Kurkukun Ƙaddara page 42

Kurkukun Ƙaddara page 42

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E42


Daga alƙalamin Boss Bature writer Of Abban Sojoji✍️


"Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan"?


Lokacin da Angel ta haura tagar nan, ta faɗo ta baya wani irin duhu ne ya mamaye idanuwanta, kanta ya soma juyawa, Ta sanya hannayenta bibbiyu ta dafe kanta, Jikinta ya soma kerma a hanzarce ta fara ƙoƙarin kamo sunan Allah acikin bakinta, sai dai abun ya faskara, sautin shessheƙar kuka ta dinga Ji acikin kunnuwanta, ranta ya dinga bata cewar batool ce take kuka, Cikin duhunnan, ta miƙi hanya gudu gudu sauri sauri hada tuntu6e, ita kanta batasan ina zata dosa ba, domin kuwa notikan kwanta  sun kwance, bata ji bata gani, a makance take tafiya burinta takai ga inda take jiyo sautin shessheƙar kukan nan, Haske ta fara hangowa a ƙarshen hanyar data biyo, da gudu ta nufi inda take hango hasken nan, tana faɗowa cikin wurin, Idanuwanta suka sauka akan katafaren filin dake da manya manyan benaye, a ƙalla sun kai Shida benayen kuma kowane matakalarshi ta haura goma sha, don akwai wanda matattakalarshi takai talatin shine wanda idan ka hau zai kai ka har third floor na ginin, Ginin yana da tsayi da faɗi, Daga sama wasu irin manya manyan fitilune da suke haskaka wurin, idan ka kalli kowani hawa na benan zakaga Wasu Tagogi wadanda glass din Jikinsu launin Ja ne, Masu girma, Babu ƙofofin ɗakuna Sai dai da alama za'a Iya samun ƙofofinsu ta can cikin hanyoyin dake akwai, wani irin kurman Ginine, Mai matuƙar ruɗarwa, wani irin fargaba ne ya ɗarsu acikin zuciyarta lokacin da tafara Jin wani irin gurnani, Ginin Ya dinga juya mata, benayen suka dinga motsi Suna Yin ƙasa da sama, Waro ido waje angel tayi Jikinta na 6ari, Ta zabura zata Juya ta koma Inda ta fito, sai dai ina babu hanya, tama rasa gane ta inda ta faɗo Cikin wurin, Tsabar ruɗi yasa ta baza da gudu ta faɗa tsakiyar wurin, hannayenta dafe da kanta saboda wani irin firgici da take aciki, tuni zufa ta wanke Jikinta sharkaf, Bata gama rikicewa ba, Daga can saman hawa na uku ta soma Jin muryar mahaifinta tajudden Yana kuka yana kwala mata gira, A matuƙar ruɗe ta juya ta baya tare da ɗaga kanta saman benan, A tsaye ta hango shi, tare da Wasu irin haluttu masu gashi gashi ajikinsu, Jibga jigba, Sun kewaye shi, Sai Cuzgar naman Jikin shi suke yi, Wata irin gigitacciyar ƙara angel tasaki, mai kuwar gaske, Ta fashe da matsanancin Kuka tana fadin"Daddy! wayyo Allah na daddyna! Shikenan sun kashe mini daddyna!! nashiga uku, Dan Allah ku ƙyale mini daddyna" Tana kuka ta watsa da gudu ta nufi ɗaya daga Cikin benayen da nufin taje ta taimaki daddynta, tana gudu ana maida ta baya, Da zarar takusa kaiwa saman benan sai taga Sun juya mata, Benan yaja da baya, Ya koma can Ciki, Haka ta dinga bin benayen tana ƙoƙarin hawa samansu, Amma wani abun ruɗarwa benayen tamkar masu Rai, sosai suke motsawa wurin yin ƙasa da sama, Jikinta duk zufa ta galabaita sosai, idanuwanta sunyi jawur, Jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruɗu ruɗu Jikin fatarta, Muryarta har ta disashe, Duk da mawuyacin halin da tashiga na tsoro da firgici hakan baisa ta fasa yunƙurin hawa benan ba, Bakomai take ji ba face mahaifinta da take hangowa can saman waɗannan halittun suna Cin naman jikinshi, sai kuka yake Yi yana miƙa mata hannu akan tazo ta taimake shi, Akan idonta halittun suka gutsire ƙafafuwanshi, Jini ya dinga tartsatsi yana gangarowa ta saman benan, Angel tashiga ruɗani, addu'a ta kubce mata, gaba ɗaya tunanin ta ya gushe, Tun tana yin kuka har ta koma tana yin na zuci, Ƙafafuwanta sai zogin azaba suke yi mata, saboda zarya da tadinga Yi, Lokacin da benayen suka gama yi mata wasa da hankali, Suka koma yadda suke, waɗannan halittun suka 6ace ma ganinta, sai dai gangar jikin mahaifin ta dake a yashe saman hawa na uku, Da gudu ta haura saman dogon benan nan wanda ya ke da matattakala Talatin, Tana tafiya tana zamewa, a haka harta samu ta haura saman shi, Tana ƙarasawa inda gangar jikin tajudden take, ta zuƙunna saman gwiwowinta, ta dinga kuka hada majina tana ambaton sunan shi tana faɗin sun kashe mini daddyna, sun rabani da farin Cikina, Wayyo Allah na, Ya Allah ka ɗauki raina nima in huta, yatsun hannunta na kerma ta ɗaga su da nufin ta shafa gangar jikinshi, nan take gangar jikin ta 6ace 6aat, a matuƙar gigice ta zazzare idanuwanta eye lashes ɗinta suka bubbuɗe, tsigar jikinta ta dinga tashi, zufa ta ko'ina, kwakwalwarta ta burkice, kafin ta yi wani yunƙurin motsawa ta soma Jin motsin tafiyar wasu abubuwa ta ko'ina, a firgice ta ɗan juya baya tana kallon Jikin wata taga dake a datse, Ras taji gabanta yai wani irin mugin bugu, Bakomai bane angel ta gani face wasu irin manyan kunamu sun ɗaga ƙarin su, Yayin da suke gangarowa daga Jikin bangon suna tunkaro inda take zuƙunne, wa'iyazubillah, ƙiris ya rage zuciyarta ta buga, saboda tsabar razanar da ta yi, ga shi jikinta babu ƙwarin da zata Iya saukowa daga saman benan, Jikinta na 6ari ta soma rarrafawa tana tunkarar banen dan ta sauko ƙasa, tana kuka tana waiwayon kunamun dake tunkarota, a wannan lokaci ta dinga kwala ma danish kira na fitar hayyaci tana faɗin yazo ya taimake ta, zasu kashe ta, ta mutu ta bani ta lalace ƙarshenta yazo, 


