💋Kurkukun ƙaddara💋
E71
Daga alƙalamin Boss bature
💋PRISONERS💋
Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka.
"Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki" ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi.
"Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi,
Gyaɗa kai Angel ta yi"shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma ɗaki, don't ever expect me to worry about you anymore."
Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita.
"Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that's why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba'asin shi, irin wannan ƙauna haka........" ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba.
"Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser ɗina shiyasa ki ka ɗaga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It's just a rash
ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke......." bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu.
"Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki" ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta.
"Bana so ba sai na gani ba" ta faɗa tana harararta
"Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, " bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel.
Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta"Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki," ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa"Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, "
A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta
"Angel bayan an ɗauke ni daga cikin ku, kamar yarda na faɗa maku, ɗaki ne su ka kaini ni kaɗai, a saman gadon su ka kwantar dani, bakomai zan iya tunawa ba, na dai san sun cire min kayan jiki na, sannan Naji ana shafa jikina ta ko'ina, ba tare dana iya motsawa ba, kafin daga bisani naji ana tsotse......." bata ƙarasa ba ganin yadda Angel ta runtse idanuwanta, muryarta ƙasa ƙasa tace mata ina sauraronki ki ci gaba da magana
"Jinin da ke fitowa ta gabana shi naji ana tsotse shi"
Zuciyar Angel tuni ta soma tashi.
"Naji zafi sosai kamar zan zauce, tsawon lokaci Ana tsotse shi har zuwa time da naji bacci ya ɗauke ni, daga nan bansan me ya faru ba, lokacin da na farka banga komai ba, sai kayan abincin da aka ajiye mini Saman table, a bunda ban yarda dashi ba a cikin kayan abincin akwai wani luluyayyan abu fari fat guda ɗaya aka ajiye shi a tsakiyar tsokokin Nama......."
Ba ta kai ƙarshen zancen nata ba, Angel ta yi saurin katse ta da cewa" Allah yasa ba ki ci ba" jin haka yasa ta haɗiyi yawu fuskarta da alamun damuwa tace"Naci Angel, yunwa nake ji sosai a lokacin, komai sai da na ci"
Angel tace"amma bayan kinci sai me ya biyo baya"?
Numfasawa Batul ta yi kafin taci gaba da cewa"bugun zuciyata ne ya ƙaru, na dinga jin faɗuwar gaba, yanzu haka da na ke yi maki magana, akwai Jan tabo saitin zuciyata, zan nuna ma ki shi idan na gama baki labarin abunda ya faru, tsawon 4 days da inayin menstruation abunda ake yi min kenan kamar na ranar farko, Bayan jinin ya ɗauke, saina samu sassauci, sai dai kewarku da ta addabe ni, damuwa ta hana ni yin walwala, haka zan zauna ni kaɗai a ɗakin ina ƙwala maku kira babu mai jina, kamar zan yi hauka Angel, tun ina kuka har na gaji na daina, Sai na koma ina yin addu'o'in da ki ka koya mana, idan na karanta su sai inji sanyi a cikin raina, har ma in shiga toilet in yi wanka, idan na fito sai in kwanta saman gadon da ke a cikin ɗakin, kullum sai an kawo min abinci amma ban ta6a ganin waɗanda su ke kawo min shi ba, sai dai in gan shi A jiye saman table, sannan duk in a ka kawo min abinci sai naga wannan Abun dana faɗa maki luluyayye, Ina jin daɗin cin shi, cikin wata uku da bana atare da ku sau Uku ina yin jinin nan akowani ƙarshen month, kuma duk in nayi abunda su ke yi mini kenan, tsotse jinin da ke fitowa......." hawaye ne kwance a cikin idanuwan ta, ita kanta Angel ɗin idanuwanta A cike suke fal da hawaye gani take kamar Akwai wani abu da su ka yi mata ta hanyar abincin da su ke bata tana ci, musamman da ta ji ta ambaci luluyayyen abun nan fari da a ke sako mata cikin abinci, hankalin ta bai kwanta da shi ba.
"Batul inaso ki faɗamin ko kin ta6a gudowa daga Cikin ɗakin da aka kai ki?" ɗaga mata kai Batul ta yi alamar eh kafin ta ɗaura da cewa"Na ta6a samun damar durawa ta window ɗin da ke a cikin toilet ɗin ɗakin, na watso da gudu Ina neman hanyar da zata dawo dani cikin ku, A tsorace na ke a lokacin bani acikin hayyacina bansan meya faru ba, na dai ji kamar na faɗi ƙasa, kaina ya bugu, Bansan wanene ya mayar dani ɗakin da aka kai ni ba, lokacin dana dawo cikin hayyacina acan na ganni kwance saman gado, tsabar takaici yasa Na fashe da kuka har na kai ga zazzaga masifa ni kaɗai kamar mahaukaciya, a ƙarshe na haƙura na koma na kwanta, ina kukan zuci......." dakatawa ta yi da yin maganar tare da sanya yatsun hannunta ta share ƙwallar da ke gangarowa ta cikin idanuwanta.
