Kurkukun Ƙaddara Page 72 by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Page 72 by Boss Bature

 


💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Daga alƙalamin Boss Bature❤


E72


Tsabar tashin da hankalin ta yai batasan sa'adda ta furta Innalillah wa'inna ilaihirraji'un! Muryarta adisashe .


Haƙiƙa ta yi danasanin maganar data gaya wa tsohuwa zafreen, Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta, Muryarta A raunace ta soma magana


"Idan har maganar dana faɗa maki ce tasa kika bani wannan za6in, ina neman alfarma a wurin ki, Ba dan hali na ba, zan zuƙunna akan gwiwowina dan in nemi yafiyarki, saboda ni na yi maki laifi bai kamata hukuncin da za ki yi mini ya shafi ƴan uwana ba.


 Girgiza kai tsohuwa zafreen tayi tare da cewa"kin ƙara tabkar wani kuskuren, Ni Ba'ayi min jayayya, sannan idan na zartar da hukun ci, babu wanda ya isa yasa in canza, Bayan haka kina yi min magana idanuwanki a cikin nawa, Anya kuwa kinsan wacece tsohuwa zafreen? Ta yi tambayar da izza, Angel dai bata ce komai ba, Jikinta duk yai sanyi.


"Idan ba ki za6i ɗaya daga cikin za6in dana lissafa ma ki ba, zan aiwatar da duka uku" fuskokin su Deeja tabi da kallo bayin Allah, Jikin su sai kerma ya ke yi, da yatsun hannayen su su ke yi mata nuna da ta ɗauki  za6i na uku, duk da basu san menene ganyan ba hankalin su yafi kwanciya da shi tunda abin ci ne.


Zuciyar Tsohuwa zafreen ta hasala sosai Jin yadda ta yi shiru bata amsa mata ba, har ta buɗe baki zata zartar da hukunci muryar Angel ta katse ta da cewa"Za6i na uku amma duk da haka ina baki haƙuri, akan ki cire ƴan uwana daga horon da zaki bani" Girgiza kai tsohuwa zafeen ta yi fuskarta babu sassauci rashin imani ne tsantsa,

Juyawa tayi tare da nufar Benan ɗakin da sauri gaints ɗin dake take mata baya su ka bi bayanta, atare su ka fuce daga cikin ɗakin.


Zubewa Angel ta yi saman gwiwowinta, sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, takaici duk ya ishe ta, ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin halin da ta jefa ƴan uwanta.


Tsananin tausayinta ne ya kama su Deeja, Jiki asanyaye su ka nufo wurinta hada su azeeza da ke a 6oye ƙarƙashin gado, A kewaye da Angel suka zuzzuƙunna suna lallashinta, Cikin shessheƙar kuka tace"Na tsani kaina, nayi danasani, zuciya ta ja mini na gaya mata magana, ga shi yanzu naja ma ku Cin ganye, Duk laifina ne, ni da ya kamata ace ina taimakon ku sai gashi ni nake ƙara jefa maku cikin matsala, " daƙyar ta ƙarasa maganar.


"Angel Ki yi haƙuri ki daina zubar da hawayen ki, ki daina ɗaurawa kan ki laifi, Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan, pls kidana kuka bamu san ganin hawayen ki na zuba"  Deeja ce ta yi maganar, Sarah tace"tun farko banso kika tanka mata ba, da duk hakan bata faru ba" idanuwanta jawur ta kalli fuskar Sarah da ta yi maganar ta mayar mata da martani"wlh zuciyace ta ɗebe ni, bansan ma na furta mata maganar ba, amma meyasa zata hukunta mu, mu duka bayan nice mai laifi"? Cikin ƙunar rai ta yi maganar, Batul tace"Saboda zalunci! Dama ai ba zata ɗauki mataki akan ki ke kaɗai ba , saboda kin nuna baki tsoronta, shiyasa ta haɗa damu don ta ƙuntata ki, kuma in sha Allah ba abunda zai faru damu, Ki kwantar da hankalin ki Angel, su ci gaba da kawo mana ganyen zamu ci, ruwa kuma ai muna da shi a cikin toilet  sai mu koma muna shan na fanfo, ba dole sai wanda su ke kawo mana ba, '


Idanuwanta arauna ce ta ke bin su da kallo mai nuni da tsantsar tausayin su da ta ke ji, ta lura basu san me ganyen ya ke nufi ba shiyasa su ka aminci za su ci, duk da acikin za6in da tsohuwa zafreen ta bata shi ne mafi sauƙi agare su.


