Kurkukun Ƙaddara chapter 31 Complete

Kurkukun Ƙaddara chapter 31 Complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dedicated to Aunty kubra❤


E31


 (Boss Bature writer of Abban Sojoji✍️)


Tea pot tsohuwa Ta ɗauka ta ƙara tsirara ruwan tea ɗin acikin cup ɗin gabanta, kafin ta ajiye pot ɗin ta ɗauki kofin takai baki tana sha" Sai da ta kur6e shi duka ta sauke kofin saman table, Tukunna tace"Tambaya ta farko, Gidan kurkukun ƙaddara Ni kaina bansan awace Nahiya yake ba, Abunda na sani shi ne ba'a Cikin kowace ƙasa Yake ba, mashin ko mota bazasu Iya kawo ki cikin kurkukun nan ba"


aruɗe angel ke kallonta, sai da takai karshen maganarta angel tace"Amma Ni lokacin da za'a kawo ni acikin mota aka ɗauko Ni, idan har zan Iya tunawa" dariya tsohuwa Ta saki, 


"iya saninki kenan, A mota aka Cafko ki, Amma Bayan nan bazaki Iya tuna Ta Cikin ina aka ƙaraso dake nan ba," shiru angel ta yi Zuciyarta cike da was wasin maganar tsohuwa, Gani take kamar ƙarya take Yi mata,


Muryar tsohuwa ce ta katse mata Zancen nata da cewa"Tambaya ta biyu,  Na jinin ka da zai Iya sadaukar dakai, Mafi rinjayen sadaukarwa Iyayene waɗanda suka Yi silar zuwan ka duniya sune suke sacrificing ɗin ɗansu, Uwa Ko Uba, Bayansu Kuma sai Cikin Blood relatives ɗinka, Domin kuwa Bare bazai ta6a Iya sadaukar dakai ba"


A matuƙar kiɗime angel ke kallon tsohuwa, Muryarta har rawa take yi wurin furta"Iyayen mutun? uwa ko Uba? Anya kuwa zan Iya yarda da maganarki? Duk irin ƙaunar dake a tsakanin Iyaye da ɗansu Zasu Iya sadaukar dashi zuwa ga wannan ƙuntatacciyar rayuwar? To Meyasa zasu Yi hakan? 


Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Kina mamaki ne?, dama nasan zaiyi wuya ki yarda da magana ta, Yanzu dai Ina sauraronki, Idan akwai tambayar da kike da ita, Ki faɗa mini kafin in tafi"


Angel dai ta jinjina maganar tsohuwa abun Ya tsaya mata arai, ya cunkushe kwakwalwarta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Tambaya Ta ƙarshe da nake so Inyi maki, Mu prisoners dake rayuwa a gidan Kurkukun ƙaddara, Jinsi ɗaya ne? Dukanmu ƴan nigeria ne? Naga da yawan mu kamar fararen fata ne, 


Tsohuwa tace"meyasa Ki kece haka"?


Angel tace"saboda Sam babu kamanceceniyar Jinsin baƙar fata atare da mafi rinjayenmu, Misali Kamar danish da Parveen da Javed Sun fi kama da ƴan ƴankin Asia, Azeeza Kuma kamanninta sak da European, Ita kuma batool tafi kama da Jinsin Larabawa, idan muka koma 6angaren Hanna da Hibba, sun fi kama da buzaye Ƴan ƙasar niger....." ɗaya bayan ɗaya saida angel ta korawa tsohuwa Bayani adangane da Jinsin da kowannan su take hasashen  yana  kama da shi, takai ƙarshen maganar, a ƙagare da son jin amsar da tsohuwa zata bata,


"Lokacin da kina atare da Iyayenki, Mutane da wani jinsi suke kwatantaki"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar  yayin da take sakin murmushi,


Yatsina fuska angel ta yi tare da cewa"Sun fi tsammanin Ni balarabiyace wasu kuma baturiya, amma asalin mahaifiyata half cast ce, auntyna ce ta faɗa mini cewa kakata mace balarabiyar ƙasar egypt ce" 


