Kurkukun Ƙaddara chapter 41 complete

Kurkukun Ƙaddara chapter 41 complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋THE DESTINED PRISON💋


E41


Daga alkalamin Boss Bature writer of Abban sojoji


Lokacin da marece Ya nutsa, deeja tafarka daga bacci ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta rungume da pillow, ɗaya bayan ɗaya take bin gadajensu da kallo, kafin ta tsayar da idonta akan shimfidar haris, ta jima tana kallon shi, kafin ta ɗauke idanuwanta, hakanan taji tana ra'ayin tabi kowani gado ta kalli fuskokin ƴan uwanta,


Don haka ta sauko daga saman gadonta, Still jikinta ba ƙwari sosai, kamar ɗiyar roba hake take yin tafiya, tun daga kan gadon su hanna taso ma bi tana kallonsu har zuwa gadon azeeza, Ta ɗan dakata da tafiya tana kallonta, wani abu daya ɗaure mata kai bacci take yi amma sai firgita take Yi, numfashinta kuma a hargitse take fitarshi, matsawa ta ɗanyi tare da samun wuri gefen gadon azeeza ta zauna, hannunta ta ɗan ɗaura bayanta ta ɗan bubbugata, aikuwa a firgice azeeza ta farka tana faman zazzare idanuwanta, lokaci ɗaya kuma ta dafe kanta da hannu ɗaya tana faman sauke ajiyar zuciya ganin deeja ce,


"Azeeza lafiya kike ta firgita kina bacci? Ko dai baki da lafiya ne"? Tayi mata tambayar cikin nuna damuwarta,


Muryar azeeza adisashe tace"Hankalina ba a kwance yake ba, deeja bana jin daɗi, baccin nan da kika ga ya ɗauke ni har mafarkin Giants sai da nayi"  idanuwanta acike tab da kwalla takai ƙarshen maganar,


Janyota deeja tayi zuwa jikinta ta dan rungumeta da hannu ɗaya, tana lallashinta,

  

  "Ki kwantar da hankalin ki My little sis, muna atare dake, babu abunda zai faru daku," 


Azeeza tace ina jin ƙishin ruwa," da sauri deeja ta raba azeeza daga jikinta, ta sauko daga saman gadon ta nufi gadon batool ta zuƙunna ta tura hannu ƙarƙashi ta ɗauko robar ruwa, Ta miƙe ta koma gadon azeeza, ta zauna tare da cire murfin ta kwafa mata ita abaki, sosai ta shiga shan ruwan, 


A wani irin firgice Azeeza Ta jefar da robar ruwan dake ahannun deeja. Ta zabura ta yunƙura ta duro daga saman gadonta ta faɗo ƙasa, Ta shige ƙarƙashin gadonta, Jikinta sai kerma yake yi, Lamarin yae matuƙar ɗagawa deeja hankali, muryarta da alamun ruɗu take kwala ma azeeza kira tana tambayarta lafiya? Meyasa ta jefar da ruwan! Kafin deeja tayi yunƙurin saukowa daga saman gadon azeeza da niyar ta duƙa ƙarƙashin gadon ta janyota, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsin buɗe ƙopar ɗakin su hankalinta a matukar tashe ta ɗago tana kallon Benan, Ba ita ba hatta masu bacci sai da suka farka jin sautin buɗe ƙopar, wani gabjejen Giant na ya faɗo Cikin ɗakin, mai faffaɗan ƙirji bayyanar shi tamkar baiyanar mutuwa ne agaresu, Wani abun ɗaure kai ma Giant ɗin daya shigo yasha banban da waɗanda suka saba zuwa kawo musu abinci, domin kuwa shi hada Star ɗaya a jikin baƙar rigar jikinshi daga gefen hannun hagu, sai lokacin deeja ta gane dalilin dayasa azeeza ta gudu ta 6oye ƙarƙashin gado, Wata irin faɗuwa gaba ce tazo ma deeja, lokaci ɗaya ta fasa ƙara mai matuƙar firgitarwa muryarta na rawa take ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! wayyo Allahna mun shiga uku! Mun bani!' wannan maganar da deeja tayi ce tasa duk wani mai bacci ya ƙarasa wartsakewa, Hankalin angel da batool yai matuƙar tashi, a matuƙar ruɗe angel ta ruƙo hannun batool suka sauko daga saman gadonta, da gudun gaske taja ta suka faɗa cikin sashen toilet ɗinsu, Suna shiga ɗaya daga cikin makewayin, Angel ta zura jam lock ta datse ƙopar, tana juyowa batool ta faɗa jikinta tana kuka take faɗin"Angel tafiya za'ayi dani, naji ajikina nice aka zo ɗauka, shikenan za'a raba ni da farin Ciki na ina ji ina gani, za'a ɗauke ni a tafi dani inda za'a cutar da rayuwata, Ba lallaima ne a dawo dani Cikin ku ba" Fashewa da kuka angel tayi Cikin shessheƙa tace" wlh bazaiyiyu ba, haƙurina ya ƙare, komai xai faru sai dai ya faru amma wlh bazan bari atafi dake ba, duk runtsi duk wuya ina atare dake, Sai dai su kashe ni" gaba ɗaya sun shiga matsanancin tashin hankali, su biyu acikin toilet sun ƙanƙame juna 


