Kurkukun Ƙaddara page 28 complete

Kurkukun Ƙaddara page 28 complete

 

Kurkukun Ƙaddara 28

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dedicated to Aunty kubra


E28


Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji


Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar,


Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta  ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata,


Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla,


Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace"MEKE FARU WA NE'?_


Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa"mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su"


Shiru angel ta ɗanyi ta ruɗe ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a ƙasa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta ɗago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, ƙanƙameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faɗin" angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daɗi, xafi yake yi mini raɗaɗi nake ji,


Ƙura ido angel tayi tana kallon ɗigon Jinin dake ajikin wandon Parveen  Nan take ta gane cewa Jinin al'ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya ɗaure mata kai,' shessheƙar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta,


Ɗago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaɗunta"Kiyi haƙuri kiyi shiru parveen zanje in faɗa ma tsohuwa," takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa,


"Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su," amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa takai hannu ta bubbuga ƙopar, almost 3 times tana knocking ƙopar, Kafin tajiyo motsinta,


Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda,


"Meke faruwa ne nake Jin koke koke" tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu,


Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa"ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buƙatar magani da kuma pads ɗin da zasu sanya" 


Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duƙar dakai ƙasa tana sakin wani irin shu'umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai,


 "Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba"?


Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana


  "I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room" har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara,


"Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za'a zo a ɗauke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani ƙato ba," zuciyarta a harzuƙe takai ƙarshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buɗe ƙopa daga can saman benan.........................


A matuƙar kiɗime angel ta juya tana kallon stairs ɗin, hatta su Batool a ruɗe suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su ƙarasa saukowa sautin takalmansu ya karaɗe kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya ƙarfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases ɗin, haƙiƙa hankalin angel yayi matuƙar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi,  juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace" na roƙe ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alƙawarin zan kula dasu," idanuwanta cike tab da ƙwalla takai ƙarshen maganar,


Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace"Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar  Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za'a zo a ɗauke shi akai shi inda za'a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a ƙarƙashina suke ba, dukan mu Ma'akaita ne dake aiki gidan kurkukun ƙaddara, Kuma a ƙa'ida wani baya shiga hurumin wani........."


kalaman tsohuwa sunyi matuƙar girgiza angel, kafin ta yi yunƙurin buɗe baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faɗin Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ' a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin ɗauka su kayi masu ta hanyar ruƙe waist ɗinsu suka yarfa su saman faffaɗan kafaɗunsu, bayin Allah Sai kuka suke Yi suna Bugun bayan giants da hannayen su, Nan take zuciyoyinsu Batool suka karaya Jikin kowan nan su yayi sanyi, har ma basu san lokacin da suka fashe da matsanancin kuka ba, Juyawa giants su kayi atare suka soma tafiya dasu ɗauke saman kafaɗunsu suka nufi stairs ɗin,


Da gudun gasken Angel ta tunkaresu Tana ƙarasawa bayansu Ta cafko hannayen parveen dake abayan giant ɗin dake ɗauke da ita, da iya ƙarfinta na ƙarshen ta janyota gaba ɗaya ta faɗo ta baya, baiwar Allah jikinta sai 6ari yake yi, ɗagowa tayi tare da rungume angel ta ƙanƙameta tana kuka tana faɗin"dan Allah angel kada ki bari su tafi dani, saboda basu dawowa da mu, bana so nabar Cikin ƴan uwana bansan inda zasu kai mu ba, Ina ji araina kamar na tafi kenan......." Giant ɗin dake a ɗauke da Parveen Ya tsaya Tsak wanda ko ba'a faɗa maka ba, zaka shaida cewar A fusace yake, domin su ba'a katse masu aiki, Da gudun gaske su Hanna da su Javed suka ƙaraso Inda su angel ke a zaune ƙasa suna kuka,


Kallonsu kawai take yi idanuwanta sun rune ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ci, Na raba ta da ƴan uwanta da ake ƙoƙarin yi,


Cikin shessheƙar kuka Batool tace" Dan Allah ki daina kuka Parveen, tsohuwa ta faɗa mana cewa Cuta ba mutuwa bace, Sai in kwanan mutun ya qare, Zasu yi maki magani ne zuwa gobe idan ku ka ji sauƙi zasu dawo mana da ku," Ita kanta batool ta karaya sosai ta yi maganar ne kawai donta ƙarfafa mata gwiwa,