Tsohuwa tace"Kinyi kyan kai, Wannan tambayar da kikayi mini, Kina da amsarta ahannunki, ina fata zaki tashi ki tafi Cikin ƴan uwanki tunda na amsa miki tambayoyinki," maƙe kafaɗa Angel tayi alamar bazata tafi ba 


"Korata kike Yi daga ɗakin ki? Tsohuwa tace"a'a kawai dai Akwai inda nake son xuwa ne" Mamaki akan fuskar angel tace"ta ina xaki bi ki fita daga Cikin ɗakin nan naki bayan naga babu ƙopa, Koda yake ba abun mamaki bane, ae naga kafin ma in shigo Ciki, Kincanzawa ɗakin suffarshi  duk don kada In yi maki leƙen asiri" tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya, Itama angel ɗin dariyar tayi, sai da suka kammala shan dariyarsu kamar wasu ta6a66u, bayan sun tsagaita da yin dariyar angel tace


"Na jima inaso in tambayeki, Ya akai kika san Tarihin rayuwata? Kinsan komai dangane dani, Bayan haka kuma inaso insan asalin sunanki, Daga kin amsa mini waɗan nan tambayoyin xan Tashi intafi Cikin ƴan uwana" 


Tsohuwa bata amsa tambayar ba, har sai da ta ɗauki tea pot ta ƙara zuba ruwan shayi a kofi ta kur6a sau biyu, Sannan ta ajiye kofin ta soma magana atsanake,


"Amsar tambaya ta farko, Duk yaron da aka sadaukar agidan kurkukun ƙaddara, Muna bibiyar rayuwarshi ne tun Yana acikin Cikin mahaifiyarshi, Har zuwa lokacin da zata haife shi, zamuyita bibiyar rayuwarshi da zarar yakai shekarun da muƙe buƙatarsa To babu makawa xamu ɗauke shi ne...."


"hakan na nufin tun ina jaririya kuna atare dani? Kenan kune kuke sanyani duk wani mugunta da nake Yiwa daddyna"? Da ruɗu akan fuskarta tayi tambayar, tsohuwa tace"A'a, bamu bane, baƙin aljanine dake atare da mahaifiyarki, Yana matuƙar sonta, Kuma yana da zafin kishi, shine maƙasudin rashin jituwar Iyayenki, Ya tsani Mahaifinki tajudden yaso ya tarwatsa shi, Amma hakan ya faskara saboda Daddnyki mutunne maison yin ibada, bai wasa da azkhar, kuma yana yawan yin sadaka, sannan babbar kariyar dake atare dashi, Yana Yin nafilfilin tsakar dare, A lokacin da benazir ta haifeki, Baƙin Aljani Ya fita daga jikinta ya koma a jikin ki, domin ɗaukar fansa akan mahaifinki, yayi amfani dake wurin ƙuntata mishi, Amma A yanzu Baƙin Aljanin baya atare dake,


Angel fa ta shiga ruɗu, duk da tana kokwanton maganar tsohuwa, Bakasafai Take yarda da zantuttukan ta ba saboda sanin Cewa Ita ɗin Babbar maƙaryaciya ce,


"Kin tambayi sunana, Zaki iya kirana Da TAMIRA Shine Asalin sunana," Tsohuwa Na kai ƙarshen maganarta, Ta yunƙura ta miƙe daga saman Kujerarar, Da sandar hannunta ta nuna ma angel hanyar fita daga ɗakin, batare da musu ba, Angel ta miƙe ta nufi hanyar fita daga Cikin ɗakin Har takai bakin ƙopat fita, Muryar tsohuwa ta dakatar da ita,


"Shawarar Da nake so Na baki, Kada ki kuskura kice zaki Sanya naci akan sai kin gano ainihin ma'anar Kurkukun ƙaddara, domin kuwa daga ranar da kikasan ma'anarshi, Bazaki sake runtsawa ba, Kuma ba zaki sake Jin daɗin abinci ba, duk wani kingin jin daɗi da ya yi saura acikin rayuwarki, Zaki rasa shi ne! Wani irin mummunan faɗuwar gaba angel taji, Har saida ta dafe kinjinta saboda bugun da zuciyarta tayi mai sautin gaske,