Adai dai wannan Lokacin Danish Ya faɗo Cikin wurin, Hannun shi ruƙe da wandonta, sai faman waige waige yake yi, karaf idanuwanshi suka sauko akan angel da ke yin rarrafe tana saukowa daga saman benan, Hankalinshi yai matuƙar tashi, da ƙarfi ya ambaci sunanta yana faɗin ta tsaya kada ta motsa ba abunda zasuyi mata, sai dai kash angel bata Iya fahimtar maganar shi, saboda bata acikin hayyacinta, Da gudu ya nufi benan da niyar yaje ya taimaka mata, kafin ya ƙarasa gwiwowin ƙafarta suka sage, Tun daga kan matattakalan farko Angel ta burki ce ta dinga mirginowa tana gangarowa ƙarshen stair ɗin, kanta da hancinta duk suka fashe suna bleeding, kafin ta faɗo ƙasa, sai da ta fita hayyacinta, Jini ya wanke fuskarta, har saman wuyanta, hatta  knuckles ɗinta saida suka gurguje, A ƙarshe ta ƙundumo kan ground floor ɗin, kanta ya dake shi, goshin ya fashe, ƴar rigar uniform ɗin dake ajikinta, tuni ta yaye ta nannaɗe ta dawo saman Cikinta, tsiraicin ya bayyana sosai, gashi ko pant babu ajikinta, Wasu irin zafafan hawaye ne suke wanke fuskar danish time ɗin daya ƙarasa ya zube agabanta saman gwiwowinshi, yayin da numfashin shi ke fita a wahalce, A wani irin yanayi mara misaltuwa yake kallonta, dama abunda yake guje mata kenan, Amma ta ƙi jin maganarshi, hannunshi na kerma ya ruƙo rigarta data nannaɗe, ya janyota ya rufe mazaunanta, a saman laps ɗinshi ya ɗaura wadonta, kafin ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da ita, zuciyarshi ta ƙara karaya ganin irin mummunan raunin da taji akan fuskarta, idanuwanshi ba zasu juri ganin angel cikin mawuyacin hali ba,