Muryarta asanyaye tace"Amma ae ba ku saba cin ganyen ba, ba mu san wani irin ganye zasu kawo mana ba, ina jin fargabar su kawo mana wanda zai cutar damu" 


Cikin kwantar da murya Hanna ta soma magana" kada ki damu kan ki, Da daɗi da ba daɗi zamu ci"


Ta yi mamakin kalaman su agare ta, maimakon su ji haushin Abunda taja masu amma sai ga shi suna lallashinta.


A hankali ta ɗaura idanuwanta akan fuskokin su Azeeza da Jamimah da Parveen tun kafin ta yi masu magana parveen ta riga ta cewa "ba sai kin ce komai ba Angel, kwanciyar hankalin ki yafi mana komai, tabbas naji ba daɗi saboda ƙaunar da ke a tsakanina da abinci amma na haƙura tunda bamu da za6i, ƙaddarar mu ce tazo mana a haka, zamu jure muci ganye....." runtse ido Angel tayi yayin da hawaye ke cigaba da tsastsafo mata saman kuncin ta.


Cikin sanyin murya Azeeza tace"Nima bani da matsala Angel, zanci ganye da babu ƙwara ba daɗi, sannan duk runtsi duk wuya idan Allah yaso mu rayu ba wanda ya isa ya hana, nidai fata na shine Allah ya ba ki ikon ku6utar damu daga Cikin kurkukun ƙaddarar nan, wlh banaso in mutu acikin shi, " maganar Azeeza ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, su kansu basu fatan suyi wulaƙantacciyar mutuwa a gidan kurkukun kamar yarda ƴar uwarsu Unaizah ta yi, idanuwan Angel jaga jaga da hawaye ta ke kallonsu ɗaya bayan ɗaya. 


Muryar jamimah tamkar zata fashe da kuka tace"Nidai banason ganye, na saba da cin nama, amma in dai Genie ɗita zata daina kuka to nima zan haƙura inci ganyen" Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Da sauri Angel ta miƙa hannu ta ruƙo Jamimah zuwa jikinta ta rungumeta sosai tamkar zata mayar da ita cikin cikinta.


"Nima bani da damuwa Angel, duk idan na tuna abunda kika faɗa  mana dangane da irin tanadin da Allah yayiwa bayinsa salihai, waɗanda suka yi imani dashi sannan su kayi tawakkali, basu sa6a mashi ba, Sai inji daɗi araina, wahalar mu a gidan duniya ne, idan muka mutu zamu ji daɗi,"  sosai Angel ta kuma fashewa da wani kukan jin abunda Yasmin tace. 


"Yana daga cikin rukunan Imani mutun yayi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kamar yarda kika koyar damu, don haka munyi imani da ƙaddararmu, zamu rungume ta hannu bibbiyu, har zuwa lokacin da Allah zai ɗauki ranmu mu huta, amma duk da haka bamu sare ba, sannan bamu fidda rai da rahamar ubangiji ba, wata rana zamuji daɗi sai dai bamu sani ba, jin daɗin namu daga gidan duniya zai fara ko kuwa sai mun koma gare shi Allah wa'alamu,"  eve ce ta yi maganar, hibba tace"ai ni tunda Angel ta faɗa mana cewa kowa zai mutu harda waɗanda suka cutar damu da waɗanda suka sadaukar da mu, wlh sai naji daɗi araina, tunda ba dawwama za mu yi acikin duniyar nan ba, dukkan mu zamu koma ga mahaliccinmu ne, Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu dasu zaibi mana haƙƙin mu, aranar da basu isa su ƙwaci kansu ba, "  Maganganun dasu ke yi sun yi matuƙar faranta ma junansu, Musamman Angel taji daɗi da su ka yi imani da ƙaddarar rayuwarsu, a shirye su ke da su fuskanci kowani irin ƙalubale da zai zo masu acikin arayuwarsu a mutu ko ayi arai.


Tun daga wannan ranar ba'a ƙara kawo masu abinci mai rai da lafiya ba, Faranti Biyu ake cuko masu Da ganye ganyen ma mai ɗaci, ga ruwan zafi har tiriri ya ke yi, saboda tsabar mugunta haka ake kawo masu shi don su sha, Rana ta farko da aka fara kawo masu ganyen babu wanda ya iya ci, ga yunwa suna ji kamar suci ƴan hancin cikinsu, suka rasa ya zasuyi, saboda bai ciyuwa agare su, basu saba cin ganye ba, Yadda aka kawo shi haka giants suka koma dashi, a cikon kwana na biyu ne da yunwar ta kusa yi masu Illah Kamar dabbobi suka zauna suna cin ganye, saboda mugun kamun da yunwa ta yi masu kamar zasu zauce, suna ci suna kuka maƙoshinsu na ƙaiƙayi ahaka suka cinye shi tass, Basu sha ruwan zafin da a ka kawo masu ba, sai dai su ka koma suna amfani dana fanfon da ke a cikin toilet ɗinsu, 

