Kurkukun Ƙaddara chapter 64 complete

Kurkukun Ƙaddara chapter 64 complete

 

Kƙ64

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


64


By Boss Bature


💋PRISONERS💋


A washe garin ranar babu wanda ya farka daga cikin su, tun jiya su ke ta sharar baccin su, jamimah ce ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta gaba ɗaya atakure ta ke A jikin Angel ta matse ta kamar zata mayar ita cikin cikinta, hada zufa a jikinta, shessheƙar ku ka ta soma yi tana ta faman ƙoƙarin janye jikin ta daga na wanda ya rungumeta ko ta samu ta miƙe.


sautin kukanta ne ya farkar da Angel a hankali ta buɗe idanuwanta waɗanda su ka kumbura, muryar jamimah ce ta janyo hankalin ta


"ni asake ni, wai wanene ya matse ni,"


Da sauri Angel ta zame hannayenta da ga jikin Jamima, ta yi zumbur ta miƙe zaune, ɗagowa jamimah ta yi fuskarta jawur da ita ƴan kumatun sun yi suntum da su, Suna haɗa ido da Angel, ta zazzaro idanuwanta waje jikinta ya hau kerma a gigice ta duro daga saman gadon tare da ɗaura hannayenta sama ta fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali.


Lamarin yayi matuƙar girgiza Angel tasan bai wuci a bun da ya faru jiya bane yasa ta tsorata da ita, Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Saukowa tai daga saman gadonta tana tunkarar jamima tare da miƙa mata hannu muryarta na ɗan rawa tace"Jamima nice fa Angel ɗin ki, meyasa kike gudu na"? Girgiza kai ta dinga ki bakinta ƙumshe da kuka ta shiga faɗin"Ni ba Angel ɗita bace, Saboda baki son mu, Jiya kamar zaki kashe ni, kika cire min haƙorina,' ta yi maganar tare da zura yatsanta ɗaya cikin bakinta don taji idan dagaske ba haƙorin, rushewa ta kuma yi na wani sabon kukan jin gi6in da ke a bakinta, Tuni hawaye sun wanke fuskar Angel, tsananin tausayinta ne ya kamata.


"Bana son ki Angel! i hate you! I don't want to see you, because you're not human, you're a genie!"


Cikin shessheƙar ku ka Jamimah ta furta maganar, yayin da ta ke ƙoƙarin  ja da baya ganin Angel na tunkaro ta, A jikin bango Jamima ta manne tana girgiza mata kai, alamar karta kuskura tazo wurin ta, zuciyar Angel ba ƙaramar karaya ta yi ba, ta rasa ina zata tsoma ranta ne taji daɗi, a gaban jamimah ta zuƙunna saman gwiwowinta, ba tare da ta iya furta komai ba.


Duk wannan abun da ke faruwa akan kunnuwan masu bacci waɗanda tuni sun jima da farkawa tun lokacin da Jamima ta rushe da kuka, Sautin ya daki dodon kunnuwan su, Tashin su kenan,  hankalinsu gaba ɗaya akan Jamima da Angel, Azeeza ce ta soma shessheƙar kuka tana zaune saman gadonta, idanuwanta akan yatsun hannayenta da su ka jigata, duk sun faffashe sai sai babu ɗigon jini ko raɗaɗi, muryar ta adisashe ta ke yin magana. 


"Na gaza yarda da abunda idanuwana su ka nuna min, bazan zargi Angel ba, amma meyasa ta take min yatsun hannuna? Meyasa ta buge mu? Laifin me mu ka mata"? Sosai ta fashe da matsanancin ku ka, Hakan ba ƙaramin rikita Angel yai ba, tana fama da jamimah ga su Azeeza sun ɗauka su ma.


Idanuwan kowannan su acike yake tab da ƙwalla, zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba, Muryar Hanna tamkar zata fashe da kuka tace"Duk irin haƙurin da nake baki Angel baki saurareni ba, har cewa nayi ki haɗa da bugun da za ki yi ma jamimah ki yi min amma shine kika ƙi saurarena, ki ka haɗamu duka ni da ita, kika buga mu ƙasa har saida haƙorinta ya cire, ko ita baki tausaya mawa ba, ita da ta ke ƙarama" 


Gaba ɗaya suna neman zautar da ita, sam ta kasa juyawa ta kallesu saboda nauyin haɗa ido da su ta ke ji,  still bata motsa ba, tana a zuƙunne gaban Jamima dake ta shessheƙar kuka, Abun ya ta6a zuciyoyin su, sun kasa fahimtar cewa ba yin kanta bane, dama zai yi wuya su fahimci hakan, kawai sun yi imani da abunda idanuwansu suka nuna musu ne.


