*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 21
Kusan tunda ya ajjiyesu ya fita yake fama da ciwon kai. A haka dai a daddafe ya zauna a kasuwar saboda lissafin shago sukeyi na qarshen sati,dole kuma akwai buqatar ya zauna din gudun rubuta kuskure.
Sanda ya qaraso yaran suka baibayeshi suna masa sannu da zuwa. Bai taba shigowa gida bannu haka ba komai,duk qanqantar abu sai ya kawo musu tsaraban kasuwa(wannan halayya ce me kyau,tana qara danqon soyayya tsakanin iyaye da 'ya'yansu,iyayenmu na da zaiyi wahala kaga sun shigo gidansu haka,koda ma'aikata bare 'yan kasuwa).
Kai tsaye ya kama hannun iftee suka wuce sashen ruqayya yana tambayarsu mamar tasu
"Daddy tana kwance tun da safe,mommy kamar bata da lafiya" iftee ta fada cikin karyar da muryar
"Batajin dadi amma zata warke very soon in sha Allah" ya fada yana murmushi.
Sanda suka shigo ta gama alwalar sallar magariba dake gabatowa tana sanya hijabinta
"Sarkin tsafta"ya fadi a ransa,duk da batajin dadi amma sashen fes yake kamar kullum. Fuskarta dauke da murmushin nan take dubansa
"Sannu da zuwa" ta fada
"Yauwa,ke za'a yiwa sannu maman wasu twince din in sha Allah" yaran tadan kalla ta gefan ido tana bude baki kadan
"Daddy,bakaso na huta"
"Hutun me?,me ya rage banda ki cikamin gida da yara,inaso na ganni da yara masu yawa Allah ma ya sani,sai gashi Allah ya qaddara zaki zama uwar 'ya'yana"
"Uhmmm,yau kuma ni za'a baiwa wannan matsayin kenan" tayi maganar tana zura hannun hijabinta. Dan kallonta yayi sai ya basar,yasan gori takeson yi masa
"Baki da mantuwa" ya fadi qasa qasa sanda yake zama hannun kujerar dake daura da ita,saita daga kanta,har zatace wani abu kuma sai ta fasa
"Baka da lafiya" ta fada a hankali. Idonsa ya lumshe yana jin qaunarta har qasan ransa,ita daya ke da qarfin maganadisun iya karantar kowanne motsi nasa
"Kaina" ya fada a taqaice
"Subhanallah,daddy bakason shan magani,tsaya kasha magani don Allah" ta fada cikin nuna maqurar damuwa
"Ki barshi idan na huta zan koma normal " kai ta girgiza cikin narkewa
"Kada muyi haka da kai daddy,yanzun idan wanine yace hakan sai kayita fada,mu shikenan ba zamu kula da lafiyarka ba?,waye muke dashi mu da yaranmu sama da kai?" Idanunsa da ya zuba mata ya lumshe gami da sakin murmushi
"Shikenan ranki ya dade" yadda ya kalletan taji kallon har cikin jikinta,idanunsa mada matuqar tasiri har yanzu ga zuciyarta.
Ba jimawa ta dawo da maganin ta balla ta miqa masa hade da gorar ruwa,baikai ga sha ba saiga haneefa Ibrahim yana biye da ita suna raba ido. Koda basuce komai ba tasan turosu akayi suyi CID,don haka tana gama bashi maganin ta juya daki dasu,shi kuma ya waiwaya yana dubansu. Kallon shi kadai yasa suka gane laifinsu,suka koma da baya suna sallama,ya amsa yana miqewa,ruqayya ta qaraso da abun sallah
"Na gode" yace yana yin waje
"Wajibina ne" ta amsa masa tana shimfida abub sallar.
Yana sallama da ita ya fara cin karo,sai cika takeyi tana batsewa hadi da kumbura. Yi yayi kaman bai ganta ba,yayi sallama yana saka kai falon. Hajiyayye ce ta amsa ta miqe tana masa sannu da zuwa,ya amsa yana zama cikin kujera,har zuwa sanda hajiyayye tabar musu gurin.
"Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki kamar wadda aka yiwa dolen faden
"Yauwa,ya jikin?"
"Ka damu ka sani ne?,tunda tunda ka tafi baka ko kirani ba,ka dawo kuma kaje ka zauna a wajen wadda ba girkinta bane" ta fadi cikin hasala. Idanu ya zuba mata kafin ya janyesu
"Wannan qorafin idan da sabo ya kamata bakinki ya gaji da fadinsu,kullum ke kenan cikin qorafi akan na shiga ganinsu?,bayan ita ko sau daya bata taba qorafi akan shigowata wajenki ba?"
