Abubuwan Mamaki 11 Game Da Ƙwaƙwalwa

Abubuwan Mamaki 11 Game Da Ƙwaƙwalwa

Halittar ƙwaƙwalwa

1]. A yayin da ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa, wato "brain cells", a wani sashi suka mutu, na wani sashin na iya karɓar aikinsu. Wannan shi ne abin da ke faruwa a ƙwaƙwalwar mai shanyewar ɓarin jiki har motsin hannu ko ƙafa su dawowa bayan shanyewarsu.

2] Ƙwaƙwalwa ba ta ɗauke da maganaɗisan jin ciwo, wato "pain receptors", saboda haka, ƙwaƙwalwa ba za ta iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki ke jin ciwo ba. Saboda haka, ciwo daga kai na zuwa ne daga sauran sassan da ke kewaye da ƙwaƙwalwa, amma ba ƙwaƙwalwar kanta ba.

3] Ƙwaƙwalwa ta fi kowane sashin jiki son kanta. Domin duk da cewa nauyinta ba ya wuce kaso uku cikin ɗari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an ba ta kaso talatin cikin ɗari (30%) na yawan jinin da zuciya ke turawa a kowane bugu.

4] A mafi yawan lokuta, ɗan Adam na amfani da dukan sassan ƙwaƙwalwarsa, saɓanin tatsuniyar da ke cewa wai ɗan Adam na iya amafani da ɗan wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ne kawai a tsawon rayuwarsa.

5] Kimanin rabin sinadaran abincin da yara ke ci suna tafiya ne wajen gina ƙwaƙwalwarsu domin koyo.

6] Kamar yadda motsa jiki ko atisaye ke ƙara lafiyar jiki, haka ma yake ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.

7]  Kamar yadda tambarin babban yatsan hannunka (thumbprint) yake daban da na kowa, haka ma yadda ƙwaƙwalwarka ke aiki daban da ta kowa.

8] Saboda ƙwaƙwalwa na aiki ne da tsarin lantarki, a yayin da mutum yake a farke, ƙwaƙwalwa na iya samar da ƙarfin lantarkin da zai iya kunna farin ƙwan lantarki. 

9] Kimanin kaso sittin cikin ɗari (60%) na ƙwaƙwalwa kitse ce.

10] Rashin isashshen bacci na rage kaifin ƙwaƙwalwa. Ɗan Adam yana buƙatar baccin kimanin awanni bakwai zuwa tara a kullum.

11] Ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa ba sa iya jure rashin iskar oksijin da sida(gulukos) na fiye da mintina biyar

-Physiotherapy Hausa

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post