Adadi Da Amfanin Sanya Harza (fibres) A Cimaka

Adadi Da Amfanin Sanya Harza (fibres) A Cimaka

Fiber

Dr. Naziru Bashir Mukhtar PhD

A kullum, ana bukatar a abincin da mutum zai ci ya hada da dangin abinci mai harza (fibres). Harza na da matukar amfani ga jiki, tana taimakawa wajen saukaka nika abinci bayan an ci da kuma taimakawa wajen yawon abincin da kuma tattara abincin da baa yi amfani da shi ba gami da aika shi zuwa ga dubura domin kasayarwa. Tana saukaka wahalar yin bayan gida da kuma gajarta lokacin yin tsuguno. Ma'ana, harza dai na taimakawa wajen inganta lafiyar ciki, hanji da dubura. Hakan ne ma ya sa harza na taimakawa wajen hana samuwar ciwon basir ko kuma saukaka cutar. 

A wani bangaren kuma, harza na taimakawa wajen rage kiba domin tana sawa ciki ya cika a ji an koshi da wuri ba tare da an ci sinadaran kuzari da yawa ba (calories).

Ga masu ciwon suga, harza na taimaka musu matuka wajen su dinga samun koshi ba tare da sugansu ya wuce misali a cikin jini ba.

Ana samun harza a abinci da yawa, musamman ganyayyaki da yayan itace da suka hada da; yalo, data, karas, salad, gurji, dafaffiyar/gasasshiyar masara, lemo, goruba, tuffa da sauransu. Ana son a kullum a ci harza da ta kai kimanin giram (gram) 25-40.

Allah Ya kara mana lafiya

Daga Dandalin: Lafiya uwar jiki

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post