Kurkukun Ƙaddara chapter 67 Complete

Kurkukun Ƙaddara chapter 67 Complete

 


💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E67


daga alƙalamin Boss Bature


Mutun uku ne suka haɗu wurin wanke mata gashin kanta saboda yawanshi, Angel da Hanna sai Seeja, Sosai suka murje gashin kan nata, Bayan sun kammala wanke mata kan, suka barta cikin toilet din don tayi wanka, Angel fa jikinta duk ya yi sanyi, a ƙagare take da su samu damar da zasu ke6e da ita don suyi magana, sai dai ga dukkan alamu ita batul ɗin bata son su yi magana, shiyasa take kakkauce mata, Bayan wasu ƴan mintuna, Batul ta fito daga wakan, dama tun kafin fitowarta Angel ta ɗauko mata sabbin kayanta, ba tare da 6ata lokaci ba, ta zura uniform din a jikinta, Masha Allah, zayyana irin kyan da batul tayi a cikin kayan nata 6ata baki ne, abunka ga fara sol, Sun ƙara fiddo mata da kyanta, don ma ta ɗanyi rama.


daga ciki ta sanya red vest dinta, sama ta ɗaura wrap coat dinta, kafin ta sanya black trouser din, Angel ce ta taimaka mata wurin ɗaure igiyar coat ɗin, ta ɗaura mata Cotton scarves ɗinta saman wuyanta, Bayan ta kammala gyara mata su tsaf a jikinta.


Su Parveen sai santin kyanta su ke yi, Hannu biyu angel ta sanya wurin janyota a jikinta, sosai ta rungumeta, tana ɗan bubbuga bayanta, in a low voice ta furta mata"Ina son magana da ke, amma na lura kamar baki so why"?  Muryarta na ɗan rawa tace"Angel, banason tuna abunda ya faru dani, pls kada ki matsa min kada ki tambaye ni komai, na roƙe ki, kuma bana so hakan ya 6ata maki rai" suna yin maganar ne ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba.


"Shikenan batul, bazan tambaye ki ba, ni kaina bana son na takura maki, zan jira ki har zuwa time da kika ji zaki iya sanar dani sai ki faɗa min" ta amsa mata da toh," Deeja dake ta kallonsu manne da juna ta fahimci cewa magana su ke yi, bayan sun raba jikinsu, ta dinga bin su azeeza tana rungume su a jikinta tana faɗa masu irin kewarsu da ta yi, Deeja kuma taja hannun Angel su ka koma gefe ɗaya,


 Tambayarta ta yi me suka tattauna da batul, ta sanar da ita cewa ta tambaye ta ne game da abunda ya faru da ita amma bata faɗa mata komai ba, Deeja tace"kada mu takura mata, tunda ta nuna bata son mu sani, mu ƙyale ta kawai, wata kil hakan zaifi mana kwanciyar hankali," Angel ta gamsu da maganar deeja. 


Badajimawa ba, Giants suka kawo masu lafiyayyan abinci, Saboda tsabar ƙauna, a baki suka dinga ba batul tana ci, sunƙi bari ta sanya hannunta taci, hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yayi ba, tabbas an zalunce ta da aka raba ta da ƴan uwanta, amma yanzu Alhamdulillah tunda gata a cikinsu, da ranta da lafiyarta.


Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka tafi dasu, A saman shimfidar sarah, suka zazzauna suna fira tare da batul, Angel tana zuƙunne gaban akwatinansu, Ta buɗe ta ɗauko Nail cutter da nail filler tare da madubi, ta dawo ta miƙe ma Sarah tace gashi ta gyara ma ƴar uwarsu akaifa, Murmushi sarah tasaki, tare da sanya hannu ta kar6a, Kafin su fara gyaran akaifar, Angel tace ta ɗan dakata, tana so su kalli faces ɗinsu a cikin madubi, ita da ƴar uwarta batul, Gefen batul ta zauna tare da ɗaga madubin, Ta haɗa fuskokinsu wuri ɗaya, Suka natsu suna kallon juna, hakanan Angel ta dinga jin faɗuwar gaba a yayin da take kallon fuskar batul ta cikin mirror, su azeeza sai faman leƙo da fuskokinsu suke yi suna kallon su.


