Kurkukun Ƙaddara page 27 complete

Kurkukun Ƙaddara page 27 complete

 

Kurkukun Ƙaddara 27

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dedicated to Aunty kubra❤


E27


Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji


*in the morning🌹✍️*


A washe garin ranar, tun kafin ta farka ta soma Jin hayaniyar su Batool, tsabar farin ciki yasa tayi saurin kai hannu ta zame bargon jikinta, ta ware round eyes ɗinta tare da kallon gadajensu, a zazzaune ta same su sai surutu suke yi kamar ba waɗan da  suka sha uban baccin nan ba, na yini guda,


Miƙewa tayi zaune ta sauko daga saman gadonta, a hankali take tafiya tana binsu da kallo, a lokacin danish bai farka ba, yana naɗe Cikin bargonshi,


Abakin gadon Batool ta tsaya tare da kasa kunne tana sauraron firar da suke Yi


"ko wanka bansamu nayi ba, Jikina duk tsami yake yi mini, tun ɗazu da muka ci apples ɗin nan bacci ya ɗauke mu bansamu nayi ba" azeeza ce tayi maganar,


Batool tace"Nifa nayi mamaki, ya akai mu kayi bacci daga Cin tufa da ayaba, kuma ba'a floor muka kwanta ba, to waye ya dawo damu saman gado"? Fuskarta da alamun ruɗi tayi maganar,


"i was confused, na kasa gane tsawon wani lokaci muka ɗauka muna yin bacci, amma gani nake kamar bamu daɗe ba, tun da har yanzu safiya ce"


Ƙumshe dariya angel tayi jin abunda suke tattaunawa, wai su duk a tunaninsu suna a jiya ne, basu san cewa sun ɗauki tsawon rana ɗaya suna bacci ba, har wata ranar ta shigo, kamar waɗan da a kayiwa wahayin surutu, Sumar kawunansu duk ta cukurkurɗe, Bakunansu hada yawun bacci,


"Yanzu haka zamu yini kenan muna jin yunwa babu abinci'? Nifa apples ɗin da tsohuwa ta bani ba abunda ya tsinana mini saboda wata irin matsiyaciyar yunwa nake ji" acewar parveen, duk fa wannan surutun da suke yi basu san cewa angel tana atsaye ta ruƙe ha6a tana kallonsu,


"Yanzu ya zamuyi kenan? Sam lokacin baya tafiya yadda ya dace, Nayi expecting ɗin ma idan muka farka daga bacci zamu ga marece yayi amma sai naga wai har yanzu muna a safiya" baki a kumbure Hanna tayi magana, Ita dai deeja sai buga tsoki take yi, abun ya motsa, haris na kwance saman gadonshi idonshi na fuskantar ceilling, 


Juyawa angel tayi tare da kallon shimfiɗar Danish, samun shi tayi a kishingiɗe, For the first time da ta ta6a yin tozali da Kyakkyawan murmushin akan fuskarshi, masha Allah, Waya ga zumar kyau, Dimples ɗin shi biyu sun lotsa sosai, yadda kasan kanshi farau kyau, ɗan zaro ido tayi tana kallon fuskarshi, farkawarshi kenan daga bacci, gaba ɗaya hankalinshi na akan su batool dake ta faman yin sambatu, Su yake yi ma murmushi jin wata shiririta, Su ɗauki tsawon Yini ɗaya suna bacci, Su kwana suna bacci amma suna faɗin cewa Basu son komai ba, Rashin ma bugi ne ke damunsu


Ɗauke idonshi yayi daga kansu batool, ta wutsiyar ido ya hangi angel tsaye tana kallonshi, da sauri ya kalleta suna haɗa ido, ya ɗauke murmushin dake akan fuskarshi, Can kuma ya kifa kanshi saman pillow, girgixa kai tayi fuskarta dauke da murmushi aranta tace"Ka gama rowar murmushin naka, wata rana abanza xaka dinga yi mini shi batare dana roka ba,"


Gyaran murya tayi masu Batool, kamar masu jira kusan atare suka ɗago suna kallonta, har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta"ANGEL"!


saukowa Batool da azeeza su ka yi daga saman gadonsu suka nufi inda take a tsaye, rungumeta azeeza tayi tana faɗin"Angel kema kinyi bacci da kika ci apples,"