A hankali giant ɗin yake saukowa daga saman staircases ɗin, haris yai matuƙar harzuƙa, Su rubina duk sun zazzare idanuwansu, damuwace ƙarara kwance akan fuskokinsu. Wasu har sun fara kuka, tun kafin ma a ɗauki ƴan uwan nasu, Duk wannan budurin da akeyi danish bai motsa ba, haka zalika Azeeza bata fito daga inda ta 6oye ba, domin kuwa tuni ta jima da sumewa, 


Yadda kasan zaki Haka giant ɗin nan Ya tunkaro wurin gadajensu, Yana zuwa tsakiyar ɗakin Yaja burki ya tsaya  ga dukkan alamu kamar kallonsu yake yi duk da basu Iya gane hakan. Tunda jikinsu gaba ɗaya a lullu6e yake da baƙaƙen kaya, hatta idanuwansu 


Ƙasa ƙasa da murya haris yace"ku ƙyale shege kada ku faɗa mishi inda suke muga ya zaiyi, Na rantse yau sai dai ayi duk wacce za'ae amma bazan Bari wannan ƙaton Ya ɗauki ɗaya daga Cikin mu ba" 


Muryar Hanna Cikin shessheƙar kuka take take roƙon giant ɗin tana faɗin"Dan Allah kada ku raba mu da ƴan uwanmu, Idan ma ɗaukar ta zama dole to ni ku ɗauke ni ku tafi dani amma na roƙe ka ka ƙyalesu, sun tsorata sosai zasu Iya rasa ransu, "


hannah na rufe baki, sauran matan suka fashe da kuka suna roƙonshi, bayin Allah hada ƙoƙarin saukowa daga saman gadajensu suna yi mashi magiya akan ya ƙyale musu ƴan uwansu, su sun amince ya ɗauke su amma kada ya ta6a musu Azeeza da batool, tabɗijancan Iska na wahalar da me kayan kara, sufa duk atunaninsu zai ji tausayinsu Ya ƙyalesu, Sai dai abunda basu sani ba, Zuciyar giant tamkar dutse take. basu da tausayi ko misƙala zarratin, babu ɗigon Imani akansu, Su fa kawai Umarni suke bi daga sama, haris da ranshi ke a6ace yace"Ku daina wahalar da kanku, babu alamun zai saurareku, tun da ba tausayi ne dasu ba, Ae mun riga da mun 6oye su, kuma babu wanda zai nuna mishi inda suke idan yaga dama yai ta tsayuwa daga yau har jibi, idan ya gaji ya kama hanya ya koma," haris fa ya ɗauko ta da zafi,


Tunda suka fara magana, gabjejen giant ɗin nan baiko motsa ba, Kamar yana sauraron me suke tattaunawa, 


Da mamaki su ke kallon Giant ɗin, ganin ya ɗaga hannayen shi biyu  yai clapping ɗinsu, Cikin rashin fahimtar me yake nufi yasa suka zazzare ido suna kallon Juna, 


Danish ne ya fara motsawa daga saman gadonshi, Ya miƙe ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, ya ɗan ɗago ya kalli giant ɗin dake a tsaye na wani lokaci kafin ya ƙarasa saukowa daga saman gadon, Yaje gaban giant ɗin  ya sara mashi, a matuƙar ruɗe suke kallon danish, abun mamaki abun al'ajabi


Daga bisa ni, su ka ga danish ya juya   Ya nufi sashen toilet ɗinsu, gaba ɗaya suka bi shi da ido, Batare da wani ya motsa ba, Zuciyoyinsu cike da fargabar me danish zaije yi acikin sashen toilet ɗinsu,


