Jikar Iya Page 17-18 Complete

Jikar Iya Page 17-18 Complete

 

Hausa Novels Document

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️

           08161316781

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Bismillahi ramanin rahim

Pages1️⃣7️⃣🆒1️⃣8️⃣

____Yanzu wannan abun kunya dame ya yi kama, wai uniform ne ya jikinku amma ku ke jin tsoro, Corporal Idi ka bani kunya wlh, yanzu a ce ka kasa ƙarya wannan tsohuwar ita da jikarta sai kai zasu yiwa haka, wlh ka fata wayon ka, ni tsabar kunyan abun nan da nake gani kana ta famar susa bazan iya kwana a gida ba, dole sai na zauna na koyamusu hankali darandare, inason yau kowa yaje gida ya huta ni zan kwana a station ɗinnan" cewar Ispecter Muhsin ya yi maganar yana fitar da iska daga bakinsa.

Su kam duk murna su ka yi da abun da ya faɗa, dan sunsan hatsabibancin wannan tsohuwar, shi kuma Ispecter Muhsin ba gani ya yi ba, sannan kuma ko kallon su baiyi ba amma yake cika baki, dan haka suke murna da ya umarcesu su tafi hakan ya musu dadi.

Iya ce da jikarta suke famar jin yinwa kasancewar dare ya yi, amma kuma sunji alamar kamar station din kamar babu kowa.

"Iya ki buɗemu mu tafi gida yinwa nake ji," cewar Indo tana maganar cikin shagwaɓa da alamar sankarta.

"Eh Indo yanzu nake shirin yin haka" cewar Iya shurun da tayi ganin andoso sune.


" Kai malam da wani katon kanka kamar wani dirom, da uwarka ce zaka barta bata ci abinci ba har warhaka, sannan kuma ga uban sauro da yake damun mu" cewar Iya tayi maganar tana tsire wanda yazo ya yatsaya musu akai.


" Ke dattijuwa ki kiyayeni, ki rike girmanki ko kuma yanzu nayi maganinki keda wannan mai kama da aljana, in baki daina tsireni da idanu ba sai na fasa idon nan" abun da ya faɗa kenan yana kallon Indo da take famar kallonsa, dan daman ita Indo ta iya tsire mutum da ido ga idon nata maa sha Allah."Au kai kuma tanan ka bullo" Iya tayi maganar tana rike da haɓa.


" Yau zanyi maganinku wannan tsohuwar keda wannan dattijuwar" ya yi maganar yana musu nuni da hannu .Ƙarnuƙar ya ƙwaso ya haɗa su da Iya da Indo a cikin gadirom ɗin, inda Iya da Indo kowa kuka yake yana ihu, inda Iya take faɗin "ɗana kayi hakuri ka cire mana wannan abun, wlh mun tuba ba za mu ƙara yi ba, anyi na farƙo anyi na ƙarshe duk wanda muka ɓata wa ma a garin nan zamu je mu nemi gafararsa, wanda kuma ya rigamu gidan gaskiya sai dai muyi addu'ar Allah ya kyauta, dan walaƙirin nan ba ƙanin ubana bane," ta ƙarashe maganar tana sharfan kuka, jin surutunta ya yi yawa sosai yasa ƙarnukan nan guda biyu su ka yi kanta suna mata haushi, nan ta fara ihu ta na faɗin "Wayyo Allahna inda ƙare yake annabi bayanan, inda ƙare yake annabi bayanan," abun da Iya take ta famar maimaitawa kenan, cikin ikon Allah suka juya su ka yi kan Indo.


"Wayyo nifa marainiya ce, ni kaɗai Uwata da Ubana suka haifa inkuka cinyeni yau ina zansa kaina, kuyi mun gafara gwara ita Iya taga jiya taga yau..." kan ta ƙarasa rufe bakinta Iya ta amsa da faɗin "au kaji ja'irar Yarinya kuma ina sa ran ganin gobe in anyi duniya dan Manzon Allah S.A.W, aini bansan bakya ƙaunata ba sai yau" a faɗar Iya Indo kuwa sai famar kuka take bata ma san abun da take furtawa bama balle na Iya.


Iya ce tayi namijin koƙari ta buɗe kofar da mukullin wajenta, inda tayi sanɗa ta fita, jan kofar tayi da hannunta ta damke tare da faɗin "to Indo nidai da bakyason naga gobe gashinan Allah ya fitar dani, yanzu ya za ki yi," ta ƙarashe maganar tana sakin dariyar mugunta.