da sauri ya kwantar da ita saman ƙirjinshi, ya matseta da hannayenshi biyu, ya kwanto da kanshi saman sumar kanta dake a yamutse, ya ɗan lumshe idanuwanshi, saboda tsabar zafin jikinta har a jikinshi yana ji, cikin wata irin raunatacciyar murya ta wanda ya galabaita ya jigata ya fita hayyacinsa ta dinga kira mishi sunan daddynta, ta zagayo da hannayenta zuwa bayanshi, ta cakumi rigarshi tana yamutsa ta, babu alamun hankali atattare da ita, santala santalan cinyoyinta sun fito farare sol dasu, sai faman motsa su take yi, tana harɗesu jikin juna, ganin rigarta na ƙoƙarin kwarewa ta ƙara nannaɗewa yasa shi yin saurin kai hannu ya damƙi ƙasan rigar ya gyara mata ita,


A hankali Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, Jininta duk ya 6ata mishi gaba rigarshi,   ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, Idanuwanta sun ƙanƙance, tausasan la66anta sun kumbura  sun ciza launinsu, tsinin hancinta yai ja sosai, jinin ne ke gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, Cikin karyayyiyar murya ya ambaci sunanta Angel, bata amsa mashi ba, don a halin da take aciki batasan wanene akanta ba, sunan daddynta kawai take iya ambato,


Cikin harshen turanci yaci gaba da cewa "Angel, kinga abunda kika ja ma kanki ko? Yanzu da ace banzo ba ya zaki yi? Kalli yadda kika raunata kanki, ta ko'ina babu lafiya a jikinki, saboda kafiya irin taki na gargaɗe ki amma kika ƙi jin magana ta, saboda baki ɗauke ni abakin komai ba, kin ɗauka cewa shiga  cikin prison abune mai sauƙi, yanzu gashi nan kin ja ma kanki yin jinya, nasan ko gobe aka nuna maki hanya fita ba zaki ƙara gigin binta ba" shi kaɗai yake ta sambatun shi, baiwar Allah, sai nishi take yi, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji ajikinta,


Haɗe fuskokinsu yai wuri ɗaya, ya mayar da hands ɗinshi Tsakanin sumar kanta da wuyanta, harshen shi ya ɗaura saman fuskarta, a hankali ya soma lashe jinin dake zuba, har sai da yaga babu sauran jinin dake ɗiga tukunna ya zame tongue ɗinshi, idanuwanta sai rurrufewa suke Yi, biji biji take ganin shi, tun tana yin numfashi daƙyar daƙyar har ta kai ga sumewa saman jikinshi, da dabara ya samu ya zame wandon unform ɗinta daga saman laps ɗin shi, Ya damƙo dogayen ƙafafuwanta, Ya shiga kiciniyar sanya mata shi,  daƙyar ya zura mata wandon yaja shi har saman waist ɗinta, bayan ya kammala, Ya ɗaɗɗago da ita, ya yarfata saman kafaɗarshi Ya miƙe Ya juya Ya nufi hanyar komawa ɗakin su, sai dai da alama danish bata taga ya koma Cikin ɗakinsu ba, 6acewa yai ya faɗo Cikin toilet ɗinsu ɗauke da ita a hannunshi, a lokacin Har ya gyara ɗaukar da ya yi mata, ya sauko ta daga saman kafaɗar shi, Ya yi mata irin ɗaukar da ake yi ma jariri, Yana kan hanyar fitowa daga Cikin toilet ɗin, Yaji motsin mutun Yana tunkaro ɗakin Da wani irin sauri Ya faɗo bakin ƙopar sashensu, Kunji yadda akai danish Ya ɗauko angel,