A lokacin batool da angel suna a zuƙunne jikin bangon toilet, sun ƙanƙame juna, Unexpected Angel tajiyo motsin buɗe kopa, tashin hankalin da ba'a sama shi date, Ƙopar dake a rufe kafin su shigo ta ciki ta sanya jamlock ta garkame ta, A matuƙar ruɗe take kallon Jikin ƙopar ganin jam lock ɗin yana motsi da kanshi ya zame kanshi, ƙopar ta buɗe, saboda tsabar tsoron da taji tuni zufa ta wanke fuskarta, batool kuwa tuni jikinta ya ɗauki wani irin zafi na fitar hayyaci, 


Duk a tunaninsu giant ne zai shigo wani abun al'ajabi sai ganin danish su ka yi ya faɗo Cikin toilet din, yana ƙarasa shigowa, Ya miƙa ma Batool hannu yace ta taso su tafi, wani irin kallon tashin hankali angel da batool suke binshi dashi, Ganin taƙi miƙa mashi hannunta yasa shi yin saurin damƙo damtsen hannunta ya janyota ta ƙarfi ya fiddo da ita daga Cikin toilet ɗin, da gudu angel tabiyo bayanshi, ta cafko hannun batool tana ƙoƙarin ƙwato ta, amma abun ya faskara domin kuwa ba ruƙon wasa yai mata ba, Adai dai lokacin da danish ya fado Cikin ɗakin, su haris suka ga ya ruƙo batool, zuciyarsu tai matuƙar karaya, lamarin yai matuƙar girgixasu, tsabar ruɗanin da suka shiga yasa suka gaza ta6uka komai, 


Kafin su yi wani yunƙuri, Danish Ya ƙarasa gaban Giant ɗin tare da batool Ya damƙa mashi ita, Giant ɗin ya sanya hannu biyu ya ɗauki batool saman kafaɗar shi batare da 6ata lokaci ba. ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, Al'ajabi ya hana su motsa, Suna ji suna gani giant ya tafi da batool tana ta kuka tamkar ranta zai fita,


Nan take angel ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, kamar jira suke Yi giant ɗin Ya fita, Haris yai wani irin kukan kura ya duro daga saman gadonshi, Ya kai ma Danish farmaki, kwalar rigarshi ya damƙa ya jijjiga shi, Hawaye na fita Cikin idanuwanshi yace"Ka kashe mu danish! Ashe dama baka da hankali? Kai wani irin wawan mutun ne sakarai soko maloho, wanda baisan Ciwon kanshi ba, wlh ka karya mini zuciyata ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka Iya ruƙo hannun batool ka damƙa ma giant ita, don aje acutar da rayuwarta, ashe na yaudari kaina bansani ba, mugu azzalumi, wawa daƙiƙi...." Kafin haris ya ƙarasa maganar shi, Gaba ɗaya sauran ƴan uwan nasu suka tarar ma danish, bugu ta ko'ina suka shiga kai mashi, Kamar sun samu jaki, Hada matan duka suka nannaɗe hannayen rigunansu suka dunga bugunshi, amma ko gizau baiyi ba. Har saida suka fasa mishi hancin shi da bakin shi jini ya soma zuba, tukunna suka sake shi, anan ƙasa ya kife idanuwanshi sunyi jawur tamkar garwashin wuta, wani irin jiri yake gani, ya rasa meke yi mishi daɗi, ta ko'ina ga6o6in jikinshi raɗaɗi suke yi mishi domin kuwa ba ƙaramin bugu suka yi mashi ba, sun haɗa mishi Jini da majina sun xautar dashi,


Kowa sai faman haki yake yi, Kuma babu wanda yaji tausayin shi, suna a tsaitsaye cirko cirko suna kallonshi, sai faman juyi yake yi,  tun da suke dashi basu ta6a jin tsanar danish ba sai yau daya nuna musu true colour dinshi, mugun zargin shi suke yi, tabbas shima yana atare da giant shiyasa yake goya musu bayan duk abunda suke yi. Ɗan jakar uba, 


Haƙiƙa Danish ya yi breaking heart dinsu, hawaye ta ko'ina akan fuskokinsu, Ji suke kamar su tattake shi ya mutu su huta, tun da baida amfani acikinsu, tare da shi ake haɗa baki a cutar da ƴan uwansu, 


"Daga rana irin ta yau kada ka ƙara kiran mu da sunan ƴan uwanka, mugu azzalumi" Javed ne yai maganar, deeja tace"dama tun jiya da aka dawo dani, naga sauyi atare dashi, ko sannu baiyi mini ba, ashe hada shi ake haɗa baki a cutar damu," 


Mubeen yace"ae ni banso muka barshi da rai ba, wlh da mun sani mun karkarya ƙasusuwan Jikin shi, " yana magana yana cije le6e,


