Kurkukun Ƙaddara page 30 Complete

Kurkukun Ƙaddara page 30 Complete

 

kurkukun kaddara

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Dedicated to Aunty Kubra❤


Daga alƙalamin boss Bature writer of Abban sojoji


E29


Tun da batool ta soma magana angel ta natsu tana kallonta, acikin zuciyarta tana Jinjina Ma batool, Yarinyar akwai tawakalli, Tana da hankali da tunani, Allah yayi mata baiwar iya sarrafa harshe wurin tsara kalamai masu kwantar da hankali, Haƙiƙa Iyayensu sunyi babbar asara Na rashin ya'ya kamar su, 


"Angel kinyi shiru baki ce Komai ba, Ina ta surutu Ni kaɗai," ajiyar zuciya angel ta sauke tare da kallon Batool tace"Am sorry Sister, naji maganganunki, sunyi mini daɗi sosai  kuma in sha Allahu,  zamu yi hakan, Zamu haɗa hannu wurin sama ma kanmu farin ciki,"


Muryar azeeza ce ta katse su da cewa"Wai har yanzu ba'a dawo mana dasu parveen ba? Jiya har mafarkinsu nayi," saukowa tayi daga saman gadon ta nufi su angel dake a tsaye ta ruƙe qugu tana kallonsu,


"Ba'a dawo dasu ba Azeeza, Mu ƙara haƙuri zuwa anjima may be Giants su kawo mana su" Batool ce ta bata amsar tambayarta,


Ta6e baki azeeza tayi  tare da cewa"Ni dai indai ba'a dawo mana dasu ba, Bazan ƙara Cin abinci ba" maganartace ta basu dariya, 


Sauran ƴan uwansu dake bacci ɗaya bayan ɗaya suka dinga farkawa, duk wanda ya buɗe ido saiya tambayi su deeja,  Angel da batool ne ke kwantar masu Da hankalinsu akan su ƙara haƙuri zuwa anjima, lokacin da kowa Yayi wanka, Suna a zazzaune saman gadajensu, Sai ga giants sun shigo kawo masu abinci, Bayin Allah duk sunyi tsammani za'a zo masu da ƴan uwansu amma sai suka ga akasin,


Koda suka koma saman dining carpet domin Cin abinci, saboda damuwa, kaɗan suke tsakura suna ci ba don suna jin daɗin abincin ba, Angel hada ƙoƙarin mikewa taje karkashin gadon batool ta ɗauko kwando, tazo tana kwashe kingin abincinta, Yasmin tace"meyasa ba zaki ci ba? Bafa Ki ci dayawa ba'? Angel tace"su parveen zan ajiye mawa, kada su dawo da yunwa anjima, Jin abunda tace ne yasa suma suka rage sauran nasu abincin don a ajiye ma su parveen, angel ta kwashe duka cikin kwandon, Taje ta 6oye a karkashin gadon batool,


Bayan tafiyarsu Giants, Hanna ta basu shawarar su motsa Jiki Ko sun samu Lokaci yayi saurin wuce wa duk don saboda tsammanin za'a dawo masu da ƴan uwansu yau, bayan sun kammala motsa Jikin nasu  Kowa Ya gaji sai uwar xufa ke tsastsafo masu, A dole suka je toilet kowa ya watsa ruwa a jikin shi, ba ƙaramin ɗaɗi suka Ji ba, saman gadajensu suka koma kowa Ya hau ya zauna fira suka soma yi atsakanin su, wani irin bacci ne yazo ma angel batare data shirya mashi ba, dama jiya ana binta bashin baccin da batayi ba, gyara kwanciyarta tayi asaman gadonta, tare da jan bargo ta lullu6e kanta, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita, 


*ANEELERH*


Almajirai ne daddabe a gaban motarta, sunyi dandazo suna jiran Ta basu sadakar kuɗi kamar yadda ta saba basu a duk lokacin da tazo zata wuce ta wurin makarantar allonsu, Sai faman zumuɗu almajiran suke Yi, Kayan Jikinsu duk sun yayyage, kowannan su na aruƙe da kokwan bararsa,


Zuge glass ɗin motar ta yi, almajiran sai kallonta suke yi, tana a zaune saman driver seat, Jikinta na asanye da atampa, riga da skirt sunbi shape ɗin jikinta, Ta yafa mayafi akanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Yayin da baby junaid ke akwance saman passenger front seat, Kayan sanyi ne ajikinshi sunyi matuƙar yi mashi kyau, baccin shi yake yi hankali kwance, ga wani irin ƙamshi dake fita ajikin shi,