*PRISONERS💔* 


hankalinsu yaƙi kwanciya, Ganin irin raunatar da angel tayi, masu karyayyiyar zuciya acikinsu tuni sun fashe da kuka, Hibba tace"wannan wata irin rayuwace, daga wannan sai wannan, yau dai bata yi mana daɗi ba, muna fama da azeeza data sume ga kuma Angel itama asume jikinta duk ciwuka, wai dan Allah meya faru da ita ne? Tana rufe baki hanna tace"pls danish ka faɗa mana a ina kaga angel, can fa nabarta a zaune, Yanzu kuma sai gashi ka shigo da ita daga Cikin toilet, yaushe ta shiga ciki? A matuƙar ruɗe tayi mashi tambayar, haris yace"Allah yasa ba wani mugun abun ka yi mata ba, Wama ya sani ko bugunta ka yi don ka huce haushin abunda muka yi maka," da sauri danish ya ɗago da idanuwanshi ya ɗaurasu kan fuskar haris da ya yi maganar,  wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyar shi, ƴan uwanshi suna yi mishi kallon mugu mara tausayi mara imani, duk sai yaji ya tsani kanshi, sam ya kasa furta komai, duk da ya ɗago ne da niyar ya mayar mishi da martanin maganar shi amma sai ya kasa,


"Yakamata muyi ƙoƙarin wurin ceto rayuwan ƴan uwanmu bawai mu tsaya muna surutu mara amfani ba" Acewar Mubeen, 


Cikin fushi haris yace"Ka faɗa mana me ka yi ma angel da har ta suma? Hawaye ne suka cika idanuwanshi, Cikin sanyin murya yace"ka bari tafarka sai ka tambaye ta me nayi mata, idan har ni na zalunce ta, kuna da right  da  xaku iya rama mata, amma bai kamata ace kuna tuhumata ba"


Naufal yace"zamu zuba ido mu gani har zuwa lokacin da zata farka wlh idan har ta fada mana cewa kaine silar halin da tashi ga, to ka kwana da sanin cewa ba zamu ƙyale ka ba," Yana magana yana galla mishi harara, Girgiza kai danish ya ɗanyi batare daya tanka ma naufal ba,  ya lura gaba ɗaya shi suke zargi akan halin da angel ta shiga, basu son cewa itace ta ja ma kanta ba,


"Ina azeeza take"? Yayi tambayar yana bin fuskokinsu da kallo, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa"Ina ruwanka da ita? Ka damu dasu ne"? Girgixa kai ya ɗanyi tare da cewa'taya bazan damu dasu ba, ƴan uwanane su, baku isa ku hanani tambayarsu ba"


 Javed yace"Har kana da bakin cewa su ɗin ƴan uwanka ne? Mugu dakai saboda rashin imani ka damƙi hannun batool ka miƙa ma wani ƙato ya ɗauke ta don aje acutar da ita, a haka har kake kiransu da ƴan uwan ka"? Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, tunawa da rashin imanin da ɗan uwansu danish yayi musu, jikin shi duk yayi sanyi, har lokacin yana zaune gefen gadon angel, daƙyar yake kallonsu saboda nauyin haɗa ido da su ya ke ji.


"Ka faɗa mana wanene kai!" har saida gabanshi ya faɗi jin tambayar da haris ya jefa mishi, muryarshi na kerma yace"wha..what u mean? Haris ni kake tambaya wanene Ni"? jinjina kai haris yai tare da cewa"Eh, so nake insan wanene kai! Danish bani kaɗai ba gaba ɗayan mu nan zargin ka muke Yi, Kawai ka faɗa mana gaskiyar wanene kai, meyasa kake atare damu" a ruɗe danish yake kallonsu,


Naufal yace"bana tunanin danish cikakken mutun ne, Saboda babu zuciya a ƙarjinshi, Haba rashin imanin yayi yawa, ka duba kaga yau tsawon shekara nawa, danish yana atare da batool, tun kafin mu mallaki hankalin mu yake atare da ita, baida wani makusancin daya wuce ita, in ka cire haris, amma yau rana ɗaya ka gaza ceton rayuwarta, sai ma ka taimaka wurin miƙa ta ga azzaluman da zasu azabtar da rayuwarta......" wani irin kukane yazo ma naufal ba arxiƙi ya katse maganar, hawaye suka soma bin fuskarshi,


Haris ya ɗaura da cewa"ba zamu ta6a mantawa da wannan ranar ba, danish ka cika butulu, mara imani da tausayi, Yarinyar nan babu irin ciwon kan da batayi ba akanmu, tana matuƙar son ƴan uwanta, idan wani baya lafiya acikinmu, batool ko bacci bata iya yi har sai yaji sauƙi, ka cuce mu danish, kuma ka karya mata zuciya, nasan batul bazata ƙara yarda dakai ba, saboda kaine silar duk wani hali da zata tsinci kanta,"