"Danish baida tausayi baida imani, yau ya tabbatar mana da hakan, shi ɗin ba jinin mu bane, don haka ya tattara ya san inda dare yai mishi tun kafin muyi silar mutuwarshi," 


Duk wannan suratan da suke Yi, danish yana kwance, numfashinsa na fita sama sama, daga gani yana acikin mawuyacin halin da shi kanshi baisan Ina zai tsoma ranshi ba,


Hancin shi dake bleeding jini duk ya wanke farar fatar fuskarshi, muryarshi adisashe yake faɗin "ku taimaka mun da ruwa in sha" wani irin kallo mai kama da harara suka shiga jefa mishi, haris yace koba ruwa ba? Ka jira ka gani, don ubanka, " rai a6ace yaje ya ɗauko robar ruwan dake a ƙarƙashin gadon Batool ya dawo ya tsaya agaban danish, Ya buɗe murfin robar ya watsa mashi ruwan duka akan fuskarshi, yana gamawa ya jefar da robar ruwa aƙasa yace"Iya taimakon da zamu Iya yi maka kenan, ni banga ma amfanin kallonka da muke Yi ba, ku wuce muje mu xauna. Mubar shege ya ji ajikin shi". Yana ji yana gani ƴan uwanshi suka juya mishi baya, Suka nufi gadajensu su ka zazzauna, zuciyoyin su acike da alhinin rashin Batool da suka Yi, 


Hanna ce ta lura babu angel acikinsu, babu wanda ya lura da cewar ta sume a bakin ƙopar shiga sashen toilet dinsu.da sauri ta miƙe daga zaunan da take a gefen gadonta, sai da ta fara zuwa karkashin gadon batool ta ɗauko wata robar ruwan, Ta nufi inda angel take kwance ƙasa, Ta buɗe murfin robar ta ɗan ɗebo ruwan a tafin hannunta ta watsa mata saman fuskarta, nan take angel taja dogon numfashi ta fatser dashi, muryar ta cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan batool tana faɗin An raba ni da ƴar uwata, innallahi'wa' inna ilaihirraji'un! Wannan wata irin rayuwace  


"Angel ki tashi xaune," muryar hanna ce ta katse ta, jikinta duk ba daɗi, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe xaune tana faman huci sumar kanta duk ta tarwatse har tana kokarin rufe mata idanuwanta, bakowa ta ke kallo ba face danish dake kwance a ƙasa yana juyi, hannayenshi dafe da forehead ɗinshi, 


Da buɗar bakinta sai cewa tayi"me danish yake yi araye batare da kun kashe shi ba"? Fuskarta babu wasa tai maganar, haris yace"munso muyi hakan amma sai muka ƙyale shi, bawai don mun haƙura ba ne, Xamu jira ne har time da za'a dawo mana da batool muga awani yanayi take ciki, idan ta tsira shima xai tsira da ranshi, muddin kuwa batool tarasa ranta a silar shi, wlh shima sai yabi bayanta, duk irin ƙaunar da nake yi mishi, xan rufe ido ne da hannu na zan kashe shi. Inya so nima daga bisani in haɗiyi zuciya in mutu" 


Zuciyar angel har wani tafarfasa take Yi, sam ba haka taso ba, ta yi niyar tayi mishi bugun mutuwa har saiya haukace, Amma sai ta haƙura ta ƙyale shi ganin irin yadda jini ya wanke fuskarshi, koba komai Ya ɗanɗani irin zafin da suka ji acikin zuciyoyinsu,


"Angel, ki tashi muje saman gado ki kwanta" girgixa kai angel tayi tare da cewa"Kibarni anan kawai, ba inda zanje yau sai naga abunda ya ture ma buzu naɗi," gyaɗa kai hanna tayi tare da miƙewa ta juya ta koma saman gadonta ta zauna,..


