Kurkukun Ƙaddara episode 48 Complete

Kurkukun Ƙaddara episode 48 Complete

 

Kurkukun Ƙaddara

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji❤


*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*


48


Lokacin da marece ya nutsa, duk sun gaji an gama shan gayu, Anci an ƙoshi, wata irin gajiya ce ta rufar musu, ba arziƙi suka lalla6a kowa Ya nufi Sabon gadon daya mallaka suka kwanta, tun suna yin fira ƙasa ƙasa har bacci yai awon gaba dasu, Ya rage saura Danish Kaɗai  zaune gefen gadonshi, don shi bai canza gado ba, har time ɗin hannayen shi na aruƙe da uniform ɗinsa Ya ƙanƙame su, Daga bisani ne Ya ɗaura su saman mattress ɗin shi.


A hankali ya sauko daga saman bed din nashi, Cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar gadon da angel take a kwance, Yana ƙarasawa bakin gadon ya zagayo ta left side Ya ɗan zuƙunna, yayin da kyawawan idanuwanshi ke akan fuskarta, ta natsu sai sharar bacci take yi, numfashinta yana fita cikin kwanciyar hankali da natsuwa, lumshe idanuwan shi yai tare da buɗe su kan fuskarta, wata irin natsuwa yaji acikin zuciyar shi, Angel ta yi mishi kyau, fiye da ko yaushe, zuciyarshi ce ta dinga tunzura shi akan ya ta6a sumar kanta, dama itace ta tsole mishi ido, Yatsun hannun shi na kerma ya ɗan ɗago dasu Ya ɗaura su samar doguwar yalwatacciyar sumar kanta, tun da ya soma shafa gashin, ya gaza janye hannayenshi, da zarar yaga tafara mutsu mutsu kamar zata farka, sai kaga yai wuf Ya zuƙunne gefen gadon yana faman sauke ajiyar zuciya, a hankali Yake sake ɗagowa Yana kallonta, Wannan karan Hada Tausasan la66anta Ya shafa da yatsan hannun shi, ya shagala Yana kallonta, Kamar daga sama Yaji an damƙi wuyan rigarshi ta baya, a matuƙar firgice Ya ɗago don ya ga wanene, Ajiyar zuciya ya sauke ganin haris Ne, har wani numfashi yake fitarwa kamar wanda yasha gudu.


"Bro, Me kake Yi anan? And why are u looking at her"? Yai tambayar yana kallon fuskar Danish da alamun tuhuma, a yayin da yake ƙoƙarin zame hannunsa daga ruƙon da ya yi ma wuyan rigar shi.


Cikin sanyin murya yace"Bakomai" Iya abunda ya furta kenan, Ya miƙe daga bakin bed ɗin nata, Ya nufi gadonshi Ya zauna daga gefe, Girgiza kai haris Ya yi, tare da bin bayan shi ya zauna a kusa dashi.


"Ka faɗa mini menene damuwar? May be ina da hanyar da zan Iya taimaka maka, Ka canza sosai Danish, Mun rasa gane kan ka, Kowa yana walwala amma banda kai, hatta sabbin uniform ɗinka dana baka, baka sanya ba, why Danish? Idan ma saboda abunda ya faru ne, ae mun yafe maka ko? Komai ya wuce" Cikin Kulawa Yake yi mishi maganar, daƙyar ya samu Danish Ya buɗe baki ya furta "Ita ce"


Aɗan ruɗe haris ya furta"Wa kenan"?


"Angel mana, tasa na ɗaukar mata alƙawari akan cewa zan nisanta kaina da ita, ko kallo kar in bari ya haɗa ni da ita, haris na shiga damuwa sosai, "


Shiru haris ya ɗanyi Na wani lokaci, Yana kallonshi, shi kanshi Ya lura da irin damuwar dake atattare dashi, Duk ya rasa sukuni, ashe duk akan angel ne,


Murmushi haris ya saki tare da cewa"ka kwantar da hankalin ka, Mutumina, indai angel ce zata nemi hanyar da zaku shirya, ae itama ta damu dakai, So bana so kana tada hankalin ka, gashi ko abincin ka baka ci ba, 


"Ae bana jin yunwa...." tunkan ya rufe baki Haris Ya katse shi da cewa"ƙarya kake yi, look at ur stomach, A shafe kamar Bangon ɗakin mu, " yatsina fuska Ya ɗanyi ba tare da ya kuma cewa komai ba.


