Kurman Baƙi Page 12
Health College

Kurman Baƙi Page 12


 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 13



https://www.mkdatasarvices.com.ng



*MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽


*_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA KADAI DON AMFANIN KANSU?_*


*_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_*


*_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA RANGWAME_*


https://www.mkdatasarvices.com.ng



_Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number wayar_


08038258489



*ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾




            Sam ba wanda yama lura da tsaiwarta a gurin,don hidimar gabansu kawai sukeyi. Su alhassan suka fara fitowa sai ta miqa musu iftee tace suyi gaba ta duqa ta dauko musu sauran ledojinsu tunda ita ta bada tata tayi gaba tana cewa


"Sai ka taho" saboda tasan zai fara da shiga sassan zainab ne. Labulen ta saka tana jan qwafa bayan ta gama irga ledojin hannun ruqayyan sannan ya nufo nata sashen,zamewa tayi ta zauna kan kujerar tana jiran shigowarsa ta kuma ga da me ya shigo matan.


              Da sallama ya shigo sashen,khalil dake tsaye har yanzu saman kujerar ya diro ya nufoshi da gudu yana kiran 


"Daddy" daukansa yayi ya daga sama yana dubansa


"Ya rigarka yake a jiqe?" Ya tambayeshi yana tattaba gaban rigar


"Lemo nasha"


"Oya jeka cireta ka canza wata" ya fada yana ajjiyeshi.


"Baki iya sannu da zuwa ba?" Ya fada yana saka hannunsa daya a aljihun rigarsa yana duban haneefa dake tattaba ledar da ya shigo da ita. Magana yayi me harshen damo,ya aika saqonne har zuwa ga Zainab wadda banda sallamar da ta amsa da qyar bata ko sake kallonsa ba 


"Au sannu da zuwa daddy"


"Yauwa,daga yau kada ki bari na sake tuna miki,be a good girl hanee"


"To daddy" miqa musu ledar hannun nasa kawai yayi,suka karba suka kici kicin budewa. Kasa daurewa tayi don ta tabbatar suka bude din saisun cinye abinda ke ciki,tadan ciza lebanta tana cewa


"Kuka bude sai kunci ubanku,kun koma kamar agololin gida,sai a wuce da leda biyu uku ku sai a baku daya" sosai ransa ya baci,don zagin baiyi kama da yaran takewa shi ba


"Ku dauka ka tafi dakinku dashi naku ne" ya fada yana kallon yaran. Da farincikinsu suka miqe suka cilla dakin nasu kuwa. Maida dubansa yayi kanta idanunsa suna nuna bacin ran dake kan fuskarsa


"Daga yau ya zama rana ta qarshe da zaki zagarmin yara a gabana,duk randa kuma kika kuskura kika sake aikata hakan to ki kuka da kanki" yayi maganar yana nunata da yatsa.


"A'ah wallah,na me?,bayan kun gama cin amanar tawa ka zagaye kaje ka daukota saboda ita bada qafafun yin tuqi ta dawo gida shine ni kuma yanzu zaka sauke a kaina?,bashi yiwuwa" ta fada tana miqewa,saidai kuma dole ta duqa saboda wani azababben gudawa da taji yana taruwa waje daya a cikinta.


"Anci amanar taki,kema idan kin iya kici tamu" ya bata amsar a zafafe yana motsawa don barin gurin. Idanunta dake rufe ta bude ta bishi da kallo,wani abu ya tsaya mata a maqoshi,bataso maganar nan ta tsaya iya haka saboda takai maqura da abinda akeyi mata,rashin adalcinsa a kanta ya fara isarta,yanzun inda ranar girkinta ne yaje yiwa ruqayyan sallama yana iya kwashe minti talatin bai fito ba,amma ita gashinan ko zama baikai ga yi ba


"Wanda ya cuci wani Allah ya saka masa"


"Ameen" ya fadi ba tare da ya waiwayo ba,saidai cikin ransa yanajin tabbas zaiyi maganin wannan rashin mutuncin nata.


              Ransa a bace ya koma sassan ruqayyan,taga hakan saman fuskarsa amma sai ta share bata tambayeshi ba,ta shiga hidimar shirya masa abinci da kunna room Heather saboda dakin yadan qara yin dumi don yau din akwai alamun sanyi sanyi. Tasan koma meye tsakaninsa da matarsa ne,ita kuma wannan ba huruminta bane.


             Pyjama dinsa ta cire masa ta dawo gefansa ta ajjiye masa tana kallon fuskarsa,har cikin ranta tana jin ba dadi to amma meye nata a ciki?,duk wanda ya debo da zafi bakinsa ai.


              Daga kai yayi suka hada ido sai tayi saurin dauke nata idanun tana warware kayan data dauko. A hankali ya kama hannunta ya riqe yana kallon kayan. Tare ya siyosu ya ajjiye wasu a bedroom dinsa na sashen zainab,amma tuni wadanda ke sashen zainab din suka zama tarihi,don daga qarshe da kansa ya bayar dasu sakamakon komawar da sukayi basu da maraba da tsumma


"Anya ko da gaske kike kin yafemin?"


