Kurkukun Ƙaddara page 62

Kurkukun Ƙaddara page 62

 

Kurkukun Ƙaddara 62

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E62


Daga alƙalamin Boss Bature


"Idan har baku bata haƙuri ba, Yau babu wanda zan bari yaci abinci acikin ku, kunsan dai halina tau," jin haka yasa suka haɗa baki wurin furta"We're really sorry sister azeeza ba zamu ƙara ba"


hada kama kunnansu kamar zomaye, hakan da su ka yi ba ƙaramin dariya yabata ba, Miƙa ma Jamima hannu tayi"muje inyi maki wankan tun da mun shirya" Ba musu ta amsa mata da toh, Saukowa azeeza tayi daga smaan gadon ta ruƙe hannun Jamima acikin nata, suka nufi toilet, Bayan shigarsu, Parveen ta koma saman gadonta tana yi musu sambatun yunwa take ji,  majnun kuma ya nufi tsakar ɗakin su Yanata Yin ƴan tsalle tsallen shi.


Ɗakin yai tsit na ɗan wani lokaci, Fitowa daga cikin sashen toilet dinsu Gabriel yai su azeeza na a biye da bayanshi ita da jamima da ta yi ma wanka, Sai murmushi suke saki Shigowasu yayi dai dai da turo ƙopar ɗakin su da aka yi, Gaba ɗaya hankulan su suka koma akan benan, Banda Angel data mannewa pillow, ta kammala shan kukan nata, ta lallashinta kanta ta yi shiru, Ajiyar zuciya suka sauke ganin Giants ne masu kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da Wooden trays kamar yadda aka saba, A jere suka nufi ɗakin bayan sun ajiye su saman carpet, suka ja da baya tare da ƙamewa, 


"Abinci ya iso, wanda bai wanko bakinshi ba, yai sauri yaje toilet muna jiran ku" Hannah ce tai musu magana, su ka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya su ka dinga miƙewa suna shiga sashen toilet ɗinsu, within minutes   kowannansu ya dawo suka zauna saman carpet domin cin abinci, ganin taƙi tasowa tazo suci yasa Deeja ɗaga murya ta ƙwala mata kira"Angel Ki taso muci abinci" shiru bata tanka mata ba, haris ma yai magana amma shiru taƙi tasowa, naufal yace su ƙyale ta, inyaso sun ajiye mata nata acikin kwando,


Har sun yi nisa da fara cin abincin, kowa ya natsu yana ci,  Majnun sai cusawa ya ke yi abankinshi Parveen nata jifar shi da harara ganin yadda yake yin cin mugunta.


Babu wanda ya lura da ita, Saukowa tai daga saman gadonta fuskarnan sharkaf da hawaye ta yi jawur da ita, tafiya take yi kamar zata kife ƙasa saboda rashin kuzarinta, bata nufi ko'ina ba sai wurin Giants dake a tsaye kamar dakarun Yaƙi.


Dab dasu ta tsaya kamar zata faɗa musu, fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin, zuciyarta a bushe take, muryarta a sanyaye ta soma yi musu magana


    "Bawani abu ya kawo ni wurinku ba, so nake ku faɗamin, yaushe zaku dawo mana da ƴan uwanmu? Batool shiru har yau, Danish kuma bansan awani hali yake ciki ba, ni dai don Allah na roƙe ku, ku taimaka ku faɗamin awani hali suke ciki, shin suna raye ko sun mutu ne, idan naji sai in haƙuri in fidda rai......" tun da Angel ta soma yi musu magana Hawaye nabin fuskarta, gaba ɗaya muryarta ta janyo hankalin su Mubeen akanta, tuni sun dakata da cin abincin suna kallonta, an rasa me buɗe baki ya dakatar da ita.


Girgiza kai ta yi tare da lashe hawayen daya gangaro saman la66anta da harshenta, kafin taci gaba da cewa"wai ku ba zaku ta6a aikata abun kirkiki ba arayuwarku? Haka zaku ƙare wurin aikata zalunci......." muryar Haris ce ta katse mata maganarta


   "Angel, pls ki matsa daga wurinsu! Kodan saboda mu, idan wani abu ya same ki mu zata shafa, mun rasa mutun uku acikin mu yanzu idan kema wani abu ya faru da ke ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance'? Fashewa tayi da matsanancin kuka, azeeza tuni ta kama yin kukan itama.