Ganyen da su ke ci ba ƙaramar illa ya ke yi masu ba, saboda basu saba ba, hakan yasa cikinsu ya dinga 6aci, babu wanda bai yi gudawa ba a cikin su, duk sun rame sun fita hayyacin su, sun zama mahaukatan ƙarfi da yaji,  addu'ar da suke samu suyi yanzu sun daina saboda Rashin lafiyar da suke fama da ita, Kullum ne sai an samu wanda zai kwanta jinya acikin su, sun jigata sosai, kamar ba za su rayu ba, tun suna ci yana 6ata masu ciki har ta kai ga yanzu sun daina yin gudawa idan su ka ci ganyen, sun fara sabawa da cin shi, cikin nasu ya daina 6acewa, Idan aka kawo masu shi zama suke yi suci shi kamar dabbobi, ruwan kuma Basu iya shanshan shi da tsafi don zai iya yi masu illah, sai sun hura shi da bakunansu kafin su samu su kora shi ta cikin maƙoshin su, yaushe rabon da su wanke uniform ɗin jikin su yau tsawon wata ɗaya kenan, babu mai yin wanka a cikin su, damuwa da baƙin cikin halin da su ke aciki sakamakon canza masu abinci da akayi da kuma rashin dawo masu da ƴan uwansu yasa duk sun rasa kwanciyar hankali. 


Sai da Angel ta yi dagaske wurin ƙoƙarin danne zuciyarta dake shirin bugawa ta hanyar dagewa dayi masu addu'a tukunna suka ɗan samu salama, natsuwa ta shiga jikinsu, yanzu suna samun damar runtsawa su yi bacci sosai, amma fa dukkan su bana tunanin za'a iya samun ɗaya  wanda bai fama da depression, wani lokacin idan ƙirjinsu yayi masu zafi zuciyoyinsu suka yi masu nauyi, haka zasu zauna su dinga karanta duk wasu addu'o'i da su ka san zasu Sanyaya masu zukatansu, kuma cikin ikon Allah da zarar sun yi komai su ke samun sauƙi, harma su samu damar yin bacci, yanzu sun fidda rai da za'a dawo masu da ƴan uwan su duba da irin tsawon lokacin da aka ɗauka babu su, Danish  Yana acikin wata na biyar a hannunsu,  Su haris suna acikin wata na huɗu,  basu san awani hali su ke aciki ba, Allah kaɗai yasan irin azabtarwar da ake yi masu, suna raye ko sun mutu basu da tabbacin hakan....................."


💔PRISONERS💔


Dare ya nutsa sosai, babu mai motsi acikinsu, Bacci su ke yi kamar matattu,  numfashin Angel ne ya soma canzawa, zufa ta soma wanke fuskarta, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, yatsun hannayenta dana ƙafarta suka soma Yin kerma, Ga dukkan alamu mafarki ta ke Yi, wanda yasa ta shiga wannan yanayin da take a ciki, su uku ne a kwance saman shimfiɗar da ta yi masu a ƙasa, Ita da Jamimah sai Azeeza.


 Sai faman yin sambatu ta ke yi  tana ambaton Sunan tsohuwa Tamira! 


Wata irin firgita ta yi Sakamakon Ta6a jikinta da akayi, a hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana faman zazzare idanuwanta, gashin kanta duk ya  tarwatse saman bayanta.


"Angel ni ce! Meyasa kike sambatu kina ambaton sunan tsohuwa Tamira? A tsananin tsorace ta ɗaura idanuwanta kan fuskar batul da ke yi mata magana, Farkawarta kenan daga bacci, fitsarine ya matse ta bayan taje toilet ta yi shi ne ta dawo ɗakin har zata kwanta sai taji muryar Angel tana sambatu acikin baccinta, wannan dalilin ne yasa ta nufi shinfiɗar su don taga meke faruwa da ita.


Bata amsa mata tambayarta ba, saboda bata a cikin natsuwarta, ganin ta miƙe tsaye ne yasa itama batul ɗin ta miƙe tana tambayarta lafiya meya faru? Babu alamun zata tanka mata, sai faman bin ɗakin su ta ke yi da kallo kamar ranar ta fara ganin shi.


"Angel dare ne fa, Me ki ke kallo? Magana fa na ke yi ma ki amma kin share ni....." tunkan batul ta ƙarasa maganar, Angel ta damƙi hannun batul tare da Janta da sauri ta nufi sashen toilet ɗin hannunsu aruƙe dana juna, bayan sun shiga sashen ne Angel ta saki hannunta, aruɗe batul ke kallon fuskarta gani take kamar angel tafara haukacewa ne shiyasa ta janyota a tsakar daren nan zuwa sashen toilet ɗinsu.


