🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️
*JIKAR IYA*
🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️🙎♀️
Mallakin
Teemerh Cool🖊️
08161316781
*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅
Bismillahi ramanin rahim
Page1️⃣1️⃣🆒1️⃣2️⃣
______Shine na dawo, na hau ginin na dawo gida, ina zuwa daman kofa a buɗe take, nan na shiga cikin sanɗa na rufe kofar, ina zuwa yadda na bar Iya a kwance ko juyi bata sake yi ba, zuwa nayi na manne da ita ns kwanta tare da rungumar hannunta,".
"Au daman ashe ke kika masa kasheri, sai ke jikar iya rikicin duniya, kowa ya ce zai ja dake karya ne, kaga yar tsuhuwa kuma hatsabibiya," nan ta mike tana gyaɗa kai kamar karan garuwa, ita ala dole an yabeta da kuma sunan da tafi so wato Jikar Iya.
"Ni ce Yar tsohuwa kuma yar Iya sannan kuma Jikar Iya, babu mai ja dani a garin ɗan batta, daman na faɗa muku mudun Jummai Ƴar gidan mai gari bata fita a gonata ba nace sai na nuna mata karshen wannan auren nata, kuma yau gashi na cika wannan alkawarin, tabbas niɗin ƴar halal ce kuma jikar iya, bana faɗa ban cika ba" ta karashe maganar tana washe baki.
"Wannan haka yake zance ki babu karya, sannan kuma duk wani shege da tantiri a garin nan kece Babansa," a faɗar Auta tayi maganar tana dandalar yaji da Lami ta taho musu da awarar gidansu.
Musa, Lami, Auta da Indo duk a zaune suke a wani gindin bishiya babba ta tsamiya, awarar suke ci hankali kwance sun mikar da ƙafa, suna ci suna hira.
"Yanzu waye ne na gaba a aikinmu?," a faɗar Lami.
" Kema ko bata faɗa ba kinsan dai Ɗan Lami ne, sannan kuma shine babban munafiki a garin nan" Musa ya yi maganar yana kaɗe hannayensa.
Auta ce ta yi carab ta ce "aini ma inason naga ankai masa siyara, dan wannan mutumin ba ƙaramin haushinsa nake ji ba, wai haka sheƙaran jiya yaje gidanmu ya yi sallama da Abbanmu" tayi maganar tana rike haɓarta kana ta ci gaba da maganar "Abbanmu yana dawo wa yaa fara mun faɗa akan wai inya ƙara ganina dake sai ya karyani" ta ƙarashe maganar da alamar zata ɗau fansa.
" Au kice wannan munafikin haka ya faɗa, to wlh gwara da kika faɗa mun, kice daman ni ya tsaneni a garin nan, Allah sarki ni marainiyar Allah mai na tsare masa" tayi maganar cikin siffar tausayi.
Can ta kwashe da dariya tare da faɗin " to wlh babu maraya sai rago, dan nima yadda ya tsaneni haka zan nuna masa cewa banida sauran imani".
"yauwa ƴar iya kin burgeni, haka nakeson ji wannan batun, dan wannan babban munafukin gaba ɗaya zamuje, dan mu ɗauki fansa" a faɗar Lami tana dariya mugunta, ita ma Indo dariya take yi tana tuna abun da zata shirya masa.
Ana cikin haka sai ga Uncle Murtala zai wuce, ganin su ne yasa shi ya karasa wajen da suke bakinsa dauke da sallama.
A maimakwan su amsa sai Musa ya juya ya kalli gabas, Indo kuma ɗaga kanta tayi sama, Lami kuma kudu ta kalla, sai Auta da take kallon arewa, kara musu sallama ya yi amma shiru babu alamun za su amsa, sai da ya musu a karo na uku sannan ya juya ya tafi.
"Dan wahala kenan yanzu zai fara mana wata nasiharsa, akan rashin zuwan mu makaranta kwana biyu, shi mutum baashida right ɗin da zaiyi abun da yake so ne, wlh sa'arsa ɗaya ma dan shi yana ƙaunarmu amma da tuni munyi maganinsa", cewar Indo tana mikewa tare da gyara ɗaurin zaninta.
Suma miƙewa suka yi akan sai gobe za su hadu, Indo ce ta ce musu su shirya goben sa shiga makaranta da safe.
