Kurkukun Ƙaddara page 26 complete

Kurkukun Ƙaddara page 26 complete

 

Kurkukun Ƙaddara 26

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dedicated To aunty kubra❤


E26


Prisoner's luv story


Muryar angel adisashe tace"Batool! Yau keda kanki kike Yi mini tsawa! Saboda kawai ina son ƙwato maku haƙƙinku da aka tauye....." kafin takai ƙarshen maganarta, Javed ya dakatar da angel ta hanyar ɗaga mata hannunshi"Is enough! Kawai kiyi mana shiru, Kina so ne, Ki shiga tsakaninmu da ita, babu ruwanki da rayuwarmu, Ki barmu a yadda kika ganmu, haka muka saba rayuwa, bin dokar kurkuku wajibi ne agare mu prisoners" wani irin shu'umin murmushi tsohuwa ta shiga saki Nan da nan walwalar fuskarta ta dawo Jin yadda Suke Goyan bayanta, ashe har yanzu Hayaƙin sihirinta na aiki yadda ya dace, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,


Tuni idanuwan angel sun Ciko tab da kwalla, tsabar baƙin Ciki Ya hana ta ƙara cewa komai, Juyawa tayi a fusace ta koma saman gadonta, Ta zauna tare da ruƙo pillow ta rungume a kirjinta,


Kallonsu tsohuwa tayi da alamun farin Ciki akan fuskarta tace"Ku cigaba da yi mun biyayya ƴa'ƴana, albarka zata tabbata akanku, " muryar parveen a ƙule tace"Abincin fa"?


Tsohuwa ta bata amsa da cewa"Ku jira ni, Ina zuwa" ta ambaci hakan tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta, baka iya hangen komai ko ka leƙa sai duhu, 


Badajimawa, Sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya a ruƙe da Kwandon kayan marmari,  Miƙa ma Su tayi" Ku je kusha, Kafin zuwa gobe zaku samu abinci" Hannunsu har kerma yake yi wurin kar6ar Kwandon daga hannunta,' Juyawa tayi tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, tare da jan kopa ta datse,


Ita dai angel sam bata yarda da kayan marmarin da tsohuwa ta basu ba, Cike fa da kwando, manyan apples ne tare da damin ayaba," a kalla kowa zai samu apples uku, da Ayaba Uku, Batool ce ta rarraba masu kayan marmarin kowa ya kar6a yana sha, koda ta miƙa ma angel hannu tasa takar6a amma bata sha ba, A ƙarƙashin pillow ɗinta ta 6oye su, tana jira taga idan sun kammala sha batare da wani abu ya faru dasu ba, itama sai tasha, Har batool sai da tayi mata magana akan bazata sha ba, tace mata ba yanzu zata sha ba, Sai zuwa anjima,


Tun da suka kammala Cin apples ɗinnan da ayaba, wani irin matsiyacin bacci ne yazo masu, lamarin ya ɗaurewa angel kai, Ganin su kwakkwance A ƙasa suna bacci, kamar waɗanda suka Sha kayan maye, Juyawa tayi da sauri tana kallon gadon danish, cike da fargabar kada ace shima baccin ya ɗauke shi, idonshi biyu ta same shi, ya kwantar da kanshi saman pillow, babu alamun bacci attare dashi, Su biyu suka rage idonsu biyu,


Tabbas tafara zargin Kayan marmarin da tsohuwa ta basu ne ya sanya su yin bacci, da yake ita da danish basu sha ba, shiyasa bacci bai ɗauke su ba, ko meyasa tayi masu haka? Kodan kada su ji yunwa ne"?


