Jikar Iya Page 15-16

Jikar Iya Page 15-16

 

Hausa Novels

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️

           08161316781

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Bismillahi ramanin rahim

Pages1️⃣5️⃣🆒1️⃣6️⃣

______Jin haka yasa ɗayan shigowa bayan kofar ya duba nan ya ganta, mugun riko yamata yadda ba za ta cubuce masa ba, dan yasan halin yarinyar nan muguwar hatsabibiya ce, dan haka yana fitowa daga tsakar gidan ya danna mata hanƙwa a hannu, sake Iya suka yi daman Indo suke nema dan haka suka tusa keyarta suka yi gaba Iya ce take binsu tana faɗin "wayyo jama'a ɓarawo ne ya shigo har gida zai tafi da Indo ku taimaka mun, dan Allah jama'a zai tafi da marainiyar Allah, mugu azzalumi a haka zaka ƙare da bakin fuska yadda fiskarka yake haka zuciyarka take, ga kuma wani bakin kaya kai kam abun ya mata yawa," tayi maganar tana binsu a baya tana kuka, Indo kam sai famar biskewa take tana faɗin "Allah ya isana kuma sai an koreka a wajen aikinma, tunda kaci mutuncin marainiyar Allah, daman nasan ka tsanane a garin nan, wlh sai ka gani akan aikinka" suna tafiya tana zaginsu babu wanda ya tanka mata, haka ita ma Iya babu wanda ya ce mata ufan har suka karasa police station, yana zuwa suka shigar da bayani akan wanda yake bakin aiki, bayan an rubuta komai da abun da Indo ta aikata, sai aka ce za'a saka Indo a gadirom dan wacce akayiwa lefin tana asibiti, dan faɗiwar da tayi sai da ta suma.

" Kai Umaruru polisa kaji tsoron mai sama, dan wlh ka gama tsuga karyarka anan duniya kana zuwa can walakili ya ɗaki banza, kai tsabar ba Allah a ranka sai ka rasa wacce za ka yiwa sharri a wannan garin sai wannan marainiyar Allah" cewar Iya da kuka ya kufce mata.

"Iya ƙyalesa wlh sai ya yabawa aya zakinta, badai Jikar Iya ya taɓo ba" cewar Indo da ake kokarin tusata cikin gadirom ɗin, kan a karasa saka Indo ciki Iya tayi super ta shige, dan a faɗarta ba za ta bar Indo ita kaɗai ba.

" Dan Allah Dattijuwa ki fito karki ɓata mana aiki, dan mu bake muke tuhuma ba" cewar wani ɗan sanda wanda yake tsaye a bakin kofar.

Kallonsa Iya tayi daga ƙasa har sama sannan ta ce " Oh ni Binta yau naga bala'i, kai da kake fari ma nayi zaton haka zuciyarka ta ke ashe duk kanwar ja ce" tayi maganar tana rike haɓanta.

Indo kuma da take a jikin ƙarfen kofofin ta ƙaraso inda ɗan sandan yake, wanda ya tsaya kamar sanda a ƙame, cikin sanɗa ta samu ta saita hannunsa sa yasa a baya ta janyo ta jikin ƙarfen nan, baki ta saka ta kallamasa cizo, inda ya saki wani kara mai cike da tsoratarwa, ihu ya ke yi yana faɗin "Wayyo Allah na ispecter wlh wannan ba mutum bace, zata ciremun ɗan yatsa na," ihu yake yana ta famar maganganu, Iya kam hannu ta saka a cikin aljihunsa duk bai sani ba, mukulli ɗaya tayi kokarin zarewa ajiki tana gama cirewa ta maida masa aljihunsa, ita kuwa Indo taki sakin sa, sai famar kalla masa cizo take yi, kuma gashi har yanzu babu wanda ya jiyosa.


Ihu yake yi amma babu wanda ya jiyosa, Iya ce ta zira hannunta a cikin wandon ɗan sandan, ihu ya saka yana faɗin wayyo ƙwartuwa ce, Oga Musa,corporal Jon, ispecter, kuna ina wlh wannan ba mutum bace kuwa wlh tsohuwar ƙwartuwa ce, wayyo babu kowa ne, sai famar ihu yake abunsa amma basu me jiyosa ba, dan tsakaninsu da ɗan nisa kaɗan, ita kuwa Iya sai famar zazzaga masa ƙarara a cikin wandonsa, tana gama zazzagawa ta cire hannunta.


"Mai ka ke faɗa ne? kana nufin inni zanyi ƙwatonci sai nayi dakai, kai yanzu nawa ka ke abuma naka nawa yake, kaga abu kamar wani ɗan yatsa shine ka ke ganin kanka namiji ne, ni Allah na tubama lokacin da nayi zamani na ai wlh baka isa kazo wajena ba, danni duk wanda yazo wajena sai na gama lalubesa tas na tabbata kai kikancen namiji ne, amma ai kai muna maza ne" tayi maganar tana cire hannunta, ita ma Indo sakesa tayi da gudu ya yi baya ya fara kokarin cire wandonsa tsabar kai kayi, Iya ce ta saka ihu tana faɗin " wayyo Allah daman kun kawo mu nan ne dan ku far mana, ashe ƙwartoyene ku zaku afkawa tsohuwa da marainiyar Allah, wayyo Allahna ka dubemu babu wani a tanan ne yana kokarin afkamana" maganar da Iya take faɗa kenan cikin ihu, ita ma Indo ihun ta shiga yi tana faɗin "Wayyo Allahna ku taimaka mana, wannan ɗan sandan yazo zai afka mana," abun da Indo ta faɗa tana kuka.