Duk sunyi zugudum cike da zullumin awani hali batool take aciki, a lokacin da ba su yi tsammani ba, suka ga hasken ɗakinsu ya ɗauke, duhu ya mamaye idanuwansu, Da sauri javed Ya miƙe ya lalubo fitilunsu Ya kunna su, ɗakin yayi haske, yau fa ba bacci dare ya koma tamkar da rana, Jimamin rashin ƴar uwarsu suke ta yi, ba wanda ya damu da danish, gaba ɗaya sun manta da azeeza dake a sume Cikin ƙarƙashin gado, 


Har dare ya tsala, babu wanda ya runtsa acikinsu, sai daga bisani ne, Haris ya lallashe su, har ya samu suka kwanta, shima ya kwanta zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin tausayin danish, amma haushin shi ya hana ya taimake shi, bashi kaɗai ba. Hatta sauran ƴan uwan nashi, duk sun damu. Da danish, tsoransu kada ya rasa ranshi, 


Ganin sunyi tsit Yasa ta fara tunanin ko sunyi bacci ne, duk da tasan zaiyi wuya yau su iya runtsawa, sai dai su yi likimo, amma wannan duk bai dame ta ba, Don yau taci alwashin saita dura tagar nan kodan taje ta taimaki rayuwar ƴar uwarta, kamar yadda tayi alƙawari, bazata bari a lalata mata rayuwar ƴar uwarta ba, yunƙurawa tayi tare da miƙewa, taje saman table ɗinsu ta ɗauko fitila, Ta juya ta nufi cikin toilet ta buɗe ta shiga ciki, wannan karan ko jam lock bata sanya ba, a buɗe tabar ƙofar, domin kuwa jininta akan akaifa yake, Komai zai faru sai dai ya faru ko a mutu ko arayu,, tsakanin ita da danish, yau saita dura tagar nan, Ita kaɗai tasan irin ƙuncin da take ji acikin zuciyarta, bayan ta ajiye fitilar a ƙasa, da ƙarfi ta janyo bokitin ƙarfen ta jingina shi jikin bangon tagar, tana  ƙoƙarin hawa taji motsin mutun ya shigo Cikin toilet ɗin, a waske ta juyo baya don taga wanene, Bata yi mamaki ganin shi ba, ai yanzu ta daina ganin shi a matsayin mutun, ita da taga zahiran ɗazu da jam lock ya cire kanshi,


A tsaye yake jikin shi duk ba ƙwari, wani abu daya ɗan ɗaure mata kai, Jini daya 6ata fuskarshi yanzu babu shi, aranta tace"nasan bai wuci shi ne ya lashe shi ba, tun da ɗazu ma naga yasha na batool, Maye kawai, " 


Yadda suke fuskantar juna, kamar abokan gaba ne suka haɗu a filin daga, banbancin kawai babu makami ahannun su,


Cikin muryar fushi tace"kada ka kuskura ka matso ku sa dani, because I can harm you, I hate you Danish, I don't wanna see you, you are a bad person without faith and compassion,"


Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"You should understand me, I am innocent, I am doing what is right........" wata irin tsawa ta daka mashi yayin da take nuna shi da index finger ɗinta tace"ban damu da duk wani abu da zaka ce ba, wawa daƙiƙi, wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har ka kuskura kace zaka hana In dura tagar nan sai na yi maka mummunar illar da zata sa ka gaza takawa da ƙafafuwanka," 


A matuƙar ruɗe danish yake kallonta,  baisan ya zai yi ya fahimtar da ita ba, 


Ganin yana yunƙurin taka ƙafarshi xai tunkarota yasa ta takai hannu ta fusgi bokitin data ajiye ta ɗaga shi sama tana faɗin"Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya, I will drop this bucket on your head idiot," a wani irin raunace yake binta da kallo, duk da irin gargaɗin da take yi mishi hakan baisa ya dakata da yin tafiyar ba, yana tunkararta,  ganin dai dagaske so yake ya hanata, aikuwa da sauri ta ajiye bokitin ta haye tare dakai hannu ta ɗaɗɗago da glass ɗin, Ta dure shi ƙasa, Tana yunƙurin hawa bisa tagar, Taji ya damƙi ƙafafuwanta daƙarfi, a ƙoƙarin ya janyota ta faɗo Cikin rashin sa'a ya zame wandon Jikinta gaba ɗaya ya sabule  ƴan fararen cinyoyinta santala santala suka bayyana a suffarsu, saboda tsabar jaraba ko waiwayon wandonta bata yi ba, A haka ta dire tagar ta faɗa ta baya.................."


