💋KURKUKUN ƘADDARA💋
E61
Daga alƙalamin Boss Bature
💔PRISONERS💔
Kwance ta ke asaman gadonshi, hannunta rungume da pillow ɗin sa ta ƙanƙame shi a ƙirjinta, bacci take yi amma sam babu kwanciyar hankali atattare da ita, sai jan numfashi ta ke yi ga cikinta da ke ta yin kukan yunwa, hatta ƙirjinta wani irin nauyi yai mata, zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi, duk irin sanyin da yanayin ke da shi hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, saboda damuwa da kuma rashin cin abinci har rama ta yi fuskarta ta faɗa, sai uban hasken da ta yi, gashin kanta kuwa kamar na mahaukaciya, rabon da ta sharce shi tun lokacin da aka tafi da Danish, wankan ma sai in sun matsa mata ta ke yin shi akai akai, haka abinci sai sun mata dole sun tasa ta gaba tukunna take ɗan tsakurar kayan marmari tasha idan ta gama ta kora da ruwa, fruit kaɗai ta ke iya sha, duk ta takura kanta,Ta hana kanta sakat kamar wadda ta aikata zunubi, ga shi rayuwarta gaba ɗaya ta koma saman gadon Danish, idan kaga ta sauko to toilet zata shiga domin yin wani uziri amma bayan haka babu ruwanta da kowa, Saman gado take naɗewa ta addabi zuciyarta da tunane tunane na damuwa, depression tuni ya fara samun gur6i acikin zuciyarta, idan damuwa ta yi mata yawa kanta har sara mata ya ke yi da matsanancin ciwon kai, zuciyarta tai mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse saman ƙirjinta haka ta ke ji, wani lokacin idan abun yai mata yawa har amai take yi, Rayuwar Angel ta zama abun tausayi, kowa tausayinta ya ke yi acikin su, sun damu da damuwarta, suna matuƙar jin takaicin halin da ta shiga kamar ba Angel ɗin su ba.................💔
Ƙasa ƙasa ta ke jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, sai surutu su ke yi duk sun cika ɗakin, tana ta faman ƙoƙarin buɗe idanuwanta amma sunƙi bata haɗin kai baccin ne bai ishe ta ba, ga kuma matsiyaciyar yunwar da ta ke ji, A hankali take motsa la66anta tana karanto addu'ar tashi daga bacci, kafin daƙyar ta iya buɗe manyan idanuwan nata waɗanda suka raunata sosai saboda kukan da take yawan yi akowani dare na Allah, bismilla ta furta yayin da ta ke yunƙurin miƙewa zaune ta jingina bayanta jikin bango, old uniform trouser ɗinta ne a jikinta baƙi, Sai jar vest ɗinta data sanya, don tafi sha'awar kwanciya bacci da ita, buɗe baki tai sakamakon hammar da tazo mata ba shiri ta ɗaura hannunta saman bakin nata Tana ambaton Alhamdulillah.
bayan ta sauke hannun ta ɗaura su saman pillow, kafin ta tsayar da idanuwanta kan ma su yin Surutun, kusan su Biyar, Zazzaune a ƙasa saman shimfiɗar Sarah, Hannah da Yasmin tare da Hibba da kuma rubina, sai Eve hada mai shimfidar Sarah, Hannunta ruƙe da nail cutter, Ita kuma Hanna tana ruƙe da nail filer, suna fira Sarah na yanke musu akaifa, idan tagama yi ma mutun ɗaya sai Hanna ta kankare mashi akaifar ta gyara mashi ita, idan ka gan su ahaka sai ka yi tsammanin basu da wata damuwa alhalin nan kuwa zuciyarsu a cunkushe take da matsananciyar damuwa.
tun da ta ɗaura idanuwanta akansu bata ɗauke ba, bakomai yake burgeta dasu ba, face yarda suke matuƙar ƙaunar junan su, Suna da kyakkyawar mu'amala a tsakanin su, Sau dayawa basu jin komai don su yi ma ɗan uwansu hidima, sa6anin wasu mutanan da zaka ga ƙashi ya hana su taimaki junan su, amma su waɗannan bayin Allahn suna da haɗin kai, tun da ta fara rashin lafiya basu ta6a bari ta wanke koda uniform ɗinta ba, hatta kayan marmarin da ta ke sha su ne suke kawo mata su har saman gadonta don ta sha, shiyasa take matuƙar ƙaunarsu.
