Kurkukun Ƙaddara page 65

Kurkukun Ƙaddara page 65

 

Kk65

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


65


By Boss Bature


*💔PRISONERS💔*


*After one week (bayan sati ɗaya)*


Tun bayan da aka tafi dasu Haris, babu wanda yai wanka a cikin su, sun zama ƙazaman ƙarfi da yaji, Saboda rashin sukuni da walwahala, hatta gashin kansu Ya fita hayyacin shi saboda rashin gyaran da bai samu akai akai,  sai yau da Angel ta lalla6a su tace su je su yi wanka zata gyara musu kansu, tukunna suka amince za su yi, Ita kanta Angel ɗin ba wankan ta ke yi ba, yau dai ne ta ke son su ɗan gyara jikin nasu. 


Gaba ɗayan su suna a sashen toilet ɗin su, banda Jamimah ita kaɗai ta rage a ɗakin zaune saman gadonta, Hannunta ruƙe da madubi, ta wage baki tana kallon gi6inta, kullum ne saita ɗauki madubi ta duba bakinta don taga idon wani haƙorin ya fito, har yanzu babu jituwa a tsakaninta da Angel.


Su hanna da ke a sashen toilet ɗinsu, kowanansu Ya zuƙunna suna fuskantar juna, kusan su bakwai ne suna jira na cikin toilets ɗin su fito don suma su samu shiga su yi wankan, Waɗanda ke acikin Makewayin Angel ce da Sarah sai Azeeza.


Angel da ke acikin toilet, tun da ta shiga, ba wanka ta ke yi ba, tana a zuƙunne gaban tukunyar fulawan nan tsawon lokaci basu ba furennin ciki  ruwa ba, saboda rashin kwanciyar hankali.


Furennin duk sun bushe sun fita hayyacin su, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta miƙe taje bakin fanfo ta cuko bokiti da ruwa ta dawo ta kwarara shi acikin tukunyar, bayan ta kammala ta juya ta kai bucket ɗin gefen fanfon ta ajiye shi, kamar ance ta waiwayo ta kalli furennin, unexpected idanuwanta suka sauka akan Sabbin tsiron furennin da suka cika tukunyar fulawar, A matuƙar ruɗe ta ke kallonsu, launuka daban daban daga cikin su akwai wani dogon fure wanda tsayin shi ya kere sauran, Lafiyayyan gaske, Ganyayyakinsa sun bubbuɗe launin punch pink ya ciza sosai.


Zazzare idanuwanta waje ta yi, Hannunta dafe da saitin ƙirjinta, don ba ƙaramin faɗuwa gabanta yai ba, walking slowly ta nufi tukunyar fulawar kamar wadda taga wani abun tsoro, duƙawa ta ɗanyi tana ƙare musu kallo, kusan guda takwas ne sabbin furennin, bakwai daga cikin su, ganyayyakin jikinsu sun ɗan bubbushe, akwai wani ɗan ƙarami fari fat irin na jikin aunty Aneelerh, sai dai wannan ganyayyakinsa kamar sun mutu, duk sun tsomare.


Tarasa tunanin me zata yi agame da waɗanann sabbin furennin da su ka yi tsiro, ta gaza fahimtar na wanene su? tunawa tai da maganar Danish, a inda yake faɗa mata cewa kowani fure yana ɗauke da ran mutun, idan har dagaske ne, taya za'ae tasan ran wanene akansu? Ga biyu ma daga cikin furennin sunfi jigata.


Wani irin faɗuwar gaba taji, ba tare da sanin dalilin hakan ba, sai ta dinga ji aranta kamar Danish yana atare da ita cikin toilet ɗin, da sauri ta juya tana ƙarewa makewayin kallo, babu kowa a wuri.


 Muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi "DANISH"! cike da sa ran zai amsa mata, shiru ba'a amsa mata kiran nata ba, kusan sau uku tana ambaton sunanshi,  


"Danish, are you here with me? Please answer my call. I really miss you my Man," she said, her voice on the verge of tears.