 Ta tafi tabar danish a tsaye hannun shi ruƙe da wandonta, don ma Allah yasa rigar uniform ɗinsu tana da ɗan tsayi ta rufe ass ɗinta duka,


Tun da ta dure tagar nan , danish ya kasa motsawa tamkar an ruƙe ƙafafuwan shi, Jikin shi yai mugun sanyi tamkar wanda aka zarewa laka, idanuwan shi na akan wandonta data bar mishi ruƙe a hannun shi, Kallon shi yake yi batare da ƙyaftawar ido ba, tsabar tashin hankali ne ƙarara akan fuskarshi , babban abunda yake jima tsoro Hannun da Angel zata faɗa, ba lallai ta Iya ganewa Ginin kurkukun ba. Domin kuwa a birkice yake. Idan har ba ka da ilmi akan shi, har ta6in hankali zaka iya samu saboda ruɗanin da zaka shiga,


Muryar shi na rawa ya furta"bazan ƙyale ta ba, why angel? Dole na bi bayanki, " Yana yunƙurin haura tagar, kunnuwan shi suka jiyo mishi sautin muryar haris dake ta ƙwala ma shi kira daga can cikin ɗakin su, Aikuwa a matuƙar ruɗe Ya fasa Yunƙurin dura tagar, da sauri Ya nannaɗe wandon angel. Ya wurga shi saman tukunyar fulawar nan ta Cikin toilet ɗin, kafin ya miƙa hannu ya ɗauki fitilar da angel ta ajiye acikin toilet ɗin, Ya juya ya nufi hanyar fita, buɗe ƙopar shi keda wuya, Sai ga haris ya faɗo sashen toilet ɗin hannun shi ruƙe da fitila,  Haska fuskar danish yai, ganin shi ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, sam ya gaza runtsawa saboda tunanin mutun biyun nan batool da kuma danish, fargabar Halin da suke aciki Ya hana shi sakat.


danish ya yi mamaki zuwan haris nemanshi , bai ta6a tsammanin wani daga Cikin su zai waiwaye shi ba. Duba da irin aika aikar da ya yi musu.


Sun ɗauki tsawon mintuna suna kallon Juna, sai daga bisani haris ya jefa mashi harara tare da cewa"Ya jikin naka"? daƙyar danish ya samu ya dai daita natsuwarshi, Cikin sanyin murya yace"Da sauƙi" ta6e baki haris yae kafin ya kuma cewa"ka zo mu koma ɗaki, naga baka ci breakfast ɗinka dana ajiye maka ba, kuma nasan kana jin yunwa, tun safe har dare ko ruwa baka sha ba,"  yana magana yana wurga mashi harara dake nuni da cewa  ba don yaso yake yi mishi maganar ba, har yanzu akwai sauran haushin shi da yake ji acikin zuciyar shi, 


Danish bai motsa ba, kallon haris kawai yake yi, shi damuwarshi akan angel ne, Baya jin zai Iya bin haris su koma ɗaki,


Jin yayi shiru yasa haris sake cewa"magana fa nake yi maka"? Fuskarshi a yamutse ya soma magana,


"Meyasa ka damu da ni? Duk irin abunda na aikata mu ku? Rai a6ace haris yace"ba wannan na tambaye ka ba, abinci nake magana, kazo muje ka ci" girgixa kai danish yai alamar a'a yace"Na ƙoshi, ka ƙyale ni koda yunwa zata kashe ni, bai shafe ka ba, lokacin dana buƙaci taimako awurinku, akan ku bani ruwa in sha, ka tuna abunda ka yi mani?


A fusace haris yaja dogon tsoki tare da matsawa ciki ya ruƙo hannun danish da niyar ya fusgoshi su tafi, da sauri danish ya ƙwace hannun shi, cikin kakkausar murya yace"Nace maka bazanci ba! Ka rabu dani! Babu ruwan kowa da rayuwata, tun da kun nuna cewa bani da amfani acikin ku," wani irin kallo haris yake bin shi da shi, kowannan su sai faman huci yake yi,


Shi burin shi haris ya tafi ya bashi wuri ko ya samu yaje ya taimaki angel, don yasan yanzu haka tana can tana neman ɗauki ta gama furgicewa,


Haris Na ƙoƙarin buɗe baki don Ya mayar mishi da martani, Muryar Deeja Ta katse mishi Hanzarin shi, daga can cikin ɗaki Ya jiyota tana ƙwala mishi Kira, don dole ya saki hannun Danish Ya juya da gudu ya koma Cikin ɗakin,


Shigar shi ke da wuya, Ya yi arba dasu deeja gaba ɗayansu agaban gadon Azeeza, tunkafin ma ya ƙarasa shiga hankalin shi yai matuƙar tashi, Ganin azeeza rungume jikin deeja, babu numfashi, kamar matatta, Su parveen sun tasa ta gaba sai kuka suke Yi, 