Ɗauke idanuwanta tai daga kansu sarah, ta shiga bin kowani gado da Kallo, Parveen tana ƙudundune saman gadonta, bata farka daga bacci ba, sai juyi take yi saman mattress ɗinta kamar zata faɗo ƙasa, Sauran gadajensu Deeja tabi da kallo, Da alama idonta biyu, ta ƙurawa ceilling ido fuskarta ɗauke da damuwa, Haris ma Yana a zaune gefen gadon shi Ya zabga uban tagumi, gwiwowin hannayenshi asaman na ƙafafun shi, tasan bai wuci damuwar rashin ɗan uwansa bane, bawan Allah duk da irin juriyar shi hakan bai hana shi yin rama ba, sauran mazan duk suna a kwance saman gadon su basu farka daga bacci ba.
Tana cikin bin gadajen su da kallo, ta soma jiyo sautin dariyar Azeeza ta cikin sashen toilet ɗin su, Da sauri takai idonta kan ƙopar, Majnun ne ya fito babu kaya ajikin shi sai gudu ya ke yi jikinsa duk lemar ruwan wankan da ta yi mashi, Gaba ɗaya su Hanna suka ɗago Suna kallon su, Lamarin ya ɗaure musu kai ganin yadda yadda ya fito babu kaya yana ta gudu acikin ɗakin su, hauka tuburan yana ta tiƙar dariya ko kunya bai ji ko da ya ke ina yasanta.
Azeeza ce Ta biyo bayanshi hannunta ruƙe da uniform ɗin shi, Sai zagaye cikin ɗakin nasu su ke yi tana ta Ƙwala mashi kiran tana faɗin"Wai ba zaka tsaya in sanya maka kayan ka ba? Salon sai ka faɗi ko, don ma ka samu na yi maka wanka shine ka ke min wulaƙanci, ba don zuciyar imani ba Allah da bazan yi maka wankan ba ƙazami kawai, mutun jiki duk ciwo, har tsoron ta6a fatar shi nake yi kamar zata fashe saboda haske........" Su hanna sai dariya su ke yi musu, ita kanta Angel sai da ta ɗan murmusa ganin yadda take ta faman bin shi yana yi mata yawo da hankali, da ga ita har shi Sai ka rasa gane wanene babba acikin su, shiyasa duk suka rainata,
kamar sun samu tv haka suka dinga binsu da kallo, babu wanda ya lura da Angel ta farka da tuni sunzo wurinta.
Fitowa daga Cikin ƙopar sashen toilet ɗin su Jamima ta yi, hannunta ruƙe da rigar uniform ɗinta, daga ita sai ɗan wandonta ja, fuskarnan a murtuƙe ta sha mur, ƴan kumatuntu sun yi suntum dasu saboda tsabar fusata, Gashin kanta da aka ɗaure mata da ribbom Ya cika bayanta, kamar na ɗiyar roba, sai baƙin rai ta ke yi,
Hayaniyarsu Ce ta farkar da sauran da suke rage suna bacci, hatta haris daya zabga uban ta gumi da deeja dake kallon ceilling saida suka dawo da dubansu akan Majnun da Azeeza.
"Azeeza!" haris ne ya kira sunanta, hakan yasa ta tsaya tana haki, Ta waigo tana kallon shi.
Tun kafin ya soma yi mata magana, ta ɗan ɗaure fuskarta, muryarta tamkar za fashe da kuka ta soma magana
"Na gaji da raina min wayau da su ke yi, don sun ga na damu dasu, shiyasa suke yi min wulaƙanci dashi da waccan mai fuskar tumaturin, tsawon one week ba wanda yai tunanin yayi musu wanka, da yake ba hankali ne dasu ba, ko tsamin jikin su basa ji, a tunani na yi musu gwaninta, yau da safe na tada dasu daga bacci naja su muka shiga toilet na datse ƙopa don inyi musu wanka, nasa su ka fara yin brush, bayan sun gama nace toh su tu6e kaya in yi musu wanka, ba ku ga irin wulaƙancin da su ka yi min ba, Jamima hada ce min wai ita bazata tu6e kaya inyi mata wanka ba, saboda tsarata ce ita, ban fita da komai ba, daƙyar na samu shi majnun nayi mashi wanka ahaka ma saida ya dinga watsa min kumfa a ido ina wanke wa, ita kuma jamima kusan dambe mu ka yi da ita, taƙi yarda inyi mata wankan, hada cewa sai dai inyi mata da wando a jikinta don kada in gan mata jiki............kasa ƙarasa maganar ta yi idanuwanta cike tab da ƙwalla, sai kace ba ita bace ta gama shan dariya tana bin majnun da gudu ba, ita babban baƙin cikinta, Jamima da take yi mata kallon tsararta, ta raina mata wayau, da ga ita har majunun sun raina azeeza saboda ƙarantarta, duk a tunaninsu tsararsu ce basu san cewa ta girmesu nesa ba kusa ba.
Dariya suka dinga yi mata, musamman parveen da bata jima da farkawa ba, Hada gabriel dake kishingiɗe saman gadonshi, farkawarshi kenan yaji azeeza tana kora jawabi.
Ganin yadda su ke ta yi mata dariya yasa ta bubbuga ƙafafuwanta ƙasa, ta zuƙunna tana kuka, Muryar Angel ce ta katse musu dariyar tasu da wani irin kasala take magana da busassun la66anta
"Ku daina mata dariya kuna ƙara 6ata mata rai, Azeeza ki daina kuka, yanzu fa ki ka gama shan dariya, ke kanki sun baki nishaɗi, sai kina yi musu uziri, kinga ke yayarsu ce, su kuma ƙannanki, dole sai ana haƙuri da juna.....' ta kai ƙarshen maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jamimah dake ta faman ɗaure fuska tana tsino ƙaramin bakinta.
"Zo nan" jin kiran Angel yasa ta ɗan saki fuskarta, ta soma tafiya tana tunkarar gadon ta, a bakin gadon ta tsaya tana kallonta"ba nan nace ki tsaya ba, dawo nan gefe na" tai maganar tana nuna mata gefen gadon, dawowa tai daga gefen gadon ta tsaya tana faman mutsustsuka rigar hannunta,
numfasawa tai tare da juyawa ta kalli majnun dake tsaye yana ta faman raba ido, hannayen shi biyu rufe da gabanshi, Parveen tace"Abanza, bayan ka gama nuna mana abun na ka shine yanzu zaka wani sa hannu ka rufe, kai ɗin nan ba ƙaramun shaƙiyi bane, ae wlh da ace nice zan maka wanka, da duk saina gurje farar fatarnan ta ka, aljani kawai" Tana magana tana jifarshi da harara idonshi akanta sai murguɗa mata baki ya ke yi.
"Zonan Majnun uban masu hankali" Angel ce ta kira shi, A hankali ya ke nufar inda take ba tare daya zame hannun shi daga gabanshi ba, a gefen gadon Ya tsaya dab da ita, Jamima tana a 6angaren dama shi yana a 6angaren hagu, kowa ya natsu yana jiran jin sasancin da Angel zata yi musu.
"Ku faɗamin meyasa kuka raina azeeza ne? Tsarar wasan ku ce ita? Daga taimako? Yau one week ba wanda ya kula da ba ku yi wanka ba, don ita ta taimaka zata yi muku shine kuke yi mata iya shege ko"! Tai maganar tana duban kowannansu,
Jamima ce tafara magana tana tsino baki
"Ae ni sai da nace mata, tabarnin inyi wankan ta ƙi bari inyi, bana son tayi min wanka, nafison su hanna su cuɗa min bayana ko ke...." tun kan ta ƙarasa maganar Angel tace"Oh saboda sune manya wanda suka isa dake, banda ita ko? Ɗaga mata kai tai alamar eh ta ƙara da cewa"azeeza fa ƴar ƙarama ce the same height as me, ta ya za'ai tayi min wanka."