 Bata bata amsa ba, sai da tafara  zagayo da hannayenta saman bayan azeeza tukunna tace"Ae ni banci appales ɗina ba, Ni da danish, Ku da kuka Ci ku kayi bacci, gaya nan yanzu kun wartsake," ɗagowa azeeza tayi daga kan Jikin angel tace"Amma ae lokaci bai motsa ba, har yanzu fa safiya ne, yau zamu yini muna jin yunwa" aɗan shagwa6e tayi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba angel ba, 


 "Sister"! Batool ce ta ambaci sunanta, tana atsaye kusa dasu, ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata tace"My other half, nayi missing dinki, ina fata kin tashi lafiya, an sha bacci" lumshe ido batool tayi fuskarta a yamutse tace"am not feeling well, sai nake ji kamar wani abu ya faru da muna bacci, na shiga ruɗu," janyota angel tayi zuwa jikinta, ta rungume ta, batool ta kwantar da kanta saman kafaɗar angel, hannu tasa tana shafa bayanta tace"Ki kwantar da hankalin ki, ba abunda ya faru, bacci kawai kuka sha," ajiyar zuciya batool ta sauke tare da raba jikinta daga na angel, still idonsu acikin na juna 


"Yakamata Ku je ku yi wanka, bazan 6oye maku ba, tsami ku ke yi, daurewa kawai nake Yi ina yin magana daku" cikin zolaya tayi maganar, gani tayi suna shinshina Jikinsu, harara batool ta jefa mata"Sister kinyi wanka shine baki tada mu daga bacci ba, Munyi wanka mu ma,"? Fuskarta akwa6e tayi maganar,


 "Ae ni bana tada mutun idan yana bacci, yanzu tun da kun farka, sai kuje ku yi,"


Juyawa batool tayi tare da kallonsu Hibba dake zaune saman gadajensu, Ko motsawa basuyi ba,


  "Ku tashi muje mu yi wanka," saukowa Kowannan su yayi daga saman gadon shi, 


  "Jiya nida danish mun wanke hada uniform ɗinmu," su6uce mata maganar tayi 


 Cike da mamaki batool tace"Jiya kuma"? Da sauri angel tace"Ina nufin ɗazu da safe, lokacin da kuna bacci, ae na fada maki ni da shi bamu Ci namu apples dinba," takai ƙarshen maganar tana  ƴan kame kame, Batool kamar bata yarda da maganarta ba, gyaɗa kai kawai ta yi tare da wuce ta nufi toilet,


Batool ce tabasu shawarar suma su wanke nasu Uniform ɗin, Sai da kowa ya cire uniform ɗinshi, Suka yi ɗaurin gaba da Bargunansu, Hada maxan su, tattara Uniform ɗin Batool tayi ita da Angel da Hanna, Suka shiga toilet sec ɗinsu, Anan Suka tara kayan wankin, Azeeza da javed ne suka ɗebo ruwa a buckets, rubina ta ɗauko masu detergent,  Su Uku Suke wankin kayan suna yi suna fira, Sauran ƴan uwan nasu ba wanda ya taya su dama su suka sanya kansu zasu wanke masu kayan, don sunce su baza su yi wanki ba kada ƙarfinsu ya qare, Gashi yau babu abinci, angel dai jinsu kawai take yi, ta ƙosa taga reactions ɗinsu idan su giants suka zo kawo masu abinci, zasu sha ruwan mamakin sanin cewa Sunyi baccin kwana ɗaya, 


Angel ta dage sai Cuɗa kayan take yi, Koda tazo kan Uniform ɗin haris saita yatsina fuska, Ta ɗago su tana shinshina su, A karshe ta wurga ma batool saman fuskarta tace"ki wanke su, Ni bazan wanke ma ƙato kaya ba" 


