi tambayar tana kallon danish, wata irin narkakkiyar zufa ta gani tana gangarowa ta cikin yalwatacciyar suman kanshi, bai iya bata amsa ba, sai dai kallon ta da yake yi,


Sai lokacin harisun tsohuwa ya samu damar buɗe baki yace"Bari na taimaka ma shi ya watsa ruwa ajikin shi," yakai ƙarshen maganar, Tare da ruƙo danish, Javed ya taimaka shi suka yi mashi jagora zuwa Cikin toilet ɗinsu, 


Bayan tafiyarsu batool ta kalli sauran ƴan uwan nasu"tun da jikin nashi da sauƙi, ku je ku kwanta," Yadda kasan ƴan gudun hijra haka suka tafi sharaf sharaf kowa Ya hau saman gadonshi Ya kwanta,


Ganin parveen taƙi tafiya yasa tace"ke fa" Hannu tasa tana ɗan sosa keyarta "Jira nake Su haris su dawo da danish yaci abincin shi, idan ya rage nima in samu in ɗan ci....." wani kallon rainin wayau batool tayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar,


  "Sai kace kinfi kowa Jin yunwa, Allah yasa idan ya fito ya cinye abincin duka sai muga ya za ki yi" angel dake zaune saman gadon danish ta yi zurfi Cikin tunaninta, bakomai ya ɗaure mata kai ba, face yadda ta iya yin karatun qur'ani tiryan tiryan tun zuwanta gidan kurkukun tasha Yin attempting karatun qur'ani tana gazawa, sai ta dinga jin raɗaɗi a maƙoshinta, A yau dai kamar umarni aka bata tayi karatun haka tadinga ji, Kuma taji kwarin guiwar yin qira'ar, kenan nan gaba zata Iya samun damar yin ibada, mamaki take yi ya akai take samun nasara akan wasu abubuwan? Tabbas Allah yana atare da ita saboda kyakkyawar niyar dake gareta, kuma tana ji aranta cewa Akwai masu yi mata addu'a, fatanta Allah yasa dadynta idan yana araye ya kasance ɗaya daga Cikin masu Yi mata addu'a, Saboda ita addu'ar Iyaye kar6a66iyace akan ƴa'ƴansu kamar yadda hadisa ya tabbatar da hakan, 

  

Shigowarsu haris  Cikin ɗakin ne ya katse mata zancen zucin nata, ta ɗago tana kallonsu, Hannayensu ruƙe dana danish, jikin shi duk lemar ruwa, Hada sumar kanshi suka wanke mashi, duk ta manne mashi saman fatar wuyanshi, Lokacin da suka ƙaraso, Saman gadon ya haye ya ɗan kishingiɗa kan shi saman pillow, jikin shi duk ya saki babu ƙwari, idanuwanshi na a lumshe,


"Abincin fa"? Angel ce tayi ma shi maganar, slowly ya dan buɗe idonshi akan fuskarta, in a throaty voice ya furta mata"I can't eat anything now, u can share it," voice ɗinshi yayi low sosai, daƙyar ta iya jin me yake cewa,'

 

Cikin rashin jin ɗaɗin maganar shi haris yace"Ko madarar ce ka ɗaure ka sha, nasan kana jin yunwa," girgiza ma shi kai ya yi"bazan iya ba, kada ku damu kanku am ok,"


Babu wanda yaji daɗi Acikinsu, Sun so koda milk ɗin ce yasha, amma ya nuna masu cewa babu yunwa attare dashi, Su parveen abun nema ya samu, zama su kayi a kasa Kowa Ya shiga kai hannu yana yagar naman kazar yana Ci, Komai saida suka Bi suka lamushe, bayan sun kammala, Haris Ya zauna gefen gadon Danish, sauran suka wuce saman beds ɗinsu suka kwanta, Angel ma tuni ta koma nata gadon, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, danish ya dawo Cikin su, sai da dare ya nutsa, tukunna haris yabar gefen gadon danish ya koma nashi gadon ya kwanta, 


Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan ta juya ta saci kallon shimfiɗarshi, yayi bacci ko baiyi bacci ba?, kasa jurewa tayi a hankali ta dan mirgina ta juya ta 6angaren da yake fuskanta, bayan shi kaɗai take iya gani, jikinshi na lulu6e da bargon da haris ya rufa mashi har zuwa kafaɗarshi,


tana kokari rufe idanuwanta, taga yana mutsu mutsu, ƙoƙarin juyowa ya yi, da sauri ta rufe idanuwanta, don kar ya gane shi take kallo, natsuwa ya yi a yayin da yake kallonta, zuciyarshi cike fal da mamakin canza mashi da tayi, yafi tunanin taji tausayin shi ne saboda halin daya shiga, wata zuciyar kuma tana saƙa mashi cewa kada ka yarda da ita, so take ka saki jiki da ita, ta samu damar kashe ka cikin sauƙi, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin sanyi yaji ba, tun da ta karanta mashi wannan abun da baisan menene ba, Sai yaji duk duniya babu abunda yake kwaɗayin ya kasance yana sauraro acikin kunnanshi idan ba shi ba,


Tunani tayi ko yayi bacci yanzu, tana mutsu mutsun buɗe idanuwanta, yayi saurin rufe nashi eyes, shima baiso ta gane cewa Ita yake Kallo, ta jima tana kallon shi, da zarar taga xai buɗe ido sai ta rufe nata idon, shima haka idon yaga zata buɗe idonta sai yayi saurin rufe nashi, Sai da suka raba da dare suna wannan wasan, Kafin Allah ya kawo bacci 6arawo yayi awon gaba dasu,


*ANEELERH*


A tsaye Take saman darduma ta kabbara sallah, Jikinta sanye da dogon Hijabi maroon colour har ƙasa ta sauko, tana ƙoƙarin yin sujjada Taji mutun saman bayanta Ya haye, Kasa ɗagowa tayi saboda gudun kada ya faɗo tasan bai wuci junaid bane, ba yau ya saba yi mata haka ba, a bedroom ɗin Mami ya kwana, har yasan ya tako daga ɗakin mami zuwa ɗakinta, a duk inda ya kwanta bacci ya ɗauke shi ko mun tsakiyar dare ne idan ya farka sai ya nemota duk inda ta shiga, Yadda kasan malamin duba, 


Bubbuga bayanta taji yana yi tare da ambaton "Doki sukuta sukuta, doki sukuta sukuta!, yana magana yana sukuwa hada cewa Mommy, Ki tashi mu tafi yawo,' a hankali ta miƙa hannu ta ruƙo shi tare da janye shi daga saman bayanta, Ya faɗo daga gefe saman dardumar, bubbuga ƙafafunshi ya shiga yi, yana raira mata kuka, daurewa kawai take yi sam bata so taji yaron yana kuka, Tsananin tausayin shi taje ji,  


Hannu ya miƙa ya ruko cazbaharta dake ajiye saman darduman, Ya miƙe zaune ya zura cazbahar saman wuyanshi, Allah Allah take ta kammala sallar kafin yayi tunanin ɗaukar qur'aninta da ta ajiye wurin daya ɗauki cazbahar, kura mata ido yayi jin taƙi tanka mashi ashagwa6e yake kiran sunanta"mommy! Ni ki tashi muyi wasan doki" yayi maganar da hausarshi da bata ƙarasa nuna ba, ya hanata sakat, daƙyar ta samu ta kammala yin sallar ta zauna zaman tahiya, Ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, Yana cigaba da yi mata shagwa6a, bayan sallame sallar ne ta samu damar kallon shi,


"Bansan meyasa kake yi mini haka ba junaid why? Bakaga sallah nake yi ba, bana hanaka in ina sallah kana hawar min bayana ba"? Wani kallo taga yana binta dashi, kamar wani mai hankali, a yanzu fa shekararshi biyu da rabi, 