 

Sai faman wurwuga idanuwanta take yi acikin toilet ɗin, duk da taga babu kowa amma ita ranta ya bata cewar Yana atare da ita.


"Danish Even if you can't speak, please make some kind of sound to let me know that you're here. I need to know if my suspicions are true, saboda a duk lokacin sa ka zo kusa dani, Inaji a jikina kuma na yarda da hakan,"


kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi a cikin toilet.


Da ƙarfi ta ƙara furta sunan shi"Danish ka amsa min" karaf akan kunnuwansu Deeja dake zuƙunne cikin sashen, su azeeza har sun fito daga wankan, hibba da parveen sun shiga, ita kaɗaice bata fito ba,


"Kamar muryar Angel nake ji acikin toilet!" yasmin ce tai maganar, Deeja  tace"kin riga ni faɗi, nima naji maganarta tana ambaton sunan Danish" hanna tace"Anya lafiyarta kuwa? Yakamata muje mu duba,"


 Kusan atare suka miƙe, zuwa bakin ƙopar toilet ɗin, knocking deeja tayi mata tare da ɗaga murya tace"Angel! Lafiya mu ka ji kina kiran sunan Danish"?


Jin muryoyin su Yasa ta dakata da yin sambatun, idanuwanta acike tab da ƙwalla, ta nufi ƙopar, bata buɗe ba, magana tayi masu cikin sanyin murya


"Babu komai, banma san na ambaci sunanshi ba, nayi missing din shi ne" 


"Shiyasa kike ta ƙwala mashi kira a cikin toilet, gaskiya Angel ba ƙaramin ƙaunar ɗan uwan nan namu ki ke yi ba, muna nan munata jiran ki ki fito, ashe kina nan kina ta sambatu halan ko wankan ba ki yi ba"? 


Fuskarta a yamutse ta basu amsa da cewa"ban kai ga yi ba, na tsaya bama furenni ruwa ne, idan na fito zan nuna maku wani abun mamaki, amma yanzu ku koma ku zauna kunsa inata magana acikin toilet bayan babu kyau,' a ƙagare take da su tafi, jin shiru yasa ta fahimci cewa sun tafi, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, ba tare da 6ata lokaci ba, ta yi wankan, suna a zaune sai gata ta fito, adai dai time ɗin da su parveen da hibba suma su ka fito daga wankan.


Kallon su ta yi gaba ɗaya idanuwansu akanta, jira suke suji me zata faɗa musu


"Kunsan me ya faru"? Girgiza mata kai su ka yi alamar a'a tace"dana shiga toilet na ɗebo ruwa na zuba ma tukunyar fulawar nan, naje in ajiye bucket ɗin, Juyowar da zan yi idanuwana su ka yi tozali da sabbin furenni masu kyan gaske, dayawa fa nayi mamakin fitowar......." bata kai ga ƙarasa maganar ba, da gudu su deeja suka shige cikin toilet ɗin, a bakin tukunyar flower ɗin suka tsaitsaya cirko cirko suna kallon furennin, gwanin ban sha'awa, sunyi matuƙar burgesu, sai dai abun da ya ruɗarsu sun kasa gane furennin wanene, sun 6ata lokaci wurin kallonsu, kamar su cinye su, daga bisani ne suka bar wurin,  sauran da basu yi wanka ba a cikinsu suka shige toilets.


Lokacin da Angel ta shiga ɗakinsu, Jamima na nan yadda suka barta, zaune tana duba madubi, azeeza tana azaune saman shimfiɗar sarah, tana sharce mata gashi, sai santin shi ta ke yi, saboda ita tsayin gashinta bai kai nasu ba,


"Sumar kan ki sak irin na Unaiza ne ƴar gidan daddy, banbancin kaɗan ne ita nata tsawo ne da shi ba yawa ke kuma naki yana da yawa kamar roba jikin shi"


"Allah sarki har kin tuna min da ita, ko yanzu tana awani hali, oho, " acewar parveen, ta yi maganar ne a yayin da ta ke ƙarasa shiga cikin ɗakin.