"Da akayi me fa?" Ta fadu tana dubansa fuskarta na nuna rashin fahimta


"Abubuwa marasa dadi keta faruwa,tunda na auro Zainab na kasa jin dadin zama da ita ko na kwana daya ne,wasu abubuwan ban taba zaton mace tana iya aikatawa miji ba sai zuwanta gidan nan,idan kace zaka kai qorafi saika zama........"


"Saika zama qaramin mutum,haka zaka ci gaba da haqurin" ta fada tana miqewa tsaye daga saman gadon ba tare data kalli qwayar idanunsa ba


"Zainab kwata kwata......."


"Please mana habeeb......" Ta katsi numfashinsa tana fadi qwayar idanunta carr cikin tashi


"Banason naji please,inaso wannan daren,banason abinda zai batashi" kansa ya girgiza yana kallonta


"Kinga bacin rai da damuwa akan fuskata amma baki damu kin tambaya ba,da abun yayimun yawa kuma nake gaya miki da kaina nan ma ruqayya ba zaki fahimceni ba?,ba zaki bani shawaran da zata zamemin fitila akan matsalata ba?" Wani murmushi me ciwo ne ya qwace mata,ta kauda kanta gefe tana tuna wasu abubuwa masu ciwo da suka wuce. Tana mamakin halin maza qwarai,mace zaki iya cinye daci da zugin radadin da namiji ya banka miki,amma shi bai iya dauke radadi da ciwo.

Yana samunsa yanzun zai ɓara kowa sai yaji. 


               Ta kusa minti biyu a haka ba wansa yace da dan uwansa wani abu,shi ya kafeta da ido ita kuma ta kawar da kanta tana kallon wani gurin na daban tare da qoqarin hadiye abinda takeji sannan ta waiwayo tana dubansa


"Ka tashi ka canza kaya muje kaci abincinka"


"Bazanci ba,ba wannan maganar akeyi ba"


"Maganar da akeyi din ai bata da muhalli a gurina,ba hurumina bane"


"Eh ba huruminki bane amma na sakaki a ciki". Ta lura da gasken gaske so yake ya tsomata a ciki,yanaso ya sanyata yin abinda taketa dannewa,sai ta saki kayan hannunta zatayi gaba tabar dakin amma sai ya damqi hannunta ya dawo za ita ya zaunar


"Amma baicikin aikin mace ta sanyaya zuciyar mijinta?,shima bada shawarar laifi ne?"


"Wacce shawara kake buqata?,sanda kake da buqatar shawarar ka nemeta ne?,ko ka manta sanda nazo da shawarar?,ka tuna abinda ka gayamin?,na cika kishi,duk zancan magauta ne kai baka da haufi akan yarinyar ka manta?,kana da tabbaci da yaqini a kanta so yanzun bai kamata kayi loosing wannan courage din ba,ba hurumina bane sulhuntaku ko na shiga maganarku ba,ko shawara ma ba dole bane na baka indai akan abinda ya shafi iyalinka ne,na roqeka ka fiddani daga sha'aninku" ta fada tana hade hannuwanta guri guda,qwalla na cika mata idanu,don tabbas ya taba Mata tsohon mikinta. Kasa cewa komai yayi,wannan ya bata qwarin gwiwar miqewa a nutse ta fita daga dakin.


               

Tana jin mahaukacin kishinsa cikin kowacce gaba da sashe na jikinta amma ya gaza gane hakan,komai tana yinsa bisa qarfafawa kai gwiwa da kuma jagorancin addu'ar da kullum takeyi dare da rana akan Allah ya bata ikon mallakar zuciyarta,kada Allah ya bata ikon cutar da zainab ko kasa yiwa saleem biyayya,tanayi maamanta tana tayata,ta tabbatar wannan shine ginshiqi na farko da yayi mata katanga daga bin son zuciyarta.


             Binta yayi da kallo jikinsa a sanyaye har ta gama ficewa ba tare da ya iya dakatar da ita ba. Iska me zafi ya furzar daga hunhunsa yana maida bayansa jikin gadon ya kwantar yana tariyo abubuwan da suka shude shekarun baya. A lokacin da idanunsa suka rufe yaji duk duniya ba abinda yakeso ya gani illa d'an kansa. A baya tunaninsa sassauqa ne akan wannan,amma tasirin kalaman mahaifiya da na qanne yasa sannu a hankali ya jarabtu dason qara aure don ya samu haihuwa kamar kowanne cikakken namiji yadda ake gaya masa. Mahaifiyarsa tayi masa nuni da Zainab cikin 'yammatan danginsa. Farar fatarta da yawan iyayinta yasa yaji kaman zata dace da yanayinsa.