Dariya su kayi gaba ɗayansu, azeeza tace"Amma kuma kike wanke ma Mubeen dasu javed? Su ba ƙattan bane"? Girgiza kai angel tayi a yayin da take matse rigar data kammala Cuɗawa, tace"Idan kika lura Haris duk yafi su girman Jiki, shifa tuttu6e6ene ga Tumbi, Kuma mummuna......" bata ƙarasa maganar ba, karaf idanuwanta suka sauka akan haris dake atsaye bakin ƙofar toilet ɗinsu, Fitowarshi kenan daga wanka, ya ruƙe qugu jikinshi na sanye da bargon daya lullu6a, fuskarnan babu walwala attare da ita, harara angel ta watsa mashi, ita fa idan ta ɗauko magana ba wanda ya isa ya hana ta ƙarasawa, don haka taci gaba da cewa"sam baida kyau, Hancinshi gajere ne, gashi baƙi, idanuwanshi mitsi mitsi," tayi maganar tana murguɗa mashi baki,


Tayi tunanin haris zai tanka mata, amma sai taga ya girgiza kai kawai, Ya wuce cikin ɗakinsu, 


Batool tace"Na lura angel baki son haris, bansan meyasa ba," takai karshen maganar tana kallonta,


"batool, he hates me for no reason, that's why I don't like him" takai ƙarshen maganar, a yayin da take kai hannu ta ɗauki Bucket ɗinta, da niyar taje cikin toilet ta zumar da ruwan kumfar ta ɗebo wani ruwan da zasuyi ɗauraya da shi,


A bakin fanfo, ta tsaya ta tura bokitin ta kunna tap din ruwa ya shiga kwararowa, zuƙunnawa tayi tana jiran bokitin ya cika,


Bakomai ya faɗo mata arai ba, face Lokacin da Tana agida Tare da daddynta, Ita ko hanyar laundry bata sani ba, daddynta da kanshi yake zuwa ya wanke mata uniform ɗinta na makaranta, Yayi goge mata su, duk wannan wahalar bata san da ita ba, shi ne yi mata wanka ya zura mata kayan ajikinta, Allah sarki rayuwa kenan, 


Ganin ruwan ya Cika bokitin, yasa takai hannu ta kashe fanfon, ta miƙe ta ruƙo handle ɗin bokitin ta fuce dashi, a lokacin har su Batool sun kammala Yin nasu sa6in, saura ɗauraya, atare suka dinga ɗauraye kayan, Azeeza ce take zuwa ta shanya su asaman igiyar dake a cikin toilet ɗinsu,


Suna dab da zasu kammala, Sai ga Yasmin ta faɗo Cikin toilet sec din Fuskarta aɗauke da murmushi sai faman washe baki take yi


"Lafiyarki kuwa kike ta faman zabga murmushi"? Batool ce tayi mata tambayar, 


Daƙyar ta samu natsuwar cewa"Giants ne suka zo kawo mana abinci, "


Da mamaki akan fuskar batool tace"are u serious? Jinjina kai Yasmin tayi"Ku dai kuzo muje mu ci abinci," azeeza tace"amma nayi mamaki, yau ba rabon mu kwana da yunwa," angel dai sai murmushi take saki tana kallonsu, ganin har yanzu basu gane cewa wata ranar bace ta zagayo,


"Bari mu mayar da buckets din Gamu nan zuwa, Allah yasa dai ba wasa kike yi mana ba," acewar azeeza,


Yasmin tace"Am serious ku dai kuyi sauri kuzo, " ta juya cike da zumuɗi ta fuce,"


Da sauri suka ƙarasa shanyar kayan nasu, hannayensu a ruƙe dana Juna suka Faɗo Cikin ɗakin, A tsaye suka samu Giants Sun ƙame, Ga kayan abinci nan saman dining carpet ɗinsu, A shaƙe, Su Mubeen duk suna a zazaune Kowa Ya natsu Jikinsu sai kerma yake Yi saboda tsabar yunwar da suke Ji,


Ƙarasa shiga Cikin Ɗakin su ka yi, a gefen ƴan uwansu suka zauna a jere, Batool, azeeza da angel,  


Parveen ce ta yaye masu jan ƙyallen tray na farko, waro ido tayi tare da wage baki ganin Tsiren nama A shaƙe Da tray din, saboda yawanshi har suci su rage da anjima su ci, Wani irin maiƙo tsiren ke yi, yaji kayan ƙamshi hada su albasa da tumatur, batare da 6ata Lokaci ba, kowa ya zura hannu yana ɗaukar tsiren naman yana Ci, yadda kasa akuyoyi haka suke taunarshi, mutun ɗaya ne yake Ci atsanake tamkar baison ci, sam baison Cin abinci, karasa uban me yake ci ya ƙoshi, ranshi ne ya bashi cewar ana kallonshi, slowly ya ɗago da idonshi, da sauri angel ta duƙar da nata idon don kada ya gane shi take kallo,