Cikin shessheƙar kuka Angel tace mashi"don bakasan yadda nake ji acikin zuciyata bane, ni ƙwara ma su kashe shi in huta, da irin wannan rayuwar mara amfani....." daƙyar ta ƙarasa maganar saboda wani irin jiri da ta soma gani acikin idanuwanta, ƙirjinta yai mata nauyi tamkar zai dare biyu, hannu ɗaya tasa ta dafe kanta, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Gabriel saurin miƙewa shi da yake a zaune ƙarshen carpet din dab da inda suke hannu biyu yasa wurin tarbeta, Ya ɗauke ta Ya nufi Gadonta, a sama ya kwantar da ita, hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, abincin ma ya fita aransu, duk suka miƙe da sauri suka nufi Gadonta don ganin meke faruwa da ita, Mutun biyu suka rage kan abincin, majnun da Jamima, kallon juna su ka yi kowannansu ya cunkusa abinci abakinshi, Suna tauna suna magana


"Ki ɗauko kwandon batul mu ɗibar masu abincin kada waɗannan dodonnin su tafi dashi," Majnun ne yai mata magana, harara ta wurga mashi"Kai bazaka je ka ɗauko ba, saini," ƙarasa cinye abincin bakinsa yai tare da yunƙurawa ya miƙe ya nufi gadon batul hada ɗan gudunsa,  Ya zuƙunna a gaban ƙarƙashin gadon ya zaro kwandon da sauri ya dawo ya zuƙunna kamar mutumin kirki, Ya dinga kwasar abincin Yana zubawa ciki komai Ya haɗe musu kusan Duka ya kwasar musu har saida kwandon yai soro, ya ɗago ya kalli Jamima dake ta tura plaintain chips abakinta.


"Tun da ni na ɗauko kwandon, Ke zaki maida yanzu" ta6e baki tayi"ae bani da ƙarfin iya ɗaukarshi, faɗuwa zanyi ƙasa, kai ka ɗauka mana" Girgiza kai majnun yai kamar babban mutun Yasa hannu ya ɗauki kwandon, Ya nufi ƙarƙashin gadon Ya tura shi ciki, yana ƙoƙarin miƙewa Yaji muryarta abayanshi"Gashi na ɗauko" kallonta yai, Robobin ruwa ne ta rungumo guda uku a ƙirjinta, sai yatsina fuska take yi, Hannu yasa ya kar6a Ya tura a ƙarƙashin gadon, yace mata ta kwaso sauran, Ta koma ta daukosu, Ta miƙa mashi ya kar6a ya ajiye musu, babu wanda Ya tuna da abinci ba su san ma sun ajiye musu ba, Hankalinsu gaba ɗaya yana akan Angel sun kewaye gadonta damuwa ce danƙare akan fuskokinsu, sai kiran sunanta suke yi tare da jijjiga jikinta don ta farka amma taƙi motsawa, hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankalin yai ba, 


"Angel! Pls ki tashi! Dan Allah ki farka!' azeeza ce keta magana tana matsar kwalla, Deeja tace"Allah yasa ba waɗancan mugayen bane su ka yi mata wani abu ba," haris yace"nima abunda na ke hasashe kenan" 


muryar Gabriel ce ta janyo hankalinsu akan shi" Ba abunda ya same ta, Yunwa ce take ji, ku miƙo min ruwa" yatsina fuska Naufal yai"kawai saboda tana jin yunwa saita yanke jiki ta faɗi? A ina ka sami wannan ilmin" Banza Gabriel yae dashi bai tanka mashi ba, Haris yace"Shisshigi ne kawai," Dogon tsoki Gabriel yaja tare da kallon Azeeza da ke ta yin kuka yace ta ɗabo mashi ruwa, Kafin tayi yunƙurin zuwa ɗebowa Sai ga majnun bakin gadon hannun shi ruƙe da bottle water yaji suna nema shine ya kawo musu, karo nafarko kenan da majnun ya ta6a yi musu abun kirki.


Ba tare da 6ata lokaci ba, Gabriel ya kar6i robar ruwan, ya samu wuri daga gefen gadonta ya zauna tare da sanya hannun shi ɗaya ya ɗago da kanta ya ɗaura shi gefen chest dinshi, azeeza ce ta buɗe mashi murfin robar hannun shi ta ruƙe a hannunta, Ya kanga ma Angel robar abakin ta, Duk suka baza ido suna jiran ganin in zata motsawa, aiko kamar jira take taji an daura mata robar ruwan abakinta, ta dinga kur6arshi kamar zata shaƙe maƙoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat! 


Saboda tsabar kunyar da ta kama su haris da Naufal Sai gashi sun sadda kansu Ƙasa, Kusan rabin ruwan ta shanye, wani irin yunƙurin amai ne yazo mata, saboda rashin ƙwarin jikinta bazata iya miƙewa taje toilet ba, asaman rigar Gabriel ta shiga kwara aman, tsananin tausayinta duk ya kamasu sai sannu suke yi mata, kamar zasu ɗauke mata ciwon haka su ke ji, duk da irin aman da ta ke yi ajikinshi bai ji komai ba, ko irin ƙyanƙyamin nan, saima ƙara ruƙe ta da ya ke yi da hannayenbshi don tuni ya miƙa ma Azeeza robar ruwan, bakomai ke fita acikin bakin nata ba face kayan marmarin data sha tun jiya da zallar ruwa, Sai nishi take yi tana faman lumshe idanuwanta.