Tsohuwa taci gaba da cewa"Ƴan uwanki suna  farin Cikin kasancewarki acikinsu, Saboda Kin kawo musu canji acikin rayuwarsu, Ina fata zaki mayar da hankali wurin faranta musu rai, Amma fa kinsan da sanin duk ranar da kika Binciko ma'anar The destined prison, daga ranar daga ke har su, Zaku fuskanci matsanancin tashin hankali, Kuma daga wannan Lokacin bazaku ƙara Yin tozali da TSOHUWA TAMIRA ba, Zaku yi ta yin gwagwarmayar rayuwa ne atsakaninku, na gargaɗe ki ne saboda Ina sane da duk wani ƙudurinki nasan bin kwakkwafin Gidan kurkukun ƙaddara, Shiyasa na sanar dake irin matsalar da zaki jefa kanki da kuma ƴan uwanki" angel na ƙoƙarin Waiwayowa baya ta kalli tsohuwa taji an ingizata waje, Ƙopar ɗakin ta rufe,


Kamar an jehota ta faɗo ƙasa, Cikin ɗakinsu, har kanta saida Ya bugu, 


Tun daga wannan Ranar Angel tashiga ruɗani, Kalaman tsohuwa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, Tarasa Ina zata tsoma ranta taji daɗi, Kowa Saida Ya lura da canzawar da tayi, Sam tadaina shiga cikinsu, Gani take kamar Dukansu mutuwa zasuyi shiyasa take janye jikinta gudun kada sabon Yayi yawa ta yadda zata rasa kanta idan ta rasa wani acikinsu, Su batool duk sunyi tsammanin rashinsu Parveen Ne yasa ta canza ta shiga damuwa, Kullum cikin Lallashinta suke yi, Akan tayi haƙuri su koma kamar yadda suka ada, Daƙyar suka samu angel ta koma Yi musu wasa da dariya, Harma tana koya musu wasu wasanni donsu farantawa junansu,


Akwana a tashi Yau tsawon Sati Biyu kenan, Ba'a dawo musu da ƴan uwansu ba  Har sun fidda rai da sake ganinsu, tun suna tambayar tsohuwa har sun gaji sun daina, kowa ya zubawa sarautar Allah Ido👀


Yau Tun da Suka tashi daga bacci suke ta jiran a kawo musu abincinsu suci amma shiru giants basu zo ba, Tun safe Har marece, Jikinsu duk Ya yi laushi, azeeza tuni ta fara Yi musu kukan yunwa, Lokacin da dare Ya ratsa hasken ɗakin Yayi duhu, Nan fa suka ƙara shiga tashin hankali ganin zasu kwana basu Ci abinci ba, la66ansu duk sun bushe, Ruwa kaɗai suke tasha tun safe, Cikinsu harya ɗaure, wasu daga Cikinsu hada amanshi su ka yi,


a ƙarshe suka haƙura Da abincin, Kowa Ya hau saman gadonshi ya kwanta, Cikin sa'a bacci ya ɗauke su, Ganin sun nutsa acikin baccin su yasa angel ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6e fuskarta da shi, Saukowa ta yi daga saman gadonta, Sumar kanta duk ta cukurkuɗe kamar ƴar mahaukaciya saboda rashin gyara, Cikin duhu take tafiya tana laluban hanya, Fitila taje ta ɗauko ta kunnata, Tana haske Saitin gadajensu Hannah, ganin babu mai motsi acikinsu Yasa tayi sauri Cikin sanɗa ta nufi sashen toilet ɗinsu, har yanzu bata haƙura da Ƙudirinta ba, Nason fasa gilashin nan, Alwashi ne ta ɗaukarwa kanta Koda zata rasa ranta saita Ga uban me ake aikatawa acikin gidan kurkukun, Duk da tana Jin fargaba akan irin gargaɗin da tsohuwa tayi mata, don a lokacin harta fara tunanin ajiye makaman yaƙinta, amma daga baya sai ta dinga jin tamkar ana tunzurata akan taje taci gaba da jaraba fasa gilashin zata Ci nasara, Zuciya da saƙe saƙe, gani take kamar idan ta fasa gilashin ta dira ta cikin tagar,  zata samu damar zuwa wurinsu deeja ne, Harma ta dawo dasu Cikin ɗakin, Da yake sune damuwarta,