"Kinsa min ido sosai," ya ambaci hakan acikin zuciyarshi, 


"Saboda ban yarda dakai ba, kai ɗin abin tuhuma ne, dole na sanya maka ido, duk wani motsinka akan idona," acikin zuciyarta tayi maganar, tamkar ta bashi amsar maganarshi alhalin kuwa batasan me yake saƙawa aranshi ba,


"Bansan meyasa kike tuhumata ba, laifin me nayi maki ne? Yayi tambayar acikin zuciyarshi,


Itama tabashi amsa acikin zuciyarta"baka yi mun laifin komai ba, sai dai Ina zarginka, taya akai jiya ka faɗo mini cikin toilet? Bayan na datse ƙopa ta ciki? Taya akai ka shigo? .........." bata kai ƙarshen zancen zucin nata ba, muryar rubina ta katse mata hanzarinta,


"Kuna ta Cin nama kun manta da shan ruwa" 


Tayi maganar tana kallon kowannan su, dakatawa su kayi da Cin naman, Hibba tace bari ta zuba masu ruwan, Bottle water ta ɗauka me sanyi, Ta tsirara masu ruwan acikin Wooden cups ɗin dake a jere, Kowa Ya mika hannu ya ɗauka yana sha, Saboda tsabar kallon angel da yake yi har sai da ya shaƙe ya hau yin tari, da sauri haris ya ɗaura hannunshi akan bayan danish yana ɗan bubbugawa, sai da ya daina yin tarin tukunna ya zame hannunshi,


Dariyar gefen fuska angel tayi saboda ta gane itace silar daya shaƙe, Ta san ya tsargune da irin kallom da tayi mashi ɗazu, abunda ke faruwa su duka biyun basu yarda da Junansu ba, Shi yana kokwanton canzawarta, ita kuma tana zarginshi da ba cikakken mutun bane, tun Daren jiya daya faɗo mata toilet batare da ya kwankwasa ta cire jam lock ya shigo ciki ba, ta ina ya shigo? Shine abunda ya sanya mata ruɗi agame da shi,


Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran da suka rage, Hada kayan marmarin da aka kawo masu da kuma snacks, Batool ta tattarasu ta kwashe acikin kwandonta, takai karkashin gadonta ta 6oye masu, 


Tattara Kayan abincin giants su kayi, Javed Ya ɗauko masu Na shekaran Jiya da suka kawo ma danish Ya miƙa masu suka kar6a, kafin suka fuce daga Cikin ɗakin,


Lokacin da Uniform ɗinsu suka bushe Kowa Ya ɗauko Ya sanya kayanshi ajikin shi,  


Saboda tsabar Jin daɗin da su ka yi, Hanna ta basu shawarar suyi wasa, 


Gaba ɗayansu suka taru, a tsakiyar ɗakin nasu, raba kansu su kayi gida Biyu, mutun bakwai bakwai, sai mutun ɗaya ya rage, itace me gabatar da wasan, wato hanna, bayani ta soma Yi masu akan yadda zasu gudanar da wasan,


"Duk wanda na canko acikin ku, zan rufe ma shi ido da tafin hannaye na, in matse su, zan ba shi sunan wanda zai gano mana, idan har ya kuskura bai canka dai da ba, da shi da wanda ya canko, kowa zaiyi masu dundu ɗaya abayansu, kun  amince" Haɗa baki su kayi wurin cewa Eh mun amince," 


Duk wannan abun da suke Yi tsohuwa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta tana kallonsu, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta ɗauke da wadataccen murmushi,


"Haris come out dakai zan fara, zaka gano mini deeja," fitowa haris yayi daga Jerin layin da yake yaje gabanta ya tsaya yana fuskantar sauran ƴan wasan, Hanna ta tsaya daga bayan shi ta zagayo da hannayenta saitin fuskarshi ta rufe mashi idanuwanshi da tafin hannayen ta,