"Meyasa ba zaka sha ba"? Tayi tambayar tana kallon danish, ganin ya ajiye nashi apples ɗin a gefenshi,


Cikin sanyin murya ya amsa mata da cewa"bana ra'ayi, zuwa anjima xansha" ya ƙarasa maganar, tare da miƙewa zaune, ya zuro da dogayen ƙafafuwanshi ƙasan gadon kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye, Har yanzu jikin nashi babu ƙwari, shiyasa tun ɗazu ya gaza saukowa daga saman gadon,


Daƙyar yake ɗaga ƙafar yana tafiya, Ji take kamar taje ta taimaka mashi sai dai batasan tana kusanta kanta dashi,


Tafiya yake yi yana waiwayon su Haris dake baje a ƙasa suna sharar bacci, sam bai kawo komai aranshi ba, Shigewa Ƙopar toilet ɗinsu yayi, Sai da ya 6ace ma ganinta tukunna ta ɗauke idonta daga kanshi, Cike da fargabar kada ya raunata kanshi, tun da ba ƙoshin lafiya gare shi ba,


Tsawon lokaci da shigarshi cikin toilet ɗin,  ta Lumshe idanuwanta tare da kishingiɗawa, da niyar ta ɗan runtsa itama, Takun tafiyar mutun tajiyo acikin kunnata, tana buɗe ido ta fasa wata irin gigitaciyar ƙara tare da sanya hannu ta rufe idanuwanta, Jikinta na kerma, A matuƙar ruɗe Ya koma Cikin 6angaren toilet ɗin nasu, Ya la6e abakin ƙopa yana leƙen ta,


Abunda ya faru Lokacin data buɗe ido, Karaf idanuwanta suka sauka akan Surar danish, Ya fito naked babu sutura ajikinshi, Wannan ne yasa tayi matuƙar firgita, Jikinta ya hau kerma, dole ta ruɗe saboda halittar dake gare shi, Dogone sosai komai Na jikinshi ba ƙarami bane, shi kuma tsawar da tayi ne yasa shi gigicewa ya juya aruɗe ya koma sashen toilet ɗin, Yana leƙenta,


Ƙanƙame jikinta tayi ta gaza motsawa, tayi matuƙar tsorata, ranta ya 6aci sosai batare data buɗe idanuwanta ba, taci gaba da surfa mashi masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai da ta gaji da zazzaga mashi masifa tukunna ta yi shiru tana faman huci har lokacin bata buɗe idanuwanta ba,


 Jin yayi shiru bai ce mata komai ba, yasa ta sassauta muryarta tare da cewa"Go back, I don't wanna see you naked, if you need something, you should ask me to give it to you"


a ƙule tayi maganar, don ba ƙaramin haushin sa taji ba, ƙato da shi zai fito babu kaya ajikinshi, yanzu da ace idonsu Batool biyu ba bacci suke yi ba, duk haka zasu ganshi, tarasa gane wani irin mutunne shi, duk da tana yi mashi uziri na halin da yake Ciki na rashin lafiyar da take tunanin ɗaura mashi ita akayi, shiyasa ya zama wani sauna dashi,


Kasa kunne tayi sosai don ta samu damar jin me yake ce mata, magana yake yi mata akan ta miƙo mashi bargonshi, yana so zai lullu6e jikinshi,


Sai lokacin ta fahimci cewa, Ya wanke kayanshi, dama haka suke Yi idan suka wanke kayansu, sai su sanya bargo su lullu6e jikinsu, maimakon tunkafin ya shiga cikin toilet ɗin ya tafi da bargon shine bai tsaya ya ɗauka ba, yanzu gashi yasata kallon haramun, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,


"wait, I will hand it to you ka koma toilet" amsa mata yayi da toh, bayan wasu daƙiƙai, ta ɗan zame tafin hannunta daga kan fuskarta, ta saci kallon Hanyar toilet ɗin, Ganin babu shi yasa ta yi saurin saukowa daga saman gadonta, takai hannu saman nashi gadon ta ɗauko bargonshi, Ta nufi bakin door ɗin farko ta tsaya tare da ɗaga murya tace"Ga bargon" zuro mata da hannun shi yayi, maimakon ta miƙa mashi bargon saita tsaya tana kallon kyawawan yatsun hannunshi, sai kace bana ɗan bil'adama ba, saboda tsabar kyau, matsalarsu ɗaya basu yanke akaifa, yadda kasan hannun shaiɗanu, Ƙumba zaƙo zaƙo, 