Ƙoƙarin Zaro kuɗi take Yi acikin ƴar purse ɗinta Bendir guda ta ciro na ƴan ɗari biyar biyar, zarowa ta dinga yi tana miƙa ma almajiran, Sai murna suke yi, suna kai hannu suna karba tare da yi mata addu'o'e Sai da ta kammala raba masu, tana yunƙurin Zuge glass ɗin motar, taga an zuro mata hannu, ras taji gabanta ya faɗi ganin hannun babban mutun sanye cikin baƙar safa,


Da sauri ta kalli fuskar mutumin, ya sanya Mask a fuskarshi, Baƙaƙen kaya ne ajikinshi, bakomai ya faɗo mata araiba face mutumin da ya Ɗauke mata baby junaid ɗinta lokacin da taje gidanta, nan take gabanta yyi mugun bugu, A tsananin tsorace ta shiga kiciniyar zuge glass ɗin motar, ganin zata datse mashi hannu yasashi yin saurin zame hannunshi 


Key tayi ma motan hannunta na kerma  ta ruƙe steering da wani irin speed ta fusgi motar da gudu ta haura saman titi tana ambaton"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" tarasa ina zata dosa, saboda tsabar ruɗi, Gani take kamar mutumin yana abiye da ita, ashe dama bibiyar rayuwarta yake yi?  Tayi tambayar acikin zuciyarta, Marece ne sosai Tana kokarin shan kwana, muryarshi ta ratsa kunnata"Baki bani sadakar ba" a gigice taja burki ta tsayar da motar,  idanuwanta azazzare ta ɗago tana kallon shi ta cikin Rear view mirror ɗin motar,


Mutumin Yana a zaune Cikin back seat na motar, a hakimce,


Tayi matuƙar razana ganin shi acikin motarta, taya akai ya shigo bayan ta rufe motar, Anya kuwa mutunne ba aljani ba? muryarta na rawa tace"dan..dan Allah na roƙe ka, kada ka cutar damu, bansan wanene kai ba, ban kuma san laifin da nayi maka ba, ka faɗi kome kake so zanyi maka shi" idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,


"Kome nake so zaki yi mini"? Ya yi tambayar yana kallonta, a tsorace tace"Eh, wlh zanyi"


Ya amsa da "Okey, " hannu taga ya zura cikin aljihun wandon Jikin shi ya lalubo wayarshi, Ya ɗan daddana ta kafin ya miƙa mata wayar"Location ɗin nan zaki bi, " batare da musu ba ta kar6i wayar tashi, idonta akan google map ɗin daya buɗo mata, daga gefenta ta ɗaura wayar, Ta ci gaba da driving tana bin location ɗin, yayin da zufa ke tsastsafo mata, zuciyarta a firgice take da tsoron inda zai kai su, Wayar shi kanta abun tsoro ce saboda ta banbanta da sauran wayoyin da ta saba gani, Babu sunan Company ajikin wayar,


Dogon titi suka Miƙa sham6al har zuwa cikin wata area, Ta jigunannun masu kuɗi, Manya manyan gine gine, Unguwar shiru babu yawaitar mutane acikinta, a bakin wani katafaren Gida ta ƙaraso da motar, yace tayi horn ta danna horn nan take Wagegen gate ɗin gidan Ya zuge awani slow, kutsa motar tayi acikin gidan, har saida ya bata umarnin ta tsayar da motar tukunna ta tsaidata, 


Buɗe murfin motar yayi tare da fitowa ya zagaya other side ɗin da junaid yake a kwance, Ya buɗe motar ya zura hannu ya ɗauke shi, Aruɗe aneelerh take kallon shi, ganin ya ɗaukar mata yaro,


"Let's go in" yayi maganar yana nuna mata hanyar zuwa cikin gidan, Jiki asanyaye ta buɗe motar ta fito tabi bayanshi, Wa'iya zubilla Ta yi matuƙar girgiza da ganin kyawun gidan ya tsaru iya tsaruwa kai kace ba'a 9ja yake ba, Duk da a tsorace take hakan bai hanata bin ko'ina da kallo ba, suna ƙarasowa bakin glass door ta falon gidan, Muryar na'ura ta karaɗe kunnuwansu, wani abun mamaki daya ɗaure mata kai, na'urar da ta soma magana tana sanar da zuwan su, sai da ta faɗi Cikakken sunan aneelerh, wato Aneelerh muhammad falgore, Ras taji gabanta ya faɗi, a karshe na'urar tace"you're permitted to come in" nan take ƙopar glass ɗin ta zuge,   