Tafiya su ka yi agaban layin na farko, Kowa yasha Jinin jikinshi, daga haris yakai hannu zai canko mutun, sai kaga suna girgiza kai, gudun kada yaja masu dundu, Cikin rashin sa'a haris Ya ruƙo hannun mubeen yace Itace, aikuwa gaba ɗaya suka fashe da dariya, mubeen kuwa rai a6ace yace"amma dai haris anyi hamago, kai baka gane hannun mace da namiji ne? Deeja ce fa akace ka kamo ba ni ba," Maganarshi tayi matuƙar basu dariya, hatta tsohuwa saida ta murmusa,


"Kamar yarda nace a dokar wasa, Idan mutun ya canko ba dai dai ba, Da shi da wanda ya canka kowa xaiyi masu dundune, don haka Mubeen da haris ku zuƙunna ku bamu bayanku,,


Mubeen yana Cika yana batsewa ya fito daga cikin layi, ya Duka shima Haris Ya duƙa, kowa ya naɗe hannun rigarshi, babu tausayi babu imani, haka suka jera layi, suka dinga kai masu dunduna abayansu, koda akazo kan angel dama haushin haris take ji, Muguwar da gwiwar hannunta  ta daddage ta buga mashi ƙulli a baya, har wani sauti ya bata durum! nan take ya kife ƙasa, dama shi mubeen tuni ya zube yana mayar da numfashi ido sun ciko tab da kwalla, koba a faɗa mashi ba yasan wacece tayi mashi wannan dundun, idanuwanshi akan fuskar angel  yaci alwashin sai ya rama idan  idan aka zo kanta,


Hanna tace"the next person is, " kowa ya kasa kunne yana jira yaji su wanene,


Murmushin mugunta ta saki kafin tace"Batool! Ki gano mana Javed," Jiki ba ƙwari Batool ta fito daga Ciki layinta, Hanna ta rufe mata ido da tafin hannunta, suka soma tafiya suna Bin layin na farko, Duk wanda ta ruƙo hannunshi saita saki, harfa ta ruƙe hannun javed ta murza shi kamar tace shine sai kuma ranta ya bata cewar bashi bane, ƙasa ƙasa da murya yake ce mata ke ni ne, ki ce ni ne,' amma ina batool sai ta tsalleke shi ta ruƙo hannun Parveen, wadda tuni fitsari ya kamata, motsa lips ɗinta tayi tare da cewa"He is the one"


Hanna tace"you're wrong" tayi maganar tare da zame hannunta daga kan fuskar batool,


Waro ido tayi ganin parveen, gaba ɗaya suka fashe da dariya, Cikin shessheƙar kuka parveen tace"Ban yafe ba, Kinja min bala'e, "


 Janyo kwalar rigarta batool tayi'hakuri zakiyi, dama kinfi kowa Cin abinci yau, Kizo kawai mu basu baya suyi mana dunduna, ba yadda ta iya haka suka duƙa, kowa yayi masu dundu abaya, parveen tasha kuka, ita kanta batool saida ta matse ƴar kwalla, don da mugunta suke yin dundun,


Komawa su kayi Cikin layi, next person da aka kirawo, Azeeza ce aka ce ta Canko masu Naufal, hanna ta rufe mata idanuwanta, Da yake Allah yayi mata baiwa, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita shinshina kamar mayya, wai da ƙamshin jikinsu take amfani, tana zuwa kan hannun naufal ta shinshina, sai ce wa tayi"Shi ne" gaba ɗaya suka sanya sowa, " tsohuwa fa yau ta samu abun nishaɗi, sai faman murmushi take yi, har lokacin basu son cewa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta ba, tana kallonsu,


Babu rabon azeeza tasha dundu, angel dai sai fargaba take yi, ta ƙosa layi yazo kanta taji wa za'ace ta canko, Har Allah Allah take Yi acikin zuciyarta,


Mutane na gaba da aka kira, Deeja ce akace ta gano Danish!!, hanna ta rufe mata idanuwanta suka tafi suna bin layi, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita saki tace bashi bane, hankalin angel yayi matuƙar tashi, fargabarta kada Deeja ta cankota, taja mata bugu, aikuwa dai deeja tana zuwa gaban angel ta damƙi hannunta, har kusan fitsari saida angel tayi, aruɗe take girgiza mata kai kamar tana ganinta, har ta buɗe baki zatace shi ne, sai kuma ta saki hannun angel ta ƙara gaba, nauyayiyar ajiyar zuciya angel ta sauke hada sanya hannu ta shafa ƙirjinta, taji daɗi,


