Jikar Iya Complete Chapter 13-14

Jikar Iya Complete Chapter 13-14

 

Complete Page 13-14 JI

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️

           08161316781

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Bismillahi ramanin rahim

Pages1️⃣3️⃣🆒1️⃣4️⃣

Bismillahi ramanin rahim

_____Indo kuwa tana ganin takai wannan budurwar ƙasa ta busawa wandonta iska, gudu take bata kula da mutane a hanya dan kowa ta gani bigesa take yi, dan haka ana ganinta ake matsawa gefe, dan kamar mota mara birki haka Indo take, bata tsaya ko ina ba sai cikin gidansu, tana zuwa tayi kan Iya tana sauke ajiyar zuciya.

Ganinta ta shigo da gudu ne kuma cikin tsoro yasa Iya ƙwasa da gudu tayi ɗaki, ita ma Indo marawa Iya baya tayi, dan a zatonta ko anbiyota ne kuma Iya tayi karo da police ne yasa ita ma ta ɗiba da gudu, dukkan su ɗaki suka yi, inda Iya ta buya ƙarkashin gado ita kuma Indo ta buya bayan kofa, dan a faɗarta in an shigo ana jin motsin Iya a ƙarƙashin gado ana zuwa za'a kamata sai ita kuma tayi waje ta banko kofar, abun da Indo take tunani kenan, ita kuwa Iya tana ta famar karatu duk abun da yazo mata baki yinsa take, har karatunsu na yarinta ma yi take, komai karantawa take a cikin zuciyarta, ita kuwa Indo banda tunanin yadda zatayi yau inta haɗu da wannan police ɗinnan mahaifin wannan budurwan, inba dan ta hangosa ba da babu abun da zaisa ta gudu dan ta jefar da budurwar, hangosa da tayi ne yasa ta ƙwasa da gudu, duk sunyi shuru kusan minti uku babu mai yiwa kowa magana, dan ko kyakykyawar numfashi basa fitarwa, Iya dai bata san mai Indo ta tsokano ba da har take gudu, dan abun da zaisa Indo tayi gudu babba ne, hakanne yasa Iya ta zuge bakinta a ƙarkashin gado.

"Indo marainiyar Allah mai ya faru ne?, wa ki ka taɓo kuma yau?" tayi maganar cikin raɗa.

Indo da take bayan kofa ta manne da bango kamar ba mutum ba, kasancewarta siriruwa ce hakanne yasa ba'a gane da mutum a bayan kofar, daƙyar ta mase murya tana faɗin "Iya tawa kuma mai share mun kuka, to yau fa faɗar babba ce dan ƴar gidan Umaru Police na taɓa" ta mayar mata cikin raɗa.

Iya kam tana jin wannan batu na Indo ta fara kokarin kuka, tana salati tana sanarwa Ubangiji kukanta, yau wannan mairainiya ta janyo mata abun da yafi karfinta, nan fa ido ya fara raina fata kuka take yi tare da majina, hannunta kuma ta damƙe bakinta, kamar irin rayon da aka hana kuka dan kar aji yana yi, ita kuwa Indo tana faɗawa Iya ta zuge bakinta tayi shiru kamar wacce tayiwa sarki ƙarya, Iya kam ga uban matsin da take ciki, dan gado ne irin na ƙarfen nan kuma ga uban shirgi a ƙarƙashin gadon, daƙyar take numfashi tsabar matsi, can dai Iya ta fara sakin tusa wannan yazo wancan ya tafi, haka take ta sakewa kuma gashi babu sausauci sannan wanda yake filin gida ma zai iya jiyo sautin tusar, daman Iya tana da matsanancin basir, kuma yana yawan tashi mata inta tsorata, ita dai sai saƙar tusar take yi ita tsabar tsoro ma bata san tana yi ba.


Jin anbuga kofar ne da ƙarfi yasa Iya faɗin "Allahumma inni a'uzubika minal ƙubusi wal'kaba'iz" tare da sake kuka, kalmar da take ta nanatawa kenan, ita kuwa Indo dake bayar kofa take faɗin "Dan Allah Iya kiyi shuru mana ana jinki fa, kuma ai wannan addu'ar da kike karantawa ta shiga gida ce ai" tayi mata maganar cikin raɗa.


"Ina mutanen gidan suke ne? ko ba kowa ne" cewar ɗan sandan, ya yi maganar yana ƙarasowa tsakar gidan.


"Ai babu inda zani wlh inban kama wannan yarinyar da ta addabi kowa a garin nan ba, dan wlh yau sai tayi ƙwanar gadirom," ya yi maganar ya na zama a ɗan kujerar da ya gani a tsakar gidan.


"Wannan haka yake oga, aka taɓa wani ma kasaka aka kwana a gadirom ballantana an taɓa jininka, ai babu uban da zai hana ƙwanar yarinyar nan a station," cewar corporal Idi dake tsaye akansa ya kame alamar yana kasa da Umaru police.


"Bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala kuwata ilah... Dan Allah Indo tuna mun mana" Iya ta kasa karasa addu'ar, ita kuma Indo kamar ta rufe Iya da duka tsabar haushi, nan ta fara raba ido jin tafiyar mutum ya doso su, su kuwa ƴan sandan maganar Iya ce ta nusarsu da gane da mutum a cikin gidan, dan haka suka yi ɗakin cikin sauri, suna ƙaraso wa Iya ta zabga ihu tana faɗin "wayyo jama'a ga ƙwarto nan ya shigo mana gida, ihu take babu sausauci, dan kan ya karasa ga janyota daga ƙarkashin gadon mutane sun taru a kofar gidan, amma kuma suna tsoron shiga gidan Iya dan sun san halinta makirar tsohuwa ce, wacce take da sharri ita da Jikarta in suka haɗa maka abu to fa babi mai fitar dakai sai Allah, dan haka kowa ya tsaya daga inda yake.


Ɗan sanda ɗayan yana daga waje shikuma ɗayanne ya shiga cikin ɗakin dan yana riko hannun Iya tasaki salati tana faɗin "Indo ta bayar kofa fito asirinmu ya tonu" tayi maganar tana sakin kuka.
Hajiya Kamala ta rasa inda zata saka kanta, saboda bakin cikin abun da Zohaib ya aikata, ita duk bata taɓa zaton zai iya aure ba tare da sanin su ba, sannan kuma yanzu da bata ga matar ba da bazai faɗa mata ba kenan, ita kadai ta raya nan tayi can ta rasa abun da zata yi taji dadi, zama tayi akan kujera ita kadai sai famar yatsina fuska take yi, wayarta take shafawa kamar bata so, wata dattijuwa ce ta shigo da sallama, a bakinta amma shuru ba'alamar za'a amsa mata, amma ita tsohuwar bata ma damu ba da alama ta saba ne, durkusawa tayi a gaban Hajiya Kamala tare da faɗin " Hajiya an kammala komai, inba damuwa zanje gida na dawo, in kuma da abun da zan ɗauko miki kafin na fita ki faɗa" cewar Dattijuwar tayi maganar tana durkushe akan kafafunta.


Wani kalon ta watsa mata kana ta maida hankalinta ga kan wayarta, sai da ta ɗau mintuna kafin ta ce "wai ke bakida hankali ne?, mai yasa baki san sanda mutum yake cikin farin ciki da bakin ciki ba, da har zaki ce inda abun da nake bukata, dalla tashi ki bani guri," tayi maganar tana daka mata tsawa tare da binta da harara tana faɗin " talakawan banza da hofi, yan wahala duk a haka zaku ƙare masiyata" ta karashe maganar tana mikewa tsaye, kai tsaye ɗakinta ta huce, inda taje ta samu waje ta mike tare da ƙara wayarta a kunnenta, shuru ta ɗanyi kafin ta ce " ke yanzu ba ta Alhaji ake ba, dan yanzu nasa da sauki tunda na riga na kore duk danginsa," tayi maganar tana haɗe rai kamar wacce ake kallonta ba waya take ba.


" Kamala ban gane me kike nufi ba?, kina so kice yanzu ba zamu koma wajen boka  ba, to duk ma ba wannan ba, naji kince yanzu bata Alhaji akeyi ba, " 

Shetti ta karasa maganar tana rababin son jin amsar da ƙawar tata zata mayar mata.


" Zuwa zamuyi wajen Malam Jin tukunna, dan akwai abun da nake da tambaya tukunna, wai yaron nan ne ya yi aure bada izininmu ba, sannan ma bansan ya yi ba sai da na kirasa muna waya na gansa da wata, ni nazata ma ƙawarsa ce wai matarsa ce," tayi maganar cikin asala.


"Kamala lalle kinyi sake akan wannan yaron tun farko, kamata ya yi kiyi masa aiki akan duk macen da zaiyi mu'amala da ita ta kasance ƴar gidan wata a mushaƙin mai kuɗi, wanda soyayyarsu ma sai an buga a newspaper, maybe ma ƴar matsiyata ce" ta ƙarashe maganar cikin takaici da abun da ɗan ƙawartata ya aikata.


"Ke dai bari Shatti, kawai yanzu ki ƙaraso muje wajen Malam Jin mu dawo tukunna, dan in banje naji bayani daga bakinsa ba bazan iya bacci ba yau".


Daga haka su ka yi sallama akan zata ƙaraso, cikin ikon Allah ba'ayi bata wani ɗauki lokaci ba sai ga Shatti ta shigo, kana ganinta kaga irin ƴar duniyar nan ce, sannan kuma idonta a buɗe yake sosai, dan da ganin kayan jikinta da jaƙar dake hannunta kasan kuɗi ya ratsata, cigam take tauna ta shigo cikin ɗakin Hajiya Kamala, tana ganin bata falo tasan tana ciki.


"Wannan Yarinyar ba haka kawai ta auri ɗanki ba, dan tayi masa mugun asiri tukunna, gashinan leƙa ki gani ba wannan bane ɗan naki, sannan kuma ba wannan bace matar tasa?" ya yi maganar yana mata nuni da ƙasar dake gabansa.
Free pages ya kusa ƙarewa.Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post