"Yanzu dai, bari na ɗauko maka chicken leg ɗinka da fruit kasha, after ka gama Sai in taimaka maka ka canza uniform ɗinka" kafin haris yai yunƙurin miƙewa tsaye Danish Ya ruƙo hannun shi, Yana faɗin"Bana Jin yunwa, zan ci da anjima, Yanzu so nake in kwanta" ɗaure fuska haris yai"meyasa kake yi min haka? Ko dan saboda na damu dakai ne"? Girgixa kai yai

'Ba haka bane, just bana jin yunwa, Nayi maka alƙawarin da anjima zanci" gyaɗa kai haris yai, tare da cewa"Uniform ɗin Fa? Yakamata Ka canza na jikin ka," Yatsina fuska yai don ba ƙaramin takura shi haris yake yi ba.


rai a6ace haris yace"Na lura ba ka damu da kan ka ba, Kamar yadda na damu dakai, shiyasa ka ke ta yi min wulaƙanci, Shikenan, Zan tafi nabarka, wlh idan har baka canza kayan nan ba, ka ci abinci, kada ka ƙara tunanin zan tanka maka" yana kai ƙarshen maganar, Yaja tsoki tare da miƙewa Ya juya ya nufi gadon shi, Ya haye ya kwanta, zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin haushin abunda Danish ke yi mishi, Gashi Allah ya jarabce shi da ƙaunar ɗan uwansa, Shi dai yana son Danish, baya son 6acin ran shi, tun suna yara, haka yake fama da shi, Baison Cin abincin baisan hayaniya, baisan yin magana, ga nuna halin ko in kula, da yake yi musu, wani lokacin ka rasa gane kan shi kamar ba cikakken mutun ba, shi dai yafi gane ma hawa saman gadon Ya rungume pillow a ƙirjin shi.


"Haris meya faru ne naga fuskarka ta canza"? Muryar deeja ce ta katse mishi zancen zucin da yake yi, kasancewar suna fuskantar juna, Gadon da yake kwance Yana facing ɗin nata, Farkawarta kenan daga bacci, Ta yi arba dashi kwance saman gadon shi ya ƙurawa ceilling ido, sai tsoki yake bugawa,


"Haris ka yi shiru baka bani amsa ba" ta6e baki ya ɗan yi kafin yace mata"Nida mutumin ne, ina ta fama dashi ya tashi yaci abinci, ya canza uniform ɗinshi, amma yaƙiya, narasa meke damun Danish, Yafiye taurin kai da kafiya" 


Mirmushin takaici deeja ta saki,"Kaine ka damu dashi ae, shiyasa yake yi maka abunda yaga dama, Tunda baya cin abincin ka ƙyale shi mana, ba cikin shi bane, idan yunwar ta addabe shi zai nema ne" girgiza kai haris yayi


"Bazaki fahimta bane, ni bazan Iya ƙyale shi ba, saboda ina zargin wani abu atattare dashi, gani nake wani abun kamar ba yin kanshi ba, Danish fa ya canza sosai, Sa6anin lokacin baya da muka sanshi,  shiyasa nake yi mishi uziri, kuma gaskiya ni, Ina matuƙar son ɗan uwana, bana jin zan iya share shi, idan shi bai son ciwon kanshi ba, Ni nasani,"


Murmushin dake akan fuskarta bai washe ba tace"Haris you're so special, fiye da tunaninka, ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yi mishi, bama shi kaɗai ba, kowama acikin mu, kana son mu, kana bamu kulawa, kai tamkar jagora ne acikin rayuwarmu....." Tun da Deeja ta soma magana cikin sanyin murya mai daɗi, haris Ya tsare ta da idanuwanshi batare da ƙiftawa ba, saboda wani irin daɗin da yake ji, sai da takai karshen maganarta, sannan yace"Haka nake fata wata rana Danish Ya ɗauki ragamar kula da ku kamar yadda nake yi, shiyasa kika ga ina ƙoƙari don ganin na gyara mashi tunaninsa," 


"Ka yi tunani mai kyau, nima ina fata Wata rana Danish Ya canza ya zama kamar kai, tabbas zamu Ji daɗi," shiru suka yi na wani lokaci suna kallon juna. Kafin Haris yace"bakomai yafi damuna ba, face rashin batool, Deeja ya zamu yi? Sun ɗauke ta almost one month babu alamar zasu dawo mana da ita, na damu sosai, duk in na tuna da batool baki ji yadda nake ji ba, gaskiya bai kamata ace mun yi shiru ba, mutanan nan fa mugayene azzulamai, zasu iya cutar da ita, kamar yadda suka yi maku," hawaye ne kwance acikin idanuwanshi, yayin da yake yin maganar.


Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ae batool sai addu'a, Har ƙwara mu da aka ɗauke mu an dawo damu within weeks, amma ita fa har One month! Wlh ji nake kamar sun kashe mana ita....." bata ƙarasa maganar ba, saboda kukan da ya tari numfashinta, da sauri ta kifa Kanta saman pillow taci gaba kuka. Hankalin haris duk yabi ya tashi, muryar shi araunace yake lallashinta, yana bata haƙuri, akan tayi shiru tadaina kuka kodan saboda ƴan uwan su dake bacci kada su farka, suji suma su shiga damuwa.


Abunda basu sani ba, tunda suka fara magana angel ta farka, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, duk da akwai tazara atsakanin gadajensu amma tana iya jiyo maganganun da suke tattaunawa, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, zuciyarta sai tafarfasa take yi, Tamkar zata 6allo ƙirjinta, aduk lokacin da ta tuna da batool, saita dinga jin kamar ana tunzurata akan ta ƙara dura tagar nan akaro na biyo taje ta nemo ta, ko Allah yasa ta dace, Dama fa ba haƙura ta yi ba, akwai dalilin dayasa ta dakata da kudurin nata, saboda ta lura shiga cikin prison ba abune mai sauƙi ba, dole saita yi mishi kyakkyawan shiri na musamman, kafin ta aiwatar da aikinta, can ƙasan zuciyarta kalaman tsohuwa tamira ne suka shiga yi mata yawo acikinta kanta, tarasa gane dalilin dayasa Suka tsaya mata aranta, tabbas akwai abunda take nufi game da makullan farin cikin nan, kuma tace Idan suka Cigaba da nuna ma danish wariya to wata rana zasu rasa madafar su, ko dan saboda haka dole ta nemi hanyar da zata karya alƙawarin dake a tsakaninta dashi, 


numfasawa ta yi tare da ƙoƙarin miƙewa zaune hannunta ruƙe da pillow, ta ɗan juya 6angaren hagu ta kalli su Deeja, har lokacin bata daina kukan ba, haris sai aikin lallashinta yake yi, tun yana akan gadon shi har ya kai ga dawowa gefen gadonta ya zauna, tare da kai hannu yana shafa sumar kanta, daƙyar ya samu Deeja ta yi shiru, ya kwantar da kanshi gefen ta, yana leƙen fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye, Angel tana jiyo shi yana faɗi"Hakan ma bazata ta6a faruwa ba, ki daina zancen mutuwa, inaji araina ƴar uwarmu tana araye, zasu dawo mana da ita ne" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"bayan sun gama amfani da ita ko? Sai sunyi mata kamar yadda su ka yi mana, ko ka manta yadda aka dawo dani ne? Tae tambayar tana kallonshi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa Jawur dasu, Zuciyarshi ta karaya sam ya kasa magana


Ta ci gaba da cewa"A wulaƙance, aka dawo dani, ji lokacin da aka dawo dasu Hanna, Hada yakushin akaifa akan wuyansu, le6e duk ya bushe ya faffashe jini yana tsastsafowa, idanuwa sun jagwale da ruwan hawaye.....haris duk da bamusan me akeyi mana ba, amma munji raɗaɗin azaba ajikin mu, mun yi jinya, mun yi kuka tamkar rayukanmu zasu fita daga gangar jikin mu, Iya cuta dai ancuci rayuwarmu," tana faman jan majina ta ɗaura da cewa"Ina tsoron Awani hali za'a dawo mana da BATOOL! ita da ta ɗauki tsawon lokaci ahannun su, mugaye azzalumai Allah kaɗai yasan me su ke ƙunsa mata a yanzu haka......"


Deeja bata kai ƙarshen maganar ta ba. Sakamakon jin sautin kukan angel, A matuƙar ruɗe su ka ɗago daga saman mattress ɗin suna kallon shimfidarta, A lokacin harta duro daga saman gadonta, da gudun gaske ta nufi sashen toilet ɗinsu ta shige, damuwa ce ta bayyana akan fuskokinsu.