Cikin rashin sa'a deeja ta canko Rubina tace shi ne" rubina taji haushi, shaƙo wuyan Deeja tayi tana jijjigata tace"saboda ke shashasha ce, ta ina hannuna yakai na danish tsayi? Ba ki ga yatsun hannayena guntaye bane? Ke baki banbancewa ne? Gaba ɗaya suka fashe da dariya, hatta danish dake a tsaye saida ya ɗan saki murmushin gefen fuska,


Hanna tana dariya tace"Ba faɗa bane wasa ne, Kuyi haƙuri kuzo ku xuƙunna, Ku kar6i la'adarku" rai a6ace Rubina ta fito daga Cikin layi, takai hannu ta jan yo wuyan rigar Deeja, suka shiga tsakiya, Suka duƙa, ɗaya bayan ɗaya kowa yazo yana yi masu dundu abaya, koda aka zo kan angel, saida ta naɗe hannun rigarta, dama haushin deeja take ji, ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta Buga mata dundu abaya, har saida deeja ta kife ƙasa tana kuka,


Girgiza kai tsohuwa tayi ganin irin muguntar da angel ke yi masu wurin Yin dundu, ta kosa layi yazo kanta taga idan ita zata Iya tsira🤣


"Tun da naga mutane sun ragu, saura mutun huɗu suka rage, bazai yiyu abaku za6i ku canka ba, Sabo da za ku yi nasara Cikin sauki, don haka gaba ɗaya ƴan wasa su dawo Kan layi," hanna ce tayi maganar idonta akan su Haris dake zuƙunne suna jinyar bayansu,


Miƙewa su kayi kowa yana hura hanci, Suka Koma Kan Layi, Tofa su angel murna ta koma Ciki, ganin sun koma su goma sha huɗu,


"Adai dai ta natsuwa, Last 4 person da suka rage, zan fadi sunayensu, akwai Eve, Angel, danish and hibba, sai kuma Ni hanna cikon ta Biyar, Yanzu Zan koma Cikin ƴan wasa, Batool ke ce zaki wakilce ni, A matsayin alƙalin wasa, a dokar wasan Sabon alƙali zai Iya faɗin nashi sabbin dokokin,"


murmushin mugunta batool tasaki, harta hango haɗin da za ta yi, Fitowa ta yi daga kan layi, Ta koma ta tsaya a inda hanna take, Ita kuma hanna ta koma Kan layi ta jera da sauran ƴan wasa


Idon kowa ya koma kan alƙalin wasa Wato batool, a tsanake ta soma magana" A matsayina na sabon alƙalin wasa, Ina da tawa sabuwar dokar, Mutane biyar da suka rage idan har na canko ɗaya daga Cikinsu, na bashi sunan wanda zai za6o mini, idan ya kuskura ya canko ba dai dai ba, dashi da wanda aka bashi sunan shi ya gano kowa Zai yi masu dundu A bayansu, Sa'an nan babu su babu Cin sauran abincin da muka rage, kason su za'a raba ma sauran Ƴan wasa ne su Cinye" tun da batool ta soma kora jawabi, hankalin angel ya ɗunguzuma, ba ita kadai ba hatta hibba da eve da hanna sai da hankalinsu ya tashi, Jin wannan Dokar ta batool, taya za'a raba ma sauran ƴan wasa abincinsu idan suka yi failing, akwai matsala babba, 


Idon batool akan Na Angel data cika ta batse, murmushi ɗauke akan fuskar batoo tace"Next person Is......." Gaba ɗaya sun baza ido suna sauraronta, hatta tsohuwa a ƙagare take da taji wa batool zata Canko,


"Danish! " a hankali ya ɗago da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu kan batool, Yana jiran Jin wa zata ce ya canko,


Tunkafin batool ta ƙarasa maganarta, angel ta shiga girgiza mata kai daga inda take a tsaye Cikin layi, Alamar kada tace ya gano ta, don tasan halin danish zaiyi wuya ya iya canko ta, ita da take da tarin maƙiya acikin wasan kowa so yake tayi failing don tasha dundun, expecially haris da Deeja, a ƙule suke da ita, don har yanzu basu daina jin raɗadin dundun da tayi masu ba,