Zufa ta ko'ina Ajikin Parveen Muryarta na kerma tace"Koda ace ban dawo ba, Idan an kawo abinci, ku dinga ajiye mini nawa" Hawaye sharkaf akan fuskarta tayi maganar, angel dai takasa cewa komai, Zuciyarta ta gama karaya,


Kafin wani ya kuma cewa wani abu, Giant ɗin yakai Hannu da niyar ya ɗauki parveen, a tsorace ta ƙankame jikin angel tana faɗin" kada ki bari su tafi dani, bazasu dawo dani ba, idan har kuna sona dagaske ku taimake ni, kada ku bari araba ni daku......" ƙanƙameta angel tayi ajikinta, Giant ɗin ya damƙi qugun Parveen, ta ƙarfi ya fisgeta daga Jikin angel ya ɗaura ta saman kafadarshi Ya juya  Cikin zafin nama Ya haura saman benan, Sauran Giants ɗin guda Biyu dake a ɗauke da rubina da Deeja suna abakin ƙofar fita suna jiran ƙarasowar shi, yana daga cikin dokar aikinsu Basa tafiya dole sai suna atare da juna, wani irin jiri ne Ya rufe idanuwan angel, anan ƙasa ta kwanta idanuwanta na zubar da hawaye, Suna Jiyo sautin muryar parveen cikin shessheƙar kuka take faɗin cewa"Angel dan Allah kiyi mini addu'a, Kuma idan gobe ba'a dawo dani ba, ku ajiye mini abinci na"


Wannan maganar ta parveen ta yi matuƙar kashe masu sassan Jikinsu, A nan suka wuni zuƙunne suna kuka, Mutun biyu ne acikinsu basu zubar da kwalla ba, Danish da Haris Saboda sun sa ma ransu cewa Za'a dawo masu da ƴan uwansu ne, duk da haka sun yi matuƙar damuwa da halin da su Parveen suka shiga, Na raɗaɗin ciwo ga kuma maraicin da zasu Yi na raba su da ƴan uwansu,


Tsohuwa dake a tsaye Bakin ƙopar ɗakinta, Ko a ha6ar xaninta bata sanya damuwar Halin  da yaran suka shiga ba, Sai da taga Sun sassauta da yin kukan tukunna Ta dogara sanda ta nufi inda suke a zuƙunne ta tsaya tana kallon fuskokinsu da suka jiƙe sharkaf da hawaye


"Idan ku ka yi haƙuri, Za'a dawo maku da ƴan uwanku ne da zarar sun samu warakar Lalurar dake damun su, Kuka bazai ta6a yi maku maganin komai ba, Illa iyaka ya ƙara haddasa maku wata damuwar, Shawarar da zan baku shi ne, Ku sanyawa zuciyar ku haƙuri da juriyar rashin ƴan uwanku, kada ku cusawa kanku damu......." bata ƙarasa maganar ba  angel ta yunƙura ta miƙe zaune  idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, muryarta a zafafe ta soma magana

  

"Har kina da bakin zuwa ki bamu haƙuri akan mu yi shiru mu daina kuka? Wlh tun da nake 6anta6a ganin Muguwar mace azzaluma irinki ba!


Ɗan zaro ido tsohuwa tayi da kwala kwalan idanuwanta tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa,


"Kince ke uwa ce agare su, meyasa da naje na faɗa maki cewa Cikinsu na ciwo, baki zo kin duba jikin su ba? Koda sannu ne kiyi masu Amatsayinki na mahaifiyarsu, Amma bakiyi hakan ba, sai dai wasu ƙattai suka zo suka ɗauke su da sunan zasu duba lafiyarsu, bayan ke ya dace kiyi hakan a  matsayinki na Ƴa mace, duk da bani da ilmi akan abun amma auntyna ta ta6a faɗa mini cewa Menstruation lalura ce ta mata da suke yi a kowani wata, zaki iya taimaka masu idan kinso basai an kaisu wani wuri ba......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Su batul duk sunyi zugudum suna sauraronsu,   