Indo ganin Iya a waje yasa ta ƙara sautin kukanta tana faɗin " wayyo Allahna Babana da Mamana yau gani Indo zuwa gareku, amanar da ku ka bawa Iya yau Iya taci amana, ta gommace ni na mutu akan ita," abun da Indo take faɗa kenan.Jin abun da Indo ta faɗa ne ya sanyayawa Iya jikinta inda tayi kokarin buɗewa Indo kofar, su kuwa ƙarnukan kan Indo su ka yi da gudu kamar za su cizeta, da gudu ta ɗiba tayi kofar ganin ɗayan ya kusan kama faɗarta yasata faɗin "Assalamu alaikum mutanen lahira Indo ce jikar Iya tazo muku..." kan ta kai ga rufe bakinta sai gata ta samu ta fita, danne kofar su ka yi ita da Iya tare da sauke ajiyar zuciya.Ganin junansu su ka yi tare da fashe wa da dariyar abun da ya faru, da kuma kowa yadda ya yi, kamar basu bane suka fara kamar faɗa a ciki.
Yana daga zaune sai ji ya yi an rufe kofar office din, taso wa ya yi tare da rike kofar yana girgizawa, tare da faɗin " wani dan iskan ne anan...." kan ya kai ga rufe bakinsa sai yaji ancullo igiya a wuyarsa, yana koƙarin cire wa daga wuyar tasa sai yaji anja ɗayan ya zama kamar irin akuyar nan ko na ce rago, yana juya wa sai yaga Jikar Iya akan taga ta kafa masa ido babu alamar zata fibta ko kuma za ta ji tsoro.Shima ido ya zare mata tare da faɗin " ke kinsan ni waye kuwa, irinku tantirai dama wanda suka fiki duk naja dasu, danni ba yakin da ba'aje dani ba, nine na kawo ƙarshen yan ta'adda dake Katsina, Zamfara, da kuma yan boko haram dake sambisa na ƙasar Borno, dan haka ki cire mun wannan abun inba haka ba ba za ki ji dadi ba" ya ƙarashe maganar yana mai mata gargaɗi.Dariya ta sake wanda ba za ka ce ita tayi ba, kallon sa ta ƙara yi a karo na biyu tare da faɗin " yau zamu tabbatar da jarumtar da kayi a yaƙin da ka ambata, sannan bamu ka haɗa da karnuka ba, ko kashemu za su yi baka da damuwa" 


Kan ta rufe bakinta iya ta bude kofar ta shigo ita kuma tana rike da igiyar a hannunta.


"Na ce mai maita abun da ka ke faɗa tantiri, ka ce kayi maganin tantirai kalan mu harma da wanda suka fimu ko, sannan tsabar rashin imani irin taka baka duba furfurar kaina ba, sannan baka ga maraicin wannan yarinyar ba shine ka haɗamu da karnuka ko" Iya tayi maganar tana zuba masa ƙarƙara a jikinsa, nan ya fara susa babu kakkautawa, yana yi yana cire kayan jikinsa sai da ya cire komai saura gajen wando abun da Iya taso kenan yana yin haka ta samo ruwa mai sanyi daga randar dake station ɗin ta kwara masa, nan abun ya masa taya ga uban sanyi gashi an ƙara masa da ruwa, sannan kuma ga uwa uba babu kaya a jikinsa, nan ya fara rawan sanyi launin idanunsa ya canza ya koma launin ja, kuka yake so ya yi amma ya kasa, sannan yana son ya yi magana shima nan ya kasa saboda yadda akorarsa suke haɗuwa na sama da kasa suka fitar da wata sauti na alamar sanyi yake ji, nan ya kame jikinsa waje guda yana haɗa hannayensa yana jujuyar dakai alamar suyi hakuri.Ƴar Iya ce labari yazo mata yadda aka tafi da Iya da Indo police station, nan hankalinta ya tashi tare da tausayin uwar tata yadda wannan yarinyar take wahalar da ita, waya tayi ta kira ɗan uwanta Alhaji Abubakar dake cikin garin Kano waya ta sanar masa.


Amma bata sheda masa cewa harda Iya ba dan kar hankalinsa ya tashi, kuma gashi dare ya yi sosai, sallama suka yi akan gobe zai shigo garin Dan batta.Shedawa Hajiya Kamala ya yi cewar gobe zai tafi ƙauye abu ne na ujila, taɓe baki ta yi alamar ita ina ruwanta, da haka ya wuce part nasa ya kwanta akan in sha Allah gobe da safe zai tafi."Eh sai mun haɗu da safe, dan Malam ya ce mu ƙaraso da sassafe akwai abun da yake son faɗa mana" cewar Shatti take faɗawa Hajiya Kamala, hira suka ɗan taɓa abun su kafin su ka yi sallama akan sai gobe.Isopecter ne yake famar ihu tare da magiya akan Iya tayi hakuri, amma Iya bata kulasa ba sai kara daure masa hannu Indo take yi inda Iya ta ɗaure kafa, sannan kuma ga wuya da igiya an haɗa shi da taga, fita Iya tayi bata wani dade ba sai gata da reza a hannunta, ganin Iya na kokarin zame masa wando ne yasa Indo ta fita daga office din dan bason ganin tsaraicin mutum, ita a faɗarta ma ko wanka in za ta yi indonta a rufe take yi, ihu yake babu kakkautawa yana neman taimako amma babu mai jiyosa, kuka yake tare da mata magiya akan ta dakata.