"Ina so insan a hawa na nawa ne aka kai ki, Na ta6a yin mafarki da ginin kuma ni idan nayi mafarki yana zama gaskiya, a yadda aka tsara mini ginin hawa Uku ne, a cikin su wannene aka kai ki'?
Girgiza kai Batul ta yi tare da cewa"Ae bazan Iya tunawa ba, amma inaji kamar ginin dana na biyo time dana gudo Acan sama Ya ke," jinjina kai Angel ta yi"shikenan Iya abunda ya faru da ke? Wanene ya dawo da ke? Ko giants ne? Kamar ƴar jarida haka Angel ta tsare ta da tambayoyi.
"A ranar ina zaune tsakiyar gado, ina ta kuka ina ambaton sunyen ku, ina faɗin ni na gaji amaidani wurin ƴan uwana, idan ba haka ba zan haɗiyi zuciya in mutu, saboda na gaji da maraicin ku gani na ke kamar mutuwa zanyi, Angel shiru babu wanda yazo gare ni, hakan ya ƙara hasala zuciyata, Dama akwai wata ƙaramar wuƙa ta fruit da aka sako min cikin kayan abinci, sai nayi tunanin in ɗauke ta in yi kamar zan kashe kaina wata'ƙil asamu wani yazo gare ni tunda suna ganin komai da na ke yi, na sauko daga saman gadon na ɗauki wuƙar tare da buɗe murya ina faɗin"ko dai su zo su maidani wurin ƴan uwana ko in kashe kaina, kowa ya huta," ina kammala yin maganar Na watsa da gudu na shige toilet ɗin ɗakin naja ƙopa na rufe, ina jiran ganin ko zasu zo gare ni, jin shiru yasa nayi tunanin in ɗan yanka hannuna Jini Ya fito ko sun gani su zo, Ina ƙoƙari ɗaura wuƙar saman hannuna da niyar in yanka, ba zato ba tsammani kunnuwana su ka soma jiyo min takun tafiyar mutun a cikin toilet ɗin, a tsananin tsorace na ɗago don inga wanene ya shigo bayan na rufe ƙopa, Tsabar tsoro Yasa na jefar da wuƙar dake a hannuna Yayin da nake kallon Shi, Giant ne sanye Cikin baƙaƙen Kaya, dogo ne yana da faffaɗan ƙirji sai dai tafiyar shi ta banbanta dana sauran Gaints da su ke kawo mana abinci, kuma shi wannan Yana magana Don har ce min yai yazo ne ya taimake ni ya maidani cikin ƴan uwana idan inaso" cikin shessheƙar kuka nace mashi kada ka cutar dani, idan har dagaske za ka iya taimaka mini, ka nuna min hanyar da zan bi in koma wurin su, ko ka ɗauke ni ka kaini."
Tun da na ambaci hakan sai naji wani irin bacci acikin idanuwana, daga nan ban ƙara sanin me ya faru dani ba, sai dai na farka na ji kin rungume ni.
Ajiyar zuciya Angel ta dinga saukewa, Hankalinta ya kwanta sosai, jin cewa ba su yi mata irin na Unaiza ba, sai dai akwai wani abu da ya ɗaure mata kai dangane da labarin da batul ta bata, shin meyasa ita basu yi sex da ita ba kamar yadda su ka yi da Unaiza? Kuma har abinci su ke bata lafiyayye, basu cutar da ita ba ko kaɗan, Iya jinin al'adarta ne su ka tsotse, after that Angel ta yi mamakin Giant ɗin daya taimaki batul ya dawo da ita cikin su, a iya saninta Giant basa magana, sai dai ko tsakaninsu da manyan su zai iya yiwuwa suna magana, Amma ita Batul Giant ɗin ya yi mata magana har ya nemi taimakonta!! lamarin ya ɗaure mata kai.
Ta yi zurfi acikin tunaninta, muryar Batul ta katseta da cewa"Rabin raina, Me ki ke tunani ne? Allah yasa labarin dana baki bai ɗaga maki hankalin ki ba, dama saida nayi fagabar hakan"
Girgiza kai Angel Ta yi"a'a hankalina bai tashi ba, just na ɗanyi mamakin wasu abubuwa ne, Yanzu dai nuna min Jan tabon da ke a saman ƙirjin ki inaso na gani" da sauri batul ta sanya hannu ta soma nannaɗe ƙasan rigar da ke a jikinta har zuwa saman ƙirjinta, daga ƙasan boobs ɗinta da suka fara tasawa, Angel ta yi tozali da Jan tabon da ke a wurin, kasancewarta fara sosai, fatar wurin ta yi jawur.