  "Bring me am waiting" figigit tayi jin muryarshi, harya gaji da miƙa hannu, da sauri ta damƙa mashi bargon, ya kar6a,


Abakin ƙofar ta tsaya tana jiran ya kammala sanya bargon ya fito itama ta samu ta shiga wankan, 


Tana Cikin tsawuwar nan, Taji takun tafiyarshi, bin ƙopar tayi da kallo, Fitowa yayi, Jikinshi ɗaure da bargon daya sanya, har zuwa chest ɗinshi,


Bata bari sun haɗa ido ba, Ya wuce ya nufi gefen gadonshi Ya zauna,  tare da jingina bayanshi a jikin bango,


Tunani tayi kodai itama ta wanke kayanta ne ? Domin kuwa tajima bata wanke su ba, har tsami suke Yi mata, 


Komawa tayi ta dauko bargonta dake yashe saman gadonta, da sauri ta nufi toilet ta shige, tsawon lokaci tana aciki, sai da ta kammala wanke kayan ta ta shanyasu, bayan tayi wanka ta ɗaura bargon a ƙirjinta, A bakin ƙofar fitowa daga sashen makewayin nasu ta la6e tana satar kallon danish, Sam bata so ya ganta in zata wuce, 


Ganin ya lumshe idanuwanshi ne, yasa ta yi tunanin yin sauri ta wuce, Cikin sanɗa take tafiya, har ta samu takai bakin gadonta ta haye ta kwanta, yinin ranar su biyu suka yi shi, ita da danish, lokacin da kayansu suka bushe ita taje ta dauko masu uniform ɗinsu, ganin ya fara bacci yasa tayi saurin warware bargon dake ajikinta, ta xura uniform ɗinta, sai daga bisani taje bakin gadon danish ta tada shi daga bacci, ta miƙa mashi nashi unifom ɗin yasa hannu ya kar6a,


Ta juya ta koma gadonta, ta zauna daga gefe, idonta akansu batool dake ta sharar bacci, koda taga yana kokarin zame bargonsa don ya zura kayanshi da sauri ta kifa kanta saman pillow, ba ita ta ɗago ba har saida ya kammala sanya kayan ajikin shi, tukunna ta ɗago da kanta,


Abu kamar wasa har dare yayi su batool basu farka daga bacci ba, Hankalin angel yaƙi kwanciya shi kanshi danish jikin shi duk yayi sanyi, har sauko yayi daga saman gadonshi yaje ya duƙa agabansu yana tatta6a su, wannan wani irin dogon bacci ne da mutun zai kwashe yini guda tun safe har dare? Anya kuwa tsohuwa abunda tayi ta kyauta masu? Sai kace wasu matattu, 


"Danish Ko dai inzo in kama maka, Mu mayar dasu saman beds ɗinsu? Ta yi tambayar tana kallon danish dake zuƙunne agaban Haris dake ta bacci, batare daya juyo ya kalle ta ba, yace  mata eh, saukowa tayi daga saman gadon ta ƙarasa inda danish yake, yasa hannu ya ruƙe ƙafafuwan Haris ita kuma ta ruƙe hannayenshi Suka ɗaga shi zuwa saman gadonshi suka kwantar da shi, Haka suka bi kowannansu ɗaya bayan ɗaya suka ɗauko shi daga ƙasa suka mayar dashi saman gadonshi, suna ajiye batool saman gadonta, gaba ɗaya hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya mamaye idanuwansu, basa iya ganin juna, 