"Tun yaushe ta farka? da ace na sani da ban yi maganar ba, bari naje in lallashe ta, nasan dole taji raɗadi acikin zuciyarta," Deeja na yunƙurin miƙewa haris yae saurin katse ta, ta hanyar yi mata magana,


"kada kije, Ayanzu bata buƙatar kowa a kusa da ita, ganinki zai ƙara karya zuciyarta saboda kece kika yi maganar..."


"Amma tana buƙatar wanda xai lallashe ta, kana ji fa tana kuka"


"Nasani, kema yanzu kika gama kukan inata aikin lallashi, Ki koma ki kwanta, Zanji da ita" sai da ya samu ya kwantar ma deeja da hankali, kafin ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu, Har satar kallon shimfiɗar danish yai ta wutsiyar idanuwanshi ya hange shi kwance saman gadonshi, aranshi yace"Kaji haushin rayuwarka, wato baka ci abincin ba, sabbin uniform ɗin ma ba za ka sanya ba, saboda Taurin kai irin naka," Guntun tsoki yaja yayin da yake shigewa cikin toilet, tunkafin ya ƙarasa ciki ya same ta zuƙunne agaban tukunyar fulawar nan, Ta tasa ta gaba sai kuka take yi kamar ranta zai fita,  


"Why angel? Wannan kukan fa da ku ke yi bazai kare ku da komai ba, Ina fama da deeja, kema kuma kin kama kuka, nasan saboda kinji maganganun da muke tattaunawa ne," a bayanta ya tsaya hannayenshi rungume saman ƙirjinshi,


Cikin shessheƙar kuka tace"Bazan Iya jurewa bane, Batool tana can Hannun fasiƙan mutanan can, Cikin mawuyacin hali, Nagaza zuwa in taimake ta, nasan Ta jira zuwana taji ni shiru, dole taji ba daɗi duk irin ƙaunar dake a tsakanina da ita," A gefenta haris Ya zuƙunna Ya soma lallashinta kamar yadda yayi ma deeja, A ƙarshe Ya ruƙo hannunta yace"Ki taso mu koma ɗaki" Maƙe mashi kafaɗa tayi"a'a Kabarni anan, Inaso zanyi ma furennin addu'a" gyaɗa kai yai tare da miƙe wa, da niyar yabar toilet ɗin, har ya juya zai fita sai kuma ya ɗan dakata tare da kallonta yace"Angel, badan halina ba, badan na isa dake ba, pls Ki karya alƙawarin dake a tsakaninki da Danish!  Idanuwanta jawur ta juyo tana kallon haris, yaci gaba da cewa"Ki tausaya mashi, dama ba cikakkar lafiya ce dashi ba, yanzu kuma kin ƙara jefa shi cikin wani hali, duk fa saboda ke ya gaza sakewa acikin mu, yaƙi cin abinci yaƙi canza uniform ɗin jikin shi, ni bansan ya akai kika sa ya ɗaukar maki alƙawari fa" fuskarshi a yamutse yayi maganar, Hannu tasa ta matse tsinin hancin ta, yayin da take kallon shi, muryar ta ƙasa ƙasa tace"haris, Nasan ban kyauta ba, nima nayi regretting da na sanya shi ya ɗaukar min alƙawari, raina ne yake a6ace, Amma har ga Allah ni bana fushi dashi ayanzu, sai da nace mashi nafasa promise ɗin, Mu shirya amma yace min shi bai fasa ba......" kaf angel ta kwashe duk yadda su ka yi atsakaninta da Danish ta sanar mashi, 


Dafe goshi haris yae da hannun shi na dama kafin ya zame shi ya ruƙe qugu yana faɗin"Oh my God, Danish matsala,   kin san shi da ruƙe alƙawari, idan har mu ka ce zamu biye mashi bamu san har tsawon wasu kwanaki za'a ɗauka ba, Yana Cutar da kanshi, Tun da ba mu san ranar da za'a dawo da Batool ba, kuma bamu da tabbacin cewa idan an dawo da ita zata yafe mishi," Dakatawa yae da yin maganar yana kallonta, itama shi take kallo, 


"Yanzu ya zamu yi kenan? Alƙawarin Ya karye" Haris ne yai tambayar, shiru angel tayi na wani lokaci tana yanke shawara daga cikin zuciyarta, 