"Yana yi maki zafi"? Angel ce ta yi maga tambayar, batul tace"A'a, bana jin zafi," jinjina kai Angel ta yi"zan yi maki addu'a, in tofa maki saman fatar wurin a yanzu, sannan da Anjima kafin mu kwanta zan ƙara yi ma ki, don inaji araina cewa Jan tabon nan ba alkhairi bane, dole akwai wani abu da ya ke nufi" ba tare da 6ata lokaci ba Angel ta karanto addu'o'i tare da tottafa mata saman fatar wurin, bayan ta kammala yin addu'ar ta ɗago su ka kalli juna.
"Allah ya tsare min ke ya kare min ke tare da sauran ƴan uwana daga sharrin waɗannan azzaluman mutanan" fuskar Batul ɗauke da murmushi ta amsa mata da ameen, ruƙo hannunta Angel ta yi acikin nata"taso mu koma Ɗaki, kada ajimu shiru, "
A tare su ka miƙa tare da nufar ƙopar fita daga cikin toilet ɗin, sam ta manta da zancen ainihin abunda ya kawota Cikin toilet ɗin.
Shigar su ɗakin keda wuya, kunnuwan su su ka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙopa, ras! gaban su ya faɗi, Azeeza da jamimah jiki na kerma su ka sauko daga saman gadagen su, atare su ka shige ƙarƙashin gado, Hankalin su sarah ba ƙaramin tashi yai ba, Kowan nan su Zuciyar shi ta hau harbawa da ƙarfi da ƙarfi, Deeja da ke kwance saman gadon Haris tuni ta zabura ra miƙe zaune, Gaba ɗaya idanuwansu na akan Matakalar benan, A bakin ƙopar fitowa daga sashen toilet ɗinsu Batul da Angel su ka dakata da yin tafiya Hannunsu ruƙe Cikin Na juna, Kowa Jira ya ke yaga wanene zaya shigo.
Jin takun tafiyar ta yasa hankalin su ya ƙara tashi, A hankali ta ke saukowa daga saman matakalar benan hannunta a ruƙe da sandarta, Kamar kullum Cikin jar shiga ta doguwar riga, Takunkumin da ke akan fuskarta Iya saman tsinin hancinta Ya tsaya, blue eyes ɗin ta, sai ɗaukar ido su ke Yi, Daga bayanta Giants ne masu take mata baya, Majiya ƙarfi dogaye masu ƙirar dakarun Yaƙi, Tuni kowan nan su yasha Jinin jikin shi.
A tsakiyar Ɗakin nasu tsohuwa zafreen Taci burki, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Babu wanda yai tunanin ya gaishe ta a cikin su saboda tsoratar da su ka yi, a ƙalla ta ɗauki mintuna tana ƙare masu kallo, kafin ta soma magana da kakkausar murya
"Ba ku Iya gaisuwa bane? Ko jira ku ke yi ni in fara gaishe da ku"? Muryoyin su na rawa su ka soma gaishe da ita, banda mutun ɗaya Angel da su azeeza waɗanda su ka 6oye a ƙarƙashin gado ita da jamamah, sun rungume juna jiki na kerma saboda tsoron da ke gare su.
"Ba haka nake so ku gaisar dani ba, saukowa za ku yi daga saman gadajen ku, Ku russina min," da sauri Sarah dasu hibba da ke zaune saman shimfiɗa su ka miƙe tsaye su Deeja su ka sauko saman gadajensu ita da parveen, a tsananin tsoroce su ka ƙarasa gabanta, Da niyar su zuƙunna mata kamar yarda ta buƙata, muryar Angel ce ta katse su
"Karku kuskura ku russina mata! Ae ita ba Allah bace, banga dalilin da zaisa mu girmama ki ba, because you don't deserve it!"
A firgice su Deeja ke kallon Angel da ta yi maganar cikin ƙwarin gwiwa, tsabar mamaki ne yasa tsohuwa zafreen Saurin wurga ƙwayar idanuwanta kan fuskar Angel tamkar zasu faɗo ƙasa, Tun da take arayuwarta wani mahaluƙi bai ta6a yi mata katsalandan ba kamar yarda Angel ta yi mata ayanzu ɗin nan, Sam ta kasa magana sai kallonta ta ke yi haɗi da jinjina kanta.
Hankalin su Deeja idan yai dubu to ya tashi, muryoyin su na rawa su ka soma ambaton sunan Angel suna bata haƙuri akan ta daina magana karta ja masu bala'e.