Mutumin yace mata su shiga Ciki, ta zura kafarta acikin katafaren falon, Tsayawa faɗar irin kyawunshi 6ata baki ne sai wanda ya gani, wani irin sanyin a.c ne ta ko'ina, Komai na Cikin falon White Colour ne atsaftace yadda kasan ba'a ta6a amfani dashi ba, saboda kyawunshi da sabuntakar furniture ɗin dake acikin shi,


Miƙa mata Junaid Ya yi, da sauri ta sanya hannu ta kar6eshi, ta rungume shi ajikinta, A saman Sofa 3 seater Ya bata Umarnin ta zauna, xama tayi tana faman baza ido, Jira take taga me za ayi mata, Acikin zuciyarta sai addu'o'in neman tsari take karantowa,


Takun takalma ta soma ji daga can saman twin stairs ɗin dake a falon, a hanzarce takai idanuwanta wurin tana kallonsu, waro ido waje tayi Jikinta ya shiga 6ari ganin Gabza gabzan Mazan dake saukowa saman benan, kowannansu na asanye Cikin shiga ta baƙaƙen kaya, A ƙalla sunkai su takwas, bakwai Suna a left hand na benan, Yayin da mutun ɗaya ke tafiya  atsanake ta right hand ɗin stairs ɗin 


Kusan atare suka sauko daga saman benan, Aneelerh bata Iya ganin komai na Jikinsu ba, Gaba ɗaya sun rufe kansu daga ƙasa har sama Cikin black dress, Dogayen riguna na maza masu haɗe da huluna kamar alkebba, Guda bakwai ɗin suka Ƙame a tsaye tare da goya hannayensu saman ƙirjinsu, shima wanda ya kawota gidan Yana a tsaye gefen hand sofa ɗin da take a zaune Ya ƙame kamar yadda sauran su ka yi 


Mutum ɗayan nan daya rage, shine Ya zauna saman sofa 2 seater, Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya, aneelerh fa tasha jinin jikinta, sai faman ƙanƙame junaid ta ke yi ajikinta, Yaro sai bacci yake yi baisan halin da Mommynsa ke ciki ba, 


"Ki natsu Ki saurari maganganun da zamu tattauna dake, mintina ƙalilan zamu salleme ki ki tafi" Na gefenta ne yayi maganar, wanda suka zo tare da shi,


Jin haka yasa ta daidaita natsuwarta, ta kasa kunne tana jiran Jin me zasu Ce, wanda take tunanin shine team leader ɗinsu, wanda ke zaune saman Sofa 2 seater akanshi ta tsayar da idanuwanta, wata irin ƙirar ƙarfi ce gare shi, taban al'ajabi, mai matuƙar jan hankali da tsoratarwa, kai daga ganin wannan babu wasa acikin lamuranshi, baƙaƙen kayan sun zauna mashi sosai, sun bayyanar da zazzafar surarshi, tayi tunanin shi zai yi mata magana amma sai taji yayi shiru,


Takun tafiya ta kuma jiyowa ta can 6angaren, Wani ƙaton ne Ya fito sanye da bakaken Kaya, Hannunshi a ruƙe da plate me ɗauke da Glass Cup, ruwan sanyi ne aciki, a saman table ɗin dake a kusa da sofa ɗin da aneelerh ke a zaune ya ɗaura plate ɗin, Cikin girmamawa yace mata"Zata iya sha" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya bar falon, duk fa waɗannan Garadan mazan na a kewaye da ita, Da farko taji tsoron tasha kada ace An sanya mata wani abu, amma daga baya saita kai hannu ta ɗauka ta ɗan kur6i ruwan, sanyi gare shi ga daɗi, bayan ta ajiye Glass ɗin, Sai ga wannan katon daya kawo mata ruwa, Ya dawo Cikin falon hannunshi ruƙe da Laptop Tsadaddan gaske, Adai dai gaban aneelerh Ya ajiye laptop ɗin saman table gefen plate ɗin da ya kawo mata ruwa,


Daddana laptop ɗin Ya shiga yi Cikin ƙwarewa, Aneeelrh dai ta zuba ido tana jiran ganin me za'a nuna mata,


Bakomai bane Ya bayyana akan screen ɗin Laptop ɗin nasu, Face Hotonsu da su kayi ranar birthday ɗin Angel, Su Huɗu, Angel ce a tsakiyarsu, Taj yana agefenta ya zuƙunna, Aneelerh da Uzair Suna atsaye fuskokinsu ɗauke da murmushi,


Tsananin mamaki ne ya kama Aneelerh ganin wannan hoton, duk da tasan Zasu Iya samun shi a social media, saboda sunyi share ɗinshi a insta da Facebook, twitter da tiktok, hada videos na birthday ɗin angel,