"Da yanzu na mutu babu ni babu ƙara cin abinci, mu fa biyu Angel ta haɗa dani da hibba ta buga mu ga ƙasa, hakan bai isheta ba, sai da ta taɗiye ƙafar rubina ta kife ƙasa tukunna hankalinta ya kwanta.........." parveen bata ƙarasa maganar ba saboda kukan daya ciyota, Angel taga haza, Zuciyarta sai tafarfasa ta ke yi, ta runtse idanuwanta sosai, tana sauraron kowannan su


"Har yanzu ƙuguna ba dai dai ya ke ba, ni banma san ya akai na dawo saman gado ba, Angel taso naƙasa min rayuwa" Acewar Sarah, tana magana tana dafe qugunta da hannu ɗaya........


Eve da ke ta matse ƙwalla ido jawur tace"Haka muma ta haɗa kawunan mu nida Yasmin Ta buga mu jikin bango, daga nan ma ni ban ƙara sanin meya faru ba" Sai da ta kammala sauraron kowan nan su, gwiwowinta duk sun sage, har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, sunan Allah take ta ambato acikin bakinta, a daddafe ta samu ta miƙe tsaye tare da juyawa tana fuskantar su.


A Yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman fuskarta, sai faman jinjina kanta ta ke yi tana kallonsu da rinannun idanuwanta, babu wanda ya motsa daga saman gadon shi, duk suna a zaune suna kallonta, Kamar yarda idanuwan ta ke fitar da hawaye haka suma nasu ke tsiyaya, magana ta ke so ta yi amma ta kasa, wani irin raɗaɗi ta ke ji acan cikin zuciyarta, ga maƙoshinta da ke a bushe sai ƙaiƙayi ya ke mata.


"Kun yarda cewa ANGEL zata iya cutar da ku!"? Muryar Deeja ce ta janyo hankalin su zuwa ga dubanta, ta yi masu tambayar ne a yayin da ta ke saukowa daga saman gadonta, Tafiya take yi kamar babu wadataccen jini a jikinta, a tsakiyar ɗakin nasu ta tsaya tana bin faces ɗinsu da kallo, ta ɗaura da cewa"Tambayar ku na ke yi, ba ku bani amsa ba, jiya da abun ya faru me ya zo maku acikin ran ku"? 


Azeeza ce ta fara yin magana acikin su"ni dai nasan Angel baza ta ta6a iya cutar da wani acikin mu ba, amma narasa gane meyasa ta yi mana hakan"? tai tambayar tana kallon Deeja,


Kamar yarda azeeza ta ce, suma sauran duk haka su ka ce, sun san bazata Iya cutar dasu ba, Angel koda wani ta gani zai cutar dasu bazata ƙyale shi ba, balle kuma ace ita da kanta ne ta yi musu hakan, abunda ya sanya musu kokwanto ya ruɗar dasu shine taya akai ta yi musu Jahilin bugun nan da kanta kuma da hannayenta!


Juyawa Deeja ta yi ta fuskanci Angel da ke atsaye kamar an dasa mata aya, Jikinta sai kerma yake yi.


"Ba laifin ta ba ne, kuma ba yin kanta bane, bakowa bane Ya jawo hakan fa ce muguwar matar nan, tsohuwa Zafreen! Itace silar komai, Idan har ba za ku manta ba, akan idon ku ta ɗaura mata sanda saman ƙirjinta, ni dama tun a lokacin raina ya bani cewar wani mugun abun ne za ta yi mata, dama  tace bamu ta6a gabza faɗa a tsakanin mu ba, kuma wai a dokar prison ba'a amince ma kowani prisoner yaji daɗin rayuwar shi ba, Allah ya isa tsakanin mu da tsohuwa Zafreen, wlh ban ta6a danasanin tafiyar Tsohuwa Tamira ba irin na jiya, Mun yi babban rashi, ƙwara ita da daɗi da ba daɗi wani lokacin tana yi mana mutunci in taso" 


Babu wanda jikin shi bai yi sanyi ba, yanzu sun fahimci cewa Ba yin kanta bane, dama basu yarda cewa zata iya yi musu hakan ba, Angel ɗin da take matuƙar ƙaunar su, in dai a kansu ne har ranta zata iya badawa don ta fanshe su, Ni shaida ce akan hakan!