Angel tuni ta wuce gefen gadonta, parveen ce ta ɗauko mata comb donta gyara masu gashin kan su, atare da Sarah suka zauna zaman gyara masu sumar kan nasu, ɗaya bayan ɗaya suka yi ma kowan nan su bayan sun fito daga wankan, mutun ɗaya ta rage bata yi wanka ba, har magana azeeza ta yi mata akan tazo ta yi mata wanka tace ita bataso, Su ƙyale ta, haƙorinta ke ciwo, alhalin ƙarya ta ke yi babu wani ciwon haƙori da ta ke yi, wankan ne bata so, Dama angel neman hanyar da zasu shirya da ita take yi, aiko tana zaune saman gadonta, ba zato ba tsammani taji an ɗauketa, ta dinga kuka tana wuntsila ƴan ƙafafuwanta tana faɗin bata so ta sauke ta, hada ƙwala masu deeja kira tana faɗin bazasu zo su cece ta ba, suna ganin genie zata cutar da ita, dariya suka dinga yi mata babu wanda ya motsa.


A cikin toilet ta sauketa, da gudu ta nufi ƙopa zata fuce Angel tai saurin rigata isa ta datse ƙopar da jamlock, kallon kallo su ka shiga yi a tsakaninsu,  


Nuna jamimah tai da yatsan hannunta tare da cewa"dama daga ganin ki ba ƙaramar fitinanniya bace, amma duk masifarki baki kai ni ba lokacin da ina ƙarama, kawai daga tsautsayi yasa na 6alle maki haƙori, shine zaki ɗaura min karan tsana, nifa ce Angel ɗin ki,' ta yi maganar tana marairaice mata fuska.


Murguɗa mata baki jamima tayi tare da juya mata ƙeya, Dariya angel ta saki tana kallon bayanta, Kamar kasanya ƙafa ka take ta saboda ƙarantarta, komai nata gwanin burgewa irin na azeeza, tana matuƙar jin tausayin su.


Jin shiru Angel din bata motsa ba yasa ta ɗan waigo ta saci kallonta, suna haɗa ido ta wurga mata harara.


Dafe ƙirji Angel ta yi da hannu ɗaya 


"Genie ɗin kika harara, aiko yanzun nan zan ƙarasa 6a66ake sauran haƙoran  na bakin ki ki koma wawulo, " jin wannan maganar yasa Jamimah fashewa da wani sabon kukan.


matsawa Angel ta yi dab da ita, ta ɗan zuƙunna saman ƙafafuwanta, tare da ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗar jamima ta juyo da ita, suna facing ɗin juna


Sassauta muryarta tayi Cikin sigar lallashi tace"its okey my little sis, stop crying, bakisan cewa hawayenki, tsada ne dasu ba, " zumbura mata ƙaramin bakinta ta yi, fuskarnan a tur6une, har wani hura hanci ta ke yi, shafa gefen fuskarta Angel ta yi da hannunta,


"Ƴar kyakkyawa da ke kamar Azeeza ta, idan muka fita daga cikin kurkukun nan, zamuje gidan daddyna, akwai suturar  sanyawata da daddyna ya siya min tun ina ƴar ƙarama, nasan zasu yi maki, bayan haka ina da kayan wasa, irinsu teddy nasan baki san su ba, hada piano ɗina, duk zan baki su, sannan in sanya ki makaranta, kema ki yi karatu, kamar yarda sauran yara su ke yi, ko baki so" ta6e baki tayi don ita bata fahimci zancenta ba, amma taji an ambaci kayan wasa, Ɗaga mata gira tai"ina so," mirmushi Angel ta saki"amma fa sai mun shirya," hura hanci ta yi, tare da cewa "Ae mun shirya" dariya Angel ta saki, Tare da janyota jikinta, ta rungumeta sosai, kafin ta raba jikin su.