"Kin gane su"? Muryar mutumin ce ta katse mata tunaninta, da sauri tace"Eh, ƴan uwana ne," ya nemi ta yi masu bayanin menene alaƙarta da su" da hannu ta nuna mashi hotonta dana uzair tace mijina ne, wannan kuma ɗan uncle ɗin shi ne, Sunan shi Tajuddeen, Ita kuma yarinyar Ɗiyarshi ce, sunanta Unaisa amma muna kiranta da Angel,'


Jinjina kai ya yi tare da cewa"Mu jami'ae ne masu zaman kansu, muna da interest akan case ɗin 6acewarsu, that's the reason why muke Bibiyarki, saboda sanin cewa ke kaɗaice zaki Iya bamu bayanan da muke so, Zamuyi maki tambayoyi, da zarar kin amsa mana zamu sallame ki ki tafi, kuma bazaki sake ganin mu ba," ta amsa ma shi da toh,


Tambayoyi suka shiga yi mata, tun daga kan alaƙar dake tsakanin su tajuddeen da Uncle abdallah har izuwa kan Alhaji ubaid, da ita kanta hada iyayenta duka saida su ka yi mata tambayoyi a dangane dasu, hatta Benazir sai da suka yi mata tambayoyi akanta, duk ta amsa masu wanda ta sani, abunda ya ɗaure mata kai hada ƙawarta Aisha suka Yi mata tambayoyi akanta, game da yarda akai mahaifinta yayi mata korar kare daga gidan shi, Lamarin ya ɗaure ma aneelerh kai, taya akai suka san kowa da take atare da shi? Su wanene waɗannan jami'an masu Uniform baƙaƙen Kaya, Taso ta tambayesu daga ina suke, amma sai suka ce mata, basu bata iznin tambayar komai agame dasu ba, Sannan suka ce ta sawa ranta cewa a mafarkine Ta haɗu dasu, kada tayi tunaninsu kuma kada ta kuskura ta yi gigin faɗa ma wani agame da su,


 bayan sun kammala Yi mata tambayoyin har bakin motarta suka rakota, ta buɗe ta shiga, suka yi mata godiya taja motar ta fuce daga Cikin gidan, Tana cikin yin driving saman titi Junaid Ya farka yana ta tsala kuka, a dole ta kashe motar daga gefe ɗaya ta rumgumo shi ajikinta tana lallashinshi, yace mata Yunwa yake Ji, ta bashi abinci yaci," tunawa da madararsa da ta ajiye mashi a backseat na motar yasa ta juya ta kai hannu ta ɗauko mashi ita, acikin bottle take, ta cire murfin ta kafa mashi abaki yana sha, yayin da ta shiga zurfin tunani, abun ya tsaya mata aranta, ita gaba ɗaya rayuwar duniyar tsoronta take ji, meya faru dasu uzair? Shiru ba labarinsu kusan shekara huɗu? Sannan ga wasu mutane suna Bibiyar rayuwarta da sunan jami'ae ne, Anya kuwa bazata gudu tabar ƙasar nan ba, na wani lokaci? Gani take kamar zata rasa ɗanta ne, kamar yadda ta rasa mutun ukun nan masu mahimmanci, tana cikin yin wannan xancen zucin junaid ya fashe da kuka yana faɗin"tasa mashi madara a hanci," da sauri takai idonta kanshi, fuskarshi ta 6aci da madarar, batasan ya akai ta janye robar daga bakinshi ba ta kwafa mashi a hancin shi, rufe bottle ɗin tayi tare da ajiyeta gefe ɗaya, ta zaro hanky cikin ƴar purse ɗinta ta shiga goge mashi madarar, bayan ta kammala ta maida hanky a cikin purse ɗin, Ta rungumeshi ajikinta tana lallashinshi, har saida yayi shiru lamo ajikinta tukunna ta tashi motar ta miƙi hanya ta nufi gida,


Lokacin da ta koma Gida, a palour ta taras da Mami  da wasu ƙawayenta suna fira, sai da ta fara gaishe su, suka amsa mata, tare da miƙa mata hannu ta  basu junaid, Ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, tana shiga ta rage kayan jikinta ta faɗa toilet tayi wanka, ta fito waist ɗinta a ɗaure da towel tana kokarin zama saman mirror chair,  alert ya shigo Cikin wayarta dake ajiye saman mattress, da sauri takai hannu ta ɗauki wayar, kamar a mafarki take ganin credit alert ɗin da aka turo mata via dollar account ɗinta, wanda a  kuɗinmu na nigeria kuɗi ne bana wasa ba, har saida ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, ta shiga ruɗu akan wannan kuɗin da aka turo mata, bayan ita ba wanda ta ba acct number ɗinta, Shi kanshi dollar account ɗin ta jima bata yi amfani dashi ba, 


