Kurkukun Ƙaddara episode 63 complete

Kurkukun Ƙaddara episode 63 complete

 

Chapter 63 kurkukun Ƙaddara

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E63


By Boss Bature


sakin bargon Angel ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi gadon jamima, hannu tasa tana duba fuskarta itama babu jini, tunawa ta yi da haƙorinta data gani ɗazu a ƙasan ɗakin su, koda ta buɗe bakin ta, tabbas haƙorin ta ɗaya ya cire, sai dai babu kumburi abakinta, lamarin ya ɗaure mata kai, mamaki ne ƙarara akan fuskarta.


 matsawa ta yi zuwa gadon Azeeza ta yaye bargonta tare da leƙa fuskarta, ko hawaye babu, yatsun hannayenta dai ne da suka faffashe, amma babu jinin daya tsastsafo akansu, idan ka kalli ciwon kamar ya kwan biyu. 


Ɗaya bayan ɗaya saida Deeja tabi kowannan su ta duba shi, lafiyar su ƙalau, Babu ko zazza6i a jikin su.


Deeja ta ruɗe sosai ta rasa tunanin me za ta yi game da wannan iko na Allah, har aranta ta aminta da cewa Allah ne ya ji ƙansu ya kawo musu ɗauki, sai dai ba ta san takun tafiyar wanene taji ɗazu ba, a cikin ɗakinsu, tabbas akwai wanda ya shigo.


"Ruwa zan sha, maƙoshi na zafi"! Muryar Angel ce ta fargar da ta, a hanzarce ta mayar da dubanta gare ta, farkawarta Kenan daga bacci, Ko idonta bata buɗe ba, a gaggauce Deeja ta nufi ƙarƙashin gadon Batul ta ɗauko ɗaya daga ciwon bottle waters ɗin da Su Jamima suka 6oye musu ɗazu, ta nufi gadon Angel ta haye sama tare da taimaka mata ta miƙe zaune, bayan ta buɗe murfin ta kafa mata abaki, ta dinga kur6ar ruwan,' 


Hankalin Deeja ba ƙaramin kwanciya yai ba, bayan ta kammala ta maida murfin robar ruwan ta ajiyeta daga ƙasan gadon, kafin ta ɗago idonta akan fuskar Angel dake ƙoƙarin buɗe nata idanuwan.


 Ido cikin Ido suke kallon Juna ita da Deeja, muryarta na ɗan rawa ta furta"Ina Danish ya ke"! Abunda ya fito daga bakinta kenan, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa ta amsa mata da cewa"Har yanzu ba a dawo dashi ba" girgiza kai Angel ta yi"ba'a dawo dashi ba, meyasa naji a jikina cewa danish ya ta6a ni!" A ruɗe Deeje ke kallonta, Jin abunda tace, tunani ta shiga yi anya Angel bata samu ta6in hankali ba? 


Da alama ta manta abubuwan da su ka faru, ta manta jahilin bugun da tayi musu, kamar wadda tayi loosing memory ɗinta.


Ganin yadda Deeja ta tsareta da ido yasa tace"meyasa kike kallo na? Wani abu ya faru ne? Nayi ma ki tambaya baki bani amsar da zata gamsar dani ba, nifa naji Danish Ya ta6a jikina, taya zaki ce min ba a dawo dashi ba'? A ruɗe ta yi mata maganar.


Deeja bata amsa mata tambayarta ba, saima ta sanya tafin hannayenta biyu ta tallabo fuskar Angel, murmushin yaƙe ne ya bayyana akan fuskarta wanda bai kai zuci ba, a hankali ta furta Alhamdulillah, Allah na gode maka, daka kawo min mafita, da yanzu bansan ya zan yi ba, Naji daɗi dana ga ƴan uwana suna bacci cikin kwanciyar hankali, na ƙara yarda cewa addinin musulunci gaskiya ne, Kuma ubangijin mu Allah maji roƙon bayinsa ne, idan su ka yi imani dashi, babu tantanma zai agaza musu a lokacin da suke cikin buƙatar taimakon shi.


da alama taji daɗi sosai, da irin taimakon da Allah ya yi musu, daba don haka ba, da yanzu batasan awani awani hali zasu tsinci kan su ba, domin kuwa ba ƙaramin jiki zasu ji ba, Jinya ce zasu yi bata wasa ba, sai kowa yaji a jikin shi, musamman Jamima da haƙorinta ya 6alle, da kuma Sarah wadda aka buga ta da ƙasa qugunta ya daku, da sauran waɗanda aka buga kansu jikin bango.