"Sannu sister, Allah ya baki lafiya" acewar javed, Suma saura suka ƙara yi mata ya jiki, sam ta kasa motsa la66anta donta amsa musu, daƙyar tafara magana kamar ma sambatu ta ke yi musu tana ambaton sunan Danish da batul, miryar deeja ce tasa ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta


  "Angel ki daure kidaina sanya damuwa aranki, Idan kina yin hakan ba ƙaramin raunata mata zuciyoyin mu kike yi ba, ke da kika saba ƙarfafa mana gwiwa, amma yau kece kike neman zaucewa saboda rashin su, kowa ya jure amma kin gaza, Ya ki ke so muyi"? Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi mata maganar.


Cizon la66a ta ta yi ba tare data iya furta mata komai ba, ruwan hannun Azeeza ya kuma kar6a Ya kuskure mata bakinta dashi, tare da wanke mata fuskarta, Kafin ya miƙa ma Azeeza robar tasa hannu ta kar6a, 


"Akwai sauran abinci"? Yai tambayar yana kallon su, har suna hada baki wurin rabka salati suna faɗin"Mun manta Bamu ɗebi abincin ba, gashi giants sun tafi dashi" Kamar zasu fashe da kuka.


Chinonsu dake sauraronsu shida jamima, jin suna neman abinci yasa Suka nufi ƙarƙashin gadon Batul atare suka ruƙo hannun kwandon, suka nufo wurinsu,  tunkan su ƙaraso Ƴan uwan nasu suka ga uban tulun abincin da suka ajiye musu, Wani irin farin Cikine ya lullu6e su, Ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, Bakin parveen washe da annuri tace"Kai ba dai kune ku ka ɗebi abincin nan ba"? Har suna haɗa baki wurin furta"Mune nan muka ajiye shi" with proud su kai maganar, suna ƙarasowa parveen ta kar6i kwandon daga hannunsu ta ruƙe shi, tace da Azeeza ta ɗauko Mayafi da zasu goge aman da Angel tay, ta masa mata da toh, ta juya ta nufi akwatin kayansu kafin ta dawo Gabriel yace ta miƙo ma shi abunda zai fara bata ta ci.


Zura hannu tayi cikin kwandon ta ɗauko meat balls ta miƙa mashi, ya kar6a ya soma bata abaki tana ci, ba ƙaramin daɗin shi su ka ji ba ganin yadda ta zaƙe tana ci.


Dawowa Azeeza tai hannunta ruƙe da ɗan mayafi ta shiga goge mashi aman da Angel ta yi a jikin vest dinsa, da saman laps ɗinsa, bayan ta kammala tace mashi ya curo mata taje ta wanke mashi, murmushi yaɗan saki tare da kallon ta yace"bakya gajiya da yi min wanki Azeeza, kibar shi zan wanke da da kaina" maƙe mashi kafaɗa tai alamar bazata bari ba, yace toh bari na ƙarasa bata abincin, sai na baki rigar,


sai da ya kammala bata ya kwantar da Angel kamar me bacci ta lumshe idanuwanta, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, Kowa ya nufi gadon shi ya zauna, parveen ta ɗauki kwandon taje ta ajiye musu a ƙarƙashin gado, miƙewa Gabriel yai daga gefen gadonta, Ya tu6e rigar jikin shi ya miƙa ma azeeza tasa hannu ta kar6a, ta nufi toilet shima yabi bayanta don ya watsa ruwa ma jikinsa.


Bacci mai daɗi ya ɗauki Angel, Su majnun dake shirin yin wasa atsakar ɗakinsu, parveen ta lalla6asu akan su yi shiru kada su tada Angel tunda sun ga bata da lafiya, suka amsa mata da toh, Kafin marece yai kowannansu na zaune, wasu sun ɗan kishingiɗa da niyar bacci ya ɗauke su, rabi da kwatansu idanuwansu arufe yake, duk don saboda Angel sunyi tsif babu mai magana, gudun kada su katse mata baccin ta.


💔PRISONERS💔


Kunnuwansu ne suka soma jiyo musu motsin buɗe ɗakin su, Ras gabansu Ya faɗi ba tare da sanin dalilin hakan ba, kusan atare kowannansu Ya buɗe idanuwanshi Hankalinsu gaba ɗaya ya koma Kan staircases ɗin, Jira suke suga waye zai shigo ko wani ne za'a dawo musu dashi tunda an riga an kawo musu abinci, Yadda suke zazzare idanuwansu akan ƙafafuwan masu shigowa tamkar ƙwayar idanuwansu zasu faɗo ƙasa,


Bakowa bace face tsohuwa Zafreen Hannunta ruƙe da sanda cikin shigarta ta jajayen kaya, Rabin fuskarta rufe yake, Iya idanuwanta ne awaje, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, Abayanta Wasu Gabza gabzan Giants ne Su biyu garada masu ɗauke da Star 2 agaban baƙar rigar jikinsu, Takun tafiyarsu yadda kasan na wani namun dawa.


