BLOOD GROUP YANA IYA HAIFAR DA ILLAR DA TAFI TA GENOTYPE GA WADANDA ZASUYI AURE.

BLOOD GROUP YANA IYA HAIFAR DA ILLAR DA TAFI TA GENOTYPE GA WADANDA ZASUYI AURE.

Blood Group

 Hussain Sulaiman Salihu ✍️

Sau da yawa ana mantawa da gwajin kalar jini wato blood group lokacin da ake gwaje-gwaje kafin aure,( ana gani kamar bashi da wani illa idan ba’a yi ba. 

Sirrin yana jikin mata musamman, wanda idan ba’a yi sa’a ba shikenan mace idan ta haifi dan fari, to bazata kara haihuwar yaro mai rai ba har abada idan har ba ta auri miji mai irin kalar jininta ba.

Sau tari muna jin labarin wasu mata, wadanda suka haihu da farko, daga nan kuma sai suyi ta yin 6arin cikin da zasu samu a gaba, sakamakon haka, bazata sake samun cikin da har zai kai lokacin da za’a haife shi ba.

A shekarun baya, ana alakanta hakan da aikin mayu, musamman kafin a samu wayewar ilimin kimiyyar lafiya, ta haka sai a qalawa wasu sharri a unguwa ace ai sune mayun da suke cinye mata da, har hakan ya sanya a tsane su a Unguwar.

YAYA ABIN YAKE FARUWA??

Akwai kalar jini da ake kira da “O negative” (O-), duk wanda yake da wannan kalar jinin, to dole sai mai irin shi ne zai bashi jini idan bashida lafiya, ko O positive(O+) bazai iya bashi jini ba, saboda shi mai O positive yana dauke da wani sinadari da ake kira da Rhesus a cikin jinin nashi, shi kuma O negative bashida shi, to duk lokacin da aka bawa O negative jinin da yake dauke da wannan Rhesus din da yake cikin jinin masu O positive, sai jikin su ya samar da wani tsaro, saboda zai dauki jinin a matsayin wata cuta da ta shiga jikin shi.

To hakane yake faruwa lokacin da namiji mai kalar jini O positive ya auri mace mai kalar jini O negative, idan suka samu juna biyu, kuma yaron cikin ya gaji kalar jinin uban nashi, to dole jinin uwar da na yaron cikin zasu hadu a cikin ta, ta haka sai tayi kamar wadda aka karawa jini kalar O positive, sai ta samar da wannan tsaron(antibodies), wannan tsaron sai yayi kokarin lalata jinin yaron.

Amma cikin ikon Allah, tsaron da ake samarwa a cikin farko bashida yawan da zai iya kashe yaron, amma dai yaron zai iya

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post