"Deeeja na kasa fahimtar komai, dan Allah ki yi min bayani, inaso inji meya faru ne, naji araina kamar wani abu ya faru, sai dai na kasa tunawa......" da  sauri Deeja tace"in sha Allah ba za ki tuna ba"


 Maganar Deeja ta ɗaure mata kai, yunƙurin saukowa tai daga saman gadonta, da sauri Deeja ta ruƙo hannunta"Ina zaki je? Dare ne fa! Ki koma ki kwanta" ba tare data juyo ta kalle ta ba, tace"Toilet zan shiga" Jin haka yasa Deeja sakin hannunta, Hankalinta bai kwanta da kalaman deeja ba, shiyasa tace mata za ta shiga toilet ne don ta samu damar ƙarewa ɗakin nasu kallo, duk don ta samu ta tuna abunda ya faru, don ta fahimci cewa akwai wani abu da take 6oye mata.


Tana ƙarasa saukowa daga saman gadon, kaitsaye idanuwanta suka sauka akan shimfiɗar su Haris, nan take taji gabanta yai wani irin bugu na tashin hankali, ganin babu kowa asaman gadajen su, sai bargunansu da matashin kansu, babu haris babu naufal babu javed  da mubeen.


A fujajen ta waiwayo tana fuskantar gadajensu Sarah, Tsayar da idanuwanta ta yi akan shimfiɗar Gabriel wayam babu kowa saman gadon shi, zuciyarta a hautsine ta wurga eye balls ɗinta kan gadon Majnoon, babu kowa, tsabar ruɗanin da ta shiga ya hana ta furta komai, Tuni deeja ta lura da yanayin da ta shiga.

 saukowa ta yi daga saman gadon,  ta nufi Inda Angel ta ke atsaye ta ɗaura hannunta ɗaya saman kafaɗarta, idanuwan ta acike tab da ƙwalla ta soma magana


"Ko ban faɗa maki ba, nasan kin riga da kin fahimci komai, abunda zuciyarki take faɗa maki gaskiya ne ba ƙarya ba, sai dai inaso mu rungumi ƙaddarar mu, mu yi haƙuri mu daure, tun da ko munyi kukan ba abunda zai haddasa mana face ciwon kai, damuwa bazata ta6a sanyawa adawo mana da ƴan uwan mu ba, haƙurin nan dai shine magani, Gaba ɗaya maganganun dana faɗa maki ayanzu, a wurinki na saba jinsu, don haka ina roƙonki, kada kice zaki sanya damuwa aranki, dama ba ƙoshin lafiya gare ki ba, kuma kinga ƴan uwan mu suma suna acikin mawuyacin hali, mune kaɗai muka rage waɗanda za su iya kwantar musu da hankali, idan ba haka ba, dukkan mu zamu fuskanci matsala ne........." tun kan ta ƙarasa maganar, Angel ta daddafe kanta saboda wani irin jiri da ta ke gani, ba arziƙi ta zunna ƙasa ta yi zaman cin tuwo, yayin da hawaye masu ɗumi ke bin fuskarta.


 "Deeja ki faɗamin! Meya faru dasu Haris? Tafiya aka yi dasu ne? Inaso na sani"! Daƙyar take magana cikin raunin na murya.


Ita kanta Deeja daurewa kawai take yi, 


"Zan faɗa maki Angel, amma kiyi min alƙawarin, ba zaki sanya damuwa aranki ba....." 


jinjina kai Angel ta yi tare da cewa 


"Nayi maki alƙawari" numfasawa deeja tayi Cikin ƙanƙanin lokaci ta labarta mata dukkan abunda ya faru, tun daga kan zuwan tsohuwa Zafreen, har izuwa sandar data ɗaura mata asaman ƙirjinta da kuma abunda ya faru bayan tafiyar zafreen!" Lamarin yayi matuƙar girgizata, Hankalinta yai mugun tashi, zuciyarta har wani tafarfasa take yi tamkar zata 6allo daga ƙirjinta saboda tsabar bugun da take yi, Idanuwanta sun kaɗa launinsu ya ciza sosai.


Hannu biyu tasa ta dafe kanta, muryarta na kerma ta shiga ambaton


"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!


Duk addu'ar da tazo bakinta karanto ta ta ke yi cikin fitar hayyacin duk don ta samu ta tsayar da zuciyarta daga tafarfasar da take yi mata, ta kuma samu sassaucin raɗaɗin da take ji, idan ba haka ba, ita kanta bazata Iya sarrafa ta ba, zata ƙara yunƙurin kashe kanta ne, kamar yarda ta yi ɗazu.