Dogon tsoki Angel taja mai sautin gaske, Tare da cewa"Ku ku ke jin tsoronta, Ni bana tsoron kowa sai Allahn da ya halicce ni shi nake tsoro, amma ba wani bawa ba, mai hannu biyu irin nawa mai ƙafafuwa biyu, wanda in mutuwa tazo ɗaukar shi bai isa ya kubce mata ba"! Idanuwan zafreen azazzare ta ke ƙarewa Angel kallo tun daga ƙasa har sama, Giants ɗin da ke a bayanta Har sun yunƙura zasu motsa tsohuwa zafreen ta dakatar da su ta hanyar ɗaga masu hannu.
"Angel dan Allah ki rufa mana asiri, Mu za ki jamawa ki yi shiru ki daina magana, Na roƙe ki badan halin mu ba," Batul ce ta yi mata maganar
Atare su Hibba su ka haɗa baki suna yi mata magiya akan ta yi shiru, ita kanta Angel ɗin ƙarfin haline kawai amma can cikin zuciyarta a tsorace take, sai dai bakinta yaƙi mutuwa, tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Batul ta sanya hannu ta toshe mata bakinta, hannu ta sanya tana kiciniyar 6an6are hannayen Batul.
Ido cikin Ido Su ke kallon Juna ita da tsohuwa Zafreen, Abunda wani bai ta6a gigin yi mata ba, ba'ayi mata magana ana kallon Cikin idanuwanta, Yau sai ga wata ƴar ƙaramar cikin prisoners tana yi mata fitsara da rashin kunya akan idonta.
A hankali tsohuwa Zafreen ta ɗaura hannunta ɗa ya saman fuskarta, tare da zame takunkumin da ya rufe fuskarta, Kowa yasha jinin jikin shi, muryarsu na kerma suka zuƙunna saman gwiwowinsu agabanta suna roƙonta akan ta yi haƙuri kada ta cutar masu da Angel ɗin su.
Tuntsirewa tsohuwa zafreen ta yi da dariya tamkar bakinta zai 6are, duk su ka bi su ka ruɗe, a lokacin Angel Ta samu damar 6an6are hannun Batul data toshe mata baki da shi, Sai faman haki ta ke yi tana zare ido.
"Well done Unaiserh!" ta ambaci hakan tare da yi mata alamar jinjina da hannunta ɗaya.
"Dole in yaba ma ki, saboda Ke ce prisoner ta farko da kika fara gaya mini magana ido cikin ido, ba tare da jin shakkata ba, sannan ke ce mutun na farko da kika fara furta min kalmar cewa ni baiwa ce kamar kowa, sa'an nan baki jin tsoro na" Bazawarin murmushi tsohuwa zafreen tasakar mata, kafin ta ɗaura da cewa"Wuyan ki Ya isa yanka, tun da har kika iya gaya mini magana, Ina jinjina maki, kin kafa tarihi a zuciyar tsohuwa Zafreen" ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da shu'umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa.
"Ni bana hukunta mutumin da ya nuna baya jin tsorona, sai dai in ta6a zuciyarshi, ta hanyar cutar da wanda ya mutu akan ƙaunarsa"! ras gaban Angel ya faɗi, Hankalinta Ya tashi, ta zazzaro idanuwanta akan fuskar zafreen, saboda ta fahimci me ta ke nufi, hatta su Deeja sun gane me ta ke nufi, gwiwowin su a sage, su ka mimmiƙe tsaye suna ja da baya, yayin da hawaye ke bin fuskokin su.
"Dan Allah kada ku cutar mu, Ku ƙyale mu mu yi rayuwarmu, Lafin me mu ka aikata ma ku ne, da ku ke son ƙarar da mu....." Kafin Deeja ta ƙarasa maganar tsohuwa zafreen ta buga sanar hannunta, muryarta a kausashe tace"Ban baku iznin Yin magana ba, " tun da ta ambaci hakan babu wanda ya ƙara magana, A hankali ta ɗaura idanuwanta kan fuskar Angel ta soma magana yayin da take tunkararta
"ZA6I UKU ZAN BAKI! A CIKI DOLE KI ƊAUKI ƊAYA, SAKAMAKON RASHIN KUNYAR DA KIKA YI MINI"! runtse ido Angel ta yi Jikinta na kerma zuciyarta a tsorace ta ke da fargabar jin Za6in da Tsohuwa zafreen za ta furta mata.
A tsanake tsohuwa Zafreen Ta ci gaba da cewa" za6i na farko shi ne I will order the giants to do terrible things to your sisters while you watch, or I will kill two of your sisters. The last option is that you will no longer get healthy food. From now on, you will only have to eat leaves like animals, Sannan ruwan shan ku zai koma na zafi,"
Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08169856268 ko 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇
https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL