Kurman Baƙi Page 20 by Huguma


Health College

Kurman Baƙi Page 20 by Huguma

 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 20

_Wai Allah🤦🏽‍♀️🤦🏽‍♀️,da qyar na qwaci kaina nayi wannan,ayimin afuwa don Allah,zainabu na gaisuwa ga jama'arta😂😂_

            Gaba daya sai ta koma kamar mutum mutumi,ta dinga binsu da idanu harta gama aman,jimmy da tafi kusa da ita ta bata ruwa ta kuskure bakinta,saleem ya karba ledar ya qulle ya yar.

"Danqari!!,ana dara......." Zainab ta fada cikin zuciyarta wadda keyi mata suya

"Inaga kamar akwai likita ko?,muje ya dubaki karmu wuce gida abun yafi haka" saleem ya fada cikin kulawa ganin yadda jikinta ya saki.


"Allah ya sawwaqe" jimmy ta fada tana komawa gadonta


"Ameen na gode" ruqayyan ta amsa mata tana fita a dakin. Batasan ya suka qare ba,ya kusa mintuna uku sannan ya fito suka wuce karban file.


"Kinga irin zallar rashin adalcin da ake gwadamin ko?" Zainab da idanunta suka cika da hawaye tace da jimmy


"Ummmm,na gani" ta amsa mata tana bata haushi saboda yadda ta karanceta,sam bata iya mu'amala da miji ba,maganganun data gaggasawa saleem kafin ya fita ta tabbatar inda wani namijin ne me saurin daukan mataki daga nan saidai tayi gidansu,kai koda a dadiro ko dandi ne tabbas ba abinda zahana ya lakada mata na jaki har dai an qwaceta. Amma maganganun da ya dasa mata a rai da me hankali ce ita ya kamata taji zafinsu ne ta kuma dauki haske.


"Banda aikin asiri.....kazo dubaninamma idanunka ya rufe ba tani kake ba?,don kawai tayi amai?"


"Ai aman kawai ne?,bashi kikeyi ba ke sanda aka kawoki asibitin nan?"


"Eh amma ni harda gudawa"


"Baiwar Allah ai ciwo ciwo ne ko?,sannan nifa a nan banga aikin asiri ba,kawai dai ta fiki sanin kanta ne da alama" kamar cakewar mashi haka maganganun jimmy suka tsaye mata a rai,ta zuba mata fusatattun idanunta tana kallonta. Banda tana tsoron kada ta yiwa kanta sanadin dinkin da za'a yi mata wallahi da sai ta gaggasa mata maganganu


"Ban gane nufinki ba"


"Maganata a bayyane take ai,baki iya kula da mijin ba,baki da lafazi baki da mu'amala,sannan ki kalli jikinki da nata daya ne?" Jimmy ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunta. Dif sukayi su duka, abinda ya kawo katsewar maganar tasu shigowar hajiyayye, jimmy ta dauke kai taci gaba da harkokinta.


               Bayan duka tambayoyi sai aka bata gwajin PT don alamu sun nuna hakan. Gwajin kuwa ya fito da sakamakon da ake zargi na juna biyu. A take akayi mata scanning don duba baby. Scanning din ko ya bada sakamako me ban mamaki. 


"Cikinki ai yayi wata biyu harda rabi ma,kuma dukkan wasu alamu sun nuna twince ne,matso ku gani" likitan ya fada yana zooming scanning din.


               Wani mugun sanyi jikin saleem din yayi,ya dinga jin tsoron Allah yana ratsashi,anya ruqayyan ba wani matsayi gareta wajen Allah ba da yakeson nuna masa ishara?. Duk wani gwaji anyi ance ruqayyan sam bata taba haihuwa,amma cikin hikimar buwayi gagara misali sai gashi yanata nuna ayoyinsa. 


            Ita kanta a karan kanta sai ta dinga jin girman Allah da girman al'amarinsa yana sake shigarta,ta dinga tasbihi a gareshi tana jin zuciyarta tana tsinkewa


"Ki yafemin don girman Allah,saboda bansan me ubangiji yake nufi da hakan ba" saleem ya fada yana tsugunnawa a gabanta harda hade hannayensa biyu


"Na yafe maka fa,na yafe maka tuni,komai da ka gani muqaddarine daga Allah" ta amsa masa tana jin nauyin duqa matan da yayi.


                Kafin su dawo hajiyayye tayi parking kayansu gaba daya saboda anyi sallama,wanda inda ta biyewa zainab motar haya zasu tara su wuce gida ba tare da sun jirashi ba.


              Tanata kumbura tana wani babbankewa ta wuce gaban mota. Itakam ruqayya ma dariya ta bata,yanzun ita kuma me ya rage mata?,Allah ya mata komai na rayuwa da mace keda burin samun bakin gwargwado,saidai ci gaba da neman qari. A gidan duniya rashin zuriya ne damuwarta,sai gashi Allah ya wanke mata hakan y bata ya bata ya sake bata wasu.


             Koda suka wuce gida bangarenta ta wuce kai tsaye abinta saboda sam batajin qwarin jikinta,gaba daya tunda tayi aman kamar laulayin aka zuba mata,zainab kuwa suka wuce da hajiyayye nata sashen,wadda ta matsa ta biyota din,tunda daima tasan nan da dan kwanaki saleem din zai wuce umra shi da hajiya. Tace dai iya yau zata zauna din,idan ya tafin ta dawo.


             Tunda ta zube a kujerar falon nata take saqawa take kwancewa,gaba daya komai yana neman qwace mata,wannan cikin na jikin ruqayya ya zame mata qadangaren bakin tulu,ya akayi har ruqayya ta rigata samun cikin ita tana zauna?,bayan ta shigo ne don ta haihu?,don ta cika gida da 'ya'ya ta yadda gida zai zama nata sai yadda tace?.


             Duk yadda hajiyayye takai ga aiki sai data sare,da farko ta dauka lalurarta yasa sashen nata yake kaca kaca haka,saita zage ta fara gyarawa. Saidai sai data fara gyaran ta fahimci lallai shayi ruwa ne,don kuwa tsohuwa kuma tsumammiyar dauda ce danqare a sashen. 


             Iya dakinta da kitchen ta gyara ta dawo ta zauna tana maida numfashi,ta dubi Zainab dake a jabe


"Gaskiya magana ta Allah muddin ba zaki gyara wannan annamimiyar qazantartaki ba to kin shiga uku wallahi,aiki tun kana na marmari har ya koma maka na jaraba?,yanzu don manzan Allah uban panties da kika tara a bandakinki cikin bathtub na meye?, harda me jini a jiki fa?"


"Don Allah kada ki qaramin tension akan wanda nake ciki,haba mana,ki barni naji da abinda yake damuna" 


"Kiji da abinda yake damunki nima zanji da nawa,don wallahi gida zan wuce,kuma ko ya tafi indai kinsan baki kwashe kayan qazantarki kafin nazo ba kada ki kirani"


"Haba dan hajiyayye zo mana" zainab din ta fada tana sasaautowa,don tasan ba wanda tafiyarsu zatazo daya da ita sai hajiyayyen


"Kiyi haquri raina ne a bace don Allah"


"Sakeni" ta fada tana zare hannunta ta koma kitchen din tana qunqunin mita


"Dadina dake shegiyar mita wallahi" zainab din ta sake fada tana jan tsaki hadi da hararar inda hajiyayye ta wuce,saita gyara zamanta tana ci gaba da qulla wadda take ganin zata fishsheta.


              Tunda ta zauna wajen ta gaza motsawa,gaba daya komai ji take ya dagule mata. Ba irin tunanin da bata saqa ba akan cikin ruqayya,har addu'a take cikin ranta


"Ya Allah kasa zuwa gobe da safe ta hadu da mummunan tsautsayin da zai kawo sanadin zubewar cikin". Duk zaman da tayi a wajen ta rasa wanne zata kama?. Dagewa zatayi tayi ciki?,ko ta bawa banza ajiyar saleem din ta dage tayi ciki?,idan ta haihu sai a dinketa gaba daya?.


             Tafi gasgata wannan shawarar kuma tafi yarda da ita,don haka dab da magariba ta miqe daga wajen data jabe ba azahar ba la'asar,duk da yadda hajiyayye keta fama da ita ta miqe din,ta wuce bedroom dinta ta wawwatsa ruwa don sauri takeyi kafin ayi kiran sallah ya zamana ta fito kafin salim din ya shigo gurinta.


              A gurguje ta biya bashin sallarta,sannan ta bude locker dinta tayi hadin magunguna,tana ji a ranta zata sake dagewa da gyara,don ta shirya samun ciki a wannan dan tsukin,idan so samu ne ma kafin yakai ga wucewa umra.


                Wata rigar shadda ta saka,wadda wuyan da fadin yadanyi mata yawa saboda sanda akayi dinkin tana da ciki tayi qiba sosai,yanzun kuwa ta zazzage ta koma ainihin jikinta. Ko kadan bata fiya damuwa da sauyawar fadin rigar ba saima jinta sakayau da takeyi saboda wankan da take jin tayi,sannan kuma aka dace shaddar wankakkiya ce,duk da babu shaidar guga a jikinta ko na gamin gafara.


            Parlor ta fito ta samu hajiyayye tare da yaran tanata fama dasu wajen gyara musu yanayin cin abincinsu,yau sashen fes yake hakanan abincin yau da hankalinsa,saita hakimce saman kujera tana dakon shigowarsa,a hankali tana jin maganin yana mata aiki,cikin qasan ranta take fatan inama ace a wannan daren ta samu rabo itama?, tabbas a yanzu 'yan biyu sune burinta,kai idan da hali ma guda uku zata roqa,so take ruqayya ta tabbatar da cewa da gaske fa gida ya zama nata,qila hakanne kadai hanya guda daya da zata saka ta saduda.

*Kuyi manage,mu hadu gobe in sha Allah,na gode da haqurin jirana*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post