Kurman Baƙi Page 14

Kurman Baƙi Page 14

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 14*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*


*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*


*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*


*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*


LOGO

INVITATION CARDS

BANK STICKERS

BUSINESS LOGO

SAVE THE DATE

P.O.S BANNERS

BIRTHDAY CARD

BOOK COVER

DATA FLAYER

BIRTHDAY VIDEOS

VIDEO INVITATION

AI PICTURES


_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_


*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*


*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku


_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_


https://wa.me/+2347084515410


_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽

________________________________             "akwai maganar da nakeson muyi,saidai bansan yadda zaku fahimceta ba" saleem din ya fada a tausashe yana jan plate din data ajjiye masa a gabansa don ya qagu ya fara cin abincin,iya qamshin abincin kadai ya isa ya sa ka zaqu kakai bakinka,kada ma ayi maganar farfesun kayan cikin da yaji spices.


            Zama tayi sosai a gabansa kaman zata koma cikinsa ko kuma an bata gadinsa tana dubansa da wani tattausan kallo. Idonsa ya lumshe ya sake budewa duka lokaci guda yana dubanta qamshinta yana kai masa ko ina


"Uwargida sarautar mata" ya samu bakinsa da fadi. Wani shagalallen murmushi mai qaramin sauti ta saki tana watsa idanunta


"Itace maganar da kace zakayi din?" Kai ya girgiza


"Bansan ya akayi bakina ya subuce ba"


"To ka gyara bakinka tun kafin umman haneefa ta iso,don nidai ba ruwana"


"Laifinki ne hajjaju,irin wanann kallon na rantse tsaf zai hanani cin abincin nan,bari kiga tun baki cikamin cikina da soyayya ba" rausayar da kai tayi tana sake sakin siririyar dariyar. Itakam har abada koyon kyawawan dabi'un da zasuja hankalin miji ba shakka sun biyata,don ko yaushe suna wanketa ne a idanun saleem,koda bata sanyawa jikinta komai da zaija hankalinsa din ba,iya kallonta kawai ya wadatar.


"Umara nakeson muje gaba daya,ni dake da hajiya sai zainab,to amma kudin hannuna basu cika ba,kudin tafiyar mutum uku ne ba kadan,kinga mutum daya bai samu ba" 


"Kai,kai ma sha Allah" ruqayyan ta fadi tana langwashe qafafunta


"Amma naji dadi qwarai da gaske,Allah ya qara budi,inda duk allura ta fita Allah ya naidata dutse"


"Ameen ameen,duka wannan addu'ar haka bayan baki da tabacin kina cikin masu zuwan?" Murmushi tayi masa me kama da harara


"Zakaje,hajiya zata je,to meye ya ragemin?,kamar nayi rabin zuwa kenan,rabin kuma sai ranar da ubangiji yayi kirana" zamansa ya gyara yana jinjina kai,ko da yaushe maslaharta itace tasa,koda yaushe buqatunsa take sakawa a gaban nata(maza nason irin wadan nan matan),to shikam me yayi masa saura game da matar kirki?.


"Amma sai hajiya tace ko ita zata haqura naje daku,ita wata shekarar idan da yawan rai tunda alhaji me rasuwa ya taba kaita hajji" Kai ruqayya ke girgizawa da sauri tana dubansa


"Kai yanzun koda tace hakan sai kayi hakan?,da yake mu muka haifa mata kai?,sam ba za'a yi haka ba,mu ya kamata mu haqura din,mune qasa da ita,yanzun ni ko Zainab wani a cikinmu zaiso idan su alhassan da khalil sun girma hakan ta faru tsakaninmu da matansu?".


                Kai ya girgiza yana jin wani sanyi a cikin ransa,lallai ya samu mace ta garin da annabi ya suffanta,yana cikin mazan da suka shigo duniya a sa'a. 


"Wai da ina ganin zanyi mata gyaran gida ne kafin mu tafin shi yasa"


"Dukka ta cancanta daddy,ta cancanci abinda yafi haka ma,hasalima inda zata buqaci ranka ka ciro ka bata baka saka mata da komai ba" ta fadu tana dubansa. Wata ajiyar zuciya ya saki yana jinjina kai cike da gamsuwa,wata irin daraja da kimarta suna linkuwa a ransa,ruqayya macace daya tamkar da dubu lallai ya shaida wannan.


                Takun Zainab taf taf shine yana hankulansu,suka waiwaya gaba daya suna dubanta. Idanunta akan ruqayya suke,ji takeyi kaman ta shaqota,taji komai a labewar da tayi,banda baqin hali da baqar zuciya da ya cakuda da baqinciki ai ita taso yiwa mugunta. Saudiyyan nan daga ruqayya din har hajiyan ai sunje,shine don tsabar hassada da qyashi me makon ita da tunda tazo duniya ba'a taba zuwa da ita ba tace a dauketa sai tace a barsu?.