"Kin yi shiru" a ƙagare yae mata maganar, har ya fara gajiya da tsayuwa,


"Kada ka damu haris, Ni nasan yadda zanyi dashi, In sha Allah a daren yau ɗin nan zan karya alƙawarin, " ajiyar zuciya haris ya sauke fuskarshi asake yace"Dama nasani zaki Iya!" ya ambaci hakan tare da juyawa da sauri ya fuce daga Cikin toilet ɗin,


Lokacin daya shiga Room ɗinsu,  Su parveen duk sun farka daga bacci, sai surutu suke yi. Kamar ba waɗanda suka sha bacci ba, Kowacce Tana daga zaune saman gadonta, Hannah tana hamma tace"Wai ina angel ɗinmu take ne? Naga banganta ba" hibba tace"yanzu haka tana acikin toilet, wani uzirin ne ya kamata," saukowa daga saman gado azeeza tayi tare da cewa"Nima toilet ɗin xan shiga" takarasa maganar tare da wuce wa ta nufi sashen toilet,  tuni haris ya jima da komawa saman gadon shi, ya zauna yana yi musu sannu da farkawa bacci, sarakan ɗumi yanzu xa'afara, gaba ɗaya suka kama dariya, Parveen na miƙa tace"Motsa Jiki zamuyi, Jiki na duk ya ruƙe, " Haris yace'ae dole, An cika ciki yayi haiƙam ta ko'ina babu space ai dole ki nemi motsa Jiki, ko kin samu Cikin ya kwance Aje toilet kamar yadda aka saba," Wani irin kallon harara take jefa mashi, Eve tace"Haris ka sanya ma sis parveen ido Allah, bansan me tayi maka ba" Ta6e baki yai"ae tunda tace ban da kyau saita gane kuren ta," Deeja dake kwance tana jin muryoyinsu Acikin kunnanta, taƙi motsawa ne don kada suga halin da take ciki na damuwa,


"Yakamata Baƙin prisoners ɗin nan su ƙaraso tunkafin Ku 6alla musu gadajensu"  javed ne yai maganar idanuwanshi rufe, yana kwance saman nashi gadon,


"Idan ma akwai wanda zai 6alla musu gado to bai wuci ku ɗin nan ba, saboda kune ƙattai da kai da haris da mubeen da naufal, gadon ma yayi maku ƙanƙanta" parveen ce tai maganar tana gatsina mashi hanci,


Wani irin kallo haris da javed suke jefa mata jin abunda tace, Naufal dai bai tanka musu ba, tun da ya farka bai mike zaune ba, mubeen dai ne ya tada kanshi saman pillow, 


"Kina wuce gona da iri parveen, da alama yau kinci kin ƙoshi, shiyasa kike gaya mana magana"  kafin parveen ta mayar mashi da martanin maganar da yayi, muryar naufal ta katse su da cew "wai ba dai har yanzu, maji daɗin gadon can Bai sanya uniform ɗinshi ba? Nagan su ajiye gefen shi," yai maganar yana kallon gadon Danish Bawan Allah ya baje sai sharar baccin shi yake yi,  haris yace"ae kasan halin shi, ba yadda banyi dashi ba, akan ya sanya kayan amma yaƙiya, abincin shi ma yaƙi ci, narasa ya zanyi da Danish yafi ƙarfina...." Haris na ƙarasa maganar, parveen tace"ae wlh indai cinyar kazar shi takai anjima tsakar dare bai ci ba, Sai na cinye ta,  in haɗa da fruit ɗin, Ni natsani inga ana wulaƙanta abinci, " Tana magana tana hura hanci,


Harara Naufal Ya jefa mata Daga kan gadon shi, Yace"Sannu MAJI DAƊIN ABINCI, uwar haɗamammu, ke da ba ki gajiya da abinci, Ga shi ni ko ajiki banga kina ƙiba ba, " murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, batare da ta bashi amsa ba," 


A6angaren Angel dake a tsugunne gaban tukunyar fulawa, ta ƙurawa furennin idanuwanta, Hankalinta ya ɗan kwanta ganin furen batool Lafiyar shi ƙalau, jikin shi yai kyau launin shi ya ciza, haka zalika furen daddynta Yayi kore shar dashi, Addu'o'i ta shiga jerowa tana tottafa ma furennin, bayan ta kammala bata miƙe ba, Zurfin tunani ta shiga akan yarda za'ae ta karya alƙawarin da ke tsakaninta da Danish, Dole ta yi mishi dabara.