"An ta6a faɗa maku cewa, Kuna bala'en kama da juna" Sarah ce tai maganar, parveen tace"wlh kuwa nima saida ki ka yi maganar nan tukunna na lura da hakan, Angel da batul suna kama sosai, musamman ta wurin shape ɗin bakinsu, duk da ba launi ɗaya bane, da kuma hasken fatarsu, gashin kansu ma Ya yi shige,  hatta tsawonsu iri ɗaya,"


 Deeja tace"ae hatta Yatsun hannuwansu dana ƙafafuwansu iri ɗaya ne sak babu bambanci, najima da sanin wannan ban ta6a faɗi bane" sarah tace"to kodai  ƴan gida ɗaya ne"? Girgiza kai Yasmin tai tare da cewa"A labarin da Angel ta bamu, ita kaɗaice Awurin daddynta, mommynta ma, tun tana yarinya ta gudu tabarta, bata da ƴar uwa mace tun da ta taso a rayuwarta,"


 Sarah tace"hmmm adai yi shiru kawai amma fa ni akwai abunda nake zargi, ina da wata baiwa da ku ba ku sani ba, tun kasancewa ta a prison, nake wannan hasashen, nasha ganin masu kama da juna wanda su basu lura da hakan ba, sai dai ina tunanin zaman tare ne yasa muke kamanceceniya da juna, yanzu a cikin ku nan, kaf ɗinku Naga kamanceceniya atsakaninku da junan ku, Hatta wannan yarinyar da aka kawo mu tare da ita, Me take da suna....." Eve ce ta ƙarasa mata maganar da cewa"Kina nufin Ƴar gidan daddy" jinjina kai tayi "eh ita nake nufi, akwai kamanceceniyarta da wani acikin ku, amma bazan faɗi ba" tana ƴar dariya ta yi maganar, 


"Ko kina nufin azeeza? Don kinga kalar gashinsu yayi shige da launin fatarsu," girgiza kai tayi"a'a, ba azeeza ba, bana so na faɗi maku ne"


Roƙon ta su ka dinga yi haɗi da yi mata magiya akan ta faɗa masu da wa take kama, da kuma sauran waɗanda ta ke hasashen suna da kamanceceniya a tsakaninsu, tace masu itafa su daina yarda da maganarta, Ƙarya ta ke yi masu"


 Haushin da suka ji ne yasa suka dunƙule hannu suna yi mata dundu abayanta, Abun saiya koma wasa, duk wannan abun da suke yi Angel da batul   suna sauraronsu, sai dai hankalinsu ba akansu Ya ke ba, Yana akan junansu, Sai kallon fuskokinsu suke yi ta cikin madubi kamar zasu lashe juna, Sai da suka gama ƴar buge bugen da sarah, kafin daga bisani, kowannansu Ya natsu, suna ta nishi kamar waɗanda suka sha gudu.


Bayan sun samu natsuwa, Sarah ta soma gyarama batul akaifarta, Allah yayi mata baiwar Iya gyara akaifa,  Batul taji daɗin ganin yadda ta gyara mata akaifarta, ta dinga yi mata godiya, Sarah tace tadaina yi mata godiya, domin kuwa babu godiya a tsakanin prisoners,"


Ataƙaice, Cikin ƴan kwanakin nan da aka dawo masu da batul, Sun samu farin ciki mara misaltuwa, Tamkar an ya ye masu damuwar dake damun so, koda yaushe suna atare da ita, dama batul akwai iya kalami mai ratsa zukata, haka zata zauna tana kwantar masu da hankalinsu, da deeja tare da Angel, waɗannan mutun ukun sun zama tamkar iyaye agare su, yanzu batul ta fara murmurewa, tsawon sati biyu da aka dawo da ita Jikinta yafara dawowa normal, babu ramar nan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, har tambayar Angel tayi bayan bata nan an ƙara ɗaukar wani cikin su Hibba, ta sanar da ita cewa ba a ƙara zuwa ɗaukarsu ba, saboda babu wanda ya ƙara yin jinin a cikinsu, Allah ya yaye masu, sun samu salama, har cikin ranta taji daɗin jin hakan, Angel taso ta tambayi batul game da labarin da Gabriel ya bata na yarinyar daya gani tana gudu saman hawa na uku, saboda a suffar da aka dawo da batul yayi dai dai da yarda ya zayyana mata ita, hada guntuwar rigar daya gani a jikinta, Tabar abun a cikin zuciyarta ne, tun da ta nuna bata son maganar.