Tun da suka soma yi mishi magana, yayi shiru yana binsu da kallo bai ko tanka musu ba, duk yadda zaiyi musu bayani yasan ba lallaine su fahimce shi ba, amma yafi su jin raɗaɗin rabuwa da batool, shi kaɗai yasan irin ƙuncin daya shiga lokacin daya janyota ya miƙa ma giant,


Sun tasa shi gaba suna jiran jin amsar dai basu, bai bi ta kansu na, ya miƙa ya tunkari inda su deeja suke zuƙunne, yana yunƙurin zuƙunnawa don ya duba lafiyar azeeza, naufal ya damƙi hannun shi tare da cewa"kada ka kuskura ka ta6a ta, babu ruwanka da rayuwarmu" murmushin takaici danish ya sakar mashi, batare daya mayar da martanin maganar shi ba, ya fusge hannun shi daga ruƙon da yae mishi, Ya zuƙunna agabansu deeja, wani irin haushin shi take ji kamar ta shaƙe wuyan shi, Tun da ya zuƙunna take ta aika mishi da harara kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wanda ake yin hararar domin shi baima san tana Yi ba, hankalin shi gaba ɗaya yana akan azeeza, dake rungume jikin deeja,


Robar ruwan da haris ya ajiye a ƙasa, Danish Ya miƙa hannu ya ɗauko ta, A baki ya kur6i ruwan, duk suna a tsaye suna kallonshi, A saman fuskar azeeza ya watsa ruwan, Wani iko na Allah nan ta ke azeeza taja dogon numfashi, Jikinta ya soma kakarwa, Cike da mamaki suka dinga kallon danish da kuma azeeza, ganin yadda yai nasarar watsa mata ruwa ta farfaɗo, 


Hannayenshi biyu ya sanya ya tallabo fuskar azeeza yana kallonta, muryarta adisashe take faɗin dan Alah kada ku bari su ɗauke ni, wlh mutuwa zanyi, ni bazan bi su ba, " 


"Azeeza"! Muryar danish ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, ta ɗan buɗe idanuwanta tana kallon shi biji biji saboda matsalar idanuwanta, da sauri su haris dasu hanna duk suka zuƙunno agabanta, suna ambaton sunanta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, badan tana gane su ba, yayin da idanuwanta ke lumshewa, muryarta na ɗan rawa tace"Dagaske ba'a tafi dani ba, ina atare da ƴan uwana"? Atare suka haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Eh, muna atare dake" har xatayi murmushi sai kuma ta fasa, tunawa da batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke. A tsorace tace dasu"Ina Batool take" nan fa kowa yai shiru, hakan yasa ta fahimci cewa An ɗauke batool, shessheƙar kuka ta fara yi musu, Danish yace"its okey azeeza, ba lafiya gare ki ba, kina buƙatar ki huta" girgixa mashi kai tayi hawaye ta ko'ina akan fuskarta tace"Yanzu shikenan an ɗauke mana batool dinmu, an tafi da ita, baiwar Allah, nayi danasanin cizon ta da nayi, dame xata ji"? Fashewa tayi da kuka, Cikin sanyin murya haris yace"Pls azeeza stop shedding ur tears, Ya riga daya faru babu wanda ya isa ya dawo dashi baya, abunda nake so daku shine muyi haƙuri mu rungumi ƙaddararmu, idan da rabon za'a dawo mana da batool, Ko min daran daɗewa, ƴar uwarmu zata dawo cikinmu ne"


Sosai haris ya shiga kwantar musu da hankalinsu, sai gashi kowa daga Cikinsu yaja baki yae shiru, danish yace"Yakamata kuje ku kwanta....." daƙyar ya ƙarasa maganar, ganin irin kallon da suke watsa mishi, Haris yace"Itafa angel? Kaƙi faɗa mana meya faru da ita, a ina ka ɗauko ta? Me kuma ya haɗa ka da ita da har kayi mata wancan jahilin bugun," 


"Haris, bani da amsar da zan baka, amma idan tafarka, zaka Iya tambayarta, " yana kai karshen maganar, Ya miƙe tare da ɗaukar robar ruwan Ya nufi gadon angel, Bai kai ga ƙarasawa ba, Ya ɗan dakata da yin tafiyar, Batare daya juyo ya kalle su ba, da wata irin kakkausar murya yace"ku wuce ku je ku kwanta," Tun da ya ambaci hakan suka fara Jin wani irin matsiyacin bacci yana niyar dauƙarsu, A daddafe kowannansu Ya miƙe Deeja ta ruko hannun azeeza a saman gadonta suka kwanta su biyu ta rungumeta ajikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin yai tsit Baka jin hayaniyar komai bacci duk yae awon gaba dasu, 