Mamaki ne ya kama su Hannah, Kowa ya ɗan zaro ido suna kallonta, Angel tace"Okey," kafin ta maida duban ta ga majnoon"what about u? Meyasa ka rainata"? da buɗar bakinsa sai cewa yae"I don't want her to bathe me because she's so little, nafa girme ta, da ma ba ita ta ke yi min ba, Danish ne yanzu baya nan, Haris yana min da naufal"
Har cikin zuciyarta taji gabanta yaɗan faɗi saboda sunan Danish da majnon ya ambata, nan take taji wata irin kewarshi ta baibaye sassan jikinta, kasa magana tai, idanuwanta bakomai suke nuno mata ba face kyakkyawar fuskarshi, da sauri ta kwantar da kanta ta kifa fuskarta saman pillow, ganin hakan yasa suka fahimci dalilin shiga damuwarta, su kansu da Majnun Ya ambaci sunan Danish sai da zuciyoyinsu suka amsa.
Haris ne yaci gaba da yin magana yana duban su Jamima dake a tsaitsaye gefe da gefen na gadonta
"daga yanzu kada na kuskura na ƙara ganin wani a cikin ku ya raina azeeza, Ƴan ranin wayau, just because u saw her a little girl like u that's why ku ka raina ta, Let me tell you that even Angel, whom you respect, is younger than azeeza."
A matuƙar ruɗe Jamimah da majnoon suka kalli haris suna faman zare ido, Mamaki ƙarara akan fuskarsu, Hatta Gabriel da Sarah sai da suka jinjina maganarshi don basu ta6a sanin hakan ba, sai da ya faɗi yanzu,
Cigaba da magana haris yai,"Angel itace ƙaramar cikin mu kafin zuwan ku, tafi kowa ƙananun shekaru, ƴar azeezar nan da kuke rainawa yayarku ce,......." muryar Jamima da kokwanto ta furta"amma ae ƴar ƙaramace ko, meyasa ita bata yi tsawon Angel ɗin mu ba"? Hada ruƙe qugu tana magana.
Kafin haris yabata amsa deeja ta kar6e da cewa"Saboda haka Allah ya halicce ta, baki ga banbancin da ke a tsakanin kowannan mu bane? Wani yana da tsawo wani Jiki wani mara ƙiba, ahaka kowa da shekarunsa" da alama jamima bata fahimci me take nufi ba, Majnun sarkin mahaukata yace"to itama taje Allah ya ƙara mata tsawon mana sai ta koma kamar Angel" bismilla parveen tai tare da yunƙurawa ta sauko daga saman gadonta, ta rarumi pilow, majnun na ganin ta yi hakan ranshi ya bashi cewar shi zata buga, aiko da gudu ya nufi sashen toilet ɗinsu yana dariya, Sai da tafara zuwa ta kar6i kayanshi da azeeza ta jefar ƙasa ta ruƙo su da hannu ɗaya, yayin ɗayan hannun ke ruƙe da pillown data ɗauko Tabi bayan shi Cikin sashen toilet ɗin, Bata jima da shiga ba suka jiyo sautin kukan shi yana zazzaga mata masifa.