"Eh dama mana ai bazatayi ba tunda tasan tana cutata" ta fada tana gyara zamanta da alama da gaske ta shirya tayita zabgo qorafin. Ganin hakan sai ya miqe tsam kawai abinsa yana wucewa bedroom dinsa,cikin ransa yana mamakin yadda yau sashen yake fes. Amma yana shiga dakinsa ya tabbatar ba itace tayi gyaran gidan ba,don bedroom dinsa yadda ya tafi ya barshi ranar data fita a girki haka ya dawo ya sameshi. Da hannu ya tattara tarkacen ya zauna gefan gadon yana jira maganin ya ratsashi. Tsahon wasu mintuna zuwa sanda yaji an fara kiran sallah ya miqe ya wuce toilet ya daura alwala sannan ya fito don wucewa masallaci.
A inda ya barta a nan ya sameta ita da hajiyayye,dama ita din tun da batasan wai tabi miji daki ko ta kebe dashi idan ya dawo daga aiki ko wani guri ba,saidai ya qaraci gararambarsa ya gaji
"Ki shiga ki gyaramin dakin nan" daga kai tayi ta kalli hajiyayye
"Don Allah qarasa ladanki mana 'yar hajiyayye" ta fada tana karyar da murya alamun lallashi. Kai hajiyayye ta daga suka hada ido da saleem saita sunkuyar da kai. Bai dauka haukan Zainab yakai har haka ba da zata aika masa bazawara gyaran dakinsa. Wani kallo ya jefeta da shi ya saka kai kawai ya fita a sashen.
Karfe goma na dare ta shiga bedroom dinsa, idanunta a kanshi yana zaune daga gefan gadonsa yana dan duba waya sama sama,shigowarta sai ya kammala abinda yakeyi din ya ajjiye wayar. Idonsa yadan lumshe saboda yadda yakeji yana dan sara masa,a hakan maganin da ruqayyan ta bashi ya sassauta akan lokacin da ya shigo gidan,sai ya maida bayansa yadan jingina da gadon bayan ya zame kadan ya kwanta a rabin gadon bayansa. Lokaci lokaci yana karantarta sanda take shige da ficenta abunta,ko sau daya bata nuna ta fahimci wani rashin lafiya tattare da shi ba,duk da ko abinci ma kadan yaci don ruqayya yau bata samu zuwa cin abincin ba,to shi dinma bakinsa ba taste shi yasa bai samu ci da yawa ba,kota wannan bangaren a nasa ganin ya kamata ta fahimci akwai abinda yake faruwa amma hakan bai samu ba. Ita kawai sabgar gabanta take,sauyawar miji ta kowacce siga bata daukeshi wani abu da za'a bawa kulawa ba.
Ta nata bangaren Idanunta a kansa jifa jifa tana satar kallonsa,ranta da zuciyarta ba abinda suke raya mata illa sauyawarsa na da nasaba da son bijire ma buqatarta,ita kuma taci alwashin ba zata lamunci a danne mata haqqi ba,ire iren wadan nan abubuwan ma qila suna daya daga cikin sanadin da ya sanya ruqayya ta rigata samun wani cikin.
Gadon ta iso ta zauna daga bayansa,zuwa sannan yaja blanket ya rufe har kafadarsa saboda sanyi sanyi da yakeji na alamun ragowar zazzabin jikinsa bai tafi ba
"Ina da buqata" ta fada sankankan kamar me bada labari. Ya dade da sabawa da wannan halayyar tata,sam bata da wani salon nunawa me gida buqata data wuce wannan
"Banajin dadi yau,nasha magani ina buqatar na huta" wani abune yazo yayi mata tsaye a wuya. Ji take zuciyarta kamar zata fashe
"Eh,ai dama na fuskanci take takenka,to ko baka da lafiya nidai haqqina nake da buqata" waiwayawa yayi kadan ya dubeta da kyau
"Kizo ki qwata idan kina iyawa" ya fadi cikin matuqar maqurar jin haushi. Mutum kamar dabba,ace ko da yaushe shi kam baisan dai dai da ba dai dai ba,yana takaicin yadda sam zainab bata gane lafiyarsa da lalurarsa indai ba kwanciya yayi magashiyyan ba,koda yaushe tata buqatar ce s gaban tasa.