Ajiyar zuciya yaɗan sauke, Aranshi yace"nasan da hakanan nace su kwanta bazasu bi umarni na ba" 


Daga gefen gadon angel ya zauna, Yana binta da kallo, sai yaji sam baya son ya tada ta daga bacci, saboda sanin tsiwarta, Its better ya ƙyale ta zuwa wani lokaci, A hankali Ya ajiye robar ruwan daga ƙasa, ya haura saman gadon, ya sanya hannayen shi biyu ya damƙi ƙafafuwanta, A tsanake Yake daddana mata su, Yana yi mata tausarsu, duk inda ya ta6a sai kaji ya bata sauti ƙass, daga bisa ni ya ruƙo yatsun hannayenta, Ya dinga jansu, bayan ya kammala, Ya kwanta daga gefenta, idanuwanshi akan fuskarta, 


"Idan tana bacci tafi kyau, da sanya zuciya natsuwa, amma idan tafarka, tsiwarta tafi komai ɗaga hankali," da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba dashi, 


Daƙin yai tsit, Ba ka Jin sautin komai saina minsharinsu, 


Bayan wani lokaci, Hasken fitilun saman ɗakinsu Ya gaure ko'ina, wanda ke nuni da cewa gari ya waye, babu alamun masu bacci zasu farka, 


Motsin buɗe ƙopa ne Ya karaɗe kunnuwan danish, A hankali Ya ɗan ware sexy eyes ɗinshi, ya yunƙura ya miƙe daga zaune ya jingina bayan shi da bango, Angel na a kwance gefenshi,  idanuwanshi sai faman lumshewa suke Yi, da alama baccin bai ishe shi ba, jikinshi duk ba daɗi, A buƙace yake da son Yin wanka, gaba ɗaya hankalin shi ya koma kan staircases jin Sautin tafiyar mutane.


Giants ne suke shigowa hannayensu ɗauke da sabbin gadaje kalar nasu, duk mutun ɗaya yana ruƙe da gado ɗaya, A jere suke saukowa daga saman benan, kusan su Goma sha biyar, Kaitsaye suka wuce can Cikin ɗakin, 6angaren da gadajensu danish suke fuskanta, A nan suka jera sabbin metal beds ɗin da suka shigo dasu, 


Duk akan idonshi, Bayan sun kammala jera gadajen, Sai ga Wani giant ɗin Ya shigo Hannun shi ruƙe da doguwar ledar kaya, mai ɗauke da sunan Prison, Bargunane acikinta tare da bedsheets da kuma pillow, Yana ƙarasowa Ciki, Batare da 6ata Lokaci ba, suka curo da zannuwan gadon suka shimfiɗa ma kowani gado, daga bisani suka ɗaura bargunan, tare da pillow, Bayan sun Kammala  A jere suka Juya suka fuce daga Cikin ɗakin, 


Mamaki ne  ya kama danish, yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, Ya nufi inda gadajen suke a jere, Yana ƙare musu kallo,


aranshi yace sabbin prisoners za'a kawo mana, Har mutun goma sha biyar? Mun cika talatin kenan," ta6e baki ya ɗanyi, Shi dai fatan shi Allah yasa kar akawo musu masu ɗan banzan surutu da tsiwa, Sai da yabi kowani gado ya ƙare ma numbobin jikinsu kallo, sun fara daga no16 har izuwa No30, Jinji na kai yai kafin Ya juya ya nufi gadon angel, daga gefe ya zauna, tare da kai hannu daga ƙasa gefen gadon, Ya ruƙo bottle water ɗin daya ajiye, har ya tarba hannu zai ɗibi ruwa ya watsa mata, Yaji motsin buɗe ƙopa, dakatawa ya ɗanyi yana jiran ganin wanene zai shigo, Yayi tsammanin xaiga new prisoners ɗin da za'a kawo musu, amma sai yaga Giants suna shigowa, Ukun farkon masu kawo musu abinci ne, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Na bayansu kuma su biyu ne hannayensu ruƙe da wasu jibga jibgan akwatuna kusan guda biyu masu girma, Suna da tayoyi daga ƙasan su, daga bayan masu ruƙe da akwaitin, akwai wani Giant ɗin kuma hannun shi ruƙe da Floor laps Masu girma, daga gani zasu yi haske sosai idan aka kunnasu, Danish dai ya zubawa sarautar Allah ido, sai kallonsu yake yi, 