Wanka ta yi mata a cikin toilet ɗin, ta kuma wanke mata gashin kanta, bayan ta gama ta goyota saman bayanta, 


Suna shiga cikin ɗakin, su parveen suka dinga sowa suna tafa musu hannu, Ganin sun shirya da juna, ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, A saman gadonta ta zaunar da ita, ta ɗauko comb ta sharce mata sumar kanta, bayan ta gama, Kalaba ta yi mata guda biyu, sun sauko gefe da gefen kafaɗarta, ta zura mata ribbon ɗinta jikin wutsiyar kalaba ɗaya, ba ƙaramin kyau ta yi ba.


Lokacin da marece ya nutsa kingin abincin su na safe da su ka ajiye, Hannah ta ɗauko musu, asaman dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Suna ci saboda gatanci abaki Angel ta dinga ba jamimah, ran azeeza ya 6aci musamman da ta dinga yi mata gwalo, yarinyar ta rainata, kishi ya rufeta, ganin yadda azeeza ke ɗaure fuskarta, yasa Angel ta koma tana basu abincin su biyu ita da Jamima, idan ta basu abaki su ka ci, itama sai taci, a haka har suka kammala.


Saman gadajensu suka haye tare da kwantawa, a ƙasa Angel ta shimfiɗa bargonta, su uku suka kwanta asaman shimfiɗar, ita da Jamima da Azeeza, sarakan kishi, duk abunda jamimah tayi sai azeeza tayi, suna a kwance saman shimfiɗar, jamima ta rungume Angel, itama azeeza ta baya ta rungumeta, sai dariya take yi, abin ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.


Ba su kwanta da niyar yin bacci ba, saboda Angel ta hanasu yin baccin marece, saboda su samu damar tashi tsakar dare su dinga yin addu'o'insu, wani irin bacci ne mai daɗi ya ɗauke su, hada masu yin min shari irinsu parveen aci ci mala ikun tauna.


Dare yana gab da yi, aka buɗe ƙopar ɗakin su, sautin bai farkar dasu daga bacci ba, A hankali Giant ɗin ke saukowa saman staircases, kafaɗarshi ɗauke da mutun, daga gani macace duba da irin shape ɗin ƙafafuwanta, uban gashin kanta ya sauko ta bayanshi inda kanta yake, ya lullu6e fuskarta, Ƴar rigar dake a jikinta guntuwa ce launin ja, daƙyar ta rufe mazannanta,  hakan ya bayyana suffar fararen cinyoyinta,  kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Yanayin tafiyar Giant ɗin da ya ɗauko ta, ta banbanta da ta sauran Giants da suka saba zuwa kawo musu abinci, akwai natsuwa da kamala atattare da shi, jikinshi gaba ɗaya a rufe yake da baƙaƙen kaya, baka ganin koda yatsan hannun shi ne, bai nufi ko ina ba, sai saman gadon da ke ɗauke da no 3 a saman shi ya kwantar da ita a hankali, tare da janyo duvet ɗin dake a saman mattress ɗin Ya lullu6e mata jikinta dashi, a hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai daya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin.......


Ko sautin rufe ƙopar bai farkar da su ba, kamar matattu, yaushe rabon da su yi irin wannan baccin su kansu sun manta, tsawon lokaci babu wanda ya farka, har dare ya yi, Hasken ceilling ya ɗauke, Na floor lamps ya kunna kan shi.


Azeeza ce ta fara yin motsi zata farka, hannunta dafe da mararta, wani irin azababben fitsari ne ya matse ta, da kasala a jikinta ta yunƙura ta miƙe zaune saman shimfiɗarsu, idanuwanta biji biji bata iya ganin komai.


muryarta cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana laluban Jikin Angel.