Wahalallan yawu kowannansu Ya haɗiya, hakanan suka dinga jin bugun zuciyarsu na hauhawa, Chinonso dake ta tsalle tsalle ganinsu yasa shi yin saurin nufar gadon parveen ya haye ya zauna gefenta hada ɗaura kanshi saman kafaɗar ta, Azeeza kuwa cikin sanɗa ta duro daga saman gadon ta faɗa ƙarƙashinsa ta la6e jikinta nata kerma, ganin ta 6oye yasa jamima lalla6awa itama ta sauko daga saman gadonta, ta shige ƙarƙashi. sauran kuwa ba wanda ya motsa kowa yasha jinin jikinsa.


Lokacin da mai girma tsohuwa Zafreen ta ƙaraso Tsakiyar ɗakin nasu, Sai kowannansu ya sadda kanshi ƙasa ba tare da sun furta komai ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, duk sun kame kansu.


"Fatan na same ku lafiya" tai tambayar tana kallon fuskokinsu, wasu daga cikinsu ne suka samu damar amsa mata da cewa"Muna lafiya"  tace"tsawon lokaci banzo na duba jikokina ba, saboda uzurirrika da suka yi min yawa, sai yau na samu damar leƙo wa, hope you're happy to see me"


kamar waɗanda aka ma dole haka suka furta mata"eh" Jinjina kai ta ɗanyi yayin da take cigaba da binsu da kallo kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar haris Ya ɗaure fuskarshi sosai, Idonshi na kallon ƙas


   "Zuwan nawa ba lallai bane yayi maku daɗi ba, domin kuwa nazo ne na raba ku da zaratan samarin dake a cikin ku" a firgice suka ɗago suna kallonta la66ansu na kerma ba tare da wani ya iya furta wani abu.


"Haris, Mubeen, Naufal, Javed, and Gabriel, A kan ku nake magana, Ba'a ta6a zuwa an ɗauke ku ba, wannan karan kurkukun ƙaddara ya buƙace ku, Don haka ba tare da 6ata lokaci ba, kowannan ku ya sauko daga saman gadon shi, A jere zaku tafi," A matuƙar ruɗe su parveen ke kallonsu, wani iko na Allah babu wanda ya musa acikinsu, Kamar yadda ta basu umarni haka suka sauko a jere suka nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, Sai waiwayon ƴan uwansu suke yi, idanuwan kowannansu cike tab da kwalla kai daga gani bada son ransu suke yin tafiyar ba, Sarrafa su aka yi, Hankalin Deeja idan ya yi duba toh ya tashi, Ba ita kaɗai ba hatta sauran matan da ke acikin su, Gashi sun gaza ɗaga koda yatsan su, Sai hawayen da ke gangarowa ta cikin idanuwansu.


"Albino, Follow their back" tai maganar ba tare da ta juya ta kalli inda chinonso yake zaune gefen parveen, Jikinshi nata kerma ya sauko daga saman gadon idon parveen akanshi, Yana tafiya yana waiwayonta kamar zaiyi tuntu6e, ahaka harya haura saman starcases ɗin Yabi bayansu Haris, Tashin hankalin da ba'a sama shi date! Kaf an kwashe mazansu, Cikin su 20 yanzu saura mutun goma sha ɗaya, Shin Ina za'a kai su haris?


Tsayar da idanuwanta ta yi akan gadon Angel dake ta sharar bacci, babu alamun zata farka, 


"Ba'a san ƙaddarar kurkuku da rauni ba, tana bacci gwanin ban sha'awa, nan badajimawa ba, zamu buƙace ki" Tayi maganar tare da matsawa dab da gadon Angel Ta ɗaura sandarta asaman ƙafarta, Nan take angel tayi wani irin juyi ta fuskanci ceilling ba tare data farka daga baccin ba, A saman ƙirjinta zafreen ta ɗaura sandar hannunta Saitin zuciyarta, Wani irin numfashi Angel ta shiga fitarwa ahargitse, Su Deeja dake kallon abunda ke faruwa kamar su ɗaura hannu aka su fasa ihu, Sai dai kash babu mai iya motsawa a cikinsu, Sai da Angel tagama banƙarewa kamar zata koma zombie, tukunna tsohuwa zafreen ta sauke sandar daga saman ƙirjinta.


A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskarta Angel, ta mayar dasu kan fuskokinsu Parveen da suka jiƙe sharkaf da hawaye, La66ansu sai kerma suke yi kamar waɗanda sanyi ya kama.