"Amma dai wannan shawarar ba komai a cikinta sai zallar rashin adalci da qyashi da hassada" Zainab ta fada fuskarta na nuna tsantsar bacin rai. Daga zaunen saleem ya daga kai ya bita da kallo. Tsaiwarta a gurin kawai ya canza atmosphere na wajen. Daurin qirjin nan ne dai na gado sai armless shirt daga ciki,qafafunta tsage tsage a waje kamar sunyi d'ai d'ai


"Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar. Cikinta ne ya juya abinda ya Sanya yawu taruwa a bakinta kenan,sai ta juya gefan hagunta ta fesar da yawun tasa bayan hannunta ta goge ragowar da ya bata mata baki. Da sauri ruqayya ta kawar da kanta gefe tana a'uziyya zuciyarta na tashi saboda tsantsami.


             Juyowa Zainab din tayi tana duban saleem


"Ta yaya zakayi shawara da ita ita kadai,bayan ba ita kadaice matarka ba?,ba ita kadaice take da haqqi a kanka ba,sai nayi magana kuma aga na cika qorafi bayan adalcinne sam ba'a yishi ba?"


"Ni kika tsayawa akai kina gayan ban miki adalci ba?" Yadda yayi mata tambayar ta bugar mata da gwiwa,amma rashin son gaskiya da jin tafi qarfin ayi mata fada sunyi mata katutu saita kauda kanta gefe ta fara halin nata wato gunaguni


"Eh ai azzaluma ka tambaya gashi tana batun ni da ita duka mu rasa ku tafi kai da hajiya saboda tsabar muguntar kowama ya rasa,bayan ko hajiyarma ta taba zuwa ai,nice ba inda na taba leqawa a qa'ida......" Ta fada hannunta a qugunta ba tare data dubeshi ba.


"Idan baki matsamin akai ba sai ranki yayi mummunan baci,sakara mara wayo" maganar ta girmi kunnenta don bai taba gwada fadin hakan ba


"Um um daddynsu,ya isa don Allah" ruqayya ta fadi qasa qasa tana tausarsa saboda ta hangi fushin da ya fara tasiri a idanunsa


"Ki qyaleni na fadi mata,naji ta fara sako batun hajiya ne,ta dauka yanzun daa ne da zan dauki iskancinta akan uwata,wanda kikayi a baya ma na kasa tsawatar miki istigfari nakeyi har yanzu"  can qasan zuciyar ruqayya cewa kawai tayi uhmmmm. Zuwan Zainab gidan tana amarya ba ita ba,hatta hajiyan ta shuka mata iskanci kala kala,ba zaka taba zaton akwai wata alaqa ta jini tsakaninta da hajiyan ba,a lokacin bai cewa komai,shi yasa ruqayyan tayi qoqari ta kama mutunci sosai a lokacin (kira ga uwayen gidaje,ina qara gaya muku sau tari ku kike siyawa kanku daraja da mutunci a farkon zuwan abokan zamanku,kuma kuke basu fuska da qofar rainaku tun farko,ki watsar da ita da me gidan gaba daya ki basu space ki maida kanki busy a lokacin da suke ganiyar cin amarcinsu,hakan shine zaifi zame miki alkhairi akan sanya idanu akan duk wani motsi nasu,ranki zaiyita baci ne kina ganin abubuwan da babu lallai suyi miki dadi,ke kuma babu tabbas din zuciyarki zata iya jurewa).


                 Wannan kame kan shine abinda ya jawo har yau duk iya iskancin Zainab da ganin ruqayyan ta tare mata gaba ta tare mata baya ba komai take iya tunkararta da shi ba.


"To ai saika dauki mataki yanzu ma bata baci ba" ta fadi a zafafe,saidai gama fadin keda wuya wani zazzafan amai ya biyo baya.


             Dan janye jiki ruqayya tayi cikin mamaki,zubewar da taga zainab din tayi a wajen ya sanyata miqewa tana fadin


"Subhanallahi lafiya?" Qarasowa tayi dab da ita tana qoqarin riqota,saidai wani yanayi dake tashi a jikinta ya sanyata matsawa gefe ta tsugunna tana mata sannu.


              Mugun galabaita ta fara yi,ita da saleem din suna tsaye a kanta. Wannan abun ya sake bawa zainab dama ta sake ragwabewa sosai ta narke kamar matacciya


"Dauko mata hijabi mu tafi asibiti" tsam ta miqe tana juya yadda Zainab din ta sake gaba daga yin amai?. Eh tayi wani irin amai mai yawa a gurin amma baici ace ta sassake haka ba.


              Sau biyu tana sallama yaran basuji ba saboda sun qure qarar tv sunata kuma damben fada akan abun wasa,harda haneefa da ya kamata ace a shekarunta ba wannan abun yakeyi ba,ita ke kula ma da khaleel.