"Bari naje na kunna fitilun ɗakin, kada ka motsa" ta faɗa mashi hakanne don tasa halin shi da ruɗu, yanzu ya rikice mata, tafiya take yi cikin ɗakin tana laluban hanya har Allah yasa taci karo da table ɗin da fitilun suke, takai hannu ta kukkuna su, ɗakin yayi haske sosai, ta ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ta juyo tana hasko inda danish yake a tsaye, Ya goya hannayenshi saman chest ɗinshi ya ɗan jingina bayanshi jikin bango, tunkararshi tayi adai dai inda yake ta tsaya, Da sauri ya rufe idanuwanshi saboda hasken fitilar dake a hannunta, ba ƙaramin cika mashi ido yayi ba, ganin haka yasa ta kawar da fitilar gefe, 

"Muje mu kwanta ko"? tayi tambayar tana kallonshi, babu musu ya amsa mata da toh, juyawa tayi gaba ta wuce nata gadon shima Ya wuce gadonshi, a  tsakankanin beds ɗinsu ta ajiye fitilar, kusan atare suka haura saman gadonsu suka kwanta suna fuskantar juna, ya tsareta da sexy eyes ɗinshi yana kallonta without blinking, ganin kallon yayi yawane yasa tace"ba zaka yi bacci ba"? Wit low voice ya amsa mata da cewa"bana jin bacci," yatsina fuska tayi sam ba haka taso ba,  saboda ta shirya yin amfani da wannan damar da take da ita,


"Danish Baka jin yunwa? Naga jiya baka ci komai ba, yau ma kuma babu abinci, why bazaka Ci apples ɗinka ba? Sai in haɗa maka da nawa ka ci"? Angel sarkin wayau, so take yaci don shima yayi bacci mai nauyi irin nasu batool, ko ta samu ta shige toilet ɗin can ta fara gudanar da aikinta na fasa Glass window ɗin nan domin Shiga Cikin gidan Kurkukun ƙaddara,


"Bana jin yunwa" shine amsar da yabata, tunani ta shiga yi ta wace hanya zata yi mashi wayau don ya yi bacci,


"Tunda ba zaka yi bacci ba, to ka daina kallona mana, Ni inaso nayi bacci bana iya bacci idan ana kallona" jin abunda tace ne yasa shi yin saurin rufe idanuwanshi,


Tsawon mintuna angel tana kallon shi, tunanin kiranshi tayi don taji idan yayi bacci" Danish" amsa mata yayi"yeah" wai bazaka runtsa ba, da buɗar bakin sa sai cewa yayi"If you don't sleep, nima bazanyi ba." serious yae maganar, rufe idanuwanta tayi"its okey, ga shi nan zanyi baccin kaima kayi" Ya amsa mata da toh, daga haka kowa yayi tsit acikinsu, 


A lokacin da tayi tunanin ya nutsa cikin Baccin shi, ta sauko daga saman gadonta, takai hannu ta ɗauki fitilar da ta ajiye a tsakankanin beds ɗinsu, cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar sashen toilet ɗinsu, duk taku ɗaya saita waiwo ta saci kallon Shimfiɗar danish, 


Tana kawowa bakin ƙopar shiga sashen ta afka ciki, ta buɗe toilet ɗin ta shige taja ƙopa ta garƙame ta,


A ƙasa ta sauke fitilar, ta taka zuwa gaban bokitin ƙarfen nan ta ɗauke shi, tsayinta bazai kai ga tagar ba, dole sai ta ƙara da tsalle, cike da ƙwarin gwiwa ta daddage ta daka uban tsalle ta ɗaga Bukitin ta bugashi jikin glass ɗin da iya ƙarfinta na ƙarshe, sai dai wani abun mamaki glass ɗin Ko zagewa baiyi ba, Kamar ta daki ƙarfe ashe abun bana wasan yara bane, Tsalle taci gaba dayi tana kwaɗa bokitin jikin glass ɗin a ƙalla tayi kusan sau Talatin amma glass ɗin Ko yaƙi tsagewa, jikinta duk ya saki ga uwar zufa dake tsastsafo mata, sai faman haki take yi kamar wadda tasha uban gudu, ta galabaita sosai, sauke bokitin tayi ƙasa, ta zukunna tana mayar da numfashi, hatta idanuwanta sai da suka Canza launi,