"Tun da ku ka taso a gidan kurkukun nan ba ku ta6a gabza faɗa a tsakanin ku ba, kullum kuna a cikin farin ciki, ba'a ta6a samun prisoners  masu ƴanci irin ku ba, Prison ta gatanta ku, Sai dai kash a dokar gidan kurkukun ƙaddara prisoners basu da ƴan cin kansu, bamu amince ma wani daga cikin ku ya ji daɗin rayuwar shi ba, yakamata ace a yanzu kun yi bankwana da farin ciki, fatan an fahimce ni" tai maganar tana binsu da shu'umin kallo.


kamar ta yi magana da duwatsu, babu wanda ya tanka mata, Wata ƴar iskar dariya zafreen ta saki tare da cewa"Dama na sani ba za ku Iya magana ba, saboda ban baku iznin yin ta ba,"  Ta ƙarasa maganar tare da juyawa Giants ɗin da ke abayanta suka take mata baya, Tana tafiya Cikin ƙasaita, sai da ta kai bakin matakalar benan ta ɗan dakata da yin tafiyar suma Giants ɗin suka tsaya da yin tafiyar, magana ta soma yi masu ba tare da ta juyo ta kalle su ba.


"Idan ƴar uwar ku ta farka, ku isar min da saƙon gaisuwata agare ta, nabarku lafiya" tana ƙarasa yin maganar tasa kai ta fuce daga cikin ɗakin tare da masu take mata baya.


Fitar su keda Wuya! Sautin rufe ƙopar ya fargar dasu, a firgice su ke kallon kallo a tsakanin su, fuskokin su ɗauke da matsananciyar damuwa, kukan ma yaƙi zuwa masu sai hawayen da ke ta wanke fuskokin su, tsananin tausayin kansu ne ya kama su, wannan wata irin rayuwace suna ji suna gani anyi masu yankar ƙauna An rabasu da ƴan uwansu, babu mai iya magana acikinsu, saboda tsabar takaici da baƙin cikin da su ke ji,


Azeeza da ke la6e ƙarƙashin gado, tasha kuka kamar ranta zai fita, ta ƙanƙame jikinta da ke ta kerma tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, itama jamima tana nan ƙarƙashin gadonta bata motsa ba, ta dai ji duk maganganun da tsohuwa zafreen tayi acikin ɗakin su, sai faman zare idanuwanta ta ke yi.


Yunƙurin buɗe baki deeja ta yi, sai dai bata kai ga furta abunda take son faɗi ba, idanuwan su, su ka sauka akan Angel da ta soma motsi tana banƙarewa, yatsun hannayenta nata kerma, wani irin gurnani take fitarwa da huci, Nan take maganar tsohuwa  zafreen ta faɗo musu aransu, wani irin mugun tsoro ne Ya kamasu, la66an Deeja na kerma tace dasu"ku tashi mu 6oye in ba haka ba, Angel zata iya cutar damu......"


kafin wani daga cikin su ya kuma furta wata kalma, Angel ta duro daga saman gadonta Yadda kasan gardin ƙato, facial muscles ɗinta har kerma su ke yi, launin ƙwayar idanuwanta sun 6ace 6at sai farin, Har wani gyara wuyanta ta ke yi, tana banƙare ƙirjinta da bayanta, gadan gadan ta nufo gadajen su, aiko jiki na 6ari Suka soma ƙoƙarin saukowa don su nemi wurin 6uya, Kamar walƙiya deeja taga Angel agabanta, Damƙar wuyanta tai tare da wujijjiga ta, kafin ta ɗaga ta da hannu ɗaya ta buga ta ga ƙasa, nan take deeja ta suma, ganin hakan yasa hankalin sauran yai matuƙar tashi, da gudu Parveen ta nufi sashen toilet ita da Hibba da Rubina da niyar su 6oye, kafin su kai ga ƙarasawa jikin ƙopar ta riga su isa, sai dai suka ganta agabansu, Hannu biyu tasa ta shaƙi wuyan Parveen dana hibba, Ta ɗaga su sama, suna ta kuka kamar ransu zai fita, Rubina na ƙoƙarin bi ta gefe ta shige, aiko ta sanya ƙafarta ɗaya ta taɗiyeta, kanta ya bugu da ƙasa jini harta hanci, Innallahi wa'inna ilaihirraji'un.


Basu ta6a ganin tashin hankali makamancin na yau ba, Angel bata ji bata gani, bugun mutuwa take nakaɗa musu, ko da ta ɗaga su pareen da hannayenta, A saman floor ta maka su, babu wanda hancinsa baiyi bleeding ba a cikinsu, saboda wani irin ƙarfine irin na dawakai, idan ta daki mutun dukkan sassan jikin shi ke amsawa.