Sai daga baya ma ta lura da rigar dake ajikinshi, Singlet ce ta abie ya sanya, ta yi mashi yawa har ƙasan ƙafafun shi takai, cike da mamaki tace"kai! Waya sanya maka rigar abie"? Fuskarshi a tur6une yace"Ni na ta" hararar shi tayi"you're lying, ina kaga wayan da zaka iya ɗauko rigarshi ka sanya? tayi maganar tare da kai hannu tana jan kumatun shi,


"Faɗa mun gaskiya My baby boy, ko mamie ce ta sanya maka ita"? Girgiza mata kai yayi"kintan Allah wlh ni nata, in na miki ƙarya Allah ya ƙona......" bata bari yakai ƙarshen maganr ba, ta ɗan hambare bakinshi" Bana haka irin wannan rantsuwar ba?ba'ajin magana ta ko"? ashagwa6e yace"Ae ae nima musha naji yana yi," tsoki taja, shiyasa batason Junaid Yana zuwa wurin shi, duk a wurin shi yake koyan wannan rantse rantsen marasa kan gado, dole sai ta ja mashi kunne, Ya daina Yi agaban ɗanta, tun da yaron wayau ne dashi komai ɗauka yake yi acikin kanshi,


"Kadaina kaji babu kyau," amsa mata yae"Toh, in na daina zaki kai ni wurin Angela"? Murmushi tasaki tare da cewa"Da alama kana son ƴar uwar nan taka junaid, sai dai bansan ya za'ae in kaika wurinta ba, Nima nemanta nake yi...." cikin sanyin murya takai ƙarshen maganar, duk inta tuna su sai taji zuciyarta ta karaya, Almost 4 years kenan babu su babu labarinsu, '


Ɗaukar Junaid ta yi a hannunta ta miƙe ta ɗaura shi saman gadonsu, tana fadin"ka koma bacci dan Allah my baby boy, bana so kayi ta 6arna pls," amsa mata yayi"to" ya lumshe idanuwanshi alamar bacci zaiyi, ƙura mashi ido tayi tana kallonshi batare da ƙyaftawa ba,


Shafa fuskarshi tayi da hannunta, kafin ta zauna daga gefen gadon, takai hannu ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,


Gallery ta shiga, ta lalubo tsoffin hotunansu tana kallo, Wani hoto ta buɗo wanda suka yi su uku, Ranar graduation ɗinsu akayi masu hoton a University of Hagen, dake a ƙasar germany, su uku su kayi hoton kowannasu yana asanye Cikin Graduation gown sunyi matuƙar yin kyau, Allah yayi halitta ta farko Aneelerh ce, A tsakiyarsu Benazir ce kyakkyawar balarabiya, Ta ƙarshe kuma wata aminiyarsu ce masha Allah, Matar akwai diri kamar ita ta ƙera kanta, kowacce da irin baiwar kyan da Allah yayi masu, sai dai kash gaba ɗayansu a halin yanzu ƙaddarar rayuwa tayi silar tarwatsewarsu, 


A tsanake take kallon hotunan nasu, tayi matuƙar yin kewar aminnanta, bazata ta6a manta irin shaƙuwar da su kayi da juna ba, runtse idanuwanta tayi tana tuna wasu maganganun da suka jima suna yi mata yawo acikin kanta, ɗaya daga Cikin aminnan nata ne ta furta su a cikin text message da ta ta6a tura mata lokacin da take Cikin tashin hankali tace"Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya  zansha poison ne in mutu........" 


Sosai aneelerh ta fashe da kuka, lokacin da ta kammala tariyo abunda ya faru, A fili tace"Allah sarki Aisha! Bansan A ina zan ƙara ganinta ba, Allah ya kare ki aduk inda kike, ni shaida ce akanki, Ke mutuniyar kirkice, bana fata, ƙaddarar rayuwa tayi silar canzaki daga yadda nasanki, ' 


Cikin shessheƙar kuka aneelerh tace"Narasa Aisha saboda korar karan da mahaifinta yayi mata, na kuma zo narasa Benazir, duk da ita don san ranta ta gudu, daga baya kuma Narasa Mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata, " jefar da wayarta tayi saman mattress, Ta kifa kanta Jikin pillow, junaid tuni ya jima da komawa bacci, 


( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post