"Angel!" firgigit tayi Jin an ambaci sunanta, da sauri ta sanya tafin hannayenta ta share hawayen dake akan fuskarta kafin ta juya ta kalli ƙopar shigowa cikin toilet ɗin, bakowa bace face Azeeza, fitowarta kenan daga cikin ɗaya daga Cikin makewayin nasu,  sai faman sakin murmushi take yi, 


"Azeeza, haka na koya maki yadda ake shiga toilet? Batare da neman izni ba"? Fuskarta aɗan ɗaure tayi mata magana, ɗaure fuska azeeza tayi tana tur6una fuska, kamar zatayi mata kuka tace"Ae Naji muryoyinku keda haris kuna magana, duk da bana jin ku sosai,  naga ya shigo, shiyasa nima na shigo"


zuba mata ido angel tayi ganin yadda take magana tana wani farfari da idanuwanta, miƙewa tsaye angel tayi tare da juyowa ta nufi bakin door ɗin inda azeeza take a tsaye, Ruƙo hannunta ta yi acikin nata, taja ta suka dawo Cikin ɗakin, a tsakiyar ɗakin suka samu su Hannah, Sun ɗauko madubin nan suna kallon fuskokinsu, Yadda kasan sun ruƙe Waya a hannunsu Suna ɗaukar Selfy, gayun ne bai ƙare ba, dama ɗazu gajiya suka yi shiyasa suka ɗan kwanta, Yanxu sun wartsake, mutun Uku ne basu sauko daga kan gadon su ba, Danish da Haris sai deeja, amma su mubeen duk sun sauko, suma suna kallon madubin, ba ƙaramin burgeta su ka yi ba, tana fata wata rana Idan Allah yasa suna da rabon tsira su ɗauki pics tare da ƴan uwanta.


kafin su ƙarasa inda su hanna suke, Tana jiyo muryar Rubina tana faɗin"Allah yasa baƙin da za'a kawo musu basu kaisu kyau ba" Yasmin tace"ke damuwarki kenan, Ni fatana Allah yasa akawo mana masu hankali da natsuwa," parveen tace'Ni kuma bana son masu shegen cin abinci, Allah yasa akawo mana Irin Danish, marasa son cin abinci, sai mu dinga yi musu wayau idan sun rage abinci mu kwashe mu cinye" tana magana tana kwatanta yadda zasu dinga kwashe abincin da hannunta, gaba ɗaya suka saki dariya, "Allah ya shirye ki parveen, baki da burin daya wuce abinci abinci, " mubeen ne yai maganar, Naufal yace"ae shiyasa na sanya mata maji daɗin abinci, sabon sunan parveen kenan, ita kuma azeeza maji daɗin shagwa6a" Yana rufe baki, Hanna tace"ita fa angel"? hannu yasa ya toshe bakin sa tare da cewa"Rufa min asiri, kunfi kusa da ita, ku bata sunan daya dace da ita," murmushi angel tasaki yayin da take kallonsu tace"Ae basai wani ya faɗi ba, Ni da kaina zan bama kaina sunan daya dace ni,"


Hayaniyarsu ce ta farkar da Danish, gaba ɗaya sun cika mashi kunnan shi sun hana shi sakat, bakomai ya faɗo mashi aranshi ba, face maganar da haris ya faɗa mashi akan sabbin uniform da kuma cin abinci, baya so haris ya daina Kula shi, ko dan saboda haka zaisa kayan, a hankali Ya miƙe zaune yakai hannu ya ɗauki uniform din ba wanda ya lura dashi acikinsu, saukowa yae daga saman gadon cikin kasala Ya nufi sashen toilet dinsu Ya shige,


Bayan wasu ƴan mintuna, Suna Cikin yin firarsu da raha, Kwatsam Suka ji parveen ta fasa ihu, Mai matuƙar razanarwa a gigice suka kalle ta, Ta zazzare idanuwanta, Yayin da take kallon bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu, Da sauri Suka kai idanuwansu kan ƙopar, Wa'iya zubillah, Tabarakallahu ahsanun kaliqin, Kusan atare suka waro idanuwansu waje tamkar eye balls ɗinsu zasu faɗo ƙasa saboda tsabar yadda suka zazzare idanuwan, Sun saki baki Galala suna kallon shi yayin da yake shigowa cikin ɗakin,


