DALILAI GUDA GOMA (10) DAKE SA JIN ZAFIN MAMA GA 'YA'YA MATA.

DALILAI GUDA GOMA (10) DAKE SA JIN ZAFIN MAMA GA 'YA'YA MATA.

Breast Itching

Mafi yawancin lokuta na rayuwar 'ya'ya mata, suna fiskantar matsalar jin zafi a mamansu. Hakan yana faruwane badan nuna  alamar wata matsala ba, saiko akan wassu kadan daga wasu matsalolin. Ciwon kyirji na 'ya mace kan iya zama babban matsala.  


Zafin mama ga 'ya'ya mata kan iya zama daya daga cikin wadannan dalilan dazan kawo kamar haka:

1 SHAYARWA:

 Mace mai shayarwa kan shiga wannan matsala ta jin zafin mama dakuma radadi a bakin mamansu yayinda suke shayarda jariri musamman idan jariri ko jaririyar  na cizon bakin maman. Allah ka albarkaci iyayenmu mata. 😰 Idan uwa tana fiskantar wannan matsalar, shawara shine taziyarci likitan yara (paediatrician) Dan samun shawarwari na musamman. 


2 CUTA (INFECTION): 

 uwa mai shayarwa zata iya kamuwa da wata cuta harmadai mace mara shayarwarma, za'aji zafi, zogi, dakuma kunburi. Idan haka yafaru a ziyarci kwararren likita zaibada maganguna (antibiotics & analgesic) dan shawokan cutar, musamman Idan aka ziyarci likitan akan lokaci. Tabbas ta ziyartar likita ne, zaisa kigane wacce irin cutace, sannan abada magangunanda suka dace. 


3 TARE MAMA MARA INGANCI: 

Tare mama (bareziya) anyisune dan tallafawa mama. Amma, Idan har bai iya tallafawa mama yadda yadaceba, zaisa tsokar datake daga mama zuwa kirji yariqa jawuwa, daga qarshe yafara zafi. 


4 CHANJE CHANJEN  SINADARAN HORMONE  (HORMONAL CHANGES): 

Canje chanjen wasu sinadarai da ake qiransu a likitance dasuna "estrogen dakuma progesterone". Wannan dalilinne ke yawan haddasa zafin mama wa 'ya'ya mata. 'Ya'ya mata kanji wannan zafin tsakanin kwanaki 3 zuwa 5 kafin watan jininsu (monthly period). 

Wanda hakan nafaruwane yayinda estrogen dakuma progesterone suka kara yawa ko ace suka kara haurawa. 


5 JUNA BIYU (CIKI) : 

Zafi dakuma zogin mama wassu alamomine nasamun ciki. Idan mace tana watannin uku (3) nafarko dasamun ciki, zata riqa fiskantar wannan matsalar. 


6KWURJI : 

Kwurji da yake daukeda iska, ruwa kodai diwa yakan fito akan mama sannan yasa mace jin zafin wurin. Wannan kwurjin yakan bace dakansa bayan wasu 'yan kwanaki, idankuma bazaki iya jiransaba ki dubi likita. 


7 CIWON DAJI (CANCER) : 

Dukda dacewa zafin mama baicika zamowa alamace ta kansar mamaba, amma wasu lokutan zafi yana daga cikin alamomin kansar mama, sannan wani launin ja, kokuma wani launin ta daban, dakuma kumburi.  Dazaran mace taga haka taziyarci asibiti cikin gaggawa. 


8  WASSU MAGANGUNA (SIDE EFFECT OF SOME MEDICATIONS):

  Wasu maganguna da akesha dan magance wasu matsalolin,  sukan sakawa mace zafin mama. Misali magananin tazaran haihuwa, maganin ciwon qoda, maganin ciwon zuciya dadai sauransu, sukan iya haifarda wannan matsalar yayinda mace take shansu.


9 RAUNI (INJURY): 

 Mamar 'ya mace kankansace bakamar yadda yakeba wannan ba rauni bane. Rauni shine lokacinda tayi wani hatsari kokuma idan ansha yimata tiyata a maman nata. Zafin yakan dauke bayan wassu 'yan kwanaki ko satuttuka. Idanko yawuce zuwa wata to gaskiya a ziyarci asibiti musamman Idan akwai kurjewa, kumburi, launin ja, ko kurji. 


10 MATSALAN BAYAN YIN TIYATA 

Wasu sukanje asibiti musamman, badan komaiba saiko dan ayi masu qarin mama. Idanko za'ayi qarin maman saiko ayi tiyata, bayan angama dawasu lukota kuwa, saisu riqajin zafi a maman. Zafin zai iya zama mai cutarwa wani lokaci kuma bazai cutarba, komadai wannene daga ciki yanada kyau a ziyarci likita.


 NOTE: wani zafin da mata suke fiskantar badaka mama bane, daka kirjinsune. Kunga kenan zuwa asibiti shine matakin dauka nafarko. πŸ™πŸ™

Allah ya albarkaci iyayenmu mata🀲🏻🀲🏻

Mashkur Abdullahi Tsafe

Health Educator

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post