Jikar Iya page 9&10 Complete

Jikar Iya page 9&10 Complete

 

Jikar Iya

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️

           08161316781

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Bismillahi ramanin rahim

Page9️⃣🆒🔟

____Ana cikin haka sai ga Malam Audi ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama, jin muryarsa yasa ta faɗin " bakomai tunda baki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki ba, tunda yaro yazo har gida ya mun rashin kunya amma sai ki karyatani, ni bazan miki baki ba amma kema sai jikokin ki sun miki abun da yafi wanda ya mun"

 ta ƙarashe maganar tana kokarin ratsawa ta gefen Malam Audi.

Riko hannunta ya yi tare da tambayarta, "haba Iya komai aka miki ai kyatsaya kimun bayani, dan Allah kiyi hakuri wanne daga cikin yaran ne ya miki lefi?" ya yi maganar yana duban su dan jira yake kawai yaji wane ya riko mutum.

Fatu kam tuni ido ya cika da ƙwalla tare faɗin "wlh ban mata komai ba, kawai ina tafiya ne sai na ganta shine na gaisheta nace ina zata, amma wlh Baba ban mata komai ba" ta ƙarasa maganar tana kai gwiwoyinta ƙasa.

Shikam Musa tuni baisan sanda ya fara fitsari ajikinsa ba, dan yasan halin Baban nasu, in mutum ya shiga hannunsa sai ya kusan hallaka mutu,  kuma baisan abun da ya yiwa Iya zai kai ga har tazo gidansu ta faɗa ba, nan dai ya fara sakin fitsari yana bin jikinsa.

" Wannan yaron ne Sule yaje har gida na yamun tas" kan ta karasa maganar tuni Malam Audi ya danko Sule, nan ya fara kai masa naushi kamar sa'ansa, wani sanda ya ɗauka daga gefe ya fara dukansa, ya zabga masa tanan sai ya dawo ta can.

" Audi inkanawa Allah ka tsaya mana ka saurari abun da yamun tukunna" Iya tayi maganar tana ɗan dariya kasa kasa.

Ƴar Iya kam mamaki take na halin mahaifiyar tata, ga dariyar da take yi na mugunta, sai da akayi wa Sule lilis sannan Iya ta soma magana "Audi dan ma abun idonka bai gane maka ba, dan abun da ya mun ni da badan ni na haifi uwarsa ba, sai na ce jikan kishiya tane, saboda zagin ƙare dangi ya mun tas, kai kace aikosa aka yi," sai ta ɗan dakata sannan ta kara gyara zama da faɗin, "wai kullum sai na zo koɗayin burodi, sannan kuma nida jikata duk mu addabi jama'a, wai tunda uwar iyayen yarinyar nan suka mutu nazo na ɗauki son duniya na ɗaura mata sannan wai nazo na ɗaure mata gindi tsuga rashin mutumci, wai tana taka uban kowa a cikin garin nan, ni kuma sai na ɗauki gajerun kafana naje, sannan wai jiya munyi silar kashe auren Yar mai gari" tayi maganar tana sakin sabuwar kuka, tare da rike bakin bayafinta tana share wa.

" Iya dan Allah kiyi hakuri, daga gobe bazai kara zama a garin nan ba, dan jibi zan turasa yaje can gidan Kawunnesa, tunda tashin kunyar yake kara kwarewa dashi a wannan garin" ya yi maganar yana nuni da Sule da ya sha kuka ya gode wa Allah.

Ƴar Iya kam tsabar jin maganganun da mahaifiyarta take faɗa yasa tayi ciki, tare da sauran yaran dan ita kunya ma take ji, wai uwarta tana zuba karya ko kunya bata ji.

farin ciki ne cikin ranta fal, a baki kuma ta ce, " au ai can ɗinma gidan yarana naga zaije, to wlh naga ta tsiya sai naje can ɗinma na zauna, kuma ga ubanka ya koreka sannan niɗin da ka tsana kuma naje na sameka" tayi maganar tana tsire Sule da ido, shikam tsabar bakin ciki ji yake kamar ya shaƙeta ma ta mutu kowa ya huta.


"Allah dai ya maka Albarka Audi, kaga munafukar Uwartasa da take sakasa tayi ciki ko, wlh karka raga mata ita ma tunda ita take saka su" Iya tayi maganar tana miƙewa tsaye tare da gyara mayafinta.


Sai da ta kai ga kofa ta ce, "To Suleee sai kazo sallama ko, za'aje birni a sha jar miya tare da burodi, kaga na can kam ma mai yanka yanka ne" tayi maganar tana dariya tare da cusa kai zata fita, Malam Audi ne ya biyo bayanta yana ƙara bata hakuri.