A saman dining Carpet ɗinsu, Giants ɗin suka sauke kayan breakfast ɗin nasu, waɗanda ke a ruƙe da akwatin nan, a tsakiyar ɗakin suka ajiyesu, Saura Giant ɗin dake ɗauke da floor lamps a hannun shi,  Daga ƙasa Ya ɗaura su, Atare suka juya hada masu kawo musu abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Fitarsu keda wuya, Danish ya soma Jin takun tafiyar wani kuma again yana saukowa daga saman benan, da sauri yakai idonshi kan me shigowa, Gaba ɗaya Jajayen kayane ajikin mutumin, doguwar riga ce bazai Iya tantance macace ko Namiji ba, gaban rigarsa taurari ne guda uku, hannunshi na dama yana a ruƙe da sanda Golden colour, daga gani tsohone, hatta takalmin shi jajaye ne, a bayanshi wasu Giants ne su Huɗu, kowanne hannayenshi na a ruƙe da kayan amfani na toilet, A tsakiyar ɗakin Mai sanye da jajayen kayan ya tsaya, Ganin haka yasa danish ya miƙe ya ɗan sara mashi, Da hannu yai mishi alamar Jinjina, kafin Ya juya ya kalli giants da suka zo atare, Da hannu yayi musu nuni da sashen shiga toilet ɗinsu, suka nufi Ciki suka shige, kusan Minti talatin Suna aciki, Kafin daga bisani suka shigo cikin ɗakin, Babu kayan da suka zo dasu a hannunsu, sun barsu acikin makewayin nasu,


Tamkar sojoji haka suke ƙame abayan Wannan ɗan tahalikin mai sanye da jajayen kaya,


Danish Yana a tsaye yana binsu da kallon mamaki,


Ware ido yayi ganin mutumin ya ɗaga hannun shi ɗaya ya ɗaura shi saman fuskarshi, nan take ya zame mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, dattijuwace fara tass, launin idanuwanta blue ne, daga gani baturiyace, tana da dogon hanci, gaban kanta hurhurace,


Ƙayataccen murmushi tasakar ma danish tare da cewa"Ƴan uwan naka bacci suke Yi? Muryarshi na ɗan rawa yace"eh" lumshe idanuwanta tayi yayin da take kallonsu tace"gwanin ban sha'awa, tunkafin in fara zama acikin ku har naji kun kwanta mini araina, 


aɗan ruɗe danish yake kallonta, kai daga ganinta kasan babu wasa atare da ita, Sam batayi kama da masu Imani ba.


"Zan tafi but I will come back. When they wake up, tell them that their new guardian has come to visit them," fuskarta asake tayi maganar,


Ya amsa mata da toh, Har ta ɗaga ƙafa zata juya sai kuma ta dan dakata, yayin da idanuwanta suka sauka akan Angel dake kwance saman gadonta, Shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta tsohuwar,  A hankali ta furta sunan ta


*Unaisa zaheer tajudeen Our destiny*


 Ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga Cikin dakin,da sauri Giants ɗin suka Bi bayanta, bayan tafiyarsu danish ya maimaita kalmar  ƙarshe da tsohuwar ta furta *Our destiny* kalmar ta tsaya mashi arai, yayi mamakin jinta, shin meyasa ta kalli angel ta ambaci sunanta a amtsayin ƙaddararsu?  ta6e lips ɗinshi ya ɗanyi tare da komawa saman gadon angel ya zauna, A tsanake yake kallon fine face ɗinta, soft lips ɗinta sun bushe sosai, robar ruwan dake a hannun shi ya kai saitin bakinsa ya kur6i ruwan tare da watsa mata shi saman fuskarta.................. 


(Mu haɗu Anjima in sha Allah, Jiya mantawa nayi banƙara maku one page da nace ba, Naji dadin Comment da ku kayi da likingAllah yabar zumunci, waɗanda keson cigaban part two, kada su manta already akwai group na facebbok, da zarar sunbiya za'asa, kada ku bari abaku labari, Littafin kurkukun ƙaddara, Salone na daban, zaku shaida hakan💪

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post