Bai gama wannan tunanin ba sautin kukanta ya karade masa kunnuwa,cikin muryar kuka take cewa
"Ai dama na sani,koda baka fadi haka ba komai ya fito a aikace,ni nasan dama da gayya ka yiwa ruqayya ciki ni baka yimin ba,to nima ciki nake da buqata haihuwa nakeso,banda ma rashin adalci ni da nake gyaran nan aini yafi cancanta ace kafi maqalewa,ni ya dace ace ina da ciki,amna saboda anqi Allah anqi ma'aiki sai gashi me ciwo daban me shan magani daban,Allah zai saka min" tana kaiwa qarshe tana sauka daga gadon.
Wani dadi yaji yana ratsashi bayan tayi zuciya ta fita a dakin,ko banza zai samu yayi bacci cikin salama,don haka ya sauko a nutse ya murza key ya rufe dakin ya dawo gadonsa yayi kwanciyarsa,idanunsa a rufe amma cikin zuciyarsa yana wassafa irin kulawar da zai samu inda ace kwanan ruqayya ne.
*******A harzuqe ta tashi washegari,don ko dakin bata leqa ba bare ta gaidashi. Abunda ya sake dugunzumata kayan da tayi order tace tanaso da sunan kayan sallan yara da nata sun iso,saidai kuma babu kudin da zata biya ta karba don duk sun tafi. Ita daya ta dinga qullawa tana kwancewa,tasan tabbas dole kafin saleem din ya wuce umra zai nema ganin kayan kowa,ita kuwa abun kunya ne ruqayya ta fiddo nasu ita ace ba abinda ta da nata sunbi ruwa.
Sai wajejen sha biyun rana ta shiga a tsaitsaye ta gaidashi,ta samu ya fito a wanka ma yana shiryawa,gefe guda kwanukan abincin data aika haneefa takai masa ne na safe,da alama ko tabasu baiyi ba bare yaci abinda yake ciki. Zuwa azahar ya fito da shirin fita ya ajjiye mata kudin cefane ya wuce.
Qaramin tsaki taja sanda yake ficewa,ta dauki kudin tana juyasu sannan ta ajjiye. Daidai sannan kira ya shigo wayarta.
Kiran raliya ne,abinda ya sanyata nutsuwa kenan ta kuma amsa kiran ba bata lokaci.
Qasa qasa takejin muryar raliyar,don sallamarta ma kaman a jigace take
"Me ya sameki ne raliya?,bana jinki sosai"
"Hala bakisha magungunan gurin basira ba?" Raliyan ta tambayeta tana numfarfashi
"Niko nasha don jiya ma kwanan asibiti nayi maimakon kwanan turaka"
"Madalla,mun samu qarin shaida,ashe matar nan bugaggiyar macuciya ce?,kin ganmu yanzu haka gidanta muka nufa, billahillazi saita fito mana da kudadenmu,ashe ita ke hada abinta a gida da duk abinda taga dama"
"Kan uba,lallai biri yayi kama da mutum,jiya da qyar na qwaci kaina raliya....."
"Ai ba'a bori da sanyin jiki,ki fito kawai mu hadu mu wuce gidanta,saita fito mana da kudinmu"
"Yanzu kuwa,mu zata gwadawa shegantaka?" Ta fada tana katse wayar. Tsam ta miqe,ta danyi tunanin wacce qarya zata yiwa saleem ya aminta da fitarta?,don tasan ko giyar wake tasha bata isa ta cewa saleem wai kudi maganin kayan matanta zata amso ba.
Lokaci ta duba,wata zuciyar ta gaya mata har taje ta dawo ba lallai saleem ya dawo ba,tunda idan ya fita bai dawowa sai magarib,ita kuwa me zata zauna ma tayi har magariba. Idan tayi wuta takai yamma,don ruwa ruwa zata zubawa basira rashin mutunci ta bata kudinta ta wuce,ta samu ta sissiya wasu kayan da zata nunawa saleem.
"Umma ina zaki?" Haneefa da tayi tsaye a gabanta ta zuba mata ido tana kallonta sanda take gyara zaman hijabin wuyanta ta fada
"Ku zauna keda.khalil,ko farfajiyar gidannan bance ku fita ba,yanzu zanje na dawo" tura baki gaba yarinyar ta fara yi tana qunquni har uwar ta fice daga gidan.
Bata ma iya isa gidan raliya ba ta tsaya daga titi yayi mata waya,ba jimawa sai ga raliyan tana tafiya iska na kadata,ta zabge lokaci daya da alama taji jiki itama yadda ya kamata.
Ba wanda ya iya magana a cikinsu don kowa idonsa ya gane masa,sai me napep kawai da raliya ta tsare musu, raliyan ce ta bashi kwatance sannan suka hau tana daukan wayarta tayi kira ta kara a kunne
"Rabi gamu nan akan hanya.....uhummm" ta fada tana yanke kiran.