Murmushi kowannan su ya saki, har lokacin Azeeza na zuƙunne ƙasa kanta saman gwiwarta, Saukowa daga saman gado Gabriel yai tare da nufar inda take, har ya kusa ya isa muryar haris ta katse shi"me zaka mata" Kallon shi Gabriel yai ba tare daya bashi amsa ba, Ya cigana da tafiya
"Kada ka kuskure kace zaka yi mata magana, shisshigin yayi yawa, wannan fa ba ƴar uwarka ba ce, yakamata kadaina manne mata" rai 6ace haris ke yi mashi magana, ko ta kanshi Gabriel baibi ba, damuwarshi akan Azeeza ne, baya son yaga tana kuka, saboda ƙaunar da ta ke yi mishi, zuƙunna yai agabanta tare da kai hannu ya ɗago da kanta fuskar nan sharkaf da hawaye ta ɗaura idonta akan nashi
"Its okey azeeza, stop shedding ur tears, i don't know why ki ke son zubar da hawayen ki, akan abunda bai kai ya kawo ba," hannayen shi ya ɗaura saman fuskarta yana goge mata hawayen, duk sun zuba ido suna kallon su banda Angel da ke ta shan kukanta ba tare da sauti na fita ba, An fama mata ciwon dake damun zuciyarta.
Ganin yaƙi jin maganar shi hada share mata hawaye hakan yasa haris yunƙura ya miƙe zai nufe su, Muryar azeeza na kerma tace"dan Allah haris ka ƙyale shi, ni bansan meyasa ku ka ɗaura mashi karan tsana ba, koda ace Gabriel shine silar abunda ya faru da Danish, bai kamata kuna mishi haka ba, tunda ya nemi yafiyarmu ya gane kuskurenshi, shi kanshi fa bada son ranshi hakan ya faru ba, Angel ta riga ta yi mana bayanin komai......"
Tunkan ta ƙarasa maganarta, deeja ta katse ta da cewa"Azeeza kina da matsala! Tausayin ki bazai ta6a bari ki ga laifin shi ba, ke kowa naki ne, dame gaskiya da mara gaskiya, yanzu dik irin abunda Gabriel yai ma ɗan uwan mu Danish ke baki gani ba? Cikin mu ba wanda bai yi zazzza6in rashin Danish ba, wannan ƙaton Ya haddasa mana baƙin Ciki acikin zuciyar mu, ya naƙasa mana ɗan uwan mu, amma ahaka kike biye mashi, har wankin kayan shi ke kike yi kamar baiwarsa, kamar fa kina ƙara bashi damar da zai cigaba da cutar da mu ne" cikin nuna 6acin rai Deeja ta yi maganar, Dama sun fi kowa tsanar Gabriel ita da Haris, Su biyun nan sun zame mashi ciwon kai da masassara, Deeja da haris tamkar abu ɗayane, Kusan halinsu ɗaya, Idan suka tsani mutun sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya, kamar dai lokacin da Aka kawo Angel da suka addabe ta kafin asasanta, Zafin zuciya ne dasu, suna da wuyar sha'ani sai dai duk da hakan suna da kyakkyawar zuciya.
Ranshi bai ta6a 6aci ba irin na yau, Zame hannayenshi yai daga saman fuskar azeeza da yake share ma hawaye, Ya miƙe tare da juyawa yana kallon haris dake a tsaye yana jifar shi da kallon tsana.
"Bafa tsoron ku nake ji ba, sannan ba ƙarfi kuka fi ni ba, duk abunda ku ke yi min na ƙyale ku ne saboda nasan laifina ne, na rasa gane ku wasu irin mutane ne, sai kace ba kusan tsautsayi ba, nifa bada son raina na aikata mashi hakan ba! yadda ku ka ji zafi acikin zuciyarku bai kai kwatankwacin wanda naji ba, a lokacin dana naushi idonshi, ga Angel nan ku tambayeta irin tashin hankalin dana shiga ae ita tasa komai, har cewa nayi ta cire idona ta sanya mashi duk don saboda tausayin shi da naji........." kasa ƙarasa maganar yai, idanuwanshi cike tab da kwalla, jikinsu Hanna ba ƙaramin sanyi yayi ba, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalaman shi,
shigowa cikin ɗakin parveen tayi hannunta ruƙe dana majnun da ta sanyawa kaya, har sun shirya, Ganin Gabriel dake tsaye ido ya canza launi ga kuma haris agabanshi, hakan yasa ta dan dakata da yin tafiyar tana kallonsu,
"kuna ɗaukata tamkar wani maƙiyin ku, nifa ba bare bane acikin ku, kawai don bamu arayu atare bane sai daga baya na tsinci kaina acikin, da ku da ni duka prisoners ne da ƙaddara ta haɗa mu rayu a wuri ɗaya, akan me zan cuci wani acikin ku? Babu wanda yafi wani fa acikin mu! Bana jin daɗin juyamin baya da ku ke yi, nifa mutunne ba dutse ba, ina da zuciya a ƙirjina, dole in ji zafin ƙiyayyar da ku ke nuna min, meyasa nima baza ku soni ba ku ƙaunace kamar yadda kukeson junan ku? Yai tambayar cikin ƙunar rai yayin da ya ke bin kowannansu da kallo.