Fuskarta da alamun ruɗi tace"kiyi min magana mana, meyasa kika kawo ni nan"?


Sai da ta fara tattara natsuwarta guri guda kafin ta soma magana


"Batool na yi wani mafarki da ban ta6a yin irin shi ba, dangane da wani kalami da tsohuwa Tamira ta ta6a furta mana......" daƙyar tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, batul duk ta gama ruɗewa

"Wani kalami kenan"!? Ta jefa mata tambayar.


"Zan faɗa maki amma kafin nan inaso ki sanar dani, Kafin zuwana gidan kurkukun nan, a ina ku ke yin rayuwa? Meyasa aka canza maku ɗaki daga asalin wanda ku ka baro"? 


"Angel meyasa kika tambaye ni"? A tsiwace tace"nidai ki bani amsar tambayata"! Yawu batul ta haɗiya kafin tace"Ni kaina bansan dalilin dayasa aka dawo damu nan ba, kawai dai nasan tsohuwa Tamira tace zata sanya a canza mana ɗaki saboda asalin wanda muke aciki yayi mana ƙanƙanta, babu wadataccen filin da zamu sakata mu wala........" A dabarbarce take yin maganar saboda yadda Angel tayi mata rumfa kamar zata rufeta da bugu.


"Amma ranar da aka kawo ni kurkukun nan, Na tsinci kaina nikaɗai acikin ɗakin nan, sai daga bisani aka buɗe ƙopa sai gaku kun shigo Ciki, daga ina ku ke"!? girgiza mata kai Batul tayi"bazan iya tunawa ba Angel, bansan inda aka kaimu ba, " numfasawa Angel tayi tare da sanya hannunta biyu cikin sumar kanta, kamar akwai wani abu da take son ganowa, ganin yadda duk tabi ta ruɗe ne yasa Batul tambayarta"meke damun ki ne? meyasa ki ka  tambayeni"?


"Saboda ina hasashen Akwai ƙopar da zamu Iya guduwa ta cikin  ɗakin nan da muke rayuwa........." batul bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba.


"Angel ƙopa fa kika ce a cikin ɗakin nan ta ina kenan? Anya kuwa kinsan me kike faɗa kuwa"?


Jinjina kai ta ɗanyi kafin ta soma magana" akwai wata magana da tsohuwa tamira ta ta6a furta mana, ban tashi tunawa ba sai Acikin mafarkin da na yi yau, abun tace mana shi ne  tana so mu ɗauka cewa mu kamar 


*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MANA  FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARMU, TABBAS MUNA DA DAMA*


Amma fa dole sai Mun yarda da kan mu, mun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare mu Sa'annan


 *MU NE MAKULLAN DA ZAMU BUƊE TA* 


Numfashi Angel taja tare da cigaba da yin magana


"Kalamaine tayi mana cikin hikma, a hasashe na, dama tun fil azal tsohuwa tamira tana son taimakon ku, shiyasa tayi silar da aka canza maku ɗaki aka kawo ku nan, bayan haka tasan da zuwana gidan kurkukun nan........" 


Ba ta kai ga ƙarasa maganar ba, Batul ta tari numfashin ta da cewa" kin manta wacece tsohuwa tamira, itama fa muguwace kamar sauran, banbancin kaɗan ne sannan ma'aikaciya ce ita agidan kurkukun nan, taya kike tunanin zata iya taimakon mu?  ta yi mata tambayar tana bin da kallo.


"Mutun koda dutse ne a ƙirjin shi ba zuciyaba, idan Allah  ya so ka da rahama sai kaga Ya rikiɗa daga mara tausayi zuwa mai tausayi, Zai iya yiwuwa tsohuwa tamira taji tausayin halin da ku ke acikine shiyasa ta nemi hanyar da zata ku6utar daku, Ita da kanta ta faɗa mana cewa tun da ta ke rainon prisoners bata ta6a samun waɗanda su ka kwanta mata aranta ba irin mu, da alama tun kafin zuwana kurkukun nan take so ta taimake ku sai dai tagaza gudun kada taja ma kanta, Shiyasa ta dakata har zuwa lokacin da aka kawo ni sai tayi amfani da kaifin basirar da nake dashi wurin sanar dani cikin hikma akan hanyar da zamu bi don mu gudu daga prison!"


Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar,  Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikma donta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai


 

........................❓❗


Dai dai nan Na ajiye alƙalamina, Shin kuna ganin dagaske ne hasashen Angel akan kalaman tsohuwa tamira?   


Nayi alƙawarin Idan har like ɗinku Ya haura 500 zan Sanya maku 2 pages anjima, a comment , Zakuji yadda za'ae su gano ƙofa, Amma indai bai kai ba, Babu post sai gobe

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post