A bunda ya faru, Tun lokacin da azeeza ta 6oye ƙarƙashin gado ta 6oye don kada giant ya ɗauke ta, gaba ɗaya sun manta da azeeza, da ta 6oye a ƙarƙashin gadon ta, Har suka kwanta basu tuna da ita ba, sai daga baya ne deeja tana kwance saman gadonta, ta yi zurfi acikin tunaninta, kwakwalwata ta soma tariyo mata abunda ya faru kafin atafi da Batool, Nan take ta dafe ƙirji, ta miƙe zaune tana Ambaton sunan azeeza, Koda sauran ƴan uwan nasu suka ji tana kiran sunan azeeza, suma sai suka wartsake kowa Ya sauko daga saman gadon shi, A gaggauce Deeja ta ɗauko dayar fitilar data rage a ɗakin, Ta ajiye ta daga ƙasa gefen gadon Azeeza, Ta zuƙunna tana leƙa kanta ciki, Anan ne taganta xaune Kamar gunki babu abunda ke motsi ajikinta,  Ta fashe da kuka Tare da kai hannu ta 6an6arota daga Jikin bangon data jingina, ta janyota wajen gadon, ta kwantar da ita saman jikinta, Su Hanna duk suka kewayesu, kowa ya zuƙunna suna ta kuka suna ambaton Sunan Azeeza, Zuciyoyinsu duk sun karaya, ganin yadda jikinta ya sandare, Cikin shessheƙar kuka hibba tace su jira ta dauko ruwa a yayyafa mata wata'ƙil su samu ta farka, tana karasa yin maganar ta miƙe ta ɗauki fitilar ta nufi gadon batool, tana laluban robobin ruwan da suka ajiye, sai dai bata samu ko ɗaya ba, duk sun ƙare, Jiki amace hibba ta dawo tana haska su da fitilar hannunta tace babu ruwa, bari naje toilet na ɗebo, har ta juya zata nufi toilet ɗin, Muryar deeja ta katse ta da cewa"Ina haris yake? Naji motsin shi ɗazu, Ya sauko daga saman gadon shi, ina tunanin toilet ya shiga, Bari na kwala mishi kira yazo," Batare da6ata lokaci ba, deeja ta shiga kwala mishi kira, Sai gashi ya faɗo Cikin ɗaki, 


Haris na ƙarasawa kusa dasu, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunan azeeza tare da cewa Meya faru da ita? Nan suka sanar dashi komai, tun daga zuwan Giant, dafe kanshi yai da hannu ɗaya, idanuwanshi sunyi jajur, zuciyarshi duk ba daɗi, Yau dai gaba ɗaya basu ji daɗin ranar ba, sun yini da baƙin Ciki acikin ransu,


Kallonsu parveen yae ganin yadda suke ta yin kuka babu ƙaƙƙautawa,  Cikin sigar lallashi yace"Ku kwantar da hankalin ku, azeeza zata farka suma ne tayi, bari naje na ɗebo ruwa a yayyafa mata" yakai karshen maganar tare da juyawa Ya nufi cikin ɗakin, Yana laluban Inda ya jefar da robar ruwan daya watsa ma danish ɗazu, Cikin sa'a yaci karo da ita can gefen dining carpet ɗinsu, Da azama ya je ya ɗauko bottle water ɗin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin su.


Lokacin daya shiga, baiga danish ba, babu shi babu alamarshi, Sai dai bai kawo komai aranshi ba, ganin ɗaya daga Cikin ƙopar toilets ɗin nasu a garƙame, sai yayi tsammanin ko yana aciki ne, ɗayan toilet ɗin ya shiga ya kunna fanfo ya tarba robar ruwan, sai da ta Cika tab, kafin Ya kashe fanfon Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya koma inda su deeja suke a zazzaune, Zuƙunnawa yai, bayan ya ajiye fitilar hannunshi, Ya tarba ruwan a tafin hannun shi ɗaya, Ya watsa ma azeeza saman fuskarta, Kowa ya baza ido yana jiran ganin ta farka, amma shiru ko motsi bata Yi ba, Nan fa hankulan su suka ƙara tashi matuƙa,


Cikin shessheƙar kuka suka haɗa baki suna roƙon azeeza akan ta taimaka musu ta farka, Haris dasu Javed sai lallashinsu suke Yi, ganin yadda duk suka shiga damuwa, parveen na kuka tace"tun da muke arayuwar mu ba mu ta6a fuskantar tashin hankali, irin na yau ba, An ɗauke mana batool, ga azeeza kuma taƙi farkawa, Ni tsorona ma kada ace ta mutu....." kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, ta kifa kanta saman gwiwarta, muryar deeja adisashe tace"dan Allah ku daina maganar mutuwa, wlh bana sonji, in sha Allah azeezan mu zata farka, babu abunda zai same ta, addu'a ya kamata muyi mata," Haris yace"wace irin addu'a? Babu abunda zata yi mana, kawai dai mu jira zuwa lokacin da zata farka," idanuwanta cike tab take ƙwalla take kallon shi,


 Tsananin tausayinsu ne ya kamata haris, bayin Allah, tun safe hankalin su ba'a kwance yake ba, ga shi har dare ya ratsa basu runtsa ba,


  Kusan sau uku haris yana yayyafa ma azeeza ruwa akan fuskarta amma taƙi farkawa, Jikinsu duk yai sanyi, haka suka zauna a kewaye da ita, suna kallonta yayin da hawaye ke cigaba da sauka a kan fuskar kowannan su.