Tsarki ya tabbata ga wanda Ya halicci wannan bawa, Maƙerin wannan kyakkyawar Halittar, mai matuƙar jan hankali da ɗaukar ido, Hatta haris da deeja dake kwance saman shimfiɗarsu, sai da  su ka miƙe zaune sakamon Ƙarar da parveen ta saki, A wani irin yanayi suke bin shi da kallo from head to toe, black trouser ɗin Ya xauna mashi sosai, A bunka ga dogon namiji, daga sama Ya sanya red vest ɗin shi, tayi tighting ɗinsa, tayi mashi kyau ta fito da ainihin Farar fatarshi, Daga saman Jar vest ɗin ya ɗaura wrap Coat ɗinsa black colour, Abunda ya ƙara ƙawata kyanta, bai ɗaure igiyoyinta ba, hakan zai baka damar ganin ƴar ta cikin,


saman dogon wuyanshi ya rataya Cotton scarves ɗinshi red colour, Ya ɗaure yalwatacciyar sumar kanshi ta baya Ta zubo mashi, Wohoho, A fagen kyau Danish Yana a mataki na farko, don da ace zai shiga gasar kyau to kuwa yana ɗaya daga Cikin waɗanda zasu lashe gasar babu tantama, Kayan sun dace dashi, yadda kasan don shi akayi su, tausasan red lips ɗinsa launin su yayi Ja sosai sunyi matching da Cotton scarves dinsa da kuma Red vest ɗinsa, Launin ƙwayar idanuwanshi, russet brown sai ɗaukar ido suke yi, ga eye lashes ɗin nan nashi  masu tsayi da cukowa sun ƙawata zagayen idanuwanshi, 


Wallah An rasa me magana acikinsu gaba ɗaya Danish Ya shammace su, Mamaki ne da al'ajabin kyawunsa sunyi matuƙar gigitasu, sun rasa gane a tsakanin shi da Angel waya fi wani kyau, ita irin zazzafan kyau ne da ita, wanda farat ɗaya ka kalle ta sai gabanka ya faɗi, shi kuma nashi wani irin sanyi ne dashi, mai narkar da zuciya,


Ganin yadda suka zuba mashi na mazurinsu suna kallon shi nan take yabi ya rikice, a ruɗe ya juya ya koma sashen toilet ɗinsu, Ya jingina bayan shi jikin bango yana faman sauke ajiyar zuciya,


"Allah yasa bani kaɗai nake gani ba" parveen ce tai maganar, azeeza tace"Ae duk mun gani, wlh Danish Yayi min kyau, kamar in sace shi, muryar parveen kamar zatai kuka tace"Yafi abinci kyau da kyan gani," gaba ɗaya suka saki dariya, Hanna tace"Speechless bansan da wasu words zanyi amfani wurin Bayyana irin kyan da danish yayi mini ba" naufal dai sai jinjina kai yake yi, da alama shima ya rasa tace wa, Inaga uwar gayya wato Angel, babu wanda ya lura da ita, tuni ta zuƙunna ƙasa, zuciyarta kamar zata buga, Bakomai take tunani ba face Hamshaƙin Kyan Fuskar Danish, Mamaki take wai a ina ya gado wannan kyan nashi? Su wanene Iyayen shi? Tama rasa da wani jinsi zata kwatanta shi, Larawa ba ne indiyawa ne, turawa ne, South korean ne, Ko kuma Nigerian ne!! A ƙarshe dai Zuciyarta ta bata amsa da cewa"Yafi kama da jinsin aljanu, kiyi tunani xaiyi wuya ya kasance mutun ne" murmushi taɗan saki, ƙuruciya ta motsa, nan take ta yadda da abunda zuciyarta ke raya mata, Muryar haris ce ta dawo da ita daga zurfin tunanin da ta shiga


(Next page gobe in sha Allah, Masu son shiga paid group na facebook Ga link Kuyi mata magana after kun biya zata sanyaku👇


https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL


waɗanda ke yin arewa book su yi following account ɗina, zasu dinga samun Littafin kurkukun ƙaddara hada abban sojoji, Ga link ku yi joining👇


https://arewabooks.com/chapter?id=6535288c429337735998e5aa

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post