"Danish zaka Canko mana ANGEL, kafin mu fara zan ƙara tunasar dakai dokar wasa, idan har kayi kuskuran canko wadda ba ita ba, Kowa zaiyi maku dundu, sa'annan babu ku babu Cin abinci an jima, za'a raba ma sauran ƴan wasa naku" wani irin murmushin mugunta haris da deeja suke saki, daɗi kamar ya kashe su, don sunsan cewa Danish bazai iya canko daidai ba, saboda halinshi da suka sani,


Cike da shaƙiyanci deeja tace"Ina fata Danish Ya gaza canko ki, Na rantse hatta spinal cord ɗinki sai ya amsa idan nayi maki wani mugun ƙulli" tayi maganar tana kwatanta yadda zata bugu bayan angel da hannunta, gaba ɗaya suka sanya dariya, angel kuwa ta ɗaure fuska babu walwala kwata kwata, duk tasha jinin jikinta,


Haris yace"ni kuwa Da gwiwar hannuna zan daki bayanta har sai ya 6urma, In yaso su Giants sunyi jinyarta a treatment room," gaba ɗaya suka sanya dariya cikin nishaɗi, idanuwan angel tuni sun cicciko tab da kwalla, tabbas ta gama karaya domin kuwa tasan danish bazai ta6a iya gano ta ba acikinsu,


Danish come forward" Batool ce ta yi maganar tana nuna shi, fitowa yayi daga Cikin layi, ya ƙarasa gaban Batool ya tsaya, saboda tsabar mugunta haris hada cewa ajira ya cire rigarshi, a ɗaure ma danish fuska da ita, don yasan tsayin Batool bazai kai na danish ba, hakan na nufin bazata Iya datse mashi ido da tafin hannayenta ba, batare daya samu ƙofar da zai iya kallonsu ba, jama'a kowa fa yaci burin bugun angela,


Hannu haris ya sanya tare da tu6e rigarshi, Ya wurga ma batool ta sanya hannu biyu ta ca6eta, idon danish akan na angel da tabi ta kame kanta, kamar ta fashe da kuka,


Ɗaure mashi fuska batool tayi da rigar haris, ta matse mashi ido sosai har saida yaji zafi,


"U can Start" ta ambaci hakan tana kallon shi, tafiya ya soma Yi yana lalubansu, ya ruƙo hannun rubina ya saki, ya ruko na azeeza ya saki, ya ruƙo na eve ya saki, ya kuma ruƙo na parveen ya saki, Kowa ya zuba ido yana kallon shi, ya cafko hannun javed ya murza shi, Kowa yayi tunanin shi zai canka amma sai suka ga ya saki hannun,


"A ƙa'idar wasan, Ba'a magana, idan na kama mutun yayi magana, kowa zaiyi mashi dunduna Biyu, sannan ya rasa abincin shi, Bayan wannan kuma Zai wanke mana uniform ɗinmu idan su ka yi ɗauɗa, zai kuma wanke toilets ɗinmu, Bayan wannan kuma ɗan wasa yana da damar da zai iya ta6a ko'ina ajikin sauran ƴan wasa domin ya samu damar canko wanda akace ya za6a, wannan ba laifi bane" alƙaliyar wasa ce ta kora masu wannan jawabin, tayi hakanne don tasan halin angel da shegen wayau, tana iya cewa zata yi ma danish raɗa don ya gano ta,


Cigaba da tafiya Danish Yayi yana ruƙo hannayensu, yana zuwa kan saitin angel ƴan hanjin cikinta suka kaɗa, kowa ya tsaresu da ido, jira kawai suke su ga idan danish zai iya gano ta,


Ruƙo hannunta na dama yayi da hannayenshi biyu, ya shafa su ya matsasu sosai, runtse idanuwanta ta yi jikinta na kerma, ba halin tace mashi itace, saboda idon kowa dake akansu,


Sakin hannunta ya yi, nan take su deeja suka soma Sakin murmushin mugunta, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, A wani slow danish Ya ɗaga ƙafarshi har zai wuce sai kuma ya ɗan dakata, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah,