Waro ido waje Hanna da sauran su ka yi, kowannan su Ya shiga ja da baya suna a jere tsakiyar ɗakin Jikin su nata kerma muryar su a tsananin tsorace suke roƙonta suna faɗin Dan Allah Angel kada ki kashe mu, ki tausaya mana halin da mu ke a ciki, laifin me muka yi maki? Yau ke da kanki kike neman halaka mu! Magana suke yi amma sam babu alamun tana jinsu, abunda basu sani na, A halin yanzu Angel ba ita ɗaya bace.


Ganin maƙiya ta ke yi musu, Burinta kawai ta kashe su har Lahira, shin ina labarin azeeza da jamima dake a la6e ƙarƙashin gado, kowannan su yasha jinin jikinshi, tsabar tsoro yahana su motsa, Sai da suka ji kukan su Hannah ya cika ɗakin, tukunna suka soma ƙoƙarin fitowa, cikin tashin Hankali yasmin da ta hango kan azeeza dana jamima dake shirin fitowa ta ƙarƙashin gado, ta dinga girgiza musu kai alamar karsu fito su koma, da hannu ta dinga yi masu alamar su koma ƙarƙashin gadon.


Ƙwaƙƙwarar damƙa Angel ta kai ma wuyan Eve da Yasmin, ta juyar dasu su ka fuskanci bango, ta daddage ta buga kansu jikin sa, tuni jininsu ya wanke jikin bangon a ƙasa suka sulale kowannan su ba numfashi, Mayar da idanuwanta ta yi akan Sarah da Hanna da suka rage, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, Zufa ta ko'ina ta shiga tsastsafo musu, sai kuka su ke yi haɗi da yi mata magiya, Sai kewaye cikin ɗakin su ke yi, Ganin da gaske fa ba ƙyale su zata yi ba, hakan yasa Sarah ta watsa da gudu zata shige sashen toilet ɗinsu, sai dai kafin ta ƙarasa, Taji an damƙi ƙafafuwanta ruƙo bana wasa ba, Gaba ɗaya ta kife saman floor Kanta ya daku, ƙugun ta ya bada wani irin sauti ruƙuƙus.


Hanna ce ta yi saura a tsakiyar ɗakin, tsautsayi ya fiddo da jamimah, Karaf akan idon Hanna tana ƙoƙarin buɗe baki tace mata ta koma ƙarƙashin gadon, kwatsam Angel ta nufo wurin Jamima, tana tafiya tamkar damusa har wani gyara wuyanta take yi, tana lashe baki, da gudun gaske Hanna ta ɗauke jamima ajikinta ta ƙanƙame ta tana faɗin


"Dan Allah kada ki yi mata komai, Kin ga ita ƙarama ce na roƙe ki, idan ma bugun ne ki haɗa da nata ki yi mini, amma ki ƙyale jamima, zata iya rasa ranta....." kafin ta ƙarasa maganar, Angel ta ware hannayenta biyu ta yi masu ƙwaƙƙwaran ruƙo, da hannar da jamimar da ta rungume a jikinta, Dukkan su ta haɗa, ta cuccu6esu ta daddage ta maka su ga saman floor, nan hake haƙorin jamima ɗaya ya 6allo daga bakinta jaga jaga da jini, har saman kumatunta, kuka tamkar ranta zai fita, tuni ta saki fitsari ta cikin wandonta saboda tsabar raɗaɗin da ta ji.


Hannah da ke ruƙe da ita tuni ta sume, kunnuwanta ne suka dinga motsi suna jiyo mata shessheƙar kukan mutun, nan fa ta shiga neman wanene, Gadajen ta dinga bi tana ɗaɗɗaga su har Allah Ya kawo ta kan gadon da azeeza ta 6oye, Tana ɗaga gadon idanuwanta suka sauka akan azeeza da ke ta yin kerma ta ƙanƙame jikinta, sam ta kasa ɗagowa ta yi tozali da fuskar Angel.


Gyara wuyan ta ta yi kamar yana yi mata ƙaiƙayi har wani sauti ya bada muƙus, A tsananin tsorace Azeeza ta soma yin rarrafe don ta gudu daga wurin, aiko ta daddage ta ɗaura ƙafarta ɗaya saman yatsun hannun azeeza ta ta ke su ta murje duk suka faffashe, jini ya soma tsastsafowa, a nan ƙasa ta baje a sume, wata irin mahaukaciyar dariya Angel ta fashe da ita.


Sautin kukan jamimah daya karaɗe cikin ɗakin nasu ne ya janyo hankalin Angel kanta, ita kaɗai ce bata kai ga suma ba, Lashe baki ta yi tare da Nufar inda jamima take a kwance ƙasa cikin mawuyacin hali, Kafin ta ƙarasa gare ta ta ji an damƙi ƙafafuwanta, Sai dai wanda ya ruƙe ƙafafuwan nata, ya gaza Kifar da ita ƙasa saboda tsabar ƙarfinta.