" Dan Girman Allah kiyi hakuri dan Allah ki dubu darajar Iyayenki, in kina yiwa manzon Allah S.A.W ki kyaleni" jin ya ambaci sunan manzon Allah S.A.W  yasa iya karasa wa da salati tare da faɗin kaci albarkacin manzon Allah na fasa maka kaciya zan maka balli-balli, nan Iya ta cire taƙardan rezan ta ya dashi gefe, nan ta shiga rike sandar girmansa yana ihu tana sassagasawa sai da ta zagaye da zagar reza tun yana ihu har ya daina motsi a wajen, jin shuru ne Iya ta ce " wayyo Indo shigo daga ciki kamar ya mutu fa?, ki shigo ki gani" tayi maganar tana kuka.Shigowa tayi da gudu tare da yin gefe tana ƙara waro ido tare da ƙara ja da baya tana faɗin " Iya kin kasheshi, mun shiga uku wlh Iya ya mutu fa" ita ma Iya dafa girjinta tayi tana faɗin "Indo ina zamu je yau ko gudu wa za mu yi, mu koma Kano garin ƴaƴana" tayi maganar tana sharsharfar kuka."Ai kuwa Iya amma abun da za mu yi kenan" tashi su ka yi, cikin sauri Iya ta ƙarasa gida ta ɗauki kuɗinta, tare da kunshin kayansu kala bibiyu, tana ɗauka tazo ta samu Indo a inda ta barta, garin dare ne zai Iya kaiwa karfe biyun dare amma ba alamar tsoro a tattare da su, tafiya suke babu alamar zasu samu abun hawa, sai da suka kai Wudin lokacin ana kokarin ƙiran sallah asuba, amma tsabar sunsan abun da suka aikata babu alamar gajiya a tattare dasu.


*GARI YA WAYE*


"Yauwa bincike ya nuna mana cewa wannan yarinyar ta yi babban shiri akansa, kuma da wannan ne yasa ta auresa amma bada hankalinsa ta auresa ba, sai da ta mallakesa sannan aka ɗaura aurennan, yanzu abun yi shine sai dai ayi masa kiranne, akan ya dawo gida kuma ayi masa abun da bazai taɓa komawa can ɗin ba," abun da Malam ya faɗawa Hajiya Kamala da Shatti kenan.


Nan ta fara tunani akan wannan al amarin kuma wannan ɗan nata tilo shine yake kula da campanynsu nacan gaba ɗaya, yanzu in ya dawo ya za'ayi da wannan al'amarin.


Ba ta da wani mafuta da ya wuce ace ya dawo ɗin, kuma ta gommace ya dawo akan yaci gaba da zama da wannan matsiyaciyar, jinin talakawa jinin tsiya gata kamar ka fureta tsabar yinwa, in banda asiri ma babu abun da zai sa Zohaib ya auri wannan yarinyar." Malam na amince ayi masa ƙiranne, ya dawo sannan kuma a haɗa da abun da za'a masa ya saketa , dan Allah Malam inason amun wannan aikin ko nawa ne zan iya biya" abun da Kamala ta faɗa kenan.


Sunyi sallama da Malam akan yau za'a fara aiki, sannan kuma za'ayi masa abun da zai saketa cikin sauki.A ɓangaren Alhaji Abubakar kuma ya yi nisa dan ya kusan zuwa garin ɗan batta, dan tunda ya tashi da safe bai haɗu da Hajiya Kamala ba, dan asubanci tayi taje gidan Shatti suka tafi wajen Malam, dan haka shima ya shirya ya tafi Ɗan batta.Garin Ɗan batta an wayi gari da rashin ganin Iya da Jikarta, kowa na maga akan sunyi kisan kai sun dugu, wasu na addu'ar Allah yasa abun ya tsaya iya haka, kuma daga can suyi can dan babu mai marmarin ganinsu a garin nan sai ƙawayenta.A station sunzo sun tadda Muhsin a Kwance babu alamar numfashi a jikinsa, sannan kuma gashi da sadar girmansa duk jini, abun ne ya basu mamaki da farko sun zata aljanu ne suka masa haka amma rashin ganin su Iya ya tabbatar musu da cewa sune suka aikata haka.


Cikin sauri akayi dashi asibiti dan jin dalilin mutuwar tasa, wasu kuma suka yi gidansu Iya amma basu samu kowa ba a gidan, dan haka suka je suka sanarwa a station ɗin cewar sun dugu fa.Nan Umaru Police ya bada shawarar a je a ɗauki ƴarta in Iya ta kawo kanta sai a saki ƴar, haka kuwa akayi har Ƴar Iya tana zaune da mijinta da yaranta akayi musu sallama tare da tafiya da ita, dan ko ma mijin nata ba'ayiwa bayani ba, sai da su kaje station ɗin ake sanar dashi cewar Mahaifiyarta ce tayi kisan kai ta gudu........


*SAURA PAGE ƊAYA FREE PAGES*
Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post