Tana shiga Cikin toilet ɗin, Taja ƙopa ta garƙameta da jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, ta ɗaga hannayenta Sama tana roƙon Allah Ya bata Ikon Fasa Glass ɗin a karo na karshe don daga yau ta sanyawa ranta cewa idan har bata fasa shi ba, ta gama zuwa tana shan wahala, zata haƙura ne,


Bayan ta kammala yin addu'ar, Da ƙwarin gwiwarta ta kai hannu ta rarumi bokitin ƙarfen, Sai da taja da baya ta watsa dagudu ta buga tsalle ta daki glass ɗin Da iya ƙarfinta na karshe, Amma wani abun takaici ko tsagewa Baiyi ba, kamar dai kullum haka taci gaba da bugun glass ɗin da bokitin amma Yaƙi nuna alamar ana bugunsa, saboda tsabar zufar dake tsastsafo mata ajikinta Tamkar wadda aka tsamo daga Cikin teku, Idanuwanta sun rune saboda wahala, Hannunta sai zogi yake yi mata, ga wani irin fitsari daya Matseta, da sauri ta jefar da bokitin gefe ɗaya ya gangara ƙasa, Tasanya hannu ta kwale wandon jikinta, Zuƙunnawa tayi a bakin magudaji tana fitsari, sai da ta kammala taje gaban fanfo tayi tsaki, tana kokarin miƙewa kwatam ta hango mutumin jingine da bango, Ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, Tun kafin ma ta ƙarasa juyawa ta gane kowanene, Sakamakon doguwar sumar kanshi data hango,


Muryarshi ce ta ratsa kunnuwanta,


"Can I give u a hand"? ras taji gabanta ya faɗi, azuciyarta tace"Danishi! Nashiga uku, kada ace ya ga abunda nake ƙoƙarin Yi, wayyo Allah na" rai a6ace ta ƙarasa juyowa tana fuskantar 6angaren da yake atsaye ya jingina bayan shi jikin bango, Rai a6ace ta nuna  shi da yatsa"Wannan wani irin shashanci ne danish? Why zaka dinga faɗo mini Cikin toilet? yanzu da ace na tu6e kaya ina wanka ko ina wani uzirin Shikenan ka gane mini tsiraci na, Wlh bazan ƙyale ka ba" A fusace ta nufi bokitin data jefar ƙasa tasa hannu ta ɗaukeshi Ta daddage ta wurga mashi bokitin, Da sauri danish ya sanya hannayen shi biyu ya cafke bokitin a hannunshi, ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu akan fuskantar,


"Raunata ni kike so Ki yi? A ƙule tace"kashe ka zanyi " Cikin sanyin murya yace"Am really sorry, na kar6i laifina, kada ranki ya 6aci, daga yau bazan sake ba faɗo maki cikin toilet ba," yakai ƙarshen maganar a yayin da ya ajiye bokitin ƙasa, ya ɗago idonshi Yana kallon Tagar da angel ke ƙoƙarin fasawa,


Zaro idanuwanta ta yi ganin yana kallon glass window ɗin da alama yaga abunda take Yi, muryarta na kerma tace"Nasan kaga abunda nake kokarin yi, So nake in fasa gilashin tagar nan, Saboda Ina da matsalar kwakwalwa, Tun lokacin da ina agidan daddyna kafin zuwana kurkukun nan, Na fasa gilassai bila adadin saboda Ni idan nayi tozali da gilas tsoro Yake bani, kuma hakan yana jaza mini matsala, Likita ma yace Idan ina yawan zama inda ke akwai glass zan Iya mutuwa" angel sarkin wayau, idanuwanta cike tab da kwalla takai karshen maganar, hada marairaice mishi fuska don Yaji tausayinta, ya kuma yarda da maganarta,