Kowa hanyar gidansu ya nufa, ina ita ma Indo tayi nata hanyar, tana tafiya tana kada sanda, tana wake wakenta ta kallin nan ta kalli can, sai da tazo zata wuce ta kantin Idi mai kanti ta tsaya, yana ganinta ya saki kuka yana addu'a cikin ransa.
"Malam Idi Allah dai yasa ba budurwarka bace ta mutu" tayi maganar tana gyaɗa kai tare da girgiza kafa.
"Jikar Iya Mahaifiyata na tuna, shine nake kuka niɗinnan abun tausayi ne" ya yi maganar yana kuka.
"Allah jiƙar uwarka Idi,"
"Amin ya rabbi, Allah jiƙan dukka iyayenmu, nida ke duk marayu ne" ya yi maganar yana rautsayar da kai.
Ƙallabinta ta gyara tare da faɗin " yauwa Idi ɗan uwana maraya, ina labarin budurwarka?," tayi maganar tana kallonsa, tuni Idi ya tsure dan baya son Indo ta faɗi wani magana dangane da budurwarsa, hakan ya yi saurin faɗin " lafiya ƙalau Indo sai alkhairi ƴar uwata marainiya, ina zuwa ne da magrib ɗinnan?, dan nima yanzu nake shirin tafiya masallaci".
Ta gano jirgin Idin so yake ta tafi, sannan kuma bayason ta faɗi wani abu dan gane da aurensu, hakan yasa ta faɗin "to zan wuce babu wani abun ne Ango Binta?," tayi maganar tana wasa da matafinta da ta ɗaure a kugunta.
"Ah ba dole ba Jikar Iya, ai wannan abune mai sauki ne," ya yi maganar yana washe haƙora tare da goge hawayen da yake fuskarsa, biskin ya ɗauko mata guda biyu tare da faɗin " ɗaya na marainiyar Allah, ɗaya kuma na tsohuwar arziki mutumiyar kirki, dan Allah ki gaishe mun da ita" ya yi maganar yana kokarin rufe kantinsa, itama gaba tayi tana dariya tana waige waige.
Saurayi da budurwa ta gani suna hira, ta kawo masa ruwan alwala, kansu taje ta tsaya ta faɗin " yanzu kai fisabiɗillahi mai kuke faɗa, kazo kasa ƴar mutane a gaba kamar tsohon maye sai kallonta ka ke" tayi maganar tana siresu da ido.
Da kallo suka bita babu wanda ya tanka mata, ganin sunyi shuru yasa taji haushi, tsakaninsu ta shiga tana faɗin "ai wannan haramun ne, ka zauna dab da ita kamar zaka zauna a cinyarta, bacin ita ɗin ba muharramarka ba ce" tayi maganar tana zuba masa harara.
Tashi tayi budurwar ta finciketa tana faɗin "wai ke dawa ki ke takama ne, da kike zabga rashin mutumcin a wannan garin?" cize bakinta tayi tare da mata wani kallon raini, ita kuwa wannan budurwar cukumarta tayi tana faɗin "wlh ki ka kara shiga gonata to sai na nuna miki iyaƙarki" tayi maganar tana rike da ita.
"Dan Allah kiyi hakuri bazan ƙara shiga gonarku ba, wlh kawai tsautsayi ne kiyi hakuri ki kyale marainiyar Allah," ganin Indo ta bata hakuri ne yasa ta saketa tare da tunani a zuciyarta tana faɗin " yau na kawo karshen rashin jin yarinyar nan a garin nan, dan tana ganin mutane suna tsoronta ne yasa take iskancinta" a fili kuma ta ce" wlh na ƙara ganin kafarki a nan wajen" tayi maganar tana mata nuni da yatsar manuni.
Kasa tayi Indo tana mata magiya, tare da haɗe hannayenta tana faɗin "kiyi hakuri kaima saurayin nata kayi hakuri, ka tayani bata hakuri" ta zube akan gwiwarta.
Ɗaga kai tayi sama tana irin basarwa, dan yau ta cire tuta wajen saurayinta, dan shima zai san ita ɗin jaruma ce, tana cikin wannan tunanin Indo tasa hannayenta biyu ta riƙe kafafunta tare da janta gaba, kafin ka ce kabo ta zube a kasa.......
An fara biya Hajiya ki hanzarta biyan kuɗinki don ki karanta cikin salama da nishaɗi, wannan littafin bama a fara ba dan shinfiɗar taburma ne, sannan kuma free page ya kusa ƙarewa.🙏🙏🙏
Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN, AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.
TEEMERH COOL🖊