"Hatta azeeza da take ƙarama acikin ku tafi hankali, ita da Angel, sune waɗanda nasan ba za su ta6a juyamin baya ba, kuma ɗin rashin fahimta ne, a bun da baku sani ba, Danish shine silar da hakan ta faru, mun samu sa6ani dashi, ya sanya hannu ya shaƙe min wuyana, nayi nayi ya saki yaƙi saki kamar zan mutun a lokacin koda ace wani daga cikin ku ne yaji an shaƙe mashi wuya za'a kashe shi cikin fitar hayyaci zai iya yin komai donya ƙwaci kanshi, to nima shine abunda nayi at end nazo ina danasani, da ace da son raina na aikata mashi hakan ai baza ku ganni ina jinya ba,"
Haƙiƙa kalaman Gabriel sun yi matuƙar yin tasiri acikin zukatansu, duk sai su ka ji ba daɗi irin wariyar da suka nuna mashi.
Hannu yasa ya share hawayen dake akan fuskarshi, Idonshi akan na haris yace"ina ƙara baku haƙuri, idan ma hakan bai yi maku ba, zan duƙa saman gwiwowina in roƙe ku akan ku yafe min, kai idon ma kuna so ku cire min idona ne don ku huce takaicin abunda nayi maku to gasunan, ku yi abinda ku ka ga dama, amma karkuce zaku raba ni da azeeza, saboda tana bani kulawa, ina jinta tamkar ƴar uwata Gabriella,"
Yana kawo nan a maganarshi, Ya zube saman gwiwowinsa, Da sauri azeeza ta miƙe tana roƙonshi akan ya tashi tsaye ya daina zubar da hawayen shi.
"Kada ka damu, komai ya wuce awurina, koda ace su basu yafe maka ba ni na yafe maka" acewar Hannah. Tana rufe baki parveen ce"tunda dai ya riga ya faru, bamu isa mu canza komai ba, don haka nima na yafe maka" Ɗaya bayan ɗaya suka dinga cewa sun yafe mashi, Mutun ukune basu tanka mashi ba, Haris da deeja da kuma Naufal, Su sunce sai an dawo musu da ɗan uwansu sun ga awani hali yake ciki tukunna zasu Yafe mashi, a ƙalla ya ji sanyi aranshi ganin dayawan su sun yafe mishi sunce zasu cigaba dayi mashi magana bazasu ƙara nuna mashi wariya ba, Yaji dadin hakan ga kuma Azeezar shi mai sanya shi farin ciki, itama tana Atare da shi, bayan komai Ya lafa, Gabriel Ya miƙe ya nufi sashen toitet ɗinsu, don yayi wanka,
ƙarasa shigowa cikin ɗakin parveen ta yi hannunta ruƙe da na majnun don tun ɗazu tana a tsaye tana sauraronsu Gabriel ganin sun samu maslaha atsakanin su yasa ta motsa, sai da ta fara wurga pillown hannunta saman gado tukunna ta nufi jamima da ke a tsaye gefen gadon Angel ta damƙo hannunta, ta haɗa su duka biyun takaisu gaban Gadon azeeza a lokacin harta koma ta zauna.
"Ku bata hakuri idan ba so kuke ranku ya 6aci ba," acewar parveen, Ɗagowa su kai suna kallon fuskar azeeza da tayi jawur.
(Next page 62 zaku same shi in kun gama wannan, Takun farko Yana gab da zuwa ƙarshe)