Komawa ta yi gefen gadonta ta zauna hannunta ruƙe da wayar tana kallonta, wani saƙonne ya kuma shigowa cikin wayarta, cikin harshen turanci aka rubuto shi, karantawa tayi kamar haka


_mun gode da haɗin kan da kika bamu_


Nan take ta gane cewa Jami'an nan ne suka Turo mata da kuɗin, ajiyar zuciya ta sauke tare da jefar da wayar saman pillow, Ta gyara kwanciyarta saman mattress ɗin, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta a cunkushe take da tunani kala kala duk akan Jami'an nan, Su kuma ko daga ina suke? Waye ya sanya su bibiyar case ɗin su tajuddeen? amma tasha ruwan mamakin Irin Ƙirar jikinsu, especially wannan ɗayan daya zauna saman sofa wanda take tunanin shi ne team leader ɗinsu, Kamar shi ya ƙera kanshi, daga gani dai jami'ae ne su bana wasa ba, ita dai fatanta Allah ya tabbatar da alkhairi akan bincikensu dana su Uncle bash,


Ta yi zurfi acikin tunaninta, tajiyo muryar baby junaid yana faɗin"Mommy kizo inji mami, " daga kwancen da take ta juya tana kallonshi, ya ruƙe qugu abakin ƙopar ɗakin, yana ta faman zumbura baki yace"Bake kika sanya mun madara a hanci ba, ae na faɗa mata, tace zata rama mini" 


Yadda yayi maganar ne ya bata dariya, har fararen haƙoranta suka bayyana, Miƙa mashi hannu tayi"zo nan My baby boy" maƙe kafa ɗa yayi"Ae baki sona, Tunda kika sanya mun madara a hanci," saukowa tayi daga saman gadon ta wuce wurin closet ɗinta, Jallabiya ta ɗauko ta zura ta ajikinta, kafin ta dawo ta nufi inda yake a tsaye, ta zuqunna agabanshi tare da kai hannu tana shafa sumar kanshi tace"My baby boy, nifa mommynka ce, ni na haife ka, bani da tamkarka aduniyar nan  inasonka fiye da kaina, jinka nake kamar bugun zuciyata,' takarasa maganar tare da sanya hannu ta ɗauke shi, kafin ta mike ta wuce cikin falon,


A lokacin ƙawayen Mami sun tafi, A zaune ta same ta saman Sofa, Riga bubu ce a jikinta, idonta na akan plasma tv, tashar arewa 24 take kallo 


Takun tafiyar aneelerh ne ya janyo hankalinta, ta juyo tare da kallonta, fuskarta asake tace"My daughter Kinyi mana laifi, Junaid ya faɗa mini abunda kika yi mashi acikin mota, ashe dama shirin kashe shi ki kayi"? cikin zolaya tayi maganar, Fuskar aneelerh ɗauke da murmushi tace"Kuskure ne mami bansan nayi mashi haka ba, kuma fa har hakuri na bashi amma shine bai kar6i uzirina ba," takai karshen maganar a yayin da take zama saman Sofa tare da junaid, Ya manne ma jikinta, 


Kallon shi mami tayi"ka yafe mata ko in rama maka"? Ashagwa6e yace"nayi mata amma idan ta ƙara, afaɗa ma uncle bash ya sanya gun ya harbe mata kai," gaba ɗaya suka kwashe da dariya aneelerh tace"amma baka da mutunci junaid, uwar taka zaka sa a harba da bindinga? Idan na mutu ya zaka yi"? Watsa hannu yayi tare da cewa"Shikenan, sai aje kasuwa asiyo wata uwar" tuntsirewa su kayi da dariya, mami tace"Aku sarkin ɗumi, Kwanan nan xan sanyaka makaranta, tun da bakinka ya buɗe, ga surutu" Aneelerh tace"nima tunanin da nake yi kenan, ko islamiyace a fara sanya shi yana zuwa kafin asanya shi ta bokan," fira suka cigaba da yi har baby junaid yayi bacci a jikinta, aneelerh bata fada ma mami game da abunda ya faru da ita ba, kamar yadda jami'an suka gargaɗeta akan ta manta da komai nasu ta ɗauka tamkar mafarki tayi shiyasa taja bakinta tayi shiru gudun kada taja ma kanta,


*Back to Prison* pls Follow my tiktok account👇

tiktok.com/@boss_bature

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post