Komawa ya yi gabanta ya tsaya tare da miƙa hannu tamkar zai kamo hannunta, sai kuma ya kauce hannunshi ya cafko sumar kanta, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, cikin sanyin murya yace"she's the one, am i right? Gaba ɗaya su Azeeza suka Daka sowa suna Tafa mashi hannu, hatta tsohuwa saida Ta ɗanyi murmushi duk da ba haka taso ba, amma Abunda ya burgeta kaifin basira irin na danish, yayi wayau, saboda yayi amfani da yanayin kakarwar da jikinta keyi, da ya ruƙo hannunta da farko ya fuskanci hakan, shiyasa ya sake dawowa ya kai hannu kamar zai damƙi hannunta, sai yayi wayan kaucewa ya damƙi gashin kanta, saboda yasan idan itace, zai samu gashin kanta har wurin qugunta, wato danish yayi amfani da kwakwalwarshi,


Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya angel ta sauke, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wata irin mahaukaciyar dariya hada dafe ciki, Taji daɗi data tsalleke tarkonsu Haris da deeja, kamar su fashe da kuka saboda tsabar 6acin rai da takaici, plan ɗinsu ya rushe,


Sai da ta kammala shan dariyar, tukunna ta sanya hannayenta biyu ta warware ma danish ɗaurin da akayi mashi akan fuska, bayan ta kammala ta xame rigar tare da wurga ma haris ita saman fuskarshi, rai a6ace haris ya ca6e rigarshi yana faman kumbura baki


Natsuwa tayi tana kallon danish dake ta faman ƙoƙarin bude idanuwanshi, eyes lashes ɗinshi sun cukurkuɗe sun hana shi buɗe ido, matsawa tayi kusa dashi sosai, ta sanya yatsun hannunta wurin buɗe mashi idanuwan, yadda zai gani da kawai, 


Fuskarta ɗauke da murmushi tace mashi"thank u so much  danish, ka taimake ni, da yau an karya mini spinal cord ɗi na, gaba ɗaya suka saki dariya, banda haris da deeja,


Ruƙo hannunta danish yayi acikin na shi, ya jata suka koma gefe ɗaya, aka cigaba da buga wasa, juyawa tsohuwa tayi batare da kowa ya ganta ba, ta koma Cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe, 


Lokacin da suka kammala wasan, Saman gadajensu suka koma, waɗanda suka sha bugu sai faman jinyar kansu suke yi, rabi da kwatarsu ba'a ɗauko tsawon lokaci ba suka kama baccin wahala,


In the night 🌌


Lokacin da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke, suka ɗauko fitilun ɗakin suka kunna su Saman Dining carpet ɗin su, Dakin yayi haske sosai, Kowa ya samu wuri saman Carpet ɗin ya zauna,  Batool taje ƙarƙashin gadonta ta ɗauko masu Kingin Tsiren namansu, Ta rarraba masu Kowa Ya kar6a Yana ci, da suka kammala Suka ci snacks ɗinsu da Sauran kayan marmarinsu, Suna Ci suna fira gwanin ban sha'awa, 


Bayan sun kammala Ci, Kowa ya kasa runtsawa, dama angel tayi tunanin daƙyar su iya yin bacci saboda baccin da suka sha A jiya, idanuwansu sunyi wuƙi wuƙi, babu alamun bacci,


Duk suna a zaune saman gadajensu, Tunani ta soma yi kodai taje toilet ta ƙara jaraba fasa glass window ɗin nan? Wata'ƙil idan ta dage kullum tana zuwa tana Bugun jikinshi, Allah ya taimaketa ya fara tsagewa, juyawa ta ɗanyi tare da kallonsu, kowa ya kishingiɗa saman gadon shi, kallon shimfiɗar danish tayi ya  kifa kanshi saman Pillow, Aranta tace Allah yasa yayi bacci, kada yayi mini irin na jiya, don na lura akwai almatsutsai akanshi, ba shi kaɗai bane,

.........................


(Waɗanda ke yin Tiktok suyi searching Boss Bature Suyi following ɗina, Face book kuma Ina da page Hafsat Bature ku danna mini, da kuma arewa Book zaku ga Boss bature, zan baku link na handle ɗina in sha Allah) Mu hadu next page

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post