             Duk macen da aka yiwa kishiya tasan zafi da

rudanin da zuciya ke fuskanta a wannan lokacin, ruqayyan ma taji haka,duk da nata za'a iya cewa ragaggge ne bayan tasan wacece Zainab din. Taso qwarai ta kwatanta masa amma a sannan suna ganiyar buga soyayyar da babu kama hannun yaro. 


              Ko kadan babu nufin hanashi qara aure a tattare da ita,duk da inda ace zai fasa zataji dadin hakan,to amma taso ya bata dama wajen zabowa kansa da ita abokiyar zama ta gari,da hakan zata kasance da farincikinta ya qaru.


"Kin cika zafin kishi ne kawai,amma duk wanda yace ga illar zee to saidai munafuki ko wanda bai mata farin sani ba,ita din bakiga yadda take maganarki ba,kuma an gayamin girmamaki take duk sanda kuka hadu a wani taro,to me ya rage me kikeso indai ba masifa da fitina ba?" Ya fada a sannan hannunsa riqe da wayarsa yana replying watsapp massages na zainab din


"Ki cirewa kanki fitina da damuwa don Allah,ta kusa shigowa komai yazo qarshe ma" maganarsa ta qarshe tafi kowacce bata mata ranta,don zatayi gyara don ta sama masa nutsuwa da farinciki ga duk auren da zai qaro sai abun ya juye kanta?. Ita ta sani

bawai alfahari ba,bata tsoron karawa da kowacce macce indai ba daga aljanna aka sauko da ita ba,to amma me?,saleem din ya sota matuqar soyayyar da ta tabbatar zai wahala wata diya mace ta samu kwatankwacinta. Banda maganar aure data taso yanzu bai taba wani abu don ya cutar da ita ko ya cusguna mata ba,wannan yasa take masa laluben macen da zai samu nutsuwa da ita,wadda itama ba zata daga mata hankali kota rabata da nata farincikin ba. To amma saboda idanunsa sun rufe,ya kuma yi nisan da bayajin kira bai hango abinda ta hango masa din ba ita.


              Bayan gama tuna dimbin laifuka da abubuwan da yayi mata na rashin kyautawa bai zaci dawowarta dakin ba a sannan.

Sai kawai ya tsinci tattausar muryarta daga bakin qofa tana fadin


"Daddy abincinka har ya gaji da jiranka,muma kaga dare yanayi kai muke jira" Da ya daga kai ya kalleta murmushi ne saman fuskarta kaman ba itace ta fita da fushi ba. Daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita kenan,kuma guda cikin failure na zainab.


             Ita muddin ya bata mata rai sai ta bata masa,muddin tayi fushi ko ranta ya baci saita nuna ta kuma furta maka


"Ko sai nazo na qarasa shiryaka ranka ya dade?" Ta fada tana rungume hannunta a qirji idanunta a kansa


"Me yasa na damu na kasa juriya da qaddara,na shiga neman aure ido rufe?,don kawai ruqayya bata haihu ba?,yanzu ita ke da

twins har da tsarabar diya mace guda,lallai rashin haquri da juriya na gaggauto mana da wasu abubuwa da lokacin riskarsu zuwa garemu.ma baiyi ba" yana gama wannan tunanin tana isowa,kaman jiranta yakeyi yasa hannu ya fusgota zuwa jikinsa,wanann sassanyan qamshin nata yayi ma hancinsa kyakkyawan maraba


"Kiyi haquri da bata miki rai da nayi"


"Nasan bakayi don kana sani ba,kayine saboda relief kakeson samu a sannan daga abinda kakeji,kayi haquri nima, wani yanayi ne da bana iya controlling kaina"


"Laifi nane,amma bazan sake ba in sha Allah,zan fuskanci consequences din ni kadai"


"Ya wuce fa,tashi ka shirya,yara har sunci nasu sun wuce". Ita ta taimaka masa ya shirya din,duk bayan sakanni sai

ya jawota ya shaqi qamshinta. Har fargaba yakeyi daren qarshe a ranakun girkinta su fita,don gobe warhaka yasan makomarsa. 


              K'arin abun mamakin koda da kudinsa ya siya turaren yace a saka masa iya dakinsa idan ma ita bata da buqata to fa bazai samu hakan ba,ya rasa dalili kamar me aljannun da suke gaba da turare.


                Da suka zauna alhassan ta aika kiran Zainab din


"Jeka kira ummanku,kace tazo muyi dinner" amsa mata yaron yayi ya juya ya fice,ita kuma ta maida hankali wajen fara serving saleem. Tana zuba masan suna hira qasa qasa,yana bin hannuwanta dake jujjuyawa wajen zuba masa abincin da kallo saboda jan lallen da tasha tun shekaran jiya,an mata ratsin baqi a farcenta. Sau da yawa akan ruqayya ne baya yarda da cewar lalle baya kyau a hannun baqaqen mata,bai sani ba ko don yakan manta da kalar lalle idan ba hannunta ba?,don idan kaga Zainab din da lalle to kan tabbatar lallai akwai biki a dangi.


*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post