A sukwane ta jiyo da kanta don taga wani isasshen ne Wannan mai ƙarfin halin, Karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar Deeja wadda hawaye suka wanke ta, muryarta cikin shessheƙar kuka ta ke faɗin Angel kin bamu mamaki yau ke da kan ki ki ke neman kashe mu, ashe dama ba ƙaunar mu ki ke yi ba, ban ta6a tunanin zaki iya raunata wani a cikin mu ba....." 


Ɗaga ƙafarta ɗaya ta yi da niyar ta murje kan deeja da ƙarfi deeja ta ambaci"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! " shi kaɗai ne abunda ta iya furtawa la66anta na kerma.


tamkar an daki kanta da guduma, haka ta sanya hannayenta biyu ta daddafe kanta, wani irin jiri ta soma gani acikin idanuwanta, muryarta na rawa ta shiga ambaton


"La Hawla Wala Quwwata Illa Billah" Jikinta ne ya soma jijjiga, ta runtse idanuwanta saboda wata irin sarawa da kanta ke yi mata, Deeja nata kallonta, tangal tangal ta soma yi zata faɗi ƙasa.


Allah sarki duk da irin abunda ta yi musu hakan bai hana Deeja yunƙurawa ta miƙe tare da yin saurin tallabo Angel don kada ta faɗi ƙasa ta bugu, A hankali ta zaunar da ita, tare da zuƙunnawa gefenta, tana ambaton  sunanta cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Angel, Allah yasa kin dawo hayyacin ki, Ni nasan ba yin kan ki bane" Tana magana hawaye nabin fuskarta, hannayenta tallabe da Angel, tsawon lokacin tun sautin kukan jamima na fita da ƙarfin shi har yakai ga disashewa, a ƙarshe ma ta sume, yanzu su biyu ne su ka rage a cikin ɗakin masu numfashi. 


Muryarta ƙasa ƙasa ta soma magana"idan har dagaske ne abunda ya faru ba mafarki ba, Deeja ki kashe ni, kawai in mutu, meyasa na aikata ma ku hakan? Da hannayena nabi kowannanku da jahilin bugu, duk da irin haƙurin da ku ke bani amma naƙi sauraron ku, saboda rashin imani........'


girgiza kai deeja ta shiga yi tana faɗin  


"ba laifin ki bane Angel, Ba yin kan ki bane, ko a mafarki bana tunanin zaki iya yi mana hakan balle kuma a zahiri......" 


raba jikin ta ta yi daga na Deeja ta yunƙura ta miƙe jiki ba ƙwari take bin kowani 6angare na ɗakin su da kallo, bakomai ta ke gani acikin idanuwanta ba face jinin su, gasu nan a kwankwance kamar gawawwaki, 


 Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Lamarin ya yi matuƙar girgizata, kamar mahaukaciya haka ta shiga bin hannayenta da kallo, Acikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne da fargaba, lokaci ɗaya ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da gudun gaske ta nufi bangon ɗakin su, Deeja ta miƙe da hanzari tabi bayanta, Daddagewa ta yi ta dinga buga kanta jikin bango da niyar ta kashe kanta, bugu bana wasa ba, Goshinta da hancinta dukansu sai da suka faffashe, Zallar jininta jawur dashi ya dinga gangarowa ta saman goshinta yana wanke fuskarta, hatta la66anta bata bari ba, cizonsu ta dinga yi da haƙoranta duk ta gurgujesu, jini ya dinga tsargowa,  duk yadda Deeja taso ta janye Angel daga jikin bangon abun ya faskara, Saboda bata acikin hayyacinta, takai maƙura, idanuwanta sun makance kunnuwanta basu ji, mutuwa kawai take son ta yi awannan lokacin, ta tsani kanta, tsana mara misaltuwa, zuciyarta tagama hasala.


Cikin muryar kuka Deeja ke roƙonta tana faɗin ta yi hakuri tadaina cutar da kanta, saboda ba yin kanta bane abunda ya faru, tace Angel ki tsaya in yi maki bayanin abunda ya faru, kada ki kashe kan ki don Allah, idan ki ka mutu kika barni ya ki ke so inyi da raina, mu kaɗai fa muka rage da zamu iya taimakon ƴan uwan mu da su ke acikin mawuyacin hali, Ki tausayamin Angel, wayyo Allahna, Ya Allah ka kawo mana ɗauki, wannan wata irin masiface! Zubewa ta yi a saman gwiwowinta, ta ci gaba da kuka hannunta dafe da goshinta.