Atare suka hada baki wurin bata haƙuri, tace masu basu ne ya kamata su bata haƙuri ba, duk da ba yin kanta bane, Ita ya dace ace ta basu haƙuri tun da da ita a ka yi amfani wurin cutar da su, don haka tana me neman yafiya agare su, su yi hakuri su yafe mata, kuma in sha Allah hakan ba zata ƙara faruwa ba, ita kanta ta yi mamakin yarda akai Sihirin tsohuwa Zafreen Ya kama jikinta, duk da shi sirihi gaskiya ne, kuma babu wanda yafi ƙarfin ya shiga jikin shi sai wanda Allah ya tsare! Shiyasa ake so bawa ya kasance mai neman tsari awurin ubangiji, ba dole sai abu ya risƙe ka ba, kace zaka fara roƙon Allah, a'a a koda yaushe ka kasance cikin neman tsari daga gare shi, addu'ar nan itace takobin mumini, after that azhkar na safe dana marece, mutun ya dage da yin shi ba fashi, da wuya kaga wanda ke yin azhkar mummunan abu ya faru dashi ba tare da Allah ya tsare shi ba!, Allah dai yasa mu dace.


Bayan Angel ta nemi yafiyar su Hankalin kowannan su ya kwanta banda mutun ɗaya, Jamima itafa har ga Allah tsoron Angel ta ke ji, 


Abun ka ga yaro Ta ƙame jikin bango sai kuka take yi musu tana faɗin itafa bata son ganin Angel, cos she's a genie ba mutun bace, ba zata zauna a ɗaki ɗaya da ita ba, sai dai su rufe ta a cikin toilet, idan an kawo abinci su dinga kai mata acan tana ci, idan har ba su yi hakan ba, ita zata koma da yin rayuwa acikin toilet ɗinne, Abu kamar wasa ta sanya musu rigima, babu wanda bai lallashe ta ba acikin su akan ta yi haƙuri amma taƙiya, ƴar tahalikar nan har bayani su ka yi mata yadda zata fahinci cewa ba laifin Angel bane amma tace musu tasan me ta ke yi, su daina ganinta ƴar ƙarama kar take kallon su, Har ita za su yi ma wayau, so su ke ta zauna tare da Angel ɗaki ɗaya don ta samu damar ƙarasa 6alle mata sauran haƙoranta da suka rage abakinta.


Maganganun Jamimah sun yi matuƙar basu dariya, ita abunda yafi 6ata mata rai, Haƙorinta ɗaya da Angel ta cire mata, Angel har ce mata ta yi ta kwantar da hankalinta, ita yarinya ce ba ta gama fanfara ba, wani haƙorin zai fito mata, amma taƙi yarda da zancenta, Ko kusa da ita taƙi bari Angel ta je, Tsabar yarda take zabgawa Angel harara kamar idonta zai faɗo ƙasa. 


Har tambayar Angel su ka yi ya akai Jiya suka dawo saman gadajen su? Sannan ya a kai basu ga jinin su da ya yi bleeding ba, a jikin bango da ƙasan ɗakin, sannan kuma ya akai Basu tashi da raɗaɗin ciwon su ba, Deeja ce ta basu amsa da cewa"Allah ne ya kawo mana ɗauki, narasa ya zanyi a lokacin saina roƙe shi, akan ya bani mafita, kuma cikin ikon Allah Sai gashi kowannan mu ya tashi babu ciwo a jikin mu," 


Mamaki ne ya kama su jin abunda tace,  jamimah uwar masu hankali hada cewa Meyasa ita ba a dawo mata da haƙorinta ɗaya ba? Angel tace idan kika kwantar da hankalin ki, kema zanyi maki addu'a akan Allah yasa haƙorin ki daya fita ya dawo, Wani kallon rainin wayau ta yi ma Angel hada gatsina mata hanci, ƙiri ƙiri itafa ta tsangwami Angel, ganin aljana ta ke yi mata.


Yunwa ce ta fara addabar su, dama dole suji yunwa wannan jijjigar da Angel ta yi masu a jiya, Kamar an kwashe abincin da suka ci, dama jiyan basu ƙarasa cinye abincin su ba, Sakamakon sumewar da Angel ta yi, hakan yasa suka ƙi ƙarasa cin abincin.