               Sanda suka farga da kallo suka bita baki sake saboda ba zasu iya cewa ga ranar qarshe data tako sashen nasu ba. Tunda ta shiga falon yanayin falon taji sam baiyi mata ba,haka ta dinga takawa cikin tsantsani don ko ina datti ne,bata tunanin jiya ya samu kyakkyawar shara,yau kuwa dama tunda tana sauri biki ya samu tayi imanin inda zata leqa kitchen dinta ko wanke wanke batayi ba.


              Kusan ginin nasu iri daya ne,wannan ya sanya bata sha wahalar gane inda bedroom dinta yake ba


"Karki shigarwa ummanmu daki fa" haneefa ta fada tana kallon ruqayya. Sosai abun ya bawa ruqayya mamaki,ta juyo tana duban yarinyar. Har tasan wani kishiya kada ta shigarwa kishiya daki?, komai ma wai zama zainab takeyi da yaran ta gaya musu?. 


               Hannu ruqayya ta saka ta yafitota tana murmushi


"Zoki nunan kayan ummanki zan dauko mata zani da hijab,asibiti daddynku zai kaita" tsalle tayo ta sauko daga saman kujerar da sun jima da cin ubanta ta nufo ruqayyan ba tare da ta maida hankali ga batun zuwa asibiti ba


"Zakisha wahala,dauko kayan ummanmu akwai wahala,don itama kullum saidai ta gaji ta dauko wanda ta gani ta mayar da sauran" bata cewa yarinyar komai ba tabi bayanta.


              Kusan idan ka ganta cikin dakin Zainab haihuwa tayi,rabonta da bedroom dinta tun haihuwar khalil. Tayi mamaki har fiye da zato na yadda ta zamu dakin nata a hargitse,hatta da shimfidar gadon a harmutse take,harda qasa qasa a kai,panties nata Brazier da cup harda spoon ma. Qasan dakin kuwa baja baja yake da karikice da bazata ma iya tsaiwa tantancesu ba. Dakin ba abinda yakeyi sai wani irin hamami hamami kamar warin dauda cakude da warin hammata. Bata sani ba amma qila tsabar tashi da jiki da hammatar Zainab din keyi da annakiyar da dakin yake da ita ne ya sanya a madadin qamshin turare... Nata turaren ya zama wadannan warika ne gud biyu. Bandaki shima na buso tashi gudunmawar qarni da zarnin ta qoofar bandakin dake a wangale.


                Gaba daya kayane jibge a rataye tun daga murfin sif din zuwa kan qofar bandakin,zannuwanta ne panties da riguna.


                Haneefa ce ta bude sif din hankalin ruqayya nakan wani tsadajjen turarensu data gani yashe a qasa an tattara kwalbar an shareta acan matse matsi mudubi,ta yiwu dazun da tana saurin zata fice ne ya fashe garin ta saka,ita kuma ba zata iya tsaiwa ba ta tattareshi gefe da zummar saita dawo,data dawo din kuma bata da lokacin bi ta kansa sai ranar da Allah yakai tsintsiyar shararta gurin.


              Zubowar kaya kawai ruqayya taji yiiiiiiffffff kamar an saki buhu. Gefe ta matsa da sauri adan tsorace,haneefa ta sheqe da dariya


"Haka ummanmu takeyi kullum idan zata saka kaya,ki zabar mata saiki barsu a gurin saikin dawo,ko natayaki mu mayar" yarinyar ta fada hankalinta kwance cikin nishadi kamar me bada labarin abun arziqi.


                  Tsaf ruqayya ta qarewa kayan kallo,tama kasa tantance meye da meye,don basu da maraba kwashen dilar kayan gwanjo


"Ke da nace kaya aiba wanki za'a kai ba,ba kayan dauda ba wankakku asibiti zataje" baki ta saki tana kallon ruqayya


"Ai sune wadannan,idan aka kawosu daga wanki watsasu mukeyi,idan muka cire kuma indai laundry basket dinmu ya cika sai mu ajjiye ciki idan an tashi kai wanki a kwaso,rannan ma daddy yace duka kayan ciki tsami sukeyi" ta fadi tana toshe hanci cikin son gwada yadda yayin a ranar tana dariya abinta don maganar har yau dariya take bata


"Ya isa,ina hanaki fadin abu ko an tambayeki bare ba'a tambayeki ba,mu kwashe kayan mu mayar" tace da haneefan.


                 Tana tilar kayan tana dauke numfashi da kau da kanta,haka ta dunga diba tana cusasu yadda ta gansu haneefa na tayata. Kafin su gama cikinta ya gama gurbata,da qyar ta iya gano zani da hijabi ta fito dasu a hannunta amma zuciyarta fal qyanqyami.


                A nan ta samesu,ta ajjiyewa zainab din kayan amma sai tayi talau alamun ba zata iya sakawa ba. Saleem dinne ya karba ya fara saka mata. Da ya gama saka matan ya riqeta suka fita farfajiyar gidan Zainab din tana layi kaman zata fadi.


                 Kwanukan abincinta ta fara tattarawa tana daukesu a wajen kafin suma su fita a kanta.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post