Idan tahuta ta dawo normal saita kuma mikewa ta ɗauki bokitin Ta cigaba da buga shi jikin Windon, Har saita galabaita tukunna saita koma ta zukunna tana haki,


A wannan Karan Da azama ta miƙe ta ɗauki Bokitin ta daddage ta ɗaga shi da niyar ta kwaɗa shi jikin glass ɗin, kwatsam Taji motsin mutun acikin Makewayin, Ras gabanta yayi wani irin mugun bugu, tsananin tsoro ya bayyana akan fuskarta, batasan Lokacin data jefar da bokitin hannunta ba, Sam ta kasa juyawa taga wanene Ya shigo Cikin toilet ɗin, Bayan kafin ta shiga sai da ta garƙame ƙopar ta ciki ta sanya jam lock, ta yadda ba wanda zai iya shigowa, tabbas kuwa wannan ko wanene to ba mutun bane sai dai aljani, tuni tasha Jinin jikinta, Zufa ta ko'ina ta shiga wanko mata,


Takun tafiya taci gaba da ji ana tunkaro inda take, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, kafin tayi tunanin juyawa baya taga wanene taji an rungumeta, sai da ya zagayo da hannayenshi saitin shafaffan cikinta tukunna ta gane wanene, tsabar ruɗi takasa furta komai, muryarshi ta juyo ƙasa ƙasa yana faɗin"mu koma ɗaki, i was scared of being alone, kin tafi kin barni ni kaɗai," tashin hankalin da ba'a dama shi date! Kwanto da kanshi yayi ta gefen wuyanta, tsigar jikinta duk ta tashi, domin kuwa wannan daƙyar ya kasance danish ne! Taya akai ya shigo toilet ɗin bayan tayi locking ƙopar, saukar numshinsa taji asaman skin ɗinta, sai ƙara ƙanƙameta yake yi yana faɗin su koma ɗaki," acikin zuciyarta ta shiga ambaton"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin," Daƙyar ta samu ta daure ta cije Takai hannu ta raba hannayenshi daya tamke cikinta dasu, a ruɗe ta juya tana kallon fuskarshi, dagaske dai shi din dai ne, danish da ta bari akwance yana bacci, da sauri takai idonta kan ƙopar toilet ɗin don taga idan ta nan ya biyo, wani abun al'ajabi, ƙopar a datse take da jam lock ɗin kamar yadda ta barta, kallonshi tayi sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, 


"Ki wuce mu tafi, bacci nake ji" yadda yayi mgnr voice dinshi a raunace,


Babu musu ta yi gaba yabi bayanta, abakin ƙopar ta tsaya ta cire jam lock ɗin, tasa kai ta fuce yana abiye da ita, ta yi tsammanin Idan aljani ne zai 6ace na aihin kuma ta ganshi kwance saman shimfiɗarshi sai da ba haka ta gani ba, Shi ɗin daine da kanshi ya taso, Tabɗi akwai gwarama domin kuwa dole ɗaya ya kasance gaskiya, Danish Ana sarrafa shi? Ko kuwa yana da sihiri ne ajikinshi ne? Ita damuwarta ba faɗo mata da yayi cikin toilet ba, a'a Taya akai ya shiga bayan ta sanya jam lock ta Ciki? Ta ina ya shigo?


Takai ƙarshen zancen zucin nata tare da haye wa saman gadonta, shima ya hau nashi gadon ya kwanta, yana fuskantar inda take kallo,


Zuba mashi ido tayi cike da tuhuma, shi kuwa ya lumshe ido alamar bacci zaiyi, ta jima tana kallonshi kanta ya gama ɗaure wa, daga bisani ne bacci yae awon gaba da ita, tsakar dare ta farka ta miƙe tabi kowani gado ta tofe su da addu'a, Bayan ta kammala ta koma ta kwanta wani sabon baccin ya kuma ɗaukarta,


(Idan kuna so Ana sanya maku 2 page arana, Ku dage Da yin Comment da likes)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post