Deeja sai tausarta ta ke yi tana bata baki akan su yi haƙuri, su lallashi junansu, tun da basu da yadda zasuyi, a ƙalla sun ɗauki kusan minatuna talatin, zuƙunne a ƙasa suna jimami, a ƙarshe ma sai suka rungume junansu, hakan da su ka yi ba ƙaramin sanyaya musu zuciyarsu ya yi ba.


Raba jikin su su kayi daga na juna, idanuwansu sunyi luhu luhu da su, 


"Angel yakamata muje mu kwanta, mu yi bacci muma, inyaso gobe da safe idan su azeeza suka farko, sai mu ƙara duba jikin su, wlh na tausaya musu sosai, Musamman Jamima da ta rasa haƙorinta ɗaya......"


Muryar Angel ce ta katse ta"babu komai akwai Allah, akwai kuma mutuwa da hisabi, ae Allah ba azzalumin bawansa bane, Yana ji yana gani, a sannu zai bi mana haƙƙin mu, naji zafin tafiya da aka yi dasu haris, saboda rashin imani da tausayi hada majnoon suka tafi ƙaramin yaron da ba cikakken hankali ne dashi ba, Allah kaɗai yasan ina zasu kai su, me zasu yi masu, Hmmmmm, in sha Allah bazan gaji dayi musu addu'a ba, Allah ya kare su aduk inda zasu kasance, duk runtsi duk wuya idan suna da rabon ƙara shan ruwa aduniya, duk irin azabtarwar da zasu yi masu, zasu rayu ne! Bansani ba zamu ƙara haɗuwa da su ko kuwa shikenan silar rabuwar mu kenan........" ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar, ta ɗan dakata tana mayar da nunfashi, kafin ta samu ta dai dai ta maganarta, 


"Zan yi mana addu'a dukkan mu idan mutuwa sauƙi ce agare mu, Allah ya ɗauki ran mu mu huta, don banga amfanin irin wannan rayuwar da mu ke yi ba, Da farko na yi mana kwaɗayin mu samu ƙopar da zamu gudu daga cikin kurkukun nan ko dan ku ɗanɗani rayuwar ƴanci, amma yanzu na zauna nayi wani tunani, Rayuwar tamu gaba ɗaya atare da kurkukun ƙaddara take, saboda ko mun samu hanyar tsira zasu cigaba da bibiyar mu ne, saboda waɗanda suka sadaukar damu na jinin mu ne! Suna atare da mu, ba zama arasa samun wasu daga Cikin su ba acikin kurkukun ƙaddarar nan! Duniyar nan acike take da ruɗani, wai har na jinin ka ne zai sadaukar da kai? mahaifi ko mahaifiya! Ko wani danginka! Idan har hakane kuwa banga abunso ga rayuwar duniyar nan ba! Saboda babu gaskiya acikinta, halaka ce tsantsa, son zuciya da kwaɗayin abun duniya yasa mutane sun rufe idonsu suna aikata abunda suka ga dama, sun manta cewa dukkan mai rai mamaci ne, zamu yi kwanciyar ƙabari, sannan za'a tada mu domin yin hisabi, Ga duk mai hankali yasan cewa rayuwar duniyar nan bakomai bace, Duk wani abu daka mallaka da zarar ka mutu zaka rasa shi! dukansu kaf ba wanda za'a rufe ka da su acikin ƙabarinka, Iya halinka ne kawai zai cece ka, to wai su irin waɗannan mutanan makafi ne? Ko kuwa kurame ne? Abun da zai ba ka mamaki mafi rinjayen su, Sun sani su ke ta ke  sanin, ko dabba tafisu tunani mai kyau, zuciya ta bushe, sun mayar da zalunci hanyar cin abincin su, duniya kawai suka sa gaba, Anata sharholiya an manta da mutuwa.......wa'iya zubillah! Ya Allah ka karemu daga fadawa hannun irin waɗannan azzaluman mutanan, Ya Allah ka shiga tsakanin mugu dana gari......" 