Har ila yau shiru ba'a dawo dasu Haris ba, Sun zuba ma sarautar Allah ido, addu'a kawai suke binsu da ita, A 6angaren Angel bata ƙara tada zancen dura tagar nan ba, saboda alƙawarin da Danish yace ta ɗaukar mashi akan bazata haurata ba, duk da a lokacin bata amsa mashi ba, sai dai taji ba za ta iya karya mashi alƙawarin ba..........


💔PRISONERS💔


Kwakkwance suke saman gadajensu, suna ta sharar bacci, har safiya ta yi amma basu farka ba, Jiya sun aikatu sosai, sai da suka wanke uniform ɗinsu duka da tsafaffin da sababbin kamar yarda suke yi in zasu wanke su sai su ɗaura bargunansu a jikin su,


 Bayan sun kammala wankin su ka shanyasu zuwa lokacin da suka bushe suka mayar da tsoffin a jikinsu, sababbin suka ninninke su acikin akwatinansu, basu huta ba saida suka wanke bargunansu, suka shanyasu saman igiya, bayan sun kammala suka wanke toilets dinsu duka uku, suka bama furennin nan ruwa, Daga bisani, suka dawo cikin ɗakinsu, shima suka gyara shi tsaf tsaf komai Ya koma normal, a lokacin dare yayi suka kwanta don su huta, in the midnight Angel ta tada kowannansu don su yi addu'a kamar yarda suka saba, ga bacci a idonsu da gajiya amma ahaka suka zaune tare da ɗaga hannayensu sama suna kai kukansu wurin Allah, bayan sun kammala ne wani baccin ya ƙara yin awon gaba dasu, Shiyasa har gari ya waye basu tashi ba, saboda basu samu isasshen bacci ba jiya. 


Azeeza da Jamimah suna a kwance saman gaɗo ɗaya, sarah tana a kwance ƙasa saman shimfiɗarta, yayin da batul ta ke a kwance saman gadon Danish ita da Angel, ƙudundune cikin bargo, atakure su ke gadon ya yi masu kaɗan ahaka suka kwana, su parveen duk suna asaman nasu gadajensu.


Wata irin zufa ce ta soma wanke fuskarta, ta dinga tsastsafo mata daga jikinta, Yatsun hannayenta da ƙafafuwanta suka soma kakarwa, Mafi yawancin lokaci idan hakan ya faru to mafarki ne ta ke yi acikin baccin ta,


_Ta tsinci kanta acikin wani gini mai girman gaske, mai ɗauke da tagogi babu ƙopa ko ɗaya a jikin shi, tsananin tsoro da firgici ya kamata, ta dinga kuka tana ambaton sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, wasu halittu ne ke fitowa ta jikin bango ɗauke da suffar namun daji, munanan gaske, gaba ɗaya ita suke tunkarowa, gashi babu hanyar da zata gudu daga cikin ginin, fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana girgiza kanta tamkar zai 6alle, Halittun na dab da ƙarasowa gabanta, Sai ga wata halitta ta faɗo ta saman ginin ɗauke da manyan fuka fuki sai shawagi take yi tana kewaye tsakiyar Ginin, kafin ta karyo kwana ta sanya hannayenta biyu ta ɗauke Angel tayi sama da ita ta fuce daga Cikin Ginin_


A dai dai nan mafarkin nata ya katse, A firgice ta farka daga baccin tana faman zare idanuwanta, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa, zufa duk ta wanke fuskarta, muryarta na rawa ta soma ambaton


"A'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem" sau uku tana ambatonta.