Tunawa da abincin da su Majnoon suka ajiye musu a jiya ne yasa Parveen ta sauko daga saman gadonta, ta nufi  ƙarƙashin gadon Batul, Ta janyo kwandon, Hibba tace"Anya bai lalace ba? Kada fa mu ci abunda cikin mu zai 6aci" Parveen ta bata amsa da cewa"Ai wlh ko ya lalace sai na ci shi, idan ma cikin ya 6aci iya kaci in ta yin zaryar shiga toilet ne, dama na saba"


 A saman Dining carpet ɗinsu ta ajiye musu kwandon tace musu Mai jin yunwa ya sauko suci, Jiki duk ba ƙwari kowan nan su ya sauko daga saman gadon shi duk da babu raɗaɗin ciwo a jikin su, sun rasa kuzarin jikin su, idan ka kalli fuskokinsu gaba ɗaya babu wanda bai faɗa ba.


Sai da suka fara zuwa toilet su ka wanko bakunan su da fuskokin su tukunna su ka dawo ɗakin, kowa ya samu wuri saman dining carpet dinsu, su ka zazzauna, Jamima sarkin rigima, ba yadda ba su yi da ita ba akan tazo ta zauna su ci abinci tace musu taya zata iya cin abinci, bayan babu haƙori  ɗaya a bakin ta.


Ganin zata 6ata masu lokaci yasa Deeja ɗaukarta, ta nufi toilet da ita, ta wanke mata bakinta da fuskarta, ta fito da ita rungume a jikinta.


Sai da Angel ta fara dudduba abincin don taga idan akwai wanda ya lalace,  lafiyar shi qalau, ya dai yi sanyi, kayan marmari ne sai flat bread wraps, da snack Hada ragowar meat balls, "


Bismilla su ka yi, suna cin abincin hawaye na bin fuskokin su, tunawa da ƴan uwan su, carpet ɗin yayi musu faɗi saboda waɗanda babu acikin su, rayuwa kenan, da ta ko'ina gefe da gefen carpet ɗin zaka gan su zazzaune sun kewaye shi.


basu ta6a tunanin za'a kwashe su haris ba, sun yi matuƙar yin kewarsu, Sun damu dasu sosai, Parveen ba kowa take tunawa ba face MAJNOON, duk in ta tuna yadda ya zo saman gadonta ya haye tare da ɗaura kanshi saman kafaɗarta, Sai taji hawaye sun cika idonta, haka da zai tafi ya dinga waiwayonta, duk da irin bugun da take yi mashi kamar ta samu jaki, yaron ba ƙaramin ƙaunarta ya ke yi ba, ta yi danasanin muguntar da ta ke yi mashi, da tasan haka zata faru da ko dungurin shi ba zata yi ba, Allah sarki majnoon.


Idan muka koma 6angaren Deeja tunaninta akan HARIS ne, zuciyarta kamar zata fashe saboda kewar shi da ta ke yi, Allah sarki haris masoyi, a duk lokacin da ta shiga wani hali yafi kowa damuwa da ita, bashi da magana saita Deeja, Yana matuƙar kyautata mata tare da sauran ƴan uwan shi, haƙiƙa sun yi babban rashi na ɗaya daga cikin jagoransu, wanda suka fi damuwa dasu, wato Haris, a zuciyar Angel waɗanda suka fi tsaya mata arai duba da irin halin da aka tafi dasu, mutun na farko BATUL ce! ba zata ta6a mantawa da irin yanayin da aka tafi da ita ba, Allah sarki batul, itama tana ɗaya daga cikin jagoran su, masu ƙarfafa musu gwiwa masu nuna damuwa akan ƴan uwan su, Bayan ita sai mutun na gaba Maji daɗin gado wato DANISH, dole ne kowa yaji jiki na rashin shi, saboda shi a raunace aka tafi dashi, babu ido ɗaya fuskarshi a wanke da jinin shi, Allah kaɗai yasan awani hali ya ke ciki a yanzu.


Anyi masu babban gi6i, ɗaya bayan ɗaya haka suka zauna suna tariyo irin muhimmancin da suke da shi awurin su, bayan Danish mutun na gaba JAVED ne! yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙaunaci Angel farkon kasancewarta a gidan kurkukun ƙaddara, kyawawan halayansa abunso ne, kowa nashi ne, yana matuƙar ƙaunar ƴan uwan shi, bayan javed mutun na gaba bakowa bane face NAUFAL, Tazarar halayan shi dana haris kaɗan ne, Yana da zafin zuciya idan aka ta6a ƴan uwan shi yana ɗaya daga cikin masu tada jijiyoyin wuya, shima ba daga baya ba, in dai akan ƴan uwan shine a shirye ya ke daya zare takobi don ayi yaƙi.