Sai a lokacin ƴan sandan suka fara jiyo ihu daga inda gadirum yake fitowa nan suka yi wajen da gudu suna zuwa suka ga yana kokarin cire gajeren wandon ciki dan wandonsa na uniform kan daman ya ciresa, sai famar susa yake yi yana Allah ya isan sa, mayyar tsohuwa tare da jikarta mai zubin aljanu, sukam ganin zai iya cire gajen wandon ma a gabansu kuma ai wannan abun kunyar su zaijawowa hakan yasa suka dauke sa suka yi waje dashi, ita kuwa Iya da jikarta sai dariya suke yi.


Leƙawa tayi tare da faɗin "wlh sune wannan shine yarona Zohaib abun muradina a ko yaushe, na ɗau burin duniya na ɗaura masa amma wannan sinanniyar zata bata mun mafarkina" tayi maganar cikin gadara da nuna isa.


" Ai Hajiya banda Allah yasa kun zo nan da wuri da kuwa kin ƙara hawa biyu to wlh ba za ki iya waya ma da ɗanki ba, dan yau sunyi da bokanta akan za'a mata aiki mai zabi, yadda zai manta ma da dukka halinsa sai ita kaɗai..." kan Malam ya kai ga zancensa ta dakatar da shi da hannunta alamar ya tsaya da zancen haka.


Nan ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "yanzu Malam mai abun yi, inason ayi mun aiki wanda yanzu zai fara ci kamar yankan wuƙa, inason a yau a fara aiki, malam ni ko nawa ne akan ɗana zan iya kashewa" tayi maganar cikin gadara da nuna ita kuɗinta zaiyi mata komai, dan wata banza ba za ta ƙwace mata ɗanta ba.


" To yanzu zaki samo Farar saniya, tare da farar rakumi da kuma farar rago, sai farar akuya da kuma farar kaza, sai tatabara da kuma tsunsu duk farare, dasu za'a fara aikin yanzu" ya yi magana ya na ci gaba da dube dubensa a ƙasa.


Shatti ce ta riƙe haɓa tana kallon malam da jin abun da ya lissafo, sai kuma ta maida hankalinta kan Ƙawartata Kamala da taƙe kokari buɗe jaƙarta, da kallo ta bita dan yadda taji malam ya lissafo abubuwan nan ba ƙaramin kuɗi za'a kashe ba, wayarta ta ciro tare da faɗin "Malam inajinka, kamun lissafi dukka sunkai nawa, danyi bansan inda zan samo wannan abun ba, kaga inyazo sai na tura maka ƙuɗin sai ka aika a siyo maka ko?" tayi maganar tana juya hannu ma Shatti.


Cikin sauri Shatti ta gyaɗa kai da sauri tana faɗin "haka ne ai ƙawata dan ya kamata ki dage, Allah ma ya rufa asiri munzo da wuri, da abun inya kai gobe da bamusan yadda zatayi dashi ba..." kan ta rufe bakinta "dan Allah Shatti ki daina tunamun maganar bayan nan, dan aikin gama ya gama yanzu, tunda munyiwa tubkar hanci" tayi maganar tana mai da hankalinta ga Malam da yake shirin fara bayani.


" To dukka dai wannan kuɗin harda na aiki ya kama 2milion ne" ya yi maganar yana ɗauko wani ɗaurin magani, nan dai bata wani bata lokaci ba ta ɗauko wayarta ta ƙarɓi account numbersa, a lokacin tayi masa transfer na 2milion.


A haka suka je ta ajiye Shatti a gidanta kana ta ƙaraso gida ita ma, bayan ta dawo ne tayi ɗakinta, wanka tayi ta na zauna akan wani kujera da yake na mutum biyu a ɗakin, kwala kira ta shiga yiwa Mero (Dattijuwar nan) amma shi tayi shuru, haka ta tashi a fusace ta ƙaraso kitchen nan ma bata ganta ba, ranta in yayi dubu yau ya ɓaci, dan ba ƙaramin yunwa take ji ba, dan bataci abincin lunch ba ga kuma na dare, zama tayi a falon ta ɗaura kafarta ɗaya kan ɗaya, tana famar girgizasa.


Sai wajen karfe taƙwas tukunna Mero ta buɗe kofar falon ta shigo da sallama a bakinta, tana jin sallamar amma bata amsa mata ba, ita kuma inda sabo ai ta saba dan haka ta ƙaraso inda Kamala ta ke ta durkusa tana faɗin " barka da hutawa Hajiya, da fatan na sameku lafiya..." kan ta rufe bakinta sai jin saukan mari tayi a fuskarta tas ta bata tako wani ɓari na kumatunta.


Har sai da ta tuntsira tsabar marin da tasha, wannan dattijuwar rike kuncinta tayi tana kokarin haɗiye kukanta amma abun yafi ƙarfinta sai da ta fitar dashi, dan inba rashin kuɗi ba da rashin inda zata saka kanta da marayun dake gabanta da kuwa wlh sai ta bar aikin nan, dan kaf gidan nan babu wani mai ganinta da kima sai Alhaji, karma kaje ga wannan yaron yana gari wato Zohaib yana da wulakanci.


" Munafuƙar tsohuwa tsabar kin tsaneni nida gidana amma zaki hanani abincin da zanci, kinje yawonki sai yanzu zaki dawo, ai daman talaka baisan ya samu waje ba, ba'a iya muku talakawa, tsohuwa mai zubin mayu, huce ki ɗauko mun abincina" tayi maganar tana haƙaɗeta gefe........Free pages ya kusa ƙarewa, an fara biyan kuɗi ki daure ki biya kuɗinki ki huta.


Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post