"Angel ki tashi ki raka ni toilet, fitsari ni ke ji ya matse ni sosai....pls Angel ki tashi kada in yi shi a wando,"


Ko motsi Angel ba ta yi ba, balle har ta sa ran za ta farka.


Jamimah ce ta jiyo muryar Azeeza da ke ta yin kuka, farkawarta kenan, ta zame jikinta daga na Angel, ta miƙe zaune tana mutsustsuka idanuwanta da yatsun hannayenta, fuskarta a ɗaure babu annuri.


Ƙura ido ta yi a kan fuskar azeeza Dake ta kerma tana kuka, Muryarta da alamun bacci bai isheta ta ambaci sunanta"Azeeza...' tana jin muryar jamimah tai saurin katse kukan nata tare da cewa"Jamimah fitsari nake ji, dan Allah ki taimaka ki raka ni toilet, ya matse ni" baki asake Jamimah ke kallonta, 


   "Toilet dinne saina raka ki? Ke baki iya zuwa? Ko tsoro kike ji ne"? ta yi tambayar tana binta da kallon rainin wayau.


 Jamimah ba ta san cewa azeeza na fama da lalurar rashin gani ba, Muryarta na rawa tace"Jamimah bana gani, idan dare yayi, makauniyace ni...."


 Ta6e baki jamima tayi mata tare da cewa"ƙarya ne, Ni zaki raina ma wayau? Idan da gaske baki gani to ya akai da rana kike gani? Nafa san me nake yi,"


Takaici ne ya ishi azeeza duk yadda taso ta fahimtar da jamima taƙi yarda cewa bata gani, hakan yasa ta miƙe a makance ta soma tafiya tana laluban hanya, jamimah sai kallon bayanta ta ke yi, abun ya ɗaure mata kai ganin yadda ta ke ta sanya hannu tana laluban hanya, cikin rashin sa'a Azeeza ta nufi bango gadan gadan duk a tunaninta ta ƙaraso bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗin ne, ta daddage zata buga kanta, Jamimah ta kware murya tare da cewa"Bango ne fa ba ƙopa fa",


Ta yi maganar tare da miƙewa da gudu ta nufi in da Azeeza ta ke a tsaye jiki na kerma don ba ƙaramin firgita ta yi ba, da taji muryar jamimah tana faɗa mata cewa bango ne ba ƙopa ba.


ba ta yi tsammanin zata taimaka mata ba, sai jin hannunta ta yi a cikin nata, ta ruƙo ta tare da jan ta zuwa cikin sashen, kafin su ƙarasa toilet ɗin tuni ta fara sakin fitsarin a wando, Suna shiga ciki ta zame wandon jikinta, da sauri jamimah ta kawar da kanta gefe don kada taga tsiraicinta, bayan ta gama yin fitsarin, ta yi tsarki kafin ta maida wandon jikinta, ta kira sunan jamimah, ta taimaka mata a daddafe su ka nufi ƙopar fita.


  "Amma dai idon ki a rufe ya ke lokacin da nake cikin yin fitsarin ko? Azeeza ce tai maganar, murmushi jamimah ta saki tare da cewa"naga komai, daga yanzu sai ki daina raina min wayau kina kira na ƴar yarinya, nima ae kina min wanka, kuma kina ganin nawa"


 Shiru Azeeza ta yi ba tare da ta tanka mata ba.

A lokacin sun fito daga sashen toilet din

  "Amma wai dagaske baki gani da daddare? To ya akai kike gani da rana? yamutsa fuska azeeza tai"ko nace maki eh, ba yarda za ki yi dani ba, ki bari idan Angel ta farka daga bacci ki tambaye ki ji, " ta amsa mata da toh.


