CIN ZUMA (DENTAL FLUOROSIS)

CIN ZUMA (DENTAL FLUOROSIS)

DENTAL FLUOROSIS

Cin zuma wato "Dental Fluorosis" lalurace ta hakora dake sauya launin hakorar ya dawo kamar kasa-kasa haka. Sai dai lalurar cin zuma wato "Dental Fluorosis" ana samun tane tun yaro yana karami, musamman yan shekaru takwas 8 zuwa kasa, kafin hakoran girma wato "Succeduous Teeth" su fara tawo wa.

MEKE JAWO CIN ZUMA "DENTAL FLUOROSIS" 

Cin zuma wato "Dental Fluorosis" na aukuwa ne ta dalilin shan ruwa mai dauke da sinadarin "Fluoride" fiye da kima, ko kuma wasu hanyoyi da yara zasuyi amfani da sinadarin "Fluoride" fiye da kima wato "Excessive fluoride intake" daga man goge hakori wato "Toothpaste" ko makamanci hakan.

Cin zuma "Dental Fluorosis" lalurar hakora ce da ke munana hakoran kawai, amma bata da illa ga lafiyar hakoran. Duk wanda ya riga ya fidda hakoran girma "Succeduous Teeth" baya daga cikin masu hatsarin kamuwa da cin zuma. 

MAGANI 

Cin zuma bashi da wani magani wanda ake amfani dashi wajen kawar dashi. Domin cin zuma baya raunata hakora sai dai yasa hakora sun chanza launi daga fari zuwa ruwan kasa-kasa. Mafiya yawan mutane masu dauke da cin zuma suna da kariyar samun ramin hakori wato "Dental caries" fiye da sauran mutane. Sabida sinadarin "Fluoride" nada matukar mahimmanci ga lafiyar hakora, sai dai idan kuma yayi yawa hakan ke jawo matsalar cin zuma lokacin girman yara. 

HANYAR KARE YARA WAJEN KAMUWA DA CIN ZUMA

Babbar hanyar kariya daga cin zuma shine, rage amfani da ruwa mai dauke da sinadarin "Fluoride" sosai, sai kuma kula da yara wajen zuba man goge hakori wato "Toothpaste" kar a barsu suna zubawa dewa ko kuma sha. 

Na karshe shine ziyartar asibiti ko likitan hakori duk bayan wata shida. 

Idan kana da damuwa data shafi hakora ko chanjin launin hakora zaka iya tuntubar asibiti ko kuma likitan hakora akoda yaushe. 

Comr Ayuba Musa (Rdst) 

12 Nov, 2023

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post