Ruƙo hannunta Deeja tayi acikin nata"Angel, Bana so kiyi mana fatan mutuwa, saboda inaso mu samu hanyar tsira kodan mu tona asirin azzaluman mutanan da su ka cutar da rayuwar mu, ke da kan ki kika faɗa mana cewa kada mu fidda rai da rahamar ubangiji duk runtsi duk wuya, Angel idan muka mutu ki tuna bamu kaɗai bane akwai sauran ƴan uwan mu dayawa acikin kurkukun nan, bayan su akwai waɗanda ake shirin kawowa cikin sa, Idan har aka cigaba da aikata zaluncin nan har yaushe ne zai tsaya? Daga ni har ke babu wanda yasan tun lokacin da aka gina kurkukun ƙaddara, Dukan mu mun tsinci kan mu ne acikin sa ne......." hawaye ta ko'ina kan fuskarta taci gaba da cewa"Inaso mu kafa tarihi, agidan kurkukun ƙaddara, duk da nasan ba lallai bane mu rayu gaba ɗayan mu ba, amma raina yana bani cewar wasu zasu iya ku6uta, daga ciki har dake Angel nake sanyawa ran fita" dakatawa ta yi da yin maganar idonta akan fuskar Angel da ke kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da cigaba da yin maganar 


 "Tarihin da nake so mu kafa shine mu kawo ƙarshen Mugayen shuwagabannin Gidan kurkukun ƙaddara, Mu tabbatar asirinsu ya tonu, inaso inga ranar da za'a rugurguza ginin nan ya dagargaje ya zamana babu shi adoron duniyar nan, zan roƙi Allah yabamu ikon aiwatar da hakan! Domin kuwa saida iznin shi ne komai zai wakana......."


 tun da Deeja ta soma magana Angel ta tsareta da ido, tsantsar mamaki ne ya kamata, yanayin yadda Deeja take yin maganar da ƙwarin gwiwarta, ya yi matuƙar ɗaure mata kai, zuciyar imani ta shige ta, yayin da ita take ƙoƙarin sarewa ta fidda rai da fita sai gashi Deeja tana ƙarfafa musu gwiwa, ko a mafarki bata ta6a tunanin Deeja zata iya tsara kalami irin haka ba, Tabbas ta samu wani ƙwarin gwiwar awurinta, nan take taji cewa zata Cigaba da nema masu hanyar fita, kodan su cimma burinsu na kawo ƙarshen kurkukun ƙaddara!! 


"Zamu iya Angel in sha Allah"! Fuskar Angel ɗauke da murmushi ta ɗan jinjina kanta tare da cewa"Kin faɗi gaskiya, zamu Iya bi'iznillahi, mune zamu kawo ƙarshen KURKUKUN ƘADDARA"!


Da alama su Deeja sun manta cewa duk abunda su ke tattaunawa a tsakanin su, Jami'an Gidan kurkukun ƙaddara suna kallon su


Sun ɗauki tsawon lokaci zaune a ƙasa suna ɗaukarwa junansu alƙawari, har saida dare ya tsala tukunna, Suka miƙe atare jiki duk ba ƙwari, hannunsu ruƙe dana juna suka nufi gadajen su parveen.


ɗaya bayan ɗaya Angel take binsu da kallo, tsananin tausayin su ne ya kamata ganin irin illar da ta yi masu, babban abunda ta ke ji ma fargaba kada su farka da safe su tuhume ta akan abunda ba laifinta bane, tuna wannan yasa hawaye suka wanke mata fuskarta, Deeja sai tausarta take yi daƙyar ta samu ta shawo kanta, Bayan ta gama kallon su tabi su da addu'a, tana tottofa musu saman bargunansu.


Sallama su ka yiwa juna ita da Deeja, akan idonta deeja ta nufi gadonta ta kwanta.


wuce wa tayi zuwa gadon Jamimah, A hankali ta haye tare da kwantawa gefenta, tasa hannu ta janyota jikinta, ta rungumeta sosai, saboda tsananin tsauyinta da take ji, baiwar Allah bata ji ba, bata gani ba, ta cire mata haƙori ɗaya, dole taji ba daɗi, ga azeeza da ta gurjewa yatsun hannayenta, kowa dai da irin tabon da tabar mashi, taji tsanar tsohuwa zafreeen fiye da tunanin me tunani saboda itace silar komai! 


ta kwana da tunanin abubuwan da su ka faru awannan ranar, Bakomai yafi tsaya mata arai ba, face yarda aka goge kowani jini na jikinsu da wanda ya zuba a ɗakin su, aka kuma maida su saman gadajen su, wannan abun ya yi matuƙar ɗaure mata kai tun lokacin da Deeja ta sanar da ita, Shin wanene yayi musu hakan❗❓

 Deeja ta sanar da ita cewa Tajiyo takun takalmin mutun acikin ɗakinsu  tsoro da firgici ne su ka hana ta buɗe ido taga wanene har saida baccin ya yi awon gaba da ita........ (Nima kuma nayi awon gaba da alƙalamina)


💔PRISONERS💔

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post