Bayan Naufal Sai MUBEEN yana ɗaya daga cikin masu faranta musu rai, ya iya jan ƴan uwan shi a jiki, mutun na ƙarshe a cikin jerin waɗannan bakowa bane face GABRIEL! duk da shi daga baya ya tsinci kanshi agidan kurkukun, Amma tabbas da ace yai rayuwa dasu ba ƙaramar gudummuwa zai bada ba! Saboda yana da zuciya, ga tausayi kowace mace yana ganinta kamar ƴar uwarshi ne, sannan yana da burin su ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddara! 


Tabbas sun yi babban rashi na zaratan samarin dake acikin su, hatta ɗakin su  ya yi musu girma saboda rashin su.


duk yadda suka so su hana kansu damuwa saida abun yaci tura, Sun sha kuka tamkar ba gobe, Deeja da Angel sai aikin lallashin su su ke yi, a ƙarshe suma suka koma suna taya su kukan, sautin kukansu ya karaɗe cikin ɗakin, Dama ba ƙoshin lafiyace da su ba, Sai da su ka yi mai isarsu tukunna suka haƙura kowa ya lallashi zuciyarshi, A saman floor ɗin ɗakin kowan nan su ya kwanta kamar matattu tsabar baƙin ci ne kawai da raɗaɗin da su ke ji a cikin zuciyarsu.


Yinin ranar babu wanda ya yi wanka a cikin su, Jikinsu sai tsami yake yi, koda giants su ka zo kawo musu abinci babu wanda ya motsa a cikin su, dama  ba yunwa su ke ji ba sun ɗan samu sun ci ragowar na jiya, babu yunwa atare dasu, Jamimah ce tai ƙoƙarin ɗauko kwandonsu tunawa da yadda su ka yi jiya ita da majnoon, itama fa hada ƴar ƙwallarta, saboda an tafin mata da abokin wasan ta, duka abincin ta dinga kwasa da hannu biyu tana turawa cikin kwandon, sai da ta kammala ta kasa ɗaukar kwandon saboda yai mata nauyi, hakan yasa ta barshi asaman dining carpet ɗin, Giants na ganin ta kammala tattara abincin, su ka kwashe trays din tare da barin ɗakin, Zama jamima ta yi ta dinga ɗaukar abincin tana ci tana kallon su Hanna dake kwance ƙasa hawaye na bin fuskokin su, Sai da ta cika cikinta ta yi kulu wash rabu hani'an tukunna ta miƙe tare da komawa cikin su itama ta kwanta kamar yadda su ka yi, ta ci gaba da matsar ƙwalla tana ambaton sunan Majnoon.


A cikin waɗannan kwanakin babu wanda bai ji jiki ba a cikin su,  kamar za su yi hauka, idan Giants suka zo kawo masu abinci haka zasu dinga zazzaga musu masifa akan su dawo musu da ƴan uwan su, sun gaji da jira, a ƙarshe da su ka fahimci cewa Giants ba sauraron su su ke yi ba, don dole su ka haƙura.


yanzu ta kai ga da zarar sun ji motsin buɗe ƙopa da gudu suke zuwa bakin benan don suga idan ƴan uwan su ne aka adawo musu da su, ashe kunnuwan su ne, su ke jiyo musu hakan saboda tsabar yarda suka sanya damuwa aran su. 


Bayin Allah duk sun rame sun fige sun fita hayyacin su, kamar ana ɗibar naman jikin su, ƙasusuwan wuyan su duk shatunsu ya fito saman fatarsu, idanuwansu sun faɗa, ganin zasu zauce saboda rashin ƴan uwansu ne yasa Angel ta tattarasu  tana yi musu nasiha akan su yi haƙuri subarma Allah komai, shi zai kawo musu mafita, ta dage sosai wurin cigaba da koya musu addu'o'in da zasu dinga yi don su samu maslaha acikin zukatan su, har tsakar dare ta ke tada su daga bacci, su zauna su na addu'a suna kai kukan su wurin Allah, kullum suna zama cikin jimami, kafin Allah ya kawo musu sauƙin damuwar da ke damun su, Sun haƙura suna zama harma su ɗan ta6a fira a tsakanin su, su yi murmushi su yi dariya.


Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08169856268 ko 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇

https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post