 A lokacin sun shiga cikin ɗakin nasu, har zasu nufi shimfiɗar da Angel ta yi musu, ba zato ba tsammani idanuwan Jamimah suka sauka akan Gado mai ɗauke da no 3, dakatawa ta yi da yin tafiyar, ta ƙurawa gadon ido ta hango mutun naɗe cikin bargo, tunani ta shiga yi wanene saman gadon? Saboda a iya saninta tunda aka kwashe mazan cikin su, babu mai kwana saman tsaffin gadajen su sai Angel! Ita kaɗaice ta ke kwana saman gadon Danish, da sauri jamimah ta juya ta kalli ɗayan 6angaren don taga ko wani daga cikin su Hibba ne Ya dawo saman gadon ya kwanta, sai dai ko da tabi gadajen su da kallo kowannan su yana nan,'


 A firgice ta wurga eye balls ɗin ta kan shimfidar Angel don ta tabbatar idan Angel ɗin tana nan, lamarin ya yi matuƙar razana ta ganin Angel baje saman bargo sai sharar baccin ta ke yi.


Azeeza da ta gaji da tsayuwa jin taƙi motsawa su tafi, muryarta a kasalance tace"Jamimah! Ke fa nake jira naji kin dakata da tafiya, Me kike yi ne, dan Allah ki kaina saman shimfiɗarmu in kwanta,"


Hankalin Jamimah ba ƙaramin tashi yai ba, muryarta atsorace ta furta"Azeeza Genie a ɗakin mu, saman gado no 3" ta yi maganar tana zazzare idanuwanta.


duk da Azeeza bata iya gani hakan bai hanata zare idanuwanta ba, zuciyarta ta yi wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta, Azeeza sarkin tsoro, 


"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! Jamimah ki faɗa min gaskiya, ko dai ƙarya kike yi min, wani irin genie kuma a cikin ɗakin mu, ki dai duba da kyau,"


 jamimah tace" kin san Allah dagaske na ke maki, kamar mutun ne saman gadon, kuma na dudduba su hibba mun cika mu goma sha ɗaya, na saman gadon shine cikon na sha biyu."


Girgiza kai azeeza tai jiki nata 6ari tace"jamimah bargo ne da pillow ba mutun ba, ni dai mu je mu kwanta, " ta yi maganar tana ƙoƙarin jan hannunta, duk tabi ta tsorata kanta.


"Ni dai sai naje na duba gadon inga wanene, ke ki ke je ki kwanta" 


Ran Azeeza ba ƙaramin 6aci yai ba, zuƙunnawa ta yi ƙasa tana rarrafawa don ta gano inda shimfiɗar Angel ta ke. 


A hankali jamimah ke tafiya tana tunkarar gadon, ga tsoro tana ji amma ta nace sai taga wanene, tana ƙarasawa bakin gadon, ta ɗan dakata, tare da miƙa hannunta yatsunta nata yin kerma ta ruƙo bargon, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta yaye bargo, a gigice ta runtse idanuwanta ta daddage ta fasa wata irin firgitacciyar ƙara wadda ta yi silar farkawar masu yin bacci.


 A matuƙar ruɗe Azeeza ta faɗa saman jikin Angel da ke kwance, Allah yaso ta isa ga shimfiɗar da kuwa zuciyarta ta buga silar ƙarar da jamimah ta fasa.


 Bakomai ne ya tsoratar da ita ba face Sumar kan matashiyar dake akwance saman gadon, dama can a tsoroce take shiyasa bata iya tantance gashine ko ba gashi ba, ita dai taga abu kamar hauka, Mai uban yawan gaske ya nanannaɗe, idanuwanta ne suka dinga nuna nata kamar gashin yana motsi, aiko ta rushe da kuka da gudun gaske tabar bakin gadon har tana tuntu6e garin gudu, hankalin su Deeja ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda jamimah ta furgice tana kuka, bata nufi ko'ina ba, sai saman jikin Angel ta faɗa mata, suka ƙanƙameta ita da azeeza,  sun tada mata hankali, ko motsi sun hana tayi tun da tafarka, duk sunbi sun furgice.


Babu wanda ya lura da abunda ya tsoratar dasu.


Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08169856268 ko 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇


https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post