Bayan ta kammala taji sauki acikin ranta, ta juya ta kalli batul dake ta sharar baccinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da zuro ƙafafuwanta ƙasa ta sauko daga saman gadon, zuciyarta acunkushe da tunanin mafarkin da ta yi yau, ta rasa gane me ma'anar mafarkin ke nufi kodai shaidan ne ya haddasa mata yin shi, sai dai tana ji acikin ranta kamar akwai wani abu da ake son nuna mata acikin mafarkin, Taya zata iya fahimtar hakan? Wani ginine ta gani acikin mafarkinta? Babu ƙofa a jikin shi sai dai tagogi, ga wasu halittu na ƙoƙarin kawo mata hari, abun da ya ɗaure mata kai, wannan halittar data 6ullo ta saman ginin dake a datse babu ƙopa, taya akai ta shigo ita? Harta taimake ta kuma ta fitar da ita daga cikin ginin da babu ƙopa a jikin shi?


 Ganin tana ƙoƙarin burkita lissafin ƙwaƙwalwarta ne yasa ta dakata da yin tunanin, da sauri ta juya ta nufi toilet don ta yi fitsari, shiga ciki tai tare da jan jam lock ta datse ƙopar, Juyawar da zatayi keda wuya taji gabanta ya faɗi ras! Ba tare da sanin dililin hakan ba, Acikin zuciyarta ta soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un" 


kusan sau shida har saida taji zuciyarta ta ɗan lafa tukunna ta ƙarasa shiga ciki, Tayi abunda ya kawota, bayan ta kammala kafin ta fita ta ɗan juya ta kalli furennin dake acikin tukunyar, wannan dogon furen daya kere tsayin sauran launin punch pink, ganyayyakin Jikin shi sunyi baƙiƙƙirin dasu, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta koma ta ɗebo ruwa a bucket takai shi bakin tukunyar ta zuƙunna tana goge bakin jikin shi da hannayenta gani take kamar goga mashi baƙin akayi, sai dai koda ta goge babu abunda ya canza har ruwa ta zuba mashi ta wanke shi yaƙi canza launi, miƙewa tayi taje ta ɗauko detergent tsabar hauka hada Soso ta zuƙunna gaban tukunyar ta dinga goge ganyayyakin jikin furen don su koma launinsu na asali, sai dai kash sunƙi komawa, kamar tana ƙara masu baƙi, a ƙarshe data gaji ta maida soson da omon, ta fito daga Cikin toilet ɗin Jikin ta ba ƙwari,  hakanan ta dinga jin kamar faɗuwar gabanta yana da nasaba da canzawar launin ganyan furen nan, duk da batasan ran wanene akan shi ba. 


A bakin ƙopar toilet ɗin ta jingina bayanta, Idanuwanta acike tab da ƙwalla, daga Cikin ɗakinsu ta soma jin motsin buɗe ƙopa, da farko ta yi tunanin giants ne masu kawo masu abinci,  shiyasa taƙi motsawa


 kwatsam! Ta soma jin shessheƙar kukan mutun acan cikin ɗakinsu, Da gudun gaske ta faɗo ɗakin a sukwane ta kai idanuwanta kan benan inda take jiyo sautin, Bakowa idanuwanta ke nuna mata ba face Majnoon fuskarshi ta yi jawur da ita, jan tabo ta ko'ina a jikin shi, jini ya kwanta sosai, daga shi sai jan wandonshi a jikin shi babu riga, ya rame sosai, kamar ba mutun ba, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tana ƙoƙarin motsa la66anta donta kira sunanshi karaf idanuwanta suka sauka akan fararen ƙafafuwan mutumin dake a gefen shi, a matuƙar ruɗe Angel ta shiga bin ƙafafuwan da kallo daga gani macace, koma wacece taji jiki na fitar hayyaci ta jigata sosai, duba da irin yarda jikinta keta kerma babu alamun lafiya atattare da ita, Hannunta ɗaya ruƙe da pant na mata launin Pink colour..........."


Adai dai nan na ajiye alƙalamina✍️🤟


(Next page Yanzu zan sa shi in sha Allah, Masu son shiga paid group na facebook Ga link Kuyi mata magana after kun biya zata sanyaku👇


https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL


waɗanda ke yin arewa book su yi following account ɗina, zasu dinga samun Littafin kurkukun ƙaddara hada abban sojoji, Ga link ku yi joining👇


https://arewabooks.com/chapter?id=6535288c429337735998e5aa


Masu son paid group na whatsapp 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post