"Indo nikan baki bamu labarin yadda aka yi kika san za'a fasa auren Jummai Ƴar mai gari?" a faɗar Musa


"Nima dai inason jin yadda akayi?" cewar  Auta


Dariyar mugunta Indo ta sake harda tunzurawa tare da faɗin "ai jiya daran dare na fita ƙarfe ɗaya da rabi, kaf kauyen nan babu kowa," sai ta ɗan tsaya kamar mai tunani kana ta ce "aini wlh yadda ake da yawa a wannan ƙauyen nayi zaton koman dare zan samu mutane".


"Dan Allah mu ki bamu labarin yadda aka yi " cewar Auta.


"Ai ina fita sai gidan Dan birni naje, ina zuwa kinsan kofar gidan nasu sunan sa get ko?".


"Eh haka ake cewa get,"


"Koma mene dai shi kadai ne mai rin wannan kofar a garin nan, kuma ni bansan yadda zan yi na buɗe kofar ba, hakan yasa na dawo ta bayan layi, na haura ta wannan kangon nan, daman da shirina, ina dira nasa fara shafe dukkan jikina da farar powder, sannan na zira farar jallabiya, shine ya cire ɗaurin kallabi na, sannan na baje gashina, shine kawai nayi ɗakinsa, cikin sa'a na samu a buɗe, hakanne ya bani damar shiga, ina shiga na gasa akan gado sunyi shesheme kasancewar ɗakin da wuta, shine nasa hannu na kashe, sannan na saki wani mugun ƙara wanda ya tasar dashi tare da abokannesa dake kan kujera ɗaya kuma daga kan karamar katifa a kasa, duk hadewa suka yi waje guda jin wannan ƙarar, jikinsu ya fara rawar ƙerma, karasawa nayi wajen tagar ɗakin, ina zuwa wajen na janye labulen, hakan yasa gasken farin wata ya haskani, bayana suka kala daga sama har kasa ganin farar kaya sannan kuma ga gashi a baje a bayana, duk da ba sosai suke kallona ba, a zabure na jiyo na kallesu, ganin farar fuska ne ya ƙara basu tsoro, hakanne yasa na washe fararen haƙorana, tare da zare idanuna kallon ɗaya suka mun suka saki ihu, ihun da suka yi ne ya karamun karfin gwiwar fara tunkarar su, ina tunkaro su ina sakin muguwar dariya, wanda ni abunne ya bani dariya yasa nake yi, amma ganin wannan ma ya ƙara tsorata su, ina tun kararsu suna ja da baya da rarrafe, har sai da nakai dab dasu, sukuma sun kai ga bango hakan yasa na tsaya ina faɗin, "zaku gane kurarku ni abokin wasan ku ne, kuma ni zakuyiwa kishiya" nan suka shiga cilacila da idanu, ɗaya daga cikinsu ne ya ce " dan Allah kuyi hakuri, nikam banida niyar aure ma balle na muku kishiya," nan na ƙara tun tsirewa da dariya, shi kuwa Umar Ango ya fi kowa a cikin su tsorata dan ko magana baya iya yi sai kuka, shima yana yin yana rufe bakinsa, nan ɗayan ma ya magantu da faɗin " nikam ka mun aikin gafara, dan banma san mace ce ko namiji ba, kuma in maganar aure ne ni wlh bana ma ganin yan mata, dan inna gansu ma kallon namiji nake musu, dan kwata kwata basa burgeni" ya yi maganar yana sakin kuka mai sauti tare da kunshe bakinsa.


"Kai ne tantirri baza ka bani amsa ba, zamu kasheka yanzun nan, kuma mu kashe banza" nayi maganar cikin tsawa.


"wlh na sani ranku ya daɗe, kun kashe banza da hofi ma, ni waye inba banza ba," ya yi maganar yana sakin wata katuwar tusa, ashe haɗe take da fitsari.


" ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba, Dan Allah kumun rai na fasa yin auren ma tunda na kula matarku ce, ni na muku alkhawarin ma bazan kara aure ba har a bada" Umar ya karashe maganar cikin firkici da kuka da rawan jiki.


" Zaku gane ne in kuka karya mun alkhawari, kuma zan tafi amma in kuka sake naji kun fadi zancen nan, a lokacin zan bayyana kuma bazan muku ta daɗi ba".


"Wane mutum, ina mu ina faɗar wannan maganar, har mu koma ga mahailcinmu, kuma gobe mukam da asuba zamu koma kauyenmu" a faɗar abokan Umar suna haɗa baki.


Nan fa nace kowa ya yi kasa da kansa kar wanda ya tashi har sai yaji anyi kiran sallah asuba tukunna.......

Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.

TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post