"To ko dai mu yi ma tsohuwa magana tazo ta duba ta kada ta mutu" acewar yasmin, har suna haɗa baki wurin cewa"Taje ta kirawo ta," Da sauri yasmin ta miƙe ta dauki fitila ta wuce ɗakin tsohuwa, lokacin da yasmin ta bubbuga ƙopar ɗakin tsohuwa bata buɗe mata ba, kusan sau takwas tana yin knocking kamar zata 6alle ƙopar har saida haris yace mata ta dawo zai iyayiyuwa bata nan,Tukunna ta ƙyale ƙopar ta dawo wurinsu ta zuƙunna,

Magiya suka soma Yi mata akan tafarka 


 "Azeezan mu ki tashi dan Allah, Badan halin mu ba, wlh ba mu gaji dake ba Muna matuƙar ƙaunarki ƙaramar mu kuma babbar mu, pls wake up, kome kike so zamuyi maki, bazamu ƙara 6ata maki rai ba, kuma ba zamu bari giants su ɗaukar mana ke ba" kamar wasu sabbin mahaukata haka suka dinga yi mata sambatu akan tafarka,  tun sunayin maganar da ƙwarinsu har ta kai ga muryoyinsu sun disashe, kowa yaja gefe suna matsar ƙwalla, idanuwansu duk sun kumbura saboda tsabar kukan da suka sha,


"Wai ina angel take ne!? Nifa banganta acikin mu ba? Yakamata wani yayi mata magana tazo taga halin da azeezan mu take aciki, tayi mata addu'a ko mun samu tafarka" Kallo kallo suka shiga yi a tsakaninsu, Jin abunda deeja tace,  gaba ɗaya sun manta da babu angel acikinsu sai da tayi wannan maganar su ka tuna da ita, Hanna tace"ɗazu acan nabarta zaune bakin ƙopar shiga sashen toilets dinmu," tayi maganar tare da juyawa tana nuna musu wurin, Basu ga komai ba, naufal yace"kodai tayi bacci ne"? Haris ya bashi amsa da cewa"ae bata a saman gadonta, ɗazu da zan shiga toilet na duba naga babu ita" a matuƙar ruɗe suke kallon juna, Eve tace"kodai ta shiga toilet ne? Bari inje in dubo ta" 


da sauri haris ya dakatar da ita tare da cewa"Ni zan dubo ta" Ya miƙe tare da kai hannu ya ɗauki fitila Ya juya ya nufi sashen toilet ɗinsu, yana gab da zai shiga, ba zato ba tsammani sai ga danish Ya faɗo hannayenshi biyu suna rungume da angel, ya tallabota a jikinshi, babu alamun tana motsi, A wani irin yanayi Su Hanna suka mimmiƙe tsaye suna kallon shi, mamaki ƙarara akan fuskokinsu, Yayin da zuciyoyinsu ke acunkushe da tambayoyi dangane da abunda ya faru da ita da har ta sume bata motsi,


An rasa me buɗe baki yayi mishi magana A cikinsu, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye Ya wuce da ita saman gadonta Ya kwantar da ita, sumar kanta duk ta hargitse, Fuskarta tayi jawur, musamman tsinin hancinta, hada ɗigon Jini, daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba,  hawayene ta ko'ina akan fuskarta, kayan Jikinta sunyi uban squeezing, Hada wandonta Daya maida mata ajikinta, Da gudu Su Hanna suka Tunkaro gadon suna tambayarshi Meya faru da angel a ina ya ɗaukota? bai tanka musu ba, Domin kuwa  A yanzu baya atare dasu, itace A gabanshi, zuciyarshi sai harbawa take yi da sauri sauri, numfashin sa da hucin zafi yake fita, a wani irin yanayi yake bin fuskarta da kallo...................."


"Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan"?


(In kinaso A ƙara posting anjima, So adage da like and comment, Har yanzu free pages ne na takun farko)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post