Danish bai kawo komai aranshi ba, har cikin zuciyarshi ya yarda da kalamanta,   matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi  biyu ya tallabo fuskarta, Idanuwan su acikin na juna, Cikin sigar lallashi yace"Am sorry angel,   don't cry pls, da kin faɗa mini tuntuni da na jima da sauke miki gilashin," ta6e baki tayi tare da cewa"Ae bazaka Iya ba, ko Ni nasha gwada cirewa amma na kasa, kullum saina sha wahalar," ta fadi hakanne don tasan Cewa danish bazai Iya ba, ita kanta da take da ƙarfi ta jaraba ta kasa balle shi da yake sai a hankali ba ƙoshin lafiya ba,


"xan jaraba in gani idan zan iya," yakai karshen maganar yana tattara hannun rigarshi, da sauri angel ta ɗauko mashi bokitin ta miƙa mashi, bakinta ƙumshe da dariya So take yasha wahala kamar yarda ta sha, Shima Yaji ajikinshi,


Girgiza mata kai yayi"bana buƙatar yin amfani da bucket, I will use my hands" dariyar rainin wayau angel tayi mashi"wlh bazaka Iya ba, Da hannu fa ka ce, haba dai, kai dai ka kar6i Bokitin inga iya ƙarfin ka," Bai saurareta ba, Ya tunkari Glass window din, Da yake Allah yayi shi da tsawo, Yafi angel tsayi ba sai yasha Wahalar yin tsalle ba kamar yarda take yi, Agaban tagar ya tsaya yana kallonta,


Angel ta ruƙe qugu, Tana jiran ganin Ikon Allah, Fuskarta ɗauke da dariyar mugunta,


hannayen shi biyu ya sanya yana shafa Jikin glass ɗin da ya yi uwar ƙura, ƙasan glass ɗin Ya ruƙo da yatsunshi, Ƙura ido angel tayi ganin glass ɗin kamar ya fara motsi, Gabanta ne ya faɗi ganin Danish ya daddage Ya 6a66ako glass ɗin tun daga tushen shi can cikin ginin dutsen da aka zura shi, Haka ya zaƙulo shi gaba ɗaya ya curo faskeken glass ɗin, Tashin hankalin da ba'a sama shi date, 


Kanta Ya gama ɗaurewa, Ta zazzaro idanuwanta waje, kwayar idon kamar zata faɗo ƙasa saboda tsabar mamaki, Gaba daya tabi ta ruɗe ta rikice, Tarasa bakin magana sai bin shi da ido take yi kamar wadda aka dasa ma Aya,


A ƙasa Ya jingine glass ɗin Jikin bango, Ya ɗago yana kakka6e tafin Hannayenshi da ƙura ta buɗe su, A wani slow Ya juya bayan shi Yana kallon angel dake atsaye Ko motsi bata Yi, Ta ƙame kamar abun bautar ƙasar india wato kirishna,


Cikin sanyin mirya ya ambaci sunanta"Angel"? Shiru bata amsa mashi ba, domin kuwa sam bata acikin hayyacinta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya dafa kafaɗunta,