"Banta6a jin tausayin wani ɗan adam ba aduniyar nan ba, kamar wadannan bayin Allah, wai su haka rayuwarsu zata ƙare? A tagayyare basu da me share masu hawayensu, basu da kafaɗar da zasu ɗaura kansu akai suyi kuka a lallashe su, Wannan wata irin Makauniyar ƙaddara ce? Tayi tambayar idonta akan tsohuwa dake a tsaye ruƙe da sanda, baka Iya gane awani hali take Ciki, domin kuwa fuskarta a haushine take, tsufanta da muninta sun ƙara bayyana


Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta 

"Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaɗai kika sa agaba, wlh rantsuwar ɗan musulmi idan har ba'a dawo mana da ƴan uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne'


Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana


"Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara...." a ruɗe angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta,


Cigaba da magana tsohuwa tayi"ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAƊANƊA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun ƙaddara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara," tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura ƙofar ɗakinta ta shige taja ƙopa ta garƙame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruɗani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun ƙaddara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za'ayi dasu? danginsu basa ƙaunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa? 


Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel,


"Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa "ALLAH"


biji biji take gani acikin idanuwanta, daƙyar ta samu ta iya zuƙunna agabansu, Muryarta a disashe tace"kuyi haƙuri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, " miƙewa kowannansu Yayi, Suna jan ƙafa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su ɗaya bayan ɗaya tayi masu addu'a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu'a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata ɗazu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife ƙasa, cikin shessheƙar kuka angel ta furta "NAYI DANA SANI" Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiɗarta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta ɗaga sama Ta soma yi masu addu'o'i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu,


A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu'a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen,


A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye,


Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita,


Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish,


Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi"Danish" a hankali ya buɗe idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta,


"Ka tashi lafiya"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin tace" Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa" ya amsa mata da toh,


Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace


"Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse ƙopa ta ciki na sanya jam lock"? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, ɗan tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips ɗinsa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa,


"Ba ka yi mini kama da maƙaryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet ɗin sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko'ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet ɗin, wanda nayi Imanin bata ainihin ƙopar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba" Cikin tuhuma take yi mashi maganar,


muryar shi a sanyaye yace" Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet ɗin shine kaɗai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba" 


Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne,


Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi, 


Mayar mata da martanin murmushin  yayi Calmly yace" kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne"?


Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa"


Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata


"Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alƙwarin hakan," ɗagowa tayi tare da kallon shi, 

  "Taya akai kasan cewa zasu dawo"? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi,


Murmushin gefen fuska ya ɗanyi, Can kuma yace"Kin manta anzo an ɗauke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne"


Girgiza kai angel tayi"amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an ƙara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an ɗauke ka daga Cikin mu"? ta jefa mashi tambayar,


"Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka ɗauke ni  bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene," 


Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa,


Miƙa hannu danish yayi tare da ruƙo nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata"angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone........" kalaman shi ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na ɗan wani lokaci, 


ƙayataccen murmushi ta saki  tana motsa lips ɗinta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana ɗaya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra'ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata ƙara bari faɗa ya haɗa su ba, Shi ma haris ɗin bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta,


"What are u thinking about"? Jin voice ɗin danish yasa ta ɗanyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta,


" baki bani amsa ba," ya tambaya yana sauraranta, 


"Dama ni ban ruƙe ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar ƴan uwana ne jini," ba ƙaramin daɗin kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes ɗinshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne,


Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba,


Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu, 


Sun ɗauki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna,"


"Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa"? Batool ce tayi mata tambayar,


"Taya xan iya runtsawa, alhalin ƴan uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne....." kukane ya ciyota, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa,  sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata ƙara karya masu zuciya ne, sai dai duk ƙoƙarinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da ɗaukar su parveen da akayi ba, 


Dafa kafaɗunta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace"pls angel, u should stop shedding your tears, kina ƙara sanya mana damuwa ne, ke da kike ƙarfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan"? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar,


Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba,  bata fahimtar me suke tattaunawa,


Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace "Nadaina batool, bazan ƙara ba, kema kada kiyi kuka" jinjina kai batool tayi"Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haɗa hannu wurin taimaka ma sauran ƴan uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu ƙarfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani, 


Ga Link na Tiktok Ɗina  kuyi following dina, Zan yi posting na vedio din Prisners da kowa na kurkuku👇 facebook page kuma Hafsat Bature


tiktok.com/@boss_bature

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post