Angel kuwa bayan tagama Wanke fuskarta da jikin jikinta, Jiri ne ya ɗebe ta, ta sulale ƙasa babu numfashi, kafin wani lokaci ɗakin nasu yai tsit, baka jin sautin hayaniyar komai, Ko'ina ka kalla a cikin ɗakin, Jinin su ne, ita kanta Deeja da ta rage idonta biyu, A gefen Angel ta kwanta idonta arufe, busassun hawaye ta ko'ina akan fuskarta, kukan zuciya take yi mai raɗaɗin haske, batasan ya za ta yi ba, ita kaɗai ta rage taya zata iya ceton rayuwar ƴan uwansu? Ita kanta ba ƙoshin lafiya gare ta ba, don ba ƙaramin dakuwa kanta yai ba, lokacin da Angel ta bugata ga ƙasa har ta sume, Allah ne ya farfaɗo da ita harta tashi. 


Cikin zuciyarta ta soma magana


_Ya Allah bamu da kowa face kai da ka halicce mu, Angel itace silar da muka san komai agame da mahaliccin mu, ta faɗa mana cewa kana ƙaunarmu kamar yadda ka ke son sauran bayin ka, kana ganin mu kuma kafi kowa sanin halin da muke aciki, mun yi imani da kai, duk da bamu da wadataccen ilmi akan ka,  Ya Allah ta tausaya mana kaji ƙan mu, ka kawo mana ƙarshen wahalar nan, rayuwar mu a ƙuntace ta ke, bamu ta6a cutar da wani ba amma mu ana azabtar da rayuwar mu, babu mai taimakon mu, babu wanda yasan da zaman mu balle a kawo mana ɗauki, muna ji muna gani ana neman halaka mu saboda rayuwar mu bata da amfani awurin su, Bafa sune silar zuwan mu duniya ba! Mu ba bayin su bane, bayin ka ne Ya Allah! Baka halicce mu don a azabtar da rayuwarmu ba face don mu bauta maka, amma meyasa waɗannan mutanan suke ƙoƙarin mayar damu dabbobin su, Ya Allah idan har dagaske kai maji roƙon bayin ka ne, Ya Allah kajiƙanmu kaji koken mu, ka kawo mana ɗauki, koda ranmu ne ka ɗauka mu koma gare ka, zaifi mana sauƙi akan wannan wulaƙantacciyar rayuwar da muke yi mara ƴan ci, Ya Allah badan halinmu, mu ci albarkacin Annabin mu Annabi muhammand (SAW) mafi soyuwa  agare ka_.........."


sosai ta runtse idanuwanta, ta yi zurfi acikin zancen zucin nata, ta soma jin motsin buɗe ƙopar ɗakin su acikin kunnuwanta, wani irin tsoro da firgici ne ya lullu6e ta, hakan yasa taƙi buɗe idanuwanta don taga wanene


 Takun tafiyar mutun ta soma ji a cikin ɗakin nasu, kamar ana kewaye ɗakin, ji take kamar ta buɗe idanuwan nata sai dai tsoro ya hana tayi hakan, tana cikin wannan Halin taji wani irin matsiyacin bacci yana fisgarta, na ban mamaki, duk yadda taso ta tsayar da kanta don kada ta runtsa hakan ya faskara don tuni yai awon gaba da ita anan inda ta ke a kwance, Tsawon lokaci Deeja tana sharar baccinta, Har dare ya nutsa, hasken saman ɗakinsu ya ɗauke Na floor lamps ɗinsu Ya kunna kanshi, Haskensu ya gauraye ko'ina tamkar da rana.


 A matuƙar firgice ta farka tare da ware manyan idanuwanta kan ceilling ɗin ɗakin, Zuciyarta na harbawa sama sama cike da fargaba, tunawa da ƴan uwanta ne yasa tai wuf ta miƙe a zaune, wani iko na Allah Kaf ɗinsu babu wanda ke kwance a ƙasa sai ita, duk suna asaman gadajen su, tamkar wani abu bai ta6a faruwa ba, babu ɗigon jinin mutun ɗaya daya kasance a cikin ɗakin, an goge komai babu shi, ɗakin ya koma fes ɗin shi, tsabar mamaki ne Yasa ta miƙe Jiki na kerma ta ke bin kowani gado da kallo, bacci su ke yi Hankali kwance, Jikinsu lullu6e da bargunan su, da sauri ta kalli gadon jamimah, tana a kwance Ga azeeza itama kwance saman nata gadon, Haka zalika parveen da rubina, eve and yasmin, suna kwance saman nasu gadajen Hada Sarah da hibba, uwa uba, Angel itama tana naɗe cikin bargonta tana bacci, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, wannan bakomai bane, 


Jikinta na kerma ta nufi gadon Angel ta sanya hannu tare da yaye bargon jikinta, don taga idon raunin goshinta na nan, babu jini akan fatar fuskarta, sai dai akwai alamun fashewar goshinta dana tsinin hancinta, sai la66anta, yanayinta ya nuna alamar cewa babu raɗaɗin ciwo atattare da ita, kamar an kwashe mata shi,'

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post