"Meke faru ne? Maimakon inga farin Ciki akan fuskarki, Ko baki ji daɗi bane? Na sauke maki glass ɗin, daga yanzu kin daina shan wahalar bugun shi da bokiti" shi kaɗai yake ta maganarshi, kwata kwata bata a hayyacinta, hura mata iska Yayi asaman fuskarta da bakinshi, Amma ƴar tahalikar nan ko ƙyata idonta bata yi ba, Janyota yayi zuwa jikinshi Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, Ya sanya hannunshi abayanta yana shafa sumar kanta, kafin ya matso da lips ɗinshi saitin kunnanta yayi mata raɗa"angel, faɗa mini meya faru? Ko kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet ɗin gaba ɗaya, yadda bazaki sake ganin shi ba? Jin taƙi yi mishi magana, ya raba jikin shi daga nata, Ya nufi gaban fanfo  Ya kunna ruwa ya ɗebo a tafin hannunshi, Ya dawo inda take atsaye kamar gunki, Ya watsa mata ruwan saman fuskarta, Nan take Taja dogon numfashi, har wani zabura tayi ganin shi agabanta, a ruɗe ta wurga idanuwanta kan tagar, Tayi tsammanin ko mafarki take Yi, amma sai taga akasin Hakan dagaske dai Danish Ya cire Glass ɗin tagar da take ta shan wahalar son fasa shi, Tsawon kwanaki, Lamarin Yayi matuƙar ɗaure mata kai, yadda har ya iya 6a66ako shi tun daga tushen shi ya zaro shi, Wanda Tayi imanin Babu wani mahaluƙin da zai Iyayin wannan aikin hakanan siddan ragadan batare da Akwai wani shiri atare da shi ba, Tsohon ginine fa kuma na dutse, A yanayin fuskarta baka iya gane halin da take Ciki, Ta yi farin Ciki da cire glass din da Danish Yayi ko kuwa batayi ba? Tabbas tayi fari ciki  mara misaltuwa sai dai mamaki Ya hana ta nuna wannan farin Ciki, Ayanzu ta ƙara zargin cewa danish Ba shi kaɗai bane, Kuma ba wani ke sarrafa shi  ba, tunda da ace wani ke sarrafa shi da baza a bari Ya cire glass ɗin nan ba, ganin irin kallon da take Yi mashi ne yasa shi ruƙo hannunta acikin nashi yace"Angel baki bani amsa ba, kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet din"? kamar wata sakarya haka take binshi da ido, sai da ya sake maimaita maganar tukunna ta iya bashi amsa da cewa"Inaso ka maida shi yadda ka ciro shi, Kaga duk lokacin dana shigo cikin toilet ɗin sai in zaro shi in kawar dashi wani wurin yadda bazai iya yin affecting ɗina ba" amsa mata yayi da toh, Ya juyawa ya nufi inda ya ajiye glass ɗin Ya ruƙo shi ya shiga kiciniyar mayar dashi, Bayan Ya kammala Ya juyo yana kallonta a lokacin Ta  juya baya tare da ranƙwafawa Ta ruƙo hannun fitilar da tazo da ita, ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi, Daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tasakar mishi, muryarta na rawa tace


"Nagode sosai danish, you're so kind, ka damu dani kuma kana bani kulawa, miƙa mashi hannunta tayi"Zo mu koma ɗaki mu kwanta, Dare yayi sosai," ƙarasawa danish yayi inda take atsaye ya zura hannunshi acikin nata, ta ruƙe sosai tana faɗin"pls keep it under wraps, saboda bana so kowa Yasan cewa Mun cire glass ɗin nan kaga tsohuwa za ta yi mana faɗa idan taji awurin wani, koba haka ba" ɗaga mata kai yayi alamar eh, tare da cewa"I will zip my lips, daga ni sai ke," Cike da jin daɗi tace"Mu biyu kaɗai muka sani, Idan naji maganar awurin wani To kaine, duk da nasan bazaka faɗa ma kowa ba," Ba ƙaramin daɗi danish yaji ba ganin yadda take ta fara'a saboda Ya cire mata gilashin dake Sanya mata jin tsoro, yayin da ita kuma angel ɗin Shine abun tsoro awurinta, don kuwa ga dukkan alamu Akwai wani abun al'ajabi attare dashi, 


Kusan atare suka duro da ƙafafuwansu Cikin ɗakin nasu, Adai dai Lokacin kunnuwansu suka soma Jiyo musu motsin buɗe ƙopar ɗakinsu, Mamaki ƙarara akan fuskarsu suka kai idanuwansu saitin benan dake a ɗakin, daga saman matattakalar benan suka Fara kallon ƙafafuwan Mutun Uku dake saukowa, masu sanye da jajayen Uniform, daga  bayansu Kuma Giants ne Hannayensu a ruƙe Da Kayan abinci......shin su wanene?  


(Mu haɗu next page In allah yakaimu da rai da lafiya) Masu